← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 109

Sashe 21

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wanda ya shigo gidan babu inda yake fara zuwa sai
angaren Alhaji saboda anan ne Haidar da Jabeer suka ce an ha
a taron.

Sai dai duk wanda ya shiga sai ya ga babu kowa face Alhajin, kuma kana shiga zai zaunar da kai.

A haka har ya fahimci tabbas labari ya je ga jikokin gidan.

Ya kuma yanke dama zuwa bayan Magriba za'a ha
a taro a sanar da kowa halin da ake ciki.

Na nesa kuwa, sai a ba su labari.

Ya dubi matasan mata da maza dake zaune a falon nasa.

"Ku tashi ku je, mun yi waya da iyayenku bayan Magriba kowa ya zo nan akwai muhimmiyar magana da za'a yi."
Wata budurwa ba
a mai kakkauran jiki, tana sanye da riga da wando na Pakistan, ta rufe kanta da hula, ta
an ta
e baki.

"Atoh, gwara dai a yi ta ta
are Kakus, don a bambance tsakanin aya da tsakuwa."
arashe tana
an yin dariya ta rainin hankali lokaci guda tana satar kallon gefen wata matashiyar budurwa dake fidda hawaye.

Ran
washi ta ji a saman kanta, ta juya ta kalli mai wannan aikin.

Yayanta ne wanda daga shi sai ita a gidan Engr Faisal.

Shekara
aya ya ba ta wannan ya sa ta fusata kuwa ta mi
e ta kai masa duka, nan za su fara kokawar da suka saba Alhaji ya yi musu tsawa.

"Bana son shashanci, duk ku tashi ku fice daga
akin nan, ba kuma na son na ji koda wasa kun aikata wani abu da zai ja magana.

Ku yi hakuri komai za ku ji zuwa bayan Magriba, kai na mayar ma bayan sallar isha'i, hakan zai fi."
"Haba Baba Alhaji, kafin lokacin ai mun suma mun farfa
o, so muke mu san komai.

Dagaske ne waccan matar, oh sorry, Autarku ta ta
a haihuwar shege?"
uwa Alhaji ya yiwa mai maganar, saurayi ne da bai fi shekaru goma sha takwas ba, sanye da wando 3 quarter da riga marar hannu.

Kansa kuwa wani shegen aski ne, kai daga kallo
aya ma za ka fahimci akwai fitina tattare da shi.

"Ko uwarka Zaituna ba ta isa ta yimin wannan zancen banzan ba ballantana uban naka da kake ta
ama shi Soja ne.

Kar kuma ku
ara sheganta matar da aka haifa ta hanyar aure.

Maza ku tashi ku ba ni guri, na kuma mayar bayan isha'i, ni da iyayenku zan yi ba da ku ba."
Sum sum suka mi
e, ya bi su da kallo kafin ya girgiza kai cike da jin takaici a ransa.

Laifin duka na Hajiya Babba ce, da ace ba ta
oyemusu ba tun farko, hakan duk ba zai faru ba.

Haulatu na zaune tana danna
aramar wayar Umma,
ari take ta cika umarnin Umman na kiran su Abban Bahijja ta sanar musu cewa sun isa gidan.

A lokacin Hajiya Rabi tuni ta yi musu sallama ta tafi bayan ta ci abinci, yamma ta yi sosai, Umma na kwance dai idanunta rufe, ga dukkan alamu kan ya matsa mata da ciwo.

Haulatu ma ta sha mamakin kwanciyarta da la'asar don ba
abi'arta ce ba, asalima ita ke hana ta.

Aka turo
ofar aka shigo babu ko sallama, Haulatu ta
aga kai ta kalle su.

Su uku ne,
aya babbar mace ce, sai wata da za ta girmi Haulatun ri
e da bebi a hannunta cikin shawul sai ko budurwa da ba za ta fi sa'arta ba.

Suka
arasa shigowa su na musu kallon tara saura, Umma ta
an mi
e zaune jiri na kwasarta daga kwancen, Haulatu ta
aure fuska ta yi tsai da idanu tana kallonsu, a shirye take da duk wacce suka zo don ba ta ga alamun rahma a saman fuskarsu ba.

Budurwar ido waje ta dube su.

"Kai!

Unbelievable!

Wallahi sun yi mugun kama fa Adda."
Wacce aka kira da Adda mai ri
e da bebi ta yamutsa fuska idanu saman Haulatu wacce ta maida kai ga danna wayar da a wajensu ko
an aikinsu sai haka.

"Sannunku." Fa
in Umma da raunanniyar murya.

"Yauwa." Babbar matar ta amsa kafin rai a cunkushe ta juya ta fita.

"Aikin banza, da alama wahalar rayuwa ce ta koro su wajenmu."
in wacce aka kira Adda kafin ta ja tsaki.

Haulatu ta yi murmushi.

"Kuma dole a kar
e mu ba."
Baki sake Adda ke kallon ikon Allah, ita kuma wannan da
arfinta ta shigo gidan?

"Da me kike ta
ama?" Fa
in Adda zuciyarta na tafarfasa, dama can ga
an adawar
akin nasu suna musu dariyar wannan mugun abu da ya fa
akin nasu.

Dariyar rainin hankali Haulatu ta yi kafin ta watsamata wani kallo da manyan idanuwanta masha Allah.

"Da me zan yi ta
ama?

Ai koyaushe Allah ke bamu ya rufa mana.

Kuma gidan nan mun shigo shi kenan, abin kunya dai Asma'u ta riga ta yi.

Ta bar muku baya da
ura tunda ta haifi
iyar so Umma Na'imatu babu yanda ku ka iya kar
a dole.

Ku godewa Allah ma da ba a gidan rediyo ku ka sha labari ba."
Umma juya kai kawai take idanunta a runtse.

"Haulatu." Shi ne kawai abin da ta iya furtawa bayan haka radadin da kanta ke yi ya hana ta magantu.

A harzu
e budurwar nan ta soma magana.

"Kut!

Sunan Hajiya kike kira kamar ki na magana da sa'arki?"
Itama a fusace ta amsa.

"Ke kika san ta a Hajiyar."
Kafin su yi wani yun
uri na magana ko rashin ta ido, Hajiya Babba ta fa
akin.

Ta dube su a fuska a daure, kasancewar ana shakkarta ya sa duk suka nutsu idan ka cire Haulatu da ta ha
a su tana watsa musu harara.

"Ku fice min a nan." Ba musu suka fice rai a
ace.

Ta
arasa shigowa ba ta ko bi ta kan Haulatu ba ta dubi Umma cike da kulawa, murya na
an rawa ta ce.

"Na'imatu meke samunki?" Ta
arashe tana kai tafin hannunta saman goshin Umma.

Aikuwa ta ji ya
auki zafi rau.

"Innalillahi, ai ba ki da lafiya.

Bari na kira Khaleefa."
"Daga baya kenan, sau nawa tana yin cutar a duniya kin ta
a kulawa?

Sai yau?"
in Haulatu tana harararta, nasihar Umman ta
azu ce akan abin da ta aikata a falon Alhaji yasa ba ta yi gigin ture hannunta daga jikin uwarta ba.

Hajiya Babba ta kalle ta, wai yau ita ce ake fa
awa ba
ar magana?

Dama akwai ranar da za'a yi jikar da za ta gasamata mai zafi haka?

Tana kallo Umma na girgizawa Haulatun kai, ita kuma ta juya a sanyaye ta fice don kiran Khaleefa ya zo dubamata
iyarta.

Bayan fitar ta Umma ta dubi Haulatu, kafin ta kai ga magana rai a tunzure Haulatu ta katse ta.

"Don Allah Umma kiyi hakuri, wallahi idan na gan ta raina ba
i yake yi.

Kuma na rantse ba zan iya cusa kaunarta cikin zuciyata ba."
Kawai sai ta fashe da kuka ta mi
e ta shige ban
aki.

Umma dai ajiyar zuciya kawai ta yi.

Ta sani dama ya lafiyar kura ballantana an jefe ta da kashi?

Fatanta Allah ya yayyafawa lamarin ruwan sanyi domin ita kam ba ta ma san yanda ta dauki Hajiya Babbar ba a yanzu.

Ha
a tana bu
atar ko na lokaci ne kafin ita ko Hajiya Babba wani ya riga kwanciya a dama, su rayu cikin aminci da zumunci.

Ko ba komai ta nuna nadamarta a fili.

Fuska a
aure ya bi wayar da kallo, sunan Hajja da ya gani ya sa shi fahimtar mai kiran.

Ya dubi nurses din dake tsaye kansu na kallon
asa sakamakon fa
a da yake kan sakacin da suke yi mishi da marasa lafiya.

Da muryarsa tausassa ya nunamusu hanyar waje da yatsa gami da fadin.

"Out."
Suka
ara furta Sorry Sir, kafin su sa kai sum sum kowannensu ya fice.

Khaleefa Dawud S Malumfashi kenan.

Bai kai ga
aukar wayar ba, ta
ara ringing karo na biyu, sai a sannan ya
aga.

"Yes Hajja."
Abin da ya furta kenan murya can
asan ma
oshi, yana mai
an runtse idanu da
an dafe goshi alamun gajiya.

"Khaleefa, maza ka zo gida yanzu ka duba Na'imatu ba ta jin dadi."
"Wace haka?" Ya furta ya na yamutse fuska tamkar tana kallonsa.

"Na ce dai ka zo yanzun nan.

Don Allah, jikinta ya yi tsanani sosai."
"Ok." Iyakar amsar da ya ba ta kenan kafin ya sauke wayar daga kunnensa ba tare da ya katse ba sai can Hajja ta yanke.

Sai da ya kwashi mintuna uku cikin yanayi na shiru da tunani, abubuwa biyu ne a ranar yau suka sosa ransa, a gida Madina ta yi mishi nata kalar laifin, ya zo asibiti nan ma ya iske marar lafiya cikin halin neman taimako amma nurses kowa na harkar gabansa.

Wannan abubuwa biyun sun yi matu
ar kai shi bango.

Sarai ya na da labarin abin da ke wakana a gidan nasu, bai dauke shi wani abu na tashin hankali ba ko na a zo a gani, shi mutum ne da ya fi damuwa da matsalar dake gabansa.

Wannan na daga cikin
abi'arsa da kowa ya sani.
ewa ya yi ya dauki waya da mu
ullin motarsa.

Koda ya fito daga ofis din sai da ya biya ofishin abokin aikinsa suka yi magana kafin ya dinga keta mutanen dake zirga-zirga a asibitin ya fice zuwa filin parking.

Umma sosai zazza
i ya rufe ta, tana kwance rufe da bargo.

Baba Saude ta shigo ta kashe Ac sakamakon sanyin da Umman ta yi
orafin tana ji.

Har aka yi sallar Magriba, Haulatu ba ta ko motsa daga gefen Umma ba.

Ta cika ta yi fam, ita so ta yi ta fita ta je ko wurin Baba Dakta ne ta fadamasa Umma ba lafiya a kai ta asibiti amma kuma Umman ta hana ta har da ha
a ta da Allah ta zauna tunda a cewarta Hajiya Babba na ta zirga-zirga kuma ta kira likita zai zo.

"Tashi ki je ki yi sallah.

Idan kin fito sai na shiga." Ta tsinci muryar Umman tana magana dakyar.
Chapter 21 · 0% Book details