← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 109

Sashe 22

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta mi
e tana
ata rai ta shiga bandakin, bayan ta fito Umma ta mi
e da taimakon Haulatun ta shiga ta
auro alwala ta fito.

A zaune ta yi sallar.

Abincin ma da aka kawo ko loma
aya ba ta sanya a baki ba.

A babban falon Hajiya Babba kuwa, ita ce zaune cike da damuwa da sanyin jiki, ta yi shiru tana jin muryar
iyarta Hadiza da suke kira Anti Dije tana famam sababin ba ta kyauta musu ba sam.

Ita ce dai ta shiga dakin Umma a dazu tare da yaranta domin tabbatarwa kanta abin da ake fadi.

"Haba Hajiya, yanzu fisabilillah kin jazamana magana a zuri'a, dama ya muka
are?

Gaskiya nidai ki lalla
a ki saka matarnan ta koma can inda ta fito, ta fadi nawa take so sai a ba ta."
"Atoh." Fadin Ihsan tana
ara zaman bebinta gami da cigaba da shayar da shi.

Kallon da Hajiya Babba ta watsa mata ya sa ta kauda kai tana
an shan mur.

"Tashi ki ficemin a nan tun kan ranki ya
aci." Ba musu Ihsan ta mi
e tana
uni.

Ita kuwa Hajiya Babba duban tsanaki ta yiwa Hadiza.

"Ke yanzu Hadiza ni kike fadawa duk abin da ya zo bakinki gaban yara?

Madadin ki taya ni neman gafarar Na'imatu na gyara kuskuran da na aikata a baya, shi ne ki ke kokarin mayar mini da hannun agogo baya?

Dakyau, to ki sani, girma ya riga da ya kama ni, ba zan kuma bari son zuciyata ta sanya ni jefa rayuwarta cikin hatsarin da ya fi na baya ba.

A shirye nake na gyara kura-kuraina duk yawansu.

Ai farkon zuwanta nima tunanin nawa bai wuce na sallamarta da kudade ba ta yanda zan
ara nesanta kaina da ita.

Amma kuma cikin ikon Allah na fahimci kuskurena musamman da na ji irin
alubalen da ta fuskanta a rayuwar da ta yi ba tare da ni ba.

Ba kuma zan bari hakan ta
ara faruwa ba muddin ina da sauran numfashi a gaba."
"Amma Hajiya kun ce tana da aure, yanzu da auren Na'imatun za ta zauna a gabanki?"
Rai a
ace Hajiya Babba ta
ara ba ta amsa.

"Auren jeka na yi ka?

Auren da babu abin da ta tsinta a ciki face ba
in cikin
a namiji?

Toh babu inda za ta je.

Daga ita har Haulatun a nan za su zauna.

Ki kuma sani kaf ta girmeku, ku kira ta da Maman Haulatu kamar zai fi akan Na'imar."
Baki bu
e kawai Hadiza ta saki tana kallon Hajiya Babba.

Sallamarsa ce ta katse maganar da ta lan
wasa harshenta da zummar furtawa uwar.

Suka dube shi, dogon saurayi fari
al, yana sanye cikin farar tshirt dinsa sai kuwa wandon jeans kalar sararin samaniya.

Fuskarnan tasa a
aure ba kuma don komai ba sai don
acin ran da ya ci karo da shi a falon Hajiyar dake
asa,
annensa ke cece kuce kamar za su kaure da dambe.

Tsawa
aya ya sanya duka suka shiga taitayinsu.

Mu'az Faisal S Malumfashi kenan.

Matashin saurayin da ke girgiza zu
atan yanmatan zuri'ar tasu.

Mutum mai sakin fuska, sai ko idan rai
Hajiya Babba ta dube shi.

"Mu'az, maza kira min Khaleefa a waya.

Tun
azun na ce ya zo ya duba jikin Na'imatu ka ji shi shiru.

Ko kuma dai mu wuce da ita asibitin?"
Ita kadai ta yi ki
a da rawarta, shi kuwa sai ma ya nemi wuri ya zauna gami da yin filo da baby bag din Ihsan dake ajiye a gefe.

"Toh Hajja a kai ta mana."
Ta kai mishi duka a cinya.

"Aush." Ya mike zaune.

"Wai me Hajja?" Ya fadi yana yamutse fuska.

"Tashi za ka yi a kai ta da motarka.

Haka take nufi Mu'az.

Bari na fiddo ta." Fa
in Hadiza tana mai mi
ewa ta kama hanyar
akin da Umman ke kwance.

Hajiya Babba ta yi mamakin wannan saukowa lokaci guda na Hadizar, sai dai ita ta san wace ce ita.

Mace ce da ta iya shirya abu a rai, ko ita da ta haife ta ta san halinta, abu zai iya ta
a ran Hadizar ta shanye a gaban idanunka, amma hakan ba yana nufin ya wuce ba, tabbas akwai abin da ta
ullata da za ta yi ramuwa a kansa.

Yanzun ma ta fi tunanin da walakin goro a miya don haka ta bi bayanta.

Shi kuwa da kallo kawai ya bi su kafin ya maida idanunsa ya lumshe.

Ya ji labarin komai, ya tarar da Mommynsa na ta farin ciki da walwala, a bakinta ma ya soma jin maganar.

Jin dadinta kuwa bai wuce sanadin takun sa
ar da take yi da Hajiya Babbar ba tun sadda Hajiya Babba ta yiwa Engr Faisal umarnin
ara aure bayan ta kawo masa wata yar uwa daga Malumfashi a sanadiyyar sa
ani da aka samu da Mommyn a sannan ta yi yaji.

Aure dai na huce haushi, wannan abu ne ya tsaya a ran Mommyn, hatta da sabon da ya yi da Hajiya Babba ba kaunar hakan take yi ba.

Ya ji a bakin Mommyn, shegiya ce Hajiya Babba ta haifa, a bakin Alhaji kuwa, ya ji gaskiyar abin don haka shi kam bai ga abin tada jijiyoyin wuya ba.

Haulatu ba ta tsaya wani ja in ja ba da su Hajiya Babba don hankalinta na ga Umman wacce ta gama she
a amai ba jimawa.

Haka ta mike ta zura nata hijabin tana kuka, Hadiza na tallafe da Umman suka fito.

Fitowarsu daga dakin zuwa falon, ya yi daidai da shigowar Khaleefa da sallama dauke a fatar bakinsa.

Jin muryarsa ya sa Mu'az
ara lumshe idanu yana mai amsa sallamar murya can
asa.

A zuri'ar kusan kowa zai ba da shaidar rashin ha
uwar jinin mazajen biyu.

Za'a hadu a gaisa idan ta kama, hira ce dai Khaleefa bai yi da shi, kamar yanda Mu'az din bai damu da sanya shi a shirginsa ba.

Shi Khaleefa na masa kallon mutumin da ya girma amma bai san ya girman ba saboda son yawace-yawacen wurare na bude idanu da more rayuwa da yake da shi, yayinda Mu'az ke masa kallon mutum mai zafi da nuna isa da gadara a komai.

Ko kallonsa Khaleefa bai yi ba, ya maida hankali ga Hadiza wacce ta fito ri
e da Umma.

Ganinsa ne ya sanya ta
an ja burki.

"Ah, kinga ma Khaleefan ai.

Bismillah zo ka duba ta, ta jiga ta sosai."
Ya dubi Umman da kyau, ko ba a fadi ba dama ga kamannin Hajiya Babba a fuskarta.

Ta juya suka koma ciki tana ba Hajiya Babba amsa cewa ga Khaleefan ya zo.

Haulatu da ba ta ji me suke fadi ba ganin sun dawo da Umma ranta ya yi zafi.

"Au kun dawo da ita dakin kenan idan ma mutuwar ce ta
arasa a ciki?!

Ni dama nasan babban burinku bai wuce ku ga gawarta ba.

Toh ni zan fita na kai Uwata asibiti, ko ba komai na san ciwonta!"
Tana fadin haka ta yi kan Hadiza dake
arin ajiye Umma saman gado da zummar tallafawa Umma ta
ara mi
arta.

Umma ta ri
e hannunta amma babu bakin magana.

"Will you excuse me?"
Jin muryar namiji ne ya sa ta waigo fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye, suka dubi junansu ido cikin ido, shi tasa fuskar a tamke tamkar an aiko masa da sa
on mutuwa, ita kuwa kallonsa take da tunanin shi kuma waye don ba ta cikin wata nutsuwa ko hayyacin yin wani lissafin.

"Likita ne, Khaleefa duba ta don Allah mu ji meke samunta haka.

Gyara a wurin ya duba ta."
Sai da ta juya ta watsawa Hajiya Babbar wani kallo ganin yanda ta ri
e mata gwuiwar hannu kafin ta matsa ta ja baya.

Khaleefa ya dubi Hajiya Babba.

"Ku na iya fita baki daya."
Suka fice, Hadiza ta hadiye
acin ranta na hararar da Haulatu ta yi uwarta.

"Mu je Haulatu, duba ta zai yi."
Ta so yin gardama amma irin kallon da Khaleefan ke watsa mata mai kama da harara ko kuma ta ce na tsana, sai kawai ta hadiye suka fita gaba daya.

Sai da ya yiwa Umman tambayoyi, ya yi rubutunsa a takarda sannan ya fiddo abin gwajin jini ya
ara duba Bp dinta, nan ya ga ya hau.

Ya dubi Umma, kawai sai ya ji matar ta kwanta masa a rai, ciki ciwo take amma sunayen Allah kawai take kira madadin sambatu na mai fama da zazza
"Sorry." Ya furta a tausashe.

Ta
an gyada kai.

"Ki rage tunani, damuwar ba ta kawo wa bawa mafita a dukkan matsalar da zai shiga."
Daga haka ya mi
e ya fito, ko ta kan Haulatu wacce ta ke tsaye bakin
ofar
akin bai yi ba ya dubi Hajiya.

"Hajja zan je zan ba da magungunan a kawo.

A kula da abin da zai sanya ta tunani ko
acin rai.

And please, tana bu
atar mai hankali a kusa da ita."
arashe, sai a nan ya dubi Haulatu dake kallonsa da nata dara-daran idanun kalar nasa.

Ta yi kasa da kai, Hajiya Babba na amsa mishi da toh.

Mu'az tun shigar su ya fice a falon saboda zuwan Khaleefa.

Ran Haulatu ya
aci, wato da ita ya ke?

Allah ne ya taimake ta dai ba ta furta komai ba, sai kawai yana matsawa ta sanya kai ta shige dakin.

Ya maida dubansa ga su Hajiya Babba ya ce a samu abinci marar nauyi a ba ta ta sanya a cikinta.

Daga nan ya wuce.

Bayan sallar Isha'i Alhaji ya tattara yara da jikokinsa wadanda ke kusa.

Ya ce a sanar da na nesa.

Sai da ya fara da addua kamar koyaushe, ya dan yi
aramar nasiha sannan ya ba su labarin Umma da Haulatu a ta
aice.

Ya kuma nuna musu ita din haifaffiya ce ta hanyar aure, ba wai zina ba.

Kar ya
ara jin wasu a ciki na sheganta Umma.

Daga nan ya garga
e su akan ko kallon banza kar ya shiga tsakaninsu da su Umman, su ri
e su hannu bibbiyu su koyawa zu
atansu kaunarsu tunda a yanzun dai an zama
aya.
Chapter 22 · 0% Book details