← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 109

Sashe 103

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan ta dubi gefenta inda ta hango Zuhra ta taho, umarni ta ba ta akan ta
auki sauran kayan rabon da ta bari a kusa da su Yaya Khaleefa su je.

Suna tafe tana nuna mata inda za ta kai.

Ita kuwa Zuhra na ajiye musu.

Khaleefa ya kasa
auke idanu a kanta, duk inda ta je ta dawo sai ya bita da kallo yana ji dagaske har zuciyarsa yana
aunarta.

Ya yi amanna akan abin da yake ji ba na wasa ba ne, ba kuma wai na kwanaki ne ba kawai a bar shi.

A'a, yanayi ne na
auna da soyayya da kuma fatan ya mallake ta a matsayin matarsa.

Duka wannan abu dake faruwa a kan idanun Hafsat wacce tun lokacin da Zaituna ta isa ga mijin nata take kula da su, har ma murmushin da Khaleefan ke bugawa yana bin su da kallo sai da ta lura.

Har wani jiri ta ji yana kwasarta daga zaune.

"Ke, je ki ki kar
omin
ata a hannun waccan uwar
an iyayin."
Ta ba
anwarta Fadila umarni, ita ko da ta maida hankali ga cin abinci, sai a lokacin ne ta lura da abin da ke faruwa.

Zaituna tuni ta koma mazauninta tana faman rainon Iman tana sauraron MC da ke ba da umarni akan
awayen Amarya da abokan Ango su fito fili.

"Meyasa za'a kar
o ta?

Wani abun ya faru ne?" Tambayar da Fadila ta jefa mata kenan.

Ita kuwa ta watsa mata harara.

"Babu ruwanki, kawai ki kar
o min
ata."
e baki ta yi tana turo baki.

"Gaskiya ki bari na kammala cin abinci wallahi.

Ni ba zan iya tashi ba."
Aikuwa tashin da ba ta yi ba kenan, Hafsat ta sha
a iya wuya, ba kunya ko ta mike da kanta ta zagaya har inda Zaituna ke zaune tare da su Fa'iza wa
anda suka suka kammala rabo an nutsu ana kallon diramar da MC ya ce a yi, wato rawa tsakanin
awar Amarya da abokin Ango, duk wanda ya
i yi kuma zai yi li
i ga abokin rawarsa.

Lokacin ri
on Iman
in ya koma ga Fa'iza, ita a sannan ma ta fidda rai ga samun Khaleefa har ta tsaida mijin aure cikin manemanta.

Kawai sai ganin Hafsat suka yi a kansu, ta ja ta tsaya tana mai sa hannu ta kar
i Iman
in a hannun Fa'iza har tana kokarin fisga da ya yi sanadin yarinyar ta firgita ta canyara kuka.

"Haba Anti Hafsat?

Don Allah ki yi mata a hankali." Cewar Zaituna, duk da ba duka abin da ta ce
in ya shiga kunnuwan Hafsat ba sakamakon ki
an da Dj ya saki, amma hakan bai hana Hafsat watsa mata kallon banza da harara ba sannan ta yi gaba.

Zaituna da Fa'iza suka dubi juna kawai.

Ita Fa'izar ma har da jan tsaki.

Koda ta yi wani furucin, Zaituna sam ba ta ji ba don hankalin ya koma kacokam ga sowar da wuri ya
auka dalilin karin da wani abokin Sadauki, Jameel ke zubawa Rumanatu da ke rawa shi ko da ganinsa irin miskilan nan ne wadanda rawar bai dame su ba.
angaren Amarya da Angonta kuwa, shi gaba
aya ma ya gaji da abin.

Sai ra
a yake mata akan ya dace a tashi haka.

Tana murmushi ta
an dube shi.

Ita ma cikin
an ra
an yanda zai ji ta ce.

"Wannan fa duk mu ake tayawa murnar aure, don Allah ka
ara ha
uri, ai an kusa tashi."
Ya jingina kansa jikin kujerar a saitin kunnenta ya ce.
uri ki ke ban?

Wani abu na ce maki zan yi?

Ko wani abun ki ke so?"
Ta kauda kai tana maida duba ga MC wanda ya yi umarni ga Dj ya tsaida ki
"Don Allah ka bari mana." Ta furta a hankali kamar mai shirin kuka da narkakkiyar muryar da ya ru
a kan Sadauki.

Da
yar ya samu ya saita kansa sannan ya ce.

"Na rantse ki ka
ara min magana da wannan yanayin daga nan babu inda za ki zarce sai gidana.

Idan ya so a biyo ki da kayanki."
Maganar MC ce ta katse Haulatu daga cewa komai, umarnin su fito fili yake ba su.

Sadauki ya ji kamar ya buge shi.

Fadi yake.

"Shi kuma wannan kamar wani ubanmu sai mulki da mallaka ya ke nuna mana."
Ita dai ba ta tanka ba sai murmushi a ciki-ciki.

Ba ta son ta yi abin da zai sa ya yi wani yun
urin don haka ta ja baki ta tsuke.

Koda aka tashi kusan su ne
arshen tafiya don sai da Sadauki ya yi bankwana da wasu abokansa da suka zo tun daga Lagos, a gobe da Asuba zasu kama hanyar Kano daga can kuma su hau jirgin dare da zai maida su.

Har gyangya
i ta fara, ba don ma Safina na motar su na
an ta
a hira ba da babu abin da zai hana baccin ya yi awon gaba da ita sosai.

Koda suka isa shi kansa Angon a gajiye yake amma fa hakan bai hana shi
ata lokaci da Amaryarsa ba don Safina na ficewa shi ma Bilal ya bar motar ya fita don ba su wuri su yi sallama.

Ta kai hannu za ta bu
e murfin ya sa hannunsa ya jawo ta gaba
aya ta dawo jikinsa har suna jin hucin fitar numfashin juna, da sauri ta sa tafin hannunta na dama a saman
irjinsa, a hankali kuma ta soma kokarin zamewa ya sa hannu
aya ya dafe yatsunta.

Ta kasa motsi kwakkwara, zuciyarta na umartarta da ta janye daga jikinsa sai dai gangar jikin ta kasa mara mata baya.

Ba ta san ya aka yi aka haihu a ragaya ba, sai dai kawai jin da ta yi sun fa
a ruwa tsundum, ganin abin na neman zarce gona da iri ne ya sanya ta saurin janye fuskarta ta kuma ja baya, shi ma babu wani karfi a jikinsa sai ya jinginar da kai yana sauke ajiyar zuciya akai-akai.

Kasa furta sai da safen ta yi don haka a hankali ta sa hannu ta bu
e murfin motar, za ta fita ya
an ri
e yatsunta.

Murya kamar ba ta Sadaukinta ba ta ji ya ce.

"Allah ya tashe mu lafiya."
A hankali ta zame yatsunta daga nasa ta amsa da amin, amsawar da babu lallai ya fita yanda ya dace.

Ba ta bada fuskar a ja ta da
ananun tsokana ba amma ina, duk da haka ba ta tsira ba wajen su Safina da Radiya.

Washegari da asubar fari bayan Haulatu ta yi sallah, Umma ta ja ta zuwa
akin da babu kowa ciki sai su biyun.

Nasiha mai ratsa jiki ta shiga yi mata na
ara nusar da ita matsayi da girma na miji.

Tun Haulatu na dannewa har hawayenta ya shiga fita.

Sun jima sosai kafin a
arshe Umma ta bi ta da kyawawan addu'o'in shiga gidan aurenta a sa'a ta kuma yi mata nuni da muhimmancin ri
o da sallah, da karatun Alkur'ani mai girma da kuma addu'a.

A ranar dama lakca ce za'a yi akan aure sai kuma dinnerparty da Ango ya shirya wanda daga can zai wuce da Amaryarsa.

KANO...

Tana zaune a
aya daga cikin
akunan gidan Mahaifin nata Malam Bashir Magaji tana goge kayanta sakamakon wutar nepa da aka kawo, kwananta uku a gidan amma babu wata alama na cin fuska ko mutuncinta a wurin mahaifin sai ma ja a jiki da kuma nasiha.

Gida ne na ilimin addini da kuma kyakkyawar tarbiyya.

Da Uwargidansa Rakiya, Mominta ta yi zaman kishi.

Rakiya ta sha wahala a zaman Momi a gidan.

Dalili kenan da ba ta samu wata tarbar arzi
i daga gareta ba, gwara ita ta biyun wacce sai bayan fitar Momi ta shigo gidan.

Ba ta wani samu matsala da ita ba.

Ita dai ga Hindatu babban farin cikinta yanda mahaifinta ya kar
e ta.

Momi har kiranta ta yi bayan dawowarta daga Dubai ta kuwa shaida mata inda take, hankalinta ya tashi ta dinga zaginta.
arshe ta ce za ta zo su tafi kuma sai ta karya dukkan wani sihiri da Baban ya yi don ya raba su.

Ita dai ba ta tanka mata ba sai ma hawayen takaici da ta zubar ganin har a sannan abubuwan da suka faru bai sa Momin ta yi nadama ba.

Sun yi waya da Haulatu kafin bikinta, nan take jin labarin aure za ta yi.

A sannan ne kuma ta zayyane mata gaskiyar halin da suke ciki a Katsina.

Ita
in ba aiki take ba, hannun dangin Umma suke sannan
an uwanta za ta aura.

Hindatu ta sha mamaki amma ba ta ji zafin
oyon da ta yi mata ba sosai musamman da ta ji dalilin Haulatun cewa ta yi ne don gudun kar
an Mutuwa ya samu labarin inda suke.

"Hindatu!

Hindatu!

Fito ko na ci ubanki!"
Jin murya kamar na Mominta ya sa ta ajiye dutsen gugar gami da kashe socket din.

Wata
anwarta dake latsa waya a saman katifa ita ma ta mi
e zaune ta dube.

"A'uzubillahi, wa ke mana ashariya a gida?

Kamar ke ake kira kuma ko?"
Jin haka yasa Hindatu
ara nutsuwa, aikuwa wannan karon sosai ta gane muryar Mominta don haka da sauri ta mi
e kusan a tare suka fita da budurwar nan.

Gwaggo kamar yanda ake kiran Rakiya uwargidan Malam, ita ce ta soma fitowa daga
akinta cikin shirin da ta yi na fita unguwa amma ta ha
ura sai yamma dalilin ranar da ake yi a garin, wannan ne ma yasa kowa ya
ume a
aka.

Momi ta banka mata uwar harara, babu abin da ya fi ba
anta mata irin atamfar da ta gani jikin Rakiyar wanda ita ma a watan ta siye shi, ko wata biyar ba ta yi da fitowa a kasuwa ba, ga kuma irin gyaran da gidan ya sha kamar ba gidan da aka yi shi da jar
asa ba a baya wanda ta sani.

"Haba Shatu, ai ko da me kika zo gidan nan, bai kyautu ki shigo mana da ashariya ba.
Chapter 103 · 0% Book details