← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 109

Sashe 55

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu
aya ta sani, koda su Safina ke mata kallon kamar ita
in ma tana son Sadauki, ba ta ce musu uffan ba, kuma har a yanzu ba ta da amsar bayarwa a karon kanta ma balle har su
ji.

Washegari kuwa aka
unguma tare da
an uwa zuwa Kano don kai Batulu.

Koda sha'awa, Haulatu ba ta ji son bin su ba.

To kusan ma babu sa'anninta a tafiyar, daga iyaye sai
awayen Batulu da kuma su Zaituna su Jannat.

Umma ma ba ta je ba.

BAYAN SATI
AYA...

Suna tsaye a farfajiyar gidan an fito yiwa su Haj Nafisa rakiya za su tafi zuwa Kano don jirginsu na dare ne.

Hawaye Zaituna da Haulatu ke yi tamkar ba za su
ara ganin juna ba.

Ita na Haulatu ban da na sabo, har da na tausayin Zaituna musamman hirarsu na
arshe a jiya inda ta ke hawaye take jaddada mata cewa ganin da ta yiwa Zaid da bikin nan ya
ara tayar mata da wani mi
i na sonsa, tana kuma jin ba mace
aya ba, ko a ta hu
u ta zo idan har a gidan Zaid ne to fa tsaf za ta zauna kuma ta yi mishi biyayya ta nuna masa
auna tamkar su ka
ai ne a gidan.

A ganin Haulatu sam Zaid bai cancanci wannan sadaukarwar ba tunda bai san halacci ba.

Haj Nafisa ta rungumo Haulatu a kafa
a tana rarrashi.

"Ki yi hakuri
iyata.

Na so kwarai na tafi da ke Malaysia, amma har gobe ban fidda rai ba.

Ummanki dai ta ce idan don ita ce, ta bar min ke halak malak, Hajjarmu ce ta
i goyan baya.

Amma ko ba yanzu ba, duk sadda kika ji kina da bu
atar zuwa gurina ki sanar da ni.

Kin ji ko?"
Haulatu ba ta san sadda ta
aga kai ta dubi Maman Zaituna ba, duban
auna da soyayya.

Idan ka cire Ummanta, ita ce mace ta biyu da ta kwanta mata a rai wacce ke
aunarta tamkar daga cikinta ta fito.

Murmushi suka sakarwa juna kafin Maman Zaituna ta sake ta ta shiga mota.

Haka Haneef ya zo suka cafke yanda suka saba, ta yi dariya.

Bayan duka sun shiga mota, direba ya ja suka tafi ana
agawa juna hannu tamkar kada a rabu.

Kasancewar ranar babu islamiyya ya sa ta shigewa
aki, lokacin uku da mintoci.

Bacci ya soma
aukarta bayan tunane-tunanen da ta fa
a mai haddasa ciwon kai, ta ji kamar cikin baccin ana tashinta.

A hankali ta bu
e idanunta, ashe zazza
i ne a jikinta don wani irin rawar sanyi ta ke yi ga kuma azababben ciwon kan da ya ninka na farko.

"SubhanAllah, Haule ashe ba kya jin dadi, ina ta mamakin wane irin bacci ne har yamma.

Maza tashi muje a kai ki asibiti.

Ke Na'imatu!"
Umma jin Hajja na kwalamata kira ta shigo dakin da sauri.

Ita ma jin da ta yi Haulatun ba lafiya ya sanya ta
an ta
a jikinta.

Nan ta taimaka mata ta saka abaya saman riga da siket
an kanti dake jikinta.

Tsabar zafin ciwo ko'ina na jikinta kakkarwa yake yi ga wani uban jiri dake kwasarta.

Karshe haka suka fito tana rungume jikin Umma, Hajja kuwa tuni ta kira direbansu a waya, Allah ya taimaka yana kusa.

Dakyar Umma ta lalla
a Hajjar ta zauna da zummar za ta kai ta.

Kai tsaye asibitin su Khaleefa suka nufa.

KANO...

Biki Buduri...

Ina tafe gobe in sha Allahu idan har na samu dama, idan kun ji shiru, a yi min uzuri.

Love you all.
*Littafin nan na kudi ne.

Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga ha
in marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *
500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*
********
A cikin wannan satin da ake, a garin Kano, an yi biki na gani na fa
i wanda a wannan shekarar a tarihin Kano shi ne bikin da ya mutane suka yiwa kallon wanda ya fi kowane biki
ayatuwa da kuma kashe ku
i tun daga kan lefe.

Lefe ne aka kawo akwatuna saiti goma ga kyauta ta mota mai tsadar gaske ga Amarya.

Tun daga nan Momi ta
ara susucewa da lamarin surukin nata, ita kuwa Hindatu ta
ara shiga tsantsar tashin hankali ta kuma gane dagaske dai Alhaji Ibrahim mai ku
in gaske ne irin ku
in da ba ta ta
a hasko su ba.

Ba ta
ara tsinkewa ba sai da aka shiga hidimar biki.

Daga suturun da ta yi amfani da su wanda Ango da kansa ya ha
a ta da Hajiya Adama aka
inko mata su masu bayyana sura da kuma tsada, har wanda Angon shi ma ya yi amfani da su, abin kallo ne.

Ranar kamu inda aka yi shi daban, haka yini.

Da kansa ya ce a rarraba bai son a ha
e wani kamu da yini, Momi ta
ara jin kanta ya fasu,
an fadarta da ma wa
anda a baya ke ganin sun fi ta ku
i ita
in mai kawo musu kaya gida su siya ce, sai ga su nan kowa na neman shige mata da son cusa kai.

Ta zama ita ce Boss
in, idan ka gan su daga ita har
iyarta ba ka ce su ne asalin Hindatu da Momi na baya ba.

Sun sauya kalarsu ma ta goge sakamakon sauyi na rayuwa.

Hatta da Momi kafin zuwan biki ta mallaki mota da kuma direban dake kai ta wurare.

Har hotunan biki ta tura wa Alhaji Badamasi don ya ji haushi, sai dai ci kanki bai ce mata ba.

Gidan Hindatu a unguwar Tudun Yola yake, sabon ginin da Alhaji Ibrahim ya siya.

Babu abin da bai saka mata ba na more rayuwa, tun kafin zuwan biki ya sa aka yi mata passport na fita
asashen waje.

Bayan biki ko sati ba su yi ba, suka
aga
asar Dubai.

Gaba daya ba ta samu damar yin waya da Haulatu ba, ta bar shi akan daga baya ta sanar da ita.

Zuwa lokacin ta kur
i zumar soyayya daga wurin Alhaji Ibrahim, sai ta ji nan duniya babu mai raba ta da shi, ba ta san me ya sauya ta ba, amma wani irin
aunarsa ta shige ta na bazata.

Babban mutum amma fa ya gwanance a iya tafiyar da mace yanda za ta dulmiya kogin soyayyarsa.

Shi kuwa
an Mutuwa dama tun farko ya kula da yanayinta na tsoro da fargaba akan auren, bai ta
a nunamata ba shi dai ya san ba na wasa bane, a barikin ma ai kowa da matakinsa.

Na'imatun koda ba ta bayar da labari ba, su matan barikin dake maitarsa sun shaida.

Koda dai dama ba son Na'imatun yake ba, kafin ma ya san da zamanta a shimfi
a sai gumu ta yi gumu.

Haka suka yi rayuwar suka
are.

KATSINA...

Suna isa asibitin kai tsaye wuri Haulatu ta samu a waiting room ta zauna cikin
aya daga cikin kujerun sakamakon jirin dake kwasarta.

Da file na gidan gaba daya aka yi amfani da shi, sai da wasu mutum uku suka fito sannan Umma ta taimakawa Haulatun suka shiga.

Yana zaune yana danna tablet
insa, ya sanya farin gilashi, tun da ya
aga file
in ya gane daga gida ne yake tunanin toh waye ba lafiya a gidan?

Sallamar Umman ce ta sa shi saurin
ago kai.

Ya mi
e cike da girmamawa yana fadin.

"Umma?

Dama ke ce?"
Ganin Haulatun ya sa shi gane ita
in ce marar lafiyar.

Lokacin kuma Umma ke ba shi amsa da cewa Haulatu ta kawo.

"Oh." Ya furta kafin ya koma mazauninsa, bayan sun zauna ya gaida Umma ta amsa da kulawa.

Ita dai tana kaunar Khaleefa tana jinsa tamkar
an cikinta.

"Meke damunta?"
Da bakinta ta amsa.

"Zazza
i ne sai kaina..ciwo."
arashe hawaye na zubomata.

Ya
an dube ta ka
an, tabbas tana jin jiki.

Karon farko da ya ji tausayinta har ransa.

Test ya bayar na jini, sai da ya tabbatar Malaria ce sannan ya rubuta magunguna don a nan ya saka Nos ta shigo aka
auki jinin ta fita.

Magunguna da allurar jijiya na ranar da washegari, sai drip da za'a sa mata yanzun sakamakon jirin da take kuma Umma tace abincin ma yinin ranar gaba daya
in ci ta yi.

Nan ma Nos ya
ara kira a waya ya ba ta umarni.

Jin allura ta zaro idanu.

"Allura kuma?" Ta furta da narkakkiyar murya na wacce ke jin ciwo tana dubansa.

Ya
an sauke ajiyar zuciya yana mai kauda kai daga dubanta don Umma tuni ta amshe zancen.

"To haka za'a bar ki da ciwo a jiki Haulatu?

Ai gwara a yi maki ko zazza
in ya sauka.

Daure ki tashi muje."
Tana turo baki da yamutse fuska haka Umma ta taimaka mata suka fita a
akin.

Bayan fitarsu ya fidda gilashin gami da jinginar da kai jikin kujera ya
an lumshe idanu.

Bai kaunar ganinta cikin wannan damuwa da rashin lafiyar.

Yana hankalce da ita tun soma bikin, duk wani taku da ma abin da ya faru na rigimar da
anwarsa suka yi da ita duk a kan Sadaukin babu abin da bai ji ba.

Idan har kuwa tana son Sadauki, bai ga dalilin takurawa a kan sai ta
aunace shi ba, shi mai mata ma kenan.

Ba ya tunanin za ta so shi.

Wannan dalilin ya sanya shi za
ar barin komai da manta komai.

Ya kuma za
i ya kauda kai daga gareta, sai dai ganinta na yau
in ya so warware dukkan shawarar da ya yankewa kansa a kwanakin da suka wuce, shawarar na kallonta matsayin
anwarsa tamkar sauran
an uwannasa.

Bai san kuma sadda abin ya
arsu a rai ba da har ya yi wannan zurfin ciki ba.

Yana ji ba girkin da ya ji Hajja na mata gori ba ta iya ba, ko tsaftar ce ba ta da ita, zai iya ha
urin zama da ita a kowane yanayi, fiye da ha
urin da yake yi a rayuwarsa da Hafsat.

'Ina za ta so ka?

Alhalin tana da Sadauki?

Shi ta ke so?'
Wata zuciyar ta yi mishi tuni sai ya ji wani zafi a rai, don haka ya bu
e idanunsa da suka ka
a.
Chapter 55 · 0% Book details