← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 109

Sashe 99

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da kowa ya watse sannan Radiya da Safina wacce ta zo gidan da zummar sai bayan biki, kuma babu inda ta yada zango sai
angaren Hajja, suka ha
u suka
ulle a
aki.

Hira suka shiga yi, Safina na labarta musu diramar da aka yi a daren jiya tsakanin Haj Hadiza, Fahima da kuma su Hajja.

"Wai fa Hajiya kuka sosai ta zo muna zaune ta shiga rerawa Hajja akan don Allah ta yafe mata.

Hajja ba ta ko kalle ta ba nake fadamaki, shi ne ta koma ga Umma.

Umma ce ta ce mata komai ya wuce.

Dakyar dai Hajja ta saurari Hajiya ta
are da yi mata nasiha.

Fahima ma har da neman gafara bayan Hajiya ta tirsasa ta.

Ni dai jikina na bani tuban muzuru Fahima ta yi, amma Hajiyarta dai na ga alamar dagaske take ko ma dai ba duka ta sauya ba, kuka fa sosai har da su majina.

Amma kuma ita ma kun san me?"
"Sai kin fa
a." Fadin Radiya da Haulatu har suna ha
a baki.

"Uhum, babanta ne zai ha
a Fahima aure da
an yayansa.

A karshe dai Hajiya ke ro
on Hajja akan ta taimaka ta yiwa su Baba Alhaji magana su saka baki kar a yiwa yarinyarta auren dole.

Hajja ta dinga yi mata fa
a akan ita babu abin da za ta ce, gwara ma a yi hakan ko Fahima za ta nutsu.

A karshe Umma ce ta kashe wutar ta lalla
a Hajja, dakyar dai ta ce a hakura zuwa bayan bikin Haulatu sai a yi maganar.

Hajiya na ta
orafin wai yaron na shaye shaye, amma baban ya dage sai an yi, idan ya so tunda ita mace ce za ta iya juya shi ta maido shi hanyar tsira, ku ji fa?"
Girgiza kai Haulatu ta yi cike da takaici.

"Abin nan yana ci min tuwo a
warya, sai ki ga namiji na tata duniyanci amma a dage mace wai sai ta aure shi a haka, amma da ace ita macen ke yin wadannan miyagun ayyukan da ta zama abar zagi da
yamata.

Har ga Allah na tausayamata, ina addu'ar kar Allah ya tabbatar da wannan abin."
"Amin Haulatu, ni kaina ta ban tausayi, ba ku ga ma yanda ta dinga kuka ba daga baya, ba ta ji labarin ha
in auren ba sai da Hajiya ke fa
awa su Hajja.

Ita dai Hajiya haka ta yiwa su Hajjar sallama ta tafi wai dama ta zo kawo Fahima ne don ba za ta yarda a yi mata aure da mashayi ba."
Murmushin takaici Haulatu ta yi, duniya kenan.

Yau kuma Fahima ce ake son aurawa mashayi.

Dole Hajiyarta ta fita hayyacinta.

"Allah ya magance mata." Abin da kawai ta ce kenan suka amsa da amin kafin su shiga hirarrakinsu.

Daurewa kawai ta ke yi tana biye musu, ko kusa ba ta ba su labarin rikicin da suke ciki ba, hakanan ta ji tana son
oye sirrinta da Yayan nata.

Zaituna ma don dai ta riga ta
ago ta ne amma da ba abin da za ta ce.

Washegari misalin
arfe biyu da mintoci na rana, ana zaune ana hira a falon Hajja, Zaituna ta fito ciki shirinta na zuwa gyaran gashi.

Don tace kitso take son yi da biki, wanken kan za ta a ranar.

Mamanta ba su iso ba sai dare.

"To ke kadai babu
an rakiya?" Fa
in Umma kenan, Haulatu ta yi caraf ta mi
e zaune daga kishingi
ar da ta yi.

"Umma ko na raka ta?"
"Ina?" Fadin Hajja da Umma lokaci guda.

Jin yadda suka ha
e baki kamar ta fa
i wani abin gudun sai suka ma ba ta dariya, Hajjah ta ce.

"Kin ga ki yi shiru da bakinki, so ki ke yau Zakiyya ta mana dirar mikiya.

Koda dai, Sadaukin Alhaji uban
an kishi sai ya wanke ni ba shiri.

Babu inda za ki je."
"Toh Hajja ita ka
ai za ta tafi?

Ga Safina na makaranta.

Sis ki saka baki please." Ta
arashe tana narke fuska kamar ta yi kuka.

Murmushi Zaituna ta yi.

"Aa fa, babu ruwana.

Dama ya lafiyar kura?

Bari na tafi kawai, zan le
a can wurin Momi Nuratu sai na ja Zuhra ta min rakiya."
"Shikenan kuwa.

Hakan ma ya fi.

Sai kun dawo." Hajja ta amsa.

Babu wanda ya yi maganar Fahima sakamakon matsalarta da ake kokarin magancewa don Baba Alhaji ya yi waya da mahaifinta ya nemi alfarma akan ya zo yana son ganinsa.

Ta juya tana
agawa Haulatun yatsunta uku tana mata dariyar mugunta.

Haulatu ta kauda kai kawai gami da komawa ta kwanta.

Ta sani yau Sadaukinta zai dawo, tun safe take baza idanu da kunnuwa ko za ta ji labarin ya shigo Katsina daga Kano amma shiru.

Hankalinta gaba daya yana kansa ta kasa sukuni duk kuwa da ba maganar ke ha
a su ba.

Zaituna na fitowa ba ta wani yi nisa ba, tana takunta cike da nutsuwa cikin shigar doguwar rigar abaya maroon da ya kar
i fatarta sosai, ranar a yau ta bu
e ba ka
an ba, don haka sai ta ke tafiyar a hankali.
agowar da za ta yi ta hangi Khaleefa na takowa ya fito daga
angaren Baba Dakta, sanye cikin shadda sky blue sai ko hula a kansa.

Ya yi tsaf abinsa cikin shigar juma'a.

Bisa al'adarsa duk rana ta juma'a ba ya komawa gida sai ya shigo gaida iyayensa.

A hankali ta sauke idanunta daga gareshi ganin bai bar kallonta ba.

"Barka da juma'a Abu Affan, fatan an yini lafiya?"
Ya sauke ajiyar zuciya, tun sadda ta zo garin ba su
ara ha
uwa ba sai yau.

Zai iya cewa kwanakin nan tana ransa, ya kuma kasa cire tunaninta a kwakwalwarsa, Hafsat ba ta ko sakaya sunansa, kai tsaye Khaleefa ta ke ce mishi amma ba ta ambaton sunansa na yanka.

Sai dai yana son girmamawa, bai dai ta
a hana ta fa
in abin da ta yi niyya ba.

"Lafiya.

Ya su Hajja?"
Da murmushin jin dadin ya amsa mata ta kara kallonsa ta ce.

"Lafiyarsu kalau."
Ga mamakinta murmushi ya yi mata, baki ta saki tana kallonsa.

Za ta iya rantsuwa bai ta
a yi mata murmushi ba sai dai ta hango yana yi ga wasu.

"Masha Allah.

Fita za ki yi?"
Tambayar ta
ara lula ta cikin duniyar farin ciki, ita kadai ta san meke cin zuciyarta kwanakin nan sai dai ba ta son maimaita tarihi dalili kenan da yasa ta ke kwa
ar kanta tana kuma
aryata kanta da gangan.

"Eh, zan je saloon.

Zuhra zan kira ta yi min rakiya."
Ya soma tafiya yana amsa mata.

"Ok.

Allah ya tsare.

A dawo lafiya."
Daga haka ya wuce ta zuwa sashen Hajja, ita kuwa ta amsa da amin da godiya tana mai binsa da kallo har ya gifta ta, kowannensu ya sha
amshin turaren
an uwansa, Zaituna ta sauke ajiyar zuciya ta
an waiga ta dube shi sannan ta juya ta cigaba da tafiya har a lokacin ba ta bar murmusawa ba ga kuma gefe guda da mamaki ya cika ta.

Wai Yaya Khaleefa ke mata murmushi?

Misalin
arfe bakwai na yammaci, Sadauki ya shigo garin Katsina.

Mu'az wanda ya je
auko shi, shi ke tu
i yayinda shi kuma ke bin garin da kallo yana ji a ransa babu abin da ya fi kewa a ciki kamar Haulatu.
an kwanakin da ya yi a
asar waje, ya samu ya yi haske sai
an rama ka
an wanda rashin ji da ganin masoyiyar tasa suka haifar.

Babu wani abu da ya yi mishi dadi a tafiyar idan ka cire hotunanta da yake kallo ya ke jin
an sanyi a ruhinsa.

Ya yanke zai je har gidan Maama, idan ta kama zai kai gwuiwoyinsa
asa akan kawai ta bar shi ya yi tozali da Haulatu, ta bar shi ya ji koda muryarta ne har ta yi mishi murmushin nan mai wanke zuciyarsa.

"Gidan Maama za ka kai ni."
Mu'az ya ji maganar kamar daga sama don ya ma fidda ran za su yi wata hira da Sadaukin tunda gaba daya ba su yi wata magana mai tsawo ba, ya kuma kula kamar akwai abin da ke damunsa.

Sai dai maganar da ya yi ya ankarar da shi damuwar don haka ya yi murmushi.

"Idan dai Haulatun Hajja ka ke son gani, tana cikin gida.

Ta dawo jiya."
an ji nauyi amma ya basar.

"Akwai kayan da zan so na kai wa Maama, amma muje kawai zuwa gobe sai na je."
Shi dai Mu'az toh kawai yace yana murmushi, wai shi za'a yiwa wayo kamar wani
aramin yaro.

Madadin su wuce
angarensu, sai ya ce ya tsaya a nan parking space na babban gidan.

Ya ce Mu'az ya wuce masa da kayan can
angarensu shi zai je ga Baba Alhaji.

Mu'az nan ma toh ne na shi, ya yi gaba, Sadauki ko kai tsaye ya nufi
angaren Hajja, ya sani shi mai laifi ne ya kuma shirya kar
ar kowane hukunci daga Bebin tasa.

Fitowarta kenan daga kicin, sanye da tshirt fara da siket da bai matse ta ba pink.

Sai ko
aramin
ankwali pink da ta rufe gashinta.
afarta sanye da safa, don Maama ta ce duk inda za ta shiga ya kasance da safa a
afarta.

Kofi ne a hannunta wanda a ta dama quaker oat, ya ji madara har ya yi fari fat.

Daidai lokacin ya shigo da sallamarsa.

Muryar da har abada ba za ta gushe a kunnuwanta ba, da wani irin sauri ta kalle shi, ya yi kyau cikin farar tshirt da blue jeans.

Yanda ta ke kallonsa haka shi ma ya ke
ara mata kallon daga sama har
asa.

Jin muryar Hajja na amsa sallamar gami da yi masa lale marhabin ya ankarar da ita, ta tuna ba sa shiri nan da nan ta yi sama da sauri-saurinta ba ta ko tsaya amsa kiran da Hajja ke mata ba.

Ajiyar zuciya ya saki ya
arasa ciki.

Umma da Safina sun je duba Maman Radiya da ba ta jin dadin jikinta.
Chapter 99 · 0% Book details