← Book details Safraz Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 112

Sashe 62

Safraz Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta ƙarasa kusa da Aayaan tana dariya tare da cewa "yaya sannu da zuwa! Gaskiya naji daɗi daka dawo.
Dai dai nan sarfraz ya dawo riƙe da robar ruwa yana buɗewa sannan ya mikawa Aayaan.
Kurɓar ruwan Aayaan yayi Sannan yace "hafsy, hafsy Nima Naji daɗi dana sameku lafiya, ina bandi?
Dariya tayi me kyau sannan tace "inaga ko yana ɗaki nima Yanzu na fito.
Shikam SARFRAZ ya zuba mata ido yana kallonta sai kuma ya Maida kallonsa kan Aayaan yace "yaya wai dama hassu hafsat yake nufi?

"Au kai dama baka saniba? Cewar Aayaan yana kallon SARFRAZ da fuskar mamaki, Sannan ya ƙara cewa "ai sunayen da ake kiran me suna Hafsat dasu sunada yawa, kaga Akwai Hafsatul ikraam, akwai Hafsatu, akwai tatuwa, akwai hafsiyyah, akwai hansa'u, Akwai tatou hmmm sunada yawa ma.

Buɗe baki SARFRAZ yayi "sunanki dama me dadine shine aka wani bata miki da Wani hassu, to nidai daga yau ikraam zan riƙa ce Miki.

Dariya haidar yayi wanda fitowar shi kenan daga kitchen rike da tray ya cikoshi da snack's kala kala "to kai a matsayin ka na wa? Dazaka chanzawa ƴar Mutane suna?
Murtuke fuska SARFRAZ yayi don beso Idan yana maganar hassu a riƙa sa mishi baki.

Fitowar Bandi ce tasa kallonsu ya koma kanshi, domin tafe yake yana miƙa kuma yana hamma a tare, alamun yunwa ce ta tasoshi daga barcin.

Ai cikin ƴan sakwanni idonshi ya washe Dalilin Aayaan daya hango, babu shiri ya karasa kusa dashi Tare da tsuguna yana dafa ƙafar Aayaan "bari na dibi albarka, yaya Yanzu ka dawo?

Murmushi kowa yayi don abinda bandi yayi ya basu dariya, sosai aka samu guri aketa hira, itama Madam haidar ta fito aka haɗu akayi dinner tare gwanin ban sha'awa.

Sosai suke ta hira, anan haidar yake ba Aayaan labarin abubuwan da sarfraz ya rikayi, har zuwa sanda Yan sanda suka tafi dasu....

girgiza Kai Kawai Aayaan yakeyi cikin ta'ajibi "Lallai sarfraz, yanzu da kaketa tsulawa Mutane Rashin kunya da ɓarna a gonakin su da sun kaika kotu fa?

Charaf haidar yace "ai Wallahi Don Kawai suna ganin mutunci nane, amma nasan da badon niba Idan akwai abinda yafi lauya sai sun kira mutshi, nifa yanzu gaba ɗaya yabi ya zubar min da mutunci a cikin unguwar nan, duk masu ganina da mutunci saida ya tsokane su.

Shidai Aayaan murmushin kawai yakeyi don yasan yanzu sarfraz ya koma dai-dai, kuma idan gobe suka isa gida wani mafarin farincikine ga ahalinsu duka.

Madam haidar ce ta Kalli hassu tace "jita harda sanya hijabi yau, sai kace wata ustaziyar gaske, bayan duk Wata tsiya tare ake tsulata dake, naga wani zubin ko gyale Bakya rufe kanki dashi zaki bisu kuyita gararamba a titi.

Sunne kai hassu tayi a cikin hijabi wai ita taji kunya.

Kallon Aayaan madam haidar tayi tare da Cewa "wai kam kasan bayan ka tafi befi so Biyar suka zauna lesson ba? Saboda Tunda SARFRAZ ya warke komai ya tabarbare basa iyayin komai sai yawo da tsokane tsokanen fada gurin mutane..

Buɗe baki Aayaan yayi yana dariya, donshi abinma ya dena bashi mamaki "to shikenan idan muka koma gida zansa a nemi makaranta mekyau sai a maidasu.

Haka dai suka cigaba da hira, daga a dauko chan sai a dauko nan, Basu suka ankara ba sai wajen ƙarfe shabiyu na dare, duk mamaki ne ya kamasu saboda ko magariba babu wanda yayi a cikinsu.

Haka kowa ya tashi don yin sallar sannan su kwanta, anan ne sarfraz yace shifa a gurin Aayaan zai kwana. Murmushi Aayaan yayi yace "to muje mana meye na rikicin?

°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tafe su umma suke ita da fauziyya misalin ƙarfe biyar na asuba don komawa gidan boka, dayake tun wancan Lokacin taketa buga-bugar inda zata samu kuɗin don aƙarasa mata aikin amma kuɗi yaƙi samuwa, yanzu ma dubu chasa'in ne ta samo su da kyar, suma Saida ta haɗa da saida wasu abubuwan nata tukuna suka kai yawan hakan, alamu ma ya nuna ko sallar asbah basu tsaya sunyi ba. Duba da lokacin aketa kiraye kirayen assalatu a ƙauyukan dake gefen inda suke.

" Waiko fauziyya me kika cewa sale ne ya barki kika fito yanzu?

"Ai umma cemai nayi jiya na baro ki hajaran majaran bakida lafiya, shine yace nayi sauri nazo na duba ki Kasancewar babu kowa dazai kula dake a gidan

Daɗi umma taji, jin cewa sale da kanshi yace azo a duba ta, tasan ko banza anjima zataga saƙonshi.

Yauma Saida suka tafiyu kamar babu gobe sannan suka isa bukkar bokan, lokacin har garin ya fara haske.

Koda suka shiga cikin bukkar tarar dashi sukayi yanajan wani dogon charbi.
Gyara zama yayi yana murmushi ganin su umma Domin be taɓa zaton za su dawoba duba da Tsawon kwanakin da aka ɗauka batare da sun dawo ba.

Ciro kuɗin umma tayi tare da ajiyewa gabanshi, Sannan ta mishi bayanin cewa rashin samun kuɗin ne ya hanata dawowa, kuma ko yanzu ma bawai sun cika bane.

Dariya bokan yayi tare da cewa fauziyya ta fita waje ta jirasu, fauziyya na fita ya matso kusa da umma yana washe baki "aida tun tuni kin faɗa min bakida kuɗi da bakisha wahala ba, domin akwai aljanin dazai shiga jikina ya kwanta dake sai ya bada kuɗin.

Bata fuska umma tayi "kamar ya aljani ya kwanta dani? Inada aure fa!

"Da gani ke Ƴar ƙauye ce, Don kinada Aure shine me? Mata nawa ne nayiwa aiki irin wannan kuma duk da auren nasu suka yarda.

Shiru umma tayi tana tunanin Yadda zata yarda wannan baƙin ƙazamin ya kwanta da ita! Ta duba, ta duba amma taga bazata iya yarda ba.

Cewa tayi "boka abar wannan maganar kawai gaskiya bazan iya ba!
Kawai ka bari zan samo cikon.

Wata uwar tsawa da ya rafka mata Saida ta firgice "mu muke magana kike Kawo mana naki tsarin? To maza ki tashi ki bani guri kafin na illataki.

Daurewa umma tayi tace "to aikin nawa fa?

"Baza'a yiba, ki tashi ki tafi nace.
Daurewa umma ta daɗa yi ta kuma cewa "to kuɗin nawa fa, ka bani kuɗaɗen dana kawo maka.

Wata sanda ya ɗauka yayi wasu iface iface ya saita umma da sandar aikuwa sai wasu tartsatsin wuta suka fara fallatsi, ai babu shiri umma ta miƙe ta fita da gudu, amma ina Saida wutar nan ta ƙona mata gefen ƙafarta.

Fauziyya na ganin umma ta fito da gudu ta ƙarasa gunta da sauri tana cewa "umma ya akayi? An gama aikin?

Kuka umma ta fashe dashi tare daba fauziyya labarin abinda ya faru, gashi inda wutar ta fallatsar mata sai wani irin zugi yakeyi mata har cikin kwakwalwarta.

Da sauri fauziyya ta kama hannun umma suka ɗauki hanyar fitowa daga dajin dan abin tsoro yaba fauziya sosai, kafin su fita bakin hanya har ƙafar umma ta kumbura tayi sumtum da ruwa, bama ta iya ɗaga kafar sai dai janta takeyi.

Namma sun daɗe tsaye a bakin hanya kafin su samu abin hawar da zai maidasu gida.

Aikam suna isa gida umma ta samu gefen katifa ta kwanta tana jerawa boka tsinuwa.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Yauma dai zaune Nawaz take a saman gadonta tayi wanka tsaff abinta tayi kyau dukda ba wata kwalliya tayi a fuskar taba.
Idan ta cinka daidai yaune Aayaan yace mata zai dawo randa sukayi wayar ƙarshe dashi, dukda shi yana kiranta Saidai bata ɗagawa saboda gudun Kada ya bata kunya, duk da haka kullum saiya Turo mata da messages sama da guda biyar. Duk na jaddada mata irin ƙaunar da yake mata da kuma ƙara tuna mata cewa ta shirya domin yana dawowa zasu angonce.

Har wata fargaba takeji idan ta gama karanta messages ɗin, amma ko babu komai ya kamata ta sama mishi wani abin da idan ya dawo zata bashi a matsayin farincikin Dawowarsa, kuma aishi dayake yi mata ba wawa bane, kuma ance ka kyautata wa me kyautata maka.

Tashi tayi cikin sanyinta ta nufi hanyar fita daga ɗakin tare dayin addu'ar Allah yasa kada ta haɗu da mummy.

Cikin iKon Allah har ta shiga kitchen ɗin bata haɗu da kowa ba, duk abubuwan da tasan zatayi Amfani dasu ta Duba, Saida ta tabbatar ta haɗa komai tukuna ta fara aikinta a nutse.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tunda suka fara shiri SARFRAZ ke cewa ya ƙosa su isa kodon yaga Nawaz, daga karshema kallon Aayaan yayi yace "yaya wai Kasan wacece Nawaz agurina kuwa?

Girgiza kai Aayaan yayi yace "a'a brother bansaniba "

Murmushi sarfraz yayi Tare da Cewa"itafa zan aura, Domin wallahi ina matuƙar kaunarta, yadda Kasan in hadiyeta haka nakeji.

*DON ALLAH KUSANI A ADDU'A.*

*MATAR RASHEED ✍️**🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*56*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

Wani irin tsinkakken miyau Aayaan ya haɗiye jin abinda SARFRAZ yace "wato yaron nan dai Akwai yarinta a Tare dashi har yanzu, in banda ma yarinta yaza'ayi ya Kalli Nawaz yace zai aureta? And kenan akwai damuwa idan muka isa gida" Abinda Aayaann ya aiyana a ranshi kenan.

"Yaya Don Allah ina so idan munje ka roƙarmin Nawaz kace don Allah ta aureni! Cewar SARFRAZ Tare Da dafa kafaɗar Aayaan.

Kallonshi Aayaan yayi Sannan yace "wai suk da kake wannan maganar dama ita Nawaz ɗin bata sonka?
Shagwaɓe fuska SARFRAZ yayi Sannan Yace "wallahi yaya gani takeyi kamar Ni wawa ne, idan nace ina sonta har dariya take yimin wai ai ta girmeni, kuma don Allah yaya ba Mutum zai iya Auren Wadda ta girmeshiba?

Shifa Aayaan abin ya Fara bashi tsoro, ganin SARFRAZ ɗin da gaske yake.

Cewa yayi "eh mutum Zai iya Auren Wadda ta girmeshi, yin hakan ma sunnah ne, tunda Manzon ,Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya auri Sayyidatuna khadija kuma ta bashi shekara 15, amma Ni yanzu nafison ka auri wadda ke sonka da kanta ba wadda za'a matsa mata ba.

Shiru SARFRAZ yayi tare da cewa "yaya kasan iyayena? Nayi missing ɗinsu sosai dasu da Yan ajinmu na makaranta , Kawai dai don ina London ɗin nan ne shiyasa ban damu da'a maidani gida ba, But inaso na gansu!

Kada ka damu Zaka gansu in'sha Allah, kuma suma sunachan suna jimamin rashin ka, amma in'sha Allah yau komai zai zama tarihi.
Chapter 62 · 0% Book details