← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 112

Sashe 23

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda gari ya waye haka bandi ya Daɗa haɗa magungunan yaba sarfraz, sannan ya tatso nonon ya kuma ɗura mai..

Ita dai hassu sai dai tayita kallonshi, yana burgeta dukda baya ko motsi, ga wani uban tausayinshi da takeji.

Tasan wahalar da baban kawarta yasha da duk wani iyalinshi lokacin da paralyze ya kamashi....
Shi yasa take jinjina ta yadda zasu kula da wannan bawan Allah.

Gashi iyayensu sun tafi gabas kiwo da neman magunguna, kuma basa dawowa Sai sun shekara wani zubin ma suna wuce shekara.
Kasancewar su dama tun usuli fulanin dajine waɗanda akasarin su basa zama a guri ɗaya....

Kuma mahaifinsu ya kasance likitan gargajiya.

Ita dama tun tasowarta bata wani saba da iyayenta ba sosai kasancewar basa zama, tafi sabawa da bandi saboda kullum suna Tare kuma yana kula da ita sosai domin duk abinda takeso shi yake yi mata, kuma sam bayason abinda zai tayar mata da hankali ko kaɗan ..

Kallonta ta maida kan bandi tace "bandi kana ganin zataji sauki har ta tashi?

"Hassu ka kwantar da hankalinka zataji sauki kuma zata tashi insha Allah..

Zanta kulawa da ita har sai su baba sun dawo sai yayi mata magani.

Koda lokacin tafiya kiwo yayi sai bandi yacewa hassu ta zauna ta kula da sarfraz, shi zaije saiya dawo...

Rakashi hanya tayi sannan ta dawo ta zuba wa Sarfraz ido tana aikin nata wato tunani....

Sai dai lokaci bayan lokaci tana zuwa duba shi...

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Ba'a daɗe ba taji iska na kaɗa tent ɗin da suke ciki ga wata kara mai ƙarfi.
Murmushi colonel yayi wa Aayaan "i guess sun iso"

"Yes sir insha Allah" Aayaan yace yana miƙewa, shima colonel mikewa yayi suka yi hanyar fita.
Ganin Nawaz batada niyyar binsu yasa colonel tsayawa "daughter taso muje mana"
Miƙewa tayi a sanyaye tabi bayansu, ile kuwa helicopter ne guda hudu duk fentin jikinsu kalar uniform ɗin sojoji, farfelar su nata juyawa kura na tashi.

Gani tayi colonel yayi gurin jirgin, shima Aayaan nan yabi, ai saita tsaya tana rarraba Idanuwa, ita gaskiya ko jirgin arziki bata taɓa hawa ba bare wannan wanda ko ƙofa bashi da ita...

Har sun shiga colonel ya waigo sai ganin Nawaz yayi can nesa a tsaye "Aayaan kalli daughter bata biyomuna ashe"
Ai cikin kwarewa Aayaan ya diro daga cikin jirgin da hanzari ya nufo inda take cikin taku ƙalilan ya iso gaban Nawaz kafin tayi wani yunkuri ya sunkuceta ya juya zuwa jirgin, Saida ya saka ta sannan shima ya shiga.

Tsaki Nawaz keta ja, azuciyar ta "nidai naga ta kaina daga wannan sai wancan, toni haka rayuwata zata ƙare ne, daga hannun wannan namijin sai hannun wancan, Allah gani gare ka...

Jin Muryar colonel tayi yana cewa"daughter kin manta nace Dake zamuje shine zaki tsaya a baya?

Firfito da idonta tayi waje " sir please I can't stay in here" wallahi tsoro nakeji

"Babu abinda zai sameki, ki kwantar da hankalinki, abinda yasa nakeso ki bimu shine don kiga yanda za'a firgita ƴan ta'addan Da suka firgita ki,

Tana tsakiya, colonel yana gefen dama Aayaan yana gefen hagu, shi dai duk hirar da akeyi yana jinsu iyakacinsa yayi murmushi, dama shi koba yanzu ba miskilancinshi yafi maganar shi yawa...

"Kamar ta zunduma ihu sanda jirgin zai tashi sama duk tabi ta daddafe seat din da driver yake kai kamar zata fincikoshi....

Idonta a rufe yake tanajin kamar zata faɗo kasa daga cikin jirgin, a cikin zuciyarta take ayyanawa "dama ace tun sanda ummina tayi tafiya duk abinda ke faruwa mafarkine ba gaskeba...
Amma ina tasan gaskiya ne babu yadda ta iya face ta amshi kaddara....

Dayake a cikin jirgi ne ƴan mintoci ƙadan taji ana cewa "mission x is detected"
Ita dai tadaiji maganar ne amma batasan ta inda take fitowa ba.

A hankali jirgin ya karkace gefen dama zaiyi corner ai ƙara Nawaz ta saki ta riƙunƙume Aayaan da karfi...

Be kalletaba be hantaba, shidai still Yana nan inda yake ko motsi beyiba ..
Yan mintoci ƙadan aka wuce gurin sai kuma a hankali a hankali jirgin yayi ƙasa..

Saida Nawaz taji kamar an tsaya sannan ta buɗe ido a hankali, ajiyar zuciya ta saki ganin da gaske an tsaya, sai sannan ta saki rigar Aayaan cikin jin kunya, beko kalleta ba ya gyara rigar shi ya dira daga jirgin .
Hannu ya miƙo mata alamun tazo ya sauketa babu musu ta mika mishi, kamar ƴar tsana haka ya direba a waje...

Duka jiragen ta gani sun sauka duk sojoji ne birjik kowa da shigar yaƙi..
Colonel wanda sai yanzu ya fito ya kalli Aayaan "Aayaan ka samata bullet proof vest saboda banaso a samu wata matsala...

Cikin dajin suka shiga suna sanɗa, basu ankara ba saikin karar bindiga sukayi a gabansu bullet ne ya fito yayi santar kan Nawaz ai cikin hanzari Aayaan yasa hannu yayi ƙasa da ita bullet ɗin ya chaki tafin hannunshi..

Ai babu shiri colonel ya Basu order harbi, tuni sukayi cikin dajin suna harbi ta ko ina, sai babbar bindigar dake hannun wani soja tun dazu yana kusa da colonel yana jiran order , yatsa kawai colonel ya hada take wannan sojan ya saki kunamar bindigar ,wani abune kamar bullet amma babba yayi cikin dajin da gudu ji kake bummmm ya fadi a kasa ..

Duka sojojin ne sukayo baya, ganin an saki fainting gas din, don ma suna sanye da hular sojoji da sai abin yayi affecting Dinsu.

Gaba ɗaya jikin Nawaz sai rawa yake yi yau itace aka saito da harsashi lallai Allah yana sonta dafa yanzu sayu buzun ta, shi ko Aayaan ko a jikinshi kamar bashi aka harba ba, bakinshi yasa a daidai inda bullet ɗin ya cakeshi yi
ya finciko bullet ɗin ya yar a gefe sannan ya yagi gefen rigar shi ya nannande gurin.

Sai sannu Nawaz takeyi mishi, ga uban tausayinshi daya kama ta, a dalilinta haka ta faru, colonel ne ya karasa inda suke "Aayaan you've really try, good job, i have an unexpected gift for u bayan mun koma barrack. Sannu hope is not that much painful?

Murmushi Aayaan yayi "sir u taught us how to ignore pain,

Murmushin shima colonel ɗin yayi "is that really working?

"Not really" cewar Aayaan Yana kallon Nawaz dake duƙe akan gwuiwotinta a gabansa...
"Tashi, don't worry I will be fine, just take care

Sai da aka ɗauki kusan minti goma sannan suka kutsa kai cikin dajin, mutanene kwance ta ko ina birjik babu wanda yake motsi

Da gudu Nawaz ta karasa kusa da mai cikin nan ta tsuguna tana taɓata, "shikenan yanzu duk kun kashesu, wallahi banda su iya waɗan can ne ƴan ta'addan, amma banda waɗannan.... Meyasa zaku kashe kowa? Ba cewa kukayi Zaku ceto suba.

"Ooooohhhhhh talkative, wai meyasa ke bakya iya ganin abu kiyi shiru ne? Aayaan yace cikin ƙosawa da maganganun ta.

Colonel ne yace "No Aayaan, meye amfanin kasan abu kuma kaƙi sanar da wani, ai kamata yayi kayi mata bayani yanda zata gane.

"Yes sir" cewar Aayaan yana Sara mishi, sannan ya kalli Nawaz "ba mutuwa suka yiba barci sukayi me kamar suma sai bayan awa ɗaya duka zasu farka.
Wani gas ake jefawa idan ya fashe to duk wanda ke gurin saiya suma amma banda wanda yasa mask, amfanin shi shine idan aka jefa za'a banbance yan ta'addan da innocent ɗin sai a kwashe su duka a kaisu asibiti su kuma yan ta'addan asa musu hand curve sannan a kwashe su duka a mikasu federal C I D.

Girgiza kai tayi alamun gamsuwa, sannan ta farabi tana nuna musu yan ta'addan ana sa musu hand curve sannan wasu sojojin suma suna ɗiban makaman su suna zubawa a cikin jirgi, wasu kuma sai ɗiban wadanda akayi kidnaping ɗin suke suna zubasu a wani jirgin daban, karasowa sukayi gurin iluu kallonshi tayi tai shiru sai tace Banda wannan shima satoshi akayi, basu Musa mataba kasancewar bai rufe fuskarshi da rawani ba, kuma babu bindiga a hannunshi.

Tsaff aka gama sawa yan ta'addan hand curve, sannan an gama kwashe mutanen da makaman,

Kunna jirgin sukayi don kai mutanen asibiti sai kuma ɗaya jirgin wanda aka zuba makamai shi kuma Abuja zai wuce...

Suma yan ta'addan aka loda a ɗaya jirgin don a wuce Abuja dasu suma,. Babu gurin dasu colonel zasu zauna sai suka zauna a gefe kafin jirgin da zaije general hospital ya dawo...

Kallon Aayaan Nawaz tayi "sannu, kanajin zafi koh? Kuma Ni naja maka, I'm sorry,

Dariya abin keba Aayaan yanda ta wani damu '' nace calm down babu zafi and I'm use to it, Sannan nake bace...

Colonel dai yana gefe yana kallonsu yana ayyana wani abu a zuciyarshi...

A hankali Nawaz tace yauwa "su sauran ba anan sukeba suna gaba,

"To ai waɗannan tuni na gama da babinsu tun kafin ki tashi daga barci, nasa anje an kwaso su su bakwai ne yan fashi ne, sai kuma yayi ƙasa da muryarshi
"Ashe kisa kikaso kiyi jiyan? Kuma inaso Nima a koyamin yanda ake sarrafa wuka....

Kunyace ta kama Nawaz ta mike tayi gaba da sauri.

Ba'a ɗauki lokaciba jirgin ya dawo ya kwashe su, asibiti ya fara kaisu Nawaz ta tarar duk waɗanda aka sace su tare sun farfaɗo wasu ana ƙara musu ruwa wasu an kawo musu abinci, anan aka faɗa mata mai cikin nan tana labour room.
Iluu ta hango, da sauri ta karasa kusa dashi "ilu ya jiki?
Godiya zai fara yi mata tayi kasa da murya tace kada ka gode min kaikayi sanadin da kowa ya kubuta, don Allah ka tuba kadena wannan abin kaji, kasan dai sauran basusan fuskarkaba to ka samu ka ƙoƙarta ta tafi gida kafin wani abun ya kuma faruwa...

Colonel ne ya kirata suzo su tafi an gama yiwa Aayaan dressing ɗin ciwon.

Nawaz ce tace "inaso naje gida!

" Zakije amma sai kin samu nutsuwa yanzu kibi Aayaan zai dauki information ɗinki sai a kira can gidanku a faɗa musu kina lafiya daga nan kuma sai a kaiki gida kafin governor ya nemeki don abaki award...

Taɓe baki tayi, irin su award manya ita award be dametaba sarfraz takeson gani,
Ai da sauri tace a ina aka kawo mutanen jiya wadanda ƴan ta'addan suka harba..
Chapter 23 · 0% Book details