← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 109

Sashe 28

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Haulatu ta bude gidan baya ta shige tana
i wa Safina dariyar mugunta don tun a hanya Safina kan su
arasa take ro
onta akan ta shiga mazaunin gaba ita a baya za ta zauna don ba ta nutsuwa idan ba ta nutsuwa idan ta na kusa da Mu'az.

Har Haulatu sai da ta tambaye ta meyasa?

Kodai tana son sa ne, amma Safina ta harareta cikin wasa.

Ta yi dariya kawai a sannan.

Mu'az ya kalle ta ta cikin madubin gaban motar.

"Dariyar ta mene ne?

Matsoraciya."
Ta ha
e fuska daidai sadda Safina ta bude gidan gaba ta zauna.

"Ni wallahi ba wanda nake tsoro sai Mahaliccina."
Ya yi murmushi.

"Good."
Shi ne kawai amsar da ya ba ta daga haka bai
ara uffan ba.

Duban Safina ya yi.

"Madam,
ara rufe
ofarnan ba ta rufu ba."
Ai kafin ma ya
arasa tuni ta bu
e ta kuma rufewa.

Haulatu ta
an ta
e baki, a ranta fadi take 'Ai ga matsoraciyar a gefenka.'
Sun yi tafiya mai
an tazara kafin su iso wani
aton wuri mai gate.

Hon ya yi aka bude suka shiga ya yi parking.

Gaba daya suka fito, Haulatu ta bude baki tana kallon wurin.

Babban wuri mai fili, a can gefe an yi gini lafiyayye mai
an girma, gefe guda kuwa wuri ne na musamman da aka yi shuke-shuke masu kyau da burgewa.

Ya dubi Safina.

"Ku na iya zagayawa kafin na kammala.

Ki nunawa
auyen nan wurare."
arashe yana duban Haulatu, ita kuwa ta
an harareshi.

Ya yi murmushi ya sanya ba
in gilashinsa.

"Ni kike harara?"
Ta kauda kai tana
an tsuke fuska ba ta tanka ba, daidai sadda wani ya zo wurinsa suka yi gaba suna maganganu.

Haulatu ta dubi Safina yanda take bin Mu'az da kallo tana wani murmushi kamar me.

Zagayowa ta yi ta dawo ta gabanta gami da jingina bayanta jikin motar.

Safina ta kauda kai tana wayancewa da fadin.

"Muje na nunamaki wu.."
Hannunta Haulatu ta ri
o hakan ya hana ta yun
urin tafiyar da ta yi niyya.

"Wai son shi kike yi?

Wannan
an wula
ancin?

Ke kuwa me za ki yi da shi don Allah?"
Nan da nan Safina ta tamke fuska.

"Kar ki
ara ce mishi
an wula
anci please.

Ko babu komai idan an cire ma
an uwantaka ya girme mu.

Kuma wallahi ma rashin fahimtarsa ne ba ki yi ba.

Yana da kirki da fara'a, kawai watakila don ba ku ta
a zama wuri guda ba."
Haulatu ta jinjina kai cikin gamsuwa, ta kar
i gyaran.

Suka soma tafiya sannan ta katse shirun.

"Ya san kina sonsa?"
Murmushi Safina ta yi tana mai sha
ar iskar wurin da ke ka
amshin ganyen gwaiba da ma na sauran kayan marmarin wajen.

"Bai sani ba, ba kuma na jin yana sona ma.

Muna hira da shi, a duk cikin kannensa ma ya fi kula ni mu yi hira kadan.

Sauran kuwa yana nunamusu hali na seniority.

Wallahi tun fa ina
arama ban san mene ne so ba nake kaunarsa."
!

Iska na wahalar da me kayan kara.

To kuma idan ya zo ya auri wata ba ke ba ya za ki ji?

Ni fa shiyasa bana son lamari na soyayya, wannan ai wahala ce.

Shi ake cewa son maso wani ko?"
arashe gami da yin dariya tana maida dubanta ga wasu kyawawan geese da ke wasa cikin
an tafkinsu.

"Uhm." Shi ne amsar da ta samu daga Safina, ba ta kara ce mata uffan ba har dai Haulatu ta fahimci ranta ya
aci ta lalla
a ta ba ta ha
uri.

Ga mamakin Haulatu har da hawaye Safina ta fitar, ta kuma jinjina girman son da Safinar ke yi ga Mu'az.

A ranta tana ji kamar ta yi dariya ko don ba ta san me ake kira da son ba?

Ba ta da masaniyar ya ake jin sa idan ya kama zuciya.

A fili dai tausarta ta dinga yi har a
arshe ta ce.

"Ke daga yau ma zan dinga ce maki Mrs Mu'az.

Sunan ya yi?"
Safina na dariya ta zaro idanu.

"Rufamin asiri don Allah.

Ai bayar da kai ne na bari ya sani ma.

Kira ni da sunana na yanka Safina.

Ki kuma taya ni addu'a please."
Murmushi Haulatu ta yi dake
ara mata kyau.

"Shikenan Mrs..au, Safina.

Ai ke tawa ce, ba zan manta da kaunar da kika nunamin ba tun ma farkon ganinki da ni.

Ba ki hantare ni ba."
Suka yiwa juna murmushi.

Tun daga nan wata
auna ta domin Allah ta
arsu a zu
atansu mai girma.

Suna tafe suna cin guava da suka tsinka suka wanke, Safina na musu hotuna a duk inda ya burge su a wayarta.

Sosai hotunan suka burge Haulatu fadi take.

"Kai nima dai Allah ya nunamin na mallaki wayarnan ta zamani.

Irin wannan wanki haka?"
"Ka ji fa
auyancin ko?"
Suka juya don jin muryar Mu'az, yana tafe a bayansu ba su san ma da zuwansa ba.

Haulatu ta turo baki.

"Wallahi ni ba
auye ba ce, ai wanda ya fito dga Kano shi zai yiwa wasu gorin
auyanci.

Ka ma ta
a zuwa Kano kuwa?"
Ya yi murmushi.

"Tun kafin ki zo duniya na san garin Kano.

Bai taba burgeni ba.
auyawa ne ku ti
is."
Nan fa ta biye masa suka fara musu, ita a dole tana fa
amasa ha
un wuraren da akwai a Kano duk kuwa da cewa da yawa ba ta je ba amma tana jin su a bakin Hindatu da ma Bahijja.

Shi kuwa yana nuna mata wannan duk ba wani abin a zo a gani ba ne.

Haulatu ta tsani tana magana ana nuna abin da take fadi bai wani taka kar ya karya ba don haka nan da nan ta cika ta yi fam.

Karshe ma shiru ta yi, Mu'az kuwa ya dinga yi mata dariya.

Safina har sakin baki ta yi ganin irin dariyar da yake yi, za ta iya rantsewa makamancinta ma ba ta jin ta ta
a ganinsa yana yi ko tare yake da mutuminsa Sadauki balle kuma su.

"Safina, na
ure yar uwarki ta yi tsit."
Itama sai ta yi dariyar jin dadin Mu'az ya kalleta yana dariya, ta ji inama zai yarda su
auki hoto tare.

Haulatu ta yi gaba, shi kuwa ya jera da Safina suna tafe yana murmushi ita kuwa tana satar kallon abin ta kamar ta ha
iye shi take ji don so.

Daga ta ga zai kalle ta sai ta yi saurin juya kai.

A hanyarsu ta komawa ma haka Haulatu ta yi ta
unci, bai ce mata komai ba shi ma.

Ina labarin
an Mutuwa???
an Mutuwa bai yi tsammanin za'a shafe sama da sati ba balle har a tunkari wata
aya bai ji labari cewa Umma ta dawo gidansa neman inda yake ba.

Kansa ya
ulle baki
aya, ya kuma rasa mene ne abin yi?

Shi ba wai neman Umma yake da zummar yana kaunarta ko son cigaba da zama da ita ba a rayuwa, aa, ko kadan, sai dai yana so ne ya koyamata hankali daga ita har Haulatun da bai ta
a jin
auna irin na
a da uba ba a kanta.

Duka wannan kwanakin ya yi su ne a gidan gona a can Gwarzo.

Ya kuma gaji da zaman, ya
osa komai ya lafa ya san inda dare ya mishi.

Ya ji labarin an yankewa su Maada hukuncin zama a gidan yari na wasu shekaru wanda ya sani babu inda zancen zai je za'a sallame su, su fito tunda su ke da manya a sama.

Yau ma waya yake yi da Hajiya Adama Loma inda yake mata
orafin shi fa ya gaji da zaman marinar nan da yake yi.

"Toh yanzu kai
an Mutuwa idan ka fito ina ka dosa?

Kar fa ka manta har yanzu wutar can ba ta mutu ba.

Ana nemanka ruwa a jallo."
Ya ja guntun tsaki ransa a
ace yake fadin.

"Ana nema na, ai ba Kanon zan koma ba.

A san yanda za'a yi dai ko wani garin nesa da Kano ne na koma can na shimfi
a sabuwar rayuwata.

Kuma kina sane da cewa ina da labarin zuwan Oga a satinnan.

Ya kamata ki yi duk abin da ya dace nima na samu halattar zuwa taron nan, akwai burin da nake son Oga ya cikamin shi.

Ko ba komai, ai na jima ina nawa
arin wajen tafiyar da har
allar mu."
Ta yi
ar dariya ta cikin wayar.

"Wannan ne ka
ai damuwarka?

Toh ka kwantar da hankalinka, jibi ne dai za'a gudanar da taron, zamu san yanda za'a yi ka halarta.

Har yanzu babu labarin matarka ko?"
ara jan tsaki karo na biyu, ta sosa mishi inda ke mai
ayi.

"Babu, amma ni na sani wancan munafukin makwafcin nawa da sanya hannunsa a ku
utar su.

Kuma ya san inda take, ban kuma san dabarar da zan yi na sani ba."
"Babu wani wuri da kake tunanin za ta je?

Ko dangin uba ko na uwa?"
Ya yi wata dariya ta zallar rainin wayo.

"Ke ma dai Adama da mantuwa kike.

Na'imatu fa
iyar Mai Kalangu, toh har wani dangi gare ta?

Haihuwar bariki rainon karuwai?

Ko ni nan da nake mata kurin na san asalinta
arya ce kawai da kuma barazanar kada ta yi gangancin guduwa ta bar ni.

Abu daya da na sani, ubanta da uwarta
an Katsina ne.

Ke bar wannan batu fa, amma ai har ta mutu ba za ta samu wani a danginsu ba.

Na dai fi tunanin duniya ta shiga.

Idan kuwa nan ne, samunta ba zai wahala ba.

Mu ne barikin."
Suka kwashe da dariya.

"Shegen sama, wai kura ta hangi biri.
an Mutuwa namu kenan.

Wato idan ana neman ba
in mugu aka same ka a shafa fatiha."
"Af, ai kifin ruwa ba ya gasa da na kogi.

Na'imatu da ni take zancen, duk inda take dai ai ba za ta sauya daga matata ba ko?

Toh kuwa za ta je ta dawo ta same ni tunda ba ta da gatan da ya wuce ni.

Kuma a lokacin zan murza kambuna."
"Atoh.

Ka san da hakan ma kake tada jijiyar wuya?
Chapter 28 · 0% Book details