← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 112

Sashe 69

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda kowa ke malelekuwa a gado yasa Nawaz ta tashi ta shiga kitchen domin tasan Aseey ba tashi zatayi ta dafa abinci ba, kuma ai da kunya ace gasu amma a bari har sai su Mummy sun shiga kitchen sun dafa abinci.

Tana cikin gyara kayan miya taji kamar motsin mutum a bayanta, ai kuwa tana juyawa sukayi ido huɗu da Aayaan.

Wata ƙayatacciyar dariya yayi mai kama da murmushi sannan ya nufi inda Nawaz ɗin take tsaye, kama kwankwasonta yayi ya haɗa da nashi Sannan yasa ɗaya hannun yana ɗago da fuskarta sama don su kalli juna dakyau "wa na kama? Wato Ni kike gudun mawa ko? Har waya kika kashe saboda kada na kira ki Koh? "To yanzu wa na kama?"
Duk yadda Nawaz ɗin ta fara sabawa da Aayaan amma hakan be hana zuciyarta bugawa sosai ba, ga jikinta sai amsawa yakeyi, bata iya buɗe baki tace mishi komai ba illa ma Idonta data rufe.

Tsintar bakinshi tayi cikin nata, saida yayi mata kiss kamar na Three minute Sannan ya cire bakinshi tare da Cewa "morning kiss"

Ita dai Nawaz har yanzu batace uffan ba Domin ta gama saduda da cewa shi ɗin mijinta ne kuma akwai manya manyan haƙƙoƙinshi akanta.

"Look! Kiyi min magana mana! Nifa nafison Nawaz mara kunya ba Nawaz me shiru shiru ba, nafison me murguɗa min baki da mai hararata ba wadda zatayi shiru tana kallona ba.

Ko yanzun ma dai batace komai ba, sakinta yayi yana murmushi Sannan ya nufi mugsrack don ɗauko mug ya haɗa tea, ai kuwa da gudu ta arta tare da cewa, "ai Wannan Nawaz ɗin ta wuce mai murguda baki me Mari da mazurai ce, inta kama ma harda duka"

Waigowa Aayaan yayi baki buɗe yana mamakin wai Nawaz dince da gaske "eh Lallai! Wallahi zamu haɗu ne sai kin min bayani dalla-dalla.

Harara taketa balla mishi harta shige ɗaki, shidai Aayaan dalau yayi yana mamakin wai Nawaz dince haka? "Lallai ne yarinya! zan kamaki a hannu?

Girkin da Nawaz batayiba kenan, sai karyar ciwonkai da tayiwa Aseey.

Kwanansu biyu da komawa gidansu Aayaan, zuwa lokacin kowa ya huce gajiya.
Aayaann Mummy ta kira tasashi yayi musu passport da visa don tafiya sudan, ita kuma mummyn SARFRAZ da daddy sukayi haramar komawa zaria saboda su fara haramar shirye shiryen biki.
Shikam SARFRAZ cewa yayi zai zauna shida Aayaan anan Maidugurin, idan Aayaan ɗin ya gama abinda yake yi zasu koma Zaria ɗin tare, haka shima Bandi yace yaga gurin zama tunda dama shine aminin SARFRAZ ɗin Ayanzu.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Sun sauka lafiya, inda suka sauka a gidan iyayen riƙon Mummy, sosai sukaji daɗi, rasa inda zasu sasu sukayi tsabar murna.
Har wata kula ta musamman akeba Nawaz jin ance ita ɗin matar Aayaan ce.
Kwanansu biyu anan mummy ta kaisu gidan aunty khatoume, sosai tayi mata bayanin yadda takeso gyaran jikin nasu ya kasance.
Inda takeso ayiwa hassu na cicciko da jiki da gyaran fata, ita dama Nawaz bai wuce na gyaran fata da Ni'ima.
Madam Aseey kuma me gaba ɗaya ne, gyaran jiki da Ni'ima da matsi.

Sosai khatoume ta bada himma don gyara su, inda a ranar farko tunda asuba ta tashi ta cika wasu manyan bawuna guda uku da ruwan turare tare da zuba musu wani haɗi na musamman.

Saida yakai minti goma da haɗawa lokacin ya rage zafi Sannan tace kowa ya shiga cikin bawo ɗaya ya zauna, Kasancewar bawon Babba ne sosai sai ya zamana duka jikinsu na ciki illah kansu ne kaɗai a waje.

Sunfi minti talatin da shiga ciki amma babu alamun Aunty khatoume zatace su fito, hatta Aseey dake ɗokin gyaran saida ta fara gajiya.
Saida aƙalla sukayi awa ɗaya da shiga Sannan tace su fito.
Nanma ɗaurin kirji tasa sukayi Sannan ta dauko wani abu kamar tunkuza ta fara murza musu ajiki, duk inda ta murza sai yayi wani irin taushi da santsi da haske kamar Fatar jariri dayake fatar ta riga ta jiku a ruwan da suka shiga.

Duk wunin ranar a wahale suka yishi, sai yamma liss Sannan suka samu damar hutawa, nanma dai magunguna ne iri iri take kawo musu a kofi tace su shanye su bata kofin.

A kwana biyu sunyi kamar basuba, hassu kam har ƙirji ya fara Cikowa kamar na cikakkiyar budurwa.

Aseey ce ta lura Kamar idan aka kawo magani Nawaz batasha, bayi take shiga ta juye.

Zuwa tayi ta samu Aunty khatoume tayi mata bayanin Abinda Nawaz ɗin keyi "Amma Aseey ba mummy tace matar Aayaan bace?" Cewar Aunty khatoume tana kallon Aseey.
"Eh matar shice amma basu tareba"

"No wonder! Nasan tsoron gamonsu takeyi shiyasa bata sha, amma kibarni da ita zanyi mata dabara.
Sosai Aseey taji daɗi domin tasan Aunty khatoume akwai aiki da cikawa.

Sai washegari Nawaz na zaune bayan ta idar da sallah, su hassu da Aseey suna Babban falourn Aunty khatoume suna kallo.

Sallama Aunty khatoume tayi ta zauna a gefen Nawaz "ƴata kina Lafiya?
Murmushi Nawaz tayi tace lafiya lau Aunty kaina ne kawai yakemin ciwo"

"Ayyah sannu kinji"

"Yauwa Aunty Nagode" Nawaz tace tana daɗa yin murmushi.

"In bazaki damuba inaso muyi wata magana dake, amma kafin nan inaso ki kalleni a matsayin uwa ko yaya.

Murmushi Nawaz tayi tace "babu komai aunty inaji"
"Kuntaɓa samun kusancin juna keda mijinki?"
Tambayar tazo ma Nawaz a bazata amma saita tuna maganarsu ta farko, kirgiza kai Nawaz tayi alamun a'a.

"Yauwa to, Nagode da bakiyimin karya ba, dama ina so na taimaka miki ne, akwai maganin dazan baki hardai kika juri shanshi to In'sha Allah koda anzo wajen kwanciya bazakisha wahala ba domin zaisa jikinki ya buɗe ne.

Ɗan murmushi Nawaz tayi "Aunty da gaske?

Murmushin manya khatoume tayi ganin ta samu amsar zargin datakeyi cikin sauƙi.

Dafa kafaɗar Nawaz tayi "dagaske ƴata amma ina so kada ki faɗawa kowa munyi wannan Maganar dake.

"To aunty amma don Allah itama hassu abata wallahi tausayinta nakeji gashi SARFRAZ ba wani hakanli bane ya isheshi.

To daughter kada ki damu itama zan riƙa bata, amma burina ki riƙe mana sirri koda wasa kada ki faɗawa kowa.

"To Aunty bazan faɗawa kowaba, nayi alkawari... Nawaz tace Tare Da jin wani daɗi a cikin zuciyarta..

Ita kuma khatoume ta tashi ta Wuce daki.

Tundaga ranar idan aka Kawo magani saita riga kowa shanyewa, wani zubin har kakkaɓe kofin takeyi.

(Nidai Nace Nawaz babu girma saina shekaru, kedai babu wuya ayi miki wayau)

Yanzu zamuji ya haduwar hassu da Sarfraz zata kaya, da kuma Oga Aayaan da madam Nawaz.

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*61*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

_*Sister SAFIYYAH HASSAN (UMMEE) Tsakanin keda A.M INUWA Bansan wayafi ƙaunar Sarfraz ba! Saboda haka bansan wa zan ba kyautar wannan page ɗin ba acikin ku biyun, kawai kuyi hakuri ku raba 50 50 😎*_

Aseey kam duk abinda Nawaz ɗin take yi tana sane da ita, sai dai tayita dariya a fakaice tana ganin wautar Nawaz ɗin a fili, wato so takeyi jikinta ya buɗe shiyasa taketa faman bankar magani, Batasan akasin haka bane zai faru.

A maimakon gyaran sati ɗaya sai mummy tace kawai ayi musu na kwana goma, kenan an ƙara kwana uku akai.
Sosai suka chanza kamar basuba musamman hassu da ada take Ƴar mitsitsiya, ita kanta Nawaz haka zata zauna tayita kallon kanta a mudubi, fatarta har wani milk milk takeyi ga wani taushi da santsi da tayi, kuma kullum cikin kamshi take koda bata shafa turare ba, abin har mamaki yake bata, wai itace ta zama haka.
Ta ɓangaren hassu kuwa jiki ya gama buɗewa sosai domin ta zama wata uwar mata duk wani shape ɗin dazai nuna ita macece ya fito fili, kayan ma da akazo mata dasu tuni sunyi mata kaɗan.

Ko sau ɗaya Aayaan be taɓa kiran kowaba, wai shi ala dole yayi fushi musamman da suka ƙara kwana ukun nan, itama mummy ganin be kiraba tasan me yake nufi shiyasa itama bata kirashiba ta shareshi kamar yadda ya sharesu tasan ya kusa shigowa hannu.

Manya manyan kwalaye guda uku Aunty khatoume ta shirya musu kayayyakin su aciki, waɗanda suka kama dasu turaren wuta, humrah, dabulun Dilke, coleccher, zuma, Tsumi, garin magunguna, turaren tsuguno dadai sauransu.
Sosai Mummy tayi mata godia ganin yadda yaran nata suka koma gwanin ban sha'awa, har kuɗi Mummyn ta ƙara mata akan wanda ta buƙata domin nuna jin daɗin ta.

Komawa gidan su iyayen riƙon mummy sukayi gaba dayansu suka kwana ɗaya domin su gama shirye shiryen su.

Sosai iyayen mummyn suke nuna farinciki, Saida suka tsaida cewa zasuzo Nigeria bayan su mummy sun koma da Wata uku, bayan sun gama haɗa komai ne Sannan sukayi haramar komawa gida Nigeria.

Babu wanda Mummy ta faɗawa zasu dawo saidai saukar su aka gani kamar daga sama, saboda da suka sauka a Airport ɗin kano bata kira driver ba kawai saita samu mota tayi shata zuwa Zaria.

Sosai Mummyn SARFRAZ taji daɗin dawowarsu domin an tsaida Ranar juma'a za'a ɗaura auren sarfraz da hassu Sannan a haɗa tarewar su data Nawaz da Aayaann, kuma mummyn Aayaan kashe watoyinta tayi sanda suka isa sudan ɗin, koda Mummyn SARFRAZ ɗin sau ɗaya suka taba yin waya.
Duk Mummyn SARFRAZ ɗin ta shiga damuwa kada suƙi dawowa gashi an raba iv card ko ina.

Shiyasa data gansu daɗi ya kamata kamar tayi mene don farinciki da murna, tsaye tayi tana kallon yadda su hassu suka koma, gani takeyi ma kamar ba hassun ba, sai Nawaz itama da gaba ɗaya ta chanza ta kara cikowa fiye da da.
Ita Aseey ma ba'a magana Domin ita abun biyu ya haɗe mata da gyaran jikin da salo da salasalar da taketa yi.

Godiya sosai mummyn sarfraz tayiwa Mummyn Aayaan Kamar zata ari baki, taji daɗin yadda taga hassu ɗin Takoma, domin dama kullum da tausayinta take kwana, tasan cewa idan SARFRAZ ya hake mata ba karamar wahala zatashaba tunda shi mabuƙaci ne, amma yanzu alamu sun nuna zata iya jurewa sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba kafin ta saba sosai.

Haikan ake shirye shiryen bikin saboda wasu daga cikin ƴan uwan Mummy da dadyn sarfraz har sun fara zuwa, saboda ya kama saura kwana huɗu biki.
Chapter 69 · 0% Book details