← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 112

Sashe 17

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai dai nan ABDUL ya shigo rikeda vacuum da warmer ya ajiye a gaban SARFRAZ "gashi bari na kawo maka mug da plate.

komawa Yayi, baifi three minutes ba ya dawo da plate da mug.....

hadawa SARFRAZ tea Yayi sannan ya zuba mishi doya da kwai Wanda yaji kayan miya Sai kamshi yakeyi....

a ka'idar SARFRAZ bayacin Abu mai nauyi da safe, iya kacin shi yasha tea da bread shima bai wuce yanka biyuba, ko kuma ya hada da kwai.

Amma jin kamshin doyar yasa yaji sha'awar yaci,

sosai yaci doyan, bayin ya shiga ya dauraye bakinshi ya wanke hannu.....

zama yayi a Saman gado suka fara hira shida ABDUL,
gyangyadi yaji Yana kamashi....

Abdul banacin abinci me nauyi da safe, gashi naci doyar nan tasamin nauyin jiki, yanzu haka barci nakeji....

dariya ABDUL Yayi "to kawai ka d'an kwanta kad'an Kona minti talatin ne koh,

cewa Yayi to, 'Dan bani duvet, kasan Bana iya barci Idan ban rufe jikinaba....

nan SARFRAZ ya kwanta ya Fara barcinshi hani'an sam yama manta da Aiken mummy...

*THREE HOURS LATER* *that's 10:45am*

SARFRAZ nagani kwance yanata faman barci Kamar Wanda yake a gida.....
Shi kuwa ABDUL mamanshi ta aikeshi ya tafi....

*gidansu SARFRAZ*

Mummy nagani tanata safa da marwa a falour ita kuma Nawaz tana zaune akan sofa tayi Tagumi,

mum ce tace "wai meke faruwane ace mutum yafita daga gida tun karfe takwas batayiba ace yanzu karfe shadaya bai dawoba kuma nakira wayarshi ba'a dagawa.

Nawaz tace "Allah dai yasa Yana Lapia ba wani abu bane ya faru,
ameen" cewar mummy.....

wayar mummy ce tahau kara,

*@matarrrasheed**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 20*

*✍🏻written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji "OUM AEYMAN"*

*Supreme writers association, we write with the ink of era, that's era is our ink*

Wayar mummy ce tahau kara, daukar wayar tayi a kidime domin number dad ce a gaban wayar .....
A kunne tasa ko
sallama ta kasa yi....
Dad ne yace ASSALAMU ALAYKUM madam!

Jikin mum ne yahau rawa tama kasa magana....
Nawaz ce tayi karfin halin Amsar wayar, "Assalamu alaykum dady mum tana bayi ne amma idan ta fito zan fad'a mata.....

A'a Ashe daughter ce" to shikenan dama cewa nayi bari na Kira naji ko kun tafi?

"A'a dad bamu tafiba, amma yanzu Insha Allah zamu tafi,"

OK to kudaiyi sauri domin garin akwai Nisa,,

To daddy insha Allah, kashe wayar tayi tana kallon mumy wacce harta Fara zufa....

" Nawaz gaskiya kin taimakeni dabadon kin amshi wayarba to nidai bansan me zancewa abban nakuba"

Nawaz tace "hmm mummy nima karfin hali Nayi, kuma ya kamata mu tashi mubi Sahu domin bamusan abinda ya faruba, domin ni nafara tsorata, yakamata ace ko ina yaje, Yadawo yanzu

"hakane daughter, Amma kuma Bayan Haka Idan Mun fita ina zamubi?
Kodayake bari nakira hajiyar naji yaje ya amso miki kayan danace, kinga idan yaje da sauki, idan kuma baijeba kinga akwai Matsala kenan.....

number hajiya tayi dialing, Amma abin haushi wayar a kashe....
Number SARFRAZ ta kara Kira namma a kashe, wayar ta wurga Saman sofa sannan ta dafa kanta " oni karimatu nabanu yau, a Ina zan saka rainane, ya Allah ka nunamin yaron nan Don darajar annabi .......

Itama Nawaz duk tayi sukuku, tana tuna rashin lapiar dayayi, "aranta take cewa ko yana cikin tukin ne ciwon cikin nashi ya tashi Allahu a'alam........

*SARFRAZ*
Juyawa yayi da nufin Gyara kwanciya, idonshi ya hango mishi wani irin labule....
Bud'e idon yayi sosai domin yanaso ya gane a Ina yake?

Da sauri ya tashi zaune domin ya tuna duka abinda ya faru,

Tunani ya Fara ya to ina ABDUL d'in, karfe nawa yanzu? Kuma nasan su mum suna gida suna ta faman jirana.....

Wayan shi ya gani a Gefen shi, da sauri ya dauka, abin mamaki saiya ganta a kashe alhali shi a kunne ya barta.....

Da sauri ya dauka Don ya kosa yaga ko karfe nawa!
12missed calls yagani kuma duka number mummy, time ya kalla 11:21am

cewa Yayi haba dai daga d'an kwantawa, Inaga dai ba dai dai yake tafiyaba,
d'ago da kanshi dazai Yayi tozali da agogon dake Ma'kale a bangon d'akin, shima dai sammakal 11:22am
Da sauri ya dira daga katifar, "yau na shiga uku, mezancewa mummy kenan gashi tanata kirana.....

wata dabara ce ta fado mishi, dialling d'in number mummy yayi....

ko kara d'aya bata gama yiba mum ta d'aga "hello SARFRAZ Allah yasa dai Lapia?
Murya kasa kasa SARFRAZ yace mummy yau Allah ya taimakeni "kinsan yanzu na bar banki saboda tsabar layi kuma saida aka kusa zuwa kaina kudin ya kare, saida muka jira aka kawo wani....

Wata sassanyan ajiyar zuciya mummy tayi "to Alhamdulillah yanzu Maza ka tafi kasuwar ka siyo kayayyaykin tsarabar.

Ni kuma yanzu zan fita naje gidan hajiya Bilki in amsowa nawaz nata, kaga ka huta kada abin yayi maka yawa......

Cewa sukayi to, sannan ya kashe wayar Yana hamdala a bisa saukin shawo kan mummy dayayi ....

hulanshi ya dauka yasa sannan ya karasa mirror ya Duba fuskarshi,
Takalminshi ya dauka yasa sannan ya duba mukullin motar ya dauka, bud'e kofar Yayi ya fita sannan ya maida ya rufemai

Harya shiga mota baiga kowaba, hakanan da sauri ya nufi super market, a hanya yanata tunanin wacce zashi wadda sukeda POS basai ya tsaya banki ya ciro kudiba,
SABODA yasan akwai layi tunda anyi salary...

sahad ya wuce, nan ya ciro list d'in da mummy ta bashi, Haka ya Fara yawo Yana za'ba, sai faman kwaso kaya yake yana jibgawa a shopping chart, wasu masu siyayyar har tsayawa suke suna Kallonshi....

shikuwa SARFRAZ damuwace ta kamashi domin wani irin mugun barci yakeji Wanda baisan dalilinshiba ......

Dakyar ya gama siyayyar, master card d'in ya mika musu su ciri kudin, domin ko magana baya sonyi,
receipt suka mika mishi had'e da master card d'in, Amsa yayi ya shiga mota ya bud'e seat d'in baya domin kayan sunfi karfin boot......

Dakyar yake tukin domin jinshi yake Kamar Bai ta'ba barciba a duniya,
Haka yayita tukin ganganci harda masu zaginshi, .

tsarewar Allah ne kawai ya kaishi gida, yana bude motar ya fita baima tsaya ya rufeba Yayi parlour, Nawaz idonshi ya ganin mishi zaune a kasan carpet......

da sauri ta Mike "SARFRAZ ka dawo?

eh kawai ya iya ce mata, nan ya zube a gefenta "kaina yana mini ciwo " yana gama fad'an Haka Sai barci kuma da alama mai nauyi ne.....

zama tayi dirshan tana mamakin meyasamu SARFRAZ da safennan.......

bata kaiga ba kanta amsaba sai ganin mummy tayi a gabanta, ledojin hannunta ta ajiye a gefe, "nawaz naga kin tasa SARFRAZ a gaba ne, meya faru?

Nawaz tace mummy babu komai, Yadai shigo a gajiyene shine yace kanshi Yana ciwo sannan ya kwanta anan,

Daria mum tayi, nawaz kenan, kinsan SARFRAZ bayason hayaniya, Inaga layin bankin dayabine da kuma siyayyar da Yayi su suka haddasamai ciwon kan, yanzu ki barshi zuwa mu gama shirya komai Insha Allah ciwon kan zai sakeshi,

tashi mujé mu had'a kayan, Mikewa Nawaz tayi "to mummy......

driver tasa ya shigo da kayan cikin motar, sannan ta shiga bedroom dinta ta kwaso leather boxes guda uku......
Kaya tayita faman zubawa a ciki, saida ta cika guda biyu sannan ta tashi ta shiga d'akin SARFRAZ ta dauka wani akwatin shima anan Ta cikashi da kayan SARFRAZ..... .

Dayan shima ta cikashi da ragowar atampopi da sabulun.....

Itadai Nawaz sai abinda mumy tace tayi takeyi.....

Sai around 12:33pm suka gama had'a komai Amma har lokacin SARFRAZ bai tashiba..

nawaz kuwa tuni tayi wanka ta shirya,
mum ce ta tasheshi SARFRAZ SARFRAZ katashi mana waiko barcin mutuwa kakeyine?

dakyar ya bude idonshi, ya tashi yanajin idon yayi mishi nauyi, dakinshi ya nufa donyin wanka......

Yana shiga wayarshi ta fara kara,
Dubawa yayi yaga Ashe ABDUL ne.....

yana dagawa ya Fara masifa haba abdul menayi maka ne, saika tafi ka barni Ina barci maimakon ka tasheni sanda zaka fita.....

Maganganun da ABDUL yake fad'a mishine sukasa ya saki wayar a kasa bai shiryaba

"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un yake ta faman maimaitawa "nashiga uku, no wonder na zama Kamar mahaukaci sai barci nake babu fullstop ba coma.

kubiyoni donjin me ABDUL yacewa SARFRAZ

*MATAR RASHEED**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 21*

*✍🏻written by Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*

*supreme writers association (SWA)*

No wonder sai barci nakeyi babu fullstop ba coma..

Amma kuwa Fatima bata kyauta min ba wallahi.

Nawaz ce ta shigo "Assalamu alaykum mummy tace na Duba Wai koka gama shiryawa,

Cewa Yayi "malama kimini jaje don Allah....

Nawaz tayi murmushi "jaje name pah?

Fuskar tausayi SARFRAZ Yayi "Dana fita daga nan gidansu ABDUL na fara zuwa, anan ya kawomin tea da doya....

Ashe acikin ruwan tea d'in kanwarshi ta zuba kwayoyin sa barci guda biyar wai saboda yasha yayi barci saboda baya iyayin barci....

Mu Kuma bamu saniba nasha, gamu da tafiya a gabanmu....

Yanzu yaza ayi kenan.
Nawaz tace kada ka damu kai dai yi sauri ka shirya....

Mummy ce ta fara kwala mata Kira *Nawaz Nawaz,
Amsawa Nawaz tayi "Na'am mummy ganinan Yana wankane be fitoba...

Da sauri ta fita zuwa wajen mum,
Mum ta kalla tadanyi murmushi "mumy ba dazu driver yace zai tafi jigawaba, shine nace don Allah idan be tafiba mu tafi tare, kinga Sai ya rage mana hanya...

Banaso tukin yayiwa SARFRAZ yawa,.

Dad'i mummy taji ganin Nawaz ta nuna damuwarta akan SARFRAZ d'in.....
"to daughter kada ki damu bari nayi mishi magana,

Mum na fita naw6az tayi d'akin SARFRAZ Da gudu, cikin rashin Sa'a ta samu ya shiga wanka,,, fitowa tayi tana jin dad'i zataje taga ummin ta.

umma ce ta fado mata "oh koya jikin umma Oho, gaskiya ta maru domin SARFRAZ bai sassauta mataba....

dai dai nan mummy ta shigo tare da driver,
Akwati biyu ya dauka ya fita, Nawaz ta dauki d'aya zata bishi, nan mummy ta hanata

"haba naywaz kin manta Bakida Lapia ne, ki bari yanzu zai gama, idan sarfraz ya fitoma zai tayashi kinji.....

"to Nawaz tace sannan ta samu guri ta zauna.....

*GIDANSU NAWAZ*

umma nagani ta tasa fauziyya a gaba "wallahi fauziyya idan baki samomin bokan dazai sa nawaz tabi duniyaba wallahi zamu raba jaha.....
Chapter 17 · 0% Book details