← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 109

Sashe 70

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nusaiba da tun soma wayar ta fahimci inda zancen ya dosa ta yi kwafa ya fi a
irga, ita ma tauna zancen take, wai Yayanta na son rival
awarta kuma yar uwarta Jannat?

Ta
!

Har abada ba mai yiwuwa ba ne.

Hakan ta ayyana a rai.

A can White House kuwa, duk wayar da Mamin Khaleefa ke yi, yana zaune a gefe yana danna wayarsa, ya shigo ya tarar tana wayar kuma ba ta katse zancen ba.

Bayan ta ajiye ta
ara yin kwafa.

"Haka kawai, Na'imatu ta zo za ta shanye mana yara.

Ku na neman fifita ta akan mu da muka haifeku?

Wai ana zaune
alau yaron nan Mu'azu ya na neman janyo mana jafa'i a cikinmu.

Ai har abada ba zamu amince masa ha
a iri da Haulatu jinin karuwai ba."
Maganar ta dake shi, dama ya
auki haske a wayar da ya tsinci Mamin tasa tana yi.

Ya kuma gane a yanzu da Momin Mu'az suke zancen.

Jikinsa ya yi sanyi ha
e da tausayin Umma da Haulatu.

Wace irin tsana ce haka ne suka yi wa bayin Allahn da ba su ji ba su gani ba?

Jannat da ta shigo dauke da tray da ruwa da lemo a sama ta ajiye a gefen Khaleefa, tsaf ta ji abin da Maminta ke fadi tun tana waya don dama duka ita da kannenta uku ana zaune ne ana ta hira bayan sun kammala cin gashin kifi da aka yi don mahaifinsu Barrister Dawud wanda shi kadai ya yi azumi a gidan, su kaf sun ce sai na Arfah za su yi hakanan Mamin.

Ba ta takurawa kowannensu akan sai ya yi ba kamar yanda ba ta yi
in ba ita ma tunda a cewarta ai ba na farillah ba ne.

Da rawar jiki ta bar falon ta koma
akinsu,
annenta duk ta ba su shekaru babu wanda zai ta ya ta hirar don haka kawai ta dauki waya ta kira Nusaiba suka yi ta zantawa suna masu jin haushin Haulatu.

A gefen Jannat kuma ta ji dadi kadan, ita burinta ma abin ya tabbata ko ba komai ta huta da fargabar Haulatun za ta raba ta da Yaya Sadauki.

Haka dai suka yi ta zantawarsu can jima Jannat ta yi caraf ta ce.

"Keee!

Wai ma tsaya, ba na ji labarin an ce Safina ke son Yaya Mu'az ba?"
"Yes, na san da maganar.

Kawai ita kin san ba kowa ya sani ba, ni ma tsintarsa na yi wani lokaci da na shiga wajensu, ina ji Najeeb na tsokanarta wai ga surukarki ta zo.

Sai da na matsa ya ke fadamin, ita ba ta ma so na ji ba."
Wani murmushi Jannat ta yi.

"Ni na tabbata ba ta da labarin wannan soyayyar."
"Tsaya, ki na nufin za ki sanar da ita?"
Dariya Jannat ta yi, ita ma Nusaiba ta dara.

"Kai da
ina da ke akwai tunani a wasu lokutan.

Kinga ko ba komai wannan ala
ar za ta rushe.

Yanzu ai za ta gane me ake nufi da
ar bariki."
Suka dara.

"Bar ni da su.

Takanas zan shigo na samu Safina na ba ta wannan labarin."
"Ai ta zo gidan sau
i, dazu ta shigo ta yiwa Momi sallama wai za ta je gidansu can za ta yi sallah.

Ki bari kawai kya same ta a can."
Jinjina kai Jannat ta yi tana mai jin dadi.

Daga nan suka yi sallama.

Ita dai babban burinta ta ga Haulatu ta koma baya a kowane
angare.

Ba Sadauki ba, ba ta fatan ta auri kowane mai hannu da shuni, ta fi son ta gan ta tayi aure a wuri
antacce yanda za ta gane shayi ruwa ne.

Khaleefa ke tu
i yana tunani, ya kuma gama fahimtar cewa ha
a idan ya fito da abin da ke ransa game da Haulatu to fa zaluncin zai yi yawa.

Shi kuma a kaunar da yake yi mata, ba irin wanda zai so kansa ba ne, kauna ce mai tsafta da zai so ta samu kwanciyar hankali daidai gwargwado wanda zai rinjayi rashinsa a gidan aurenta.

Wannan dalili ya sa shi yankewa har a rai cewa ya ha
ura da Haulatu.

Zai kuma cigaba da bin ta da addu'ar Allah ya yi mata za
in miji nagari, shi ma kuma Allah ya kawo mishi wacce ta fi ta.

Da wannan, ya rufe babin tunanin yana mai ji har ransa gwara da bai furta ba.

Washegari...

KANO...
an Mutuwa zaune a falon gidansa ya zurfafa cikin tunani.

Wai shi Na'imatu ke gasawa maganganu har haka?

Ganin ta samu
ancin da bai taka kara ya karya ba?

Ya yi
wafa.

A ransa ya na jin eh ya ji ya yarda ya gama da babin Na'imatu, kuma ya rasa wannan damar da ya ke so na tsunduma harkar siyasa, amma fa ba zai bari ta ci bulus ba.

Zai sa Uban Dodo ya yi mata turen aljanun da za su hana ta zaman lafiya da za su hana ta aure gaba
aya.

Kai shi babban burinsa ma a
ora mata cutar mutuwa, wacce ba ta da magani sai dai ta sadar da ita ga gushewarta.

"Da ni kike zancen Na'imatu."
"Me ka ce?"
Bai san da cewa zancen zucin da ya ke yi ya fito fili ba sai da ya ji muryar Hindatu sannan ya ankara, tana daga gefensa zaune saman kafet din dake malale a falon tana cin gashin kaza ga wani sassanyan lemun kwakwa a gefenta.

Ya yi murmushin ya
"No babu komai Bebi.

Gama ci mu yi
ar magana."
Ta amsa da toh kafin ta maida hankali tana yi tana tunanin ko me zai ce?

Ita duk dadi ya cik
a ta kwanakin nan sakamakon samar mata admission da ya yi a jami'ar Bello Maitama za ta
ora karatunta.

Sai da ta kammala ta tattara komai sannan ta dawo ta zauna a gefensa.

"Na gama."
Ya numfasa.

"Dama batun uwargidata da na yi maki ne, ina son ce maki yanzu ba ma tare.

Mun rabu."
Hindatu ta
an fiddo ido,
"Toh, lafiya kuwa?

Me ya yi zafi haka?

Kai amma ban ji dadin wannan zancen ba."
Har ga Allah kuwa ba ta ji din ba.
an Mutuwa ya
an yamutse fuska.

"Kinsa halin kishi irin naku na mata.

Da zarar kun ji miji ya
ara aure shi ke nan sai cibi ya zama
ari.

Allah dai ya kyauta.

Bari na
an fita akwai wanda zamu hadu da shi ne."
"Amma Yalla
ai ba za ka lalla
a ta ba ko..."
Kallon da ya wurga mata ne yasa ta yin
if da bakinta.

Kallo ne da bai ta
a yi mata ba.

Ya ha
e fuska.

"Ba huruminki ba ne wannan.

Na fadamaki abin da ya kyautu ki sani ne don kawai kar ki sanya min alamar tambaya."
Daga nan ya fice fuu yana zura takalminsa ya bar ta.

Kamar ta tunasar da shi sallar Azahar da ba ta ga ya yi ba amma inaa tuni ya fice.

Ta sauke ajiyar zuciya.

Wayarta ta dauko ta dannawa Haulatu kira.

Ta ci sa'a kuwa ta amsa.

"Ke dai kin yi wuya
ar nan, ko ta whatsapp na maki magana sai ki dinga amsamin kamar ba kya so, wayar ma babu damar na kira na sameki a kusa.

Ko wani laifin na maki?"
ar guntuwar dariya Haulatu ta yi.

"Hajjaju Makkatu ki yi hakuri.

Kin san ina ta shirin fara karatu, Alhajin da Umma ke aiki a wajensu ne ya biya min na
arasa makaranta, mutumin kirki ne sosai.

Ya na daukar dawainiyar marayu da marasa karfi da dama."
Hindatu ta fiddo ido waje cike da mamaki da kuma farin ciki.

"Wai Allah!

Wannan abun farin ciki da yawa yake.

Nima fa ma fadamaki ko kwana biyar ba'a yi ba Yalla
ai ya samar min admission zan koma makaranta, amma fannin kasuwanci ya samar min.

Ashe dai ke ma za ki koma?

Amma na ji dadi ba kadan ba, gaskiya ko waye wannan Alhajin mutumin kirki da shi wallahi."
Haulatu ta yi murmushi mai sauti ta cikin wayar.

"Ke ma na maki murna sosai.

Ai gwara maki karatun.

Kin ga ko ba ki yi aiki ba, karatunki zai taimake ki nan gaba."
"In sha Allahu.

Ke, ciki ne da ni fa."
Sai da ta ji shiru ta wayar don a zatonta ma ko kiran ya yanke tunda dai kati sama da na dubu biyar ta zuba a wayar.

Ta fiddo daga kunnenta ta ga ba kiran ne ya yanke ba.

"Hello, na ji kin yi shiru?

Kin ji abin da nace kuwa?"
"Eh na ji, afuwan hankalina ne ya
auke ina aiki ne.

Kai na maki murna.

Allah ya saukeki lafiya."
"Amin.

Kin.." Hindatu za ta
ara magana da shirin labarta mata da zancen sakin uwargidanta da ya yi sai ta ji Haulatu ta katse ta da fadin.

"Big Mama, please mu yi magana anjima ko ta whatsapp, an sanya ni aiki ne kar su ga na tsaya amsa waya.

Kin san fa ana azumi."
Ta jinjina kai kamar su na ganin juna.

"Shikenan, ni ma dama shi ya hana ni azumin wai kar na wahalar masa da Bebi.

Bari na
yale ki toh.

A gaida Umma."
"Uhum, za ta ji."
Daga haka suka yi sallama, Hindatu ta mi
e, ta gaji da zaman shirun wannan ya sa dama ta
udirce za ta le
a makwafta a gaisa da juna, ko babu komai ta samu
an uwa na zumunci.

Katsina...

A gefen Haulatu ko, sadda suka yi waya da Hindatu tana zaune tana ferar dankali a kusa da kicin daga ita sai tshirt da zani sakamakon yanayi na zafin da ake yi ga kuma hadari da ya hadu, ana saka ran samun ruwa kowane lokaci.

Dama kwanakin nan zafin sai hamdala a garin.

Jikinta duk ya yi sanyi jin wai Hindatu na da ciki, sam ba ta cewa kowa wani abu a kai ba.

Dakyar ta ture batun a ranta ta cigaba da aikinta.

Safina tana tare da Mahaifiyarta Haj Fatu da suke kira Yaya, hirarsu suke yi game da bikin da za'a yi na
iyar
anwar Yaya a can Abuja.
Chapter 70 · 0% Book details