← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 109

Sashe 87

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Za ta gifta ta, kusan tana sani ta sanya mata
afa aikuwa ta yi wata irin kifawa ta tafi tun daga tsakiyar benen har
asa, nan da nan bakinta ya fashe, wayar hannunta kuwa wata irin faduwa ta yi da screen din ya tsage.

Mutanen dake zaune a falon suka yo kanta suna salati, Fahima tuni ta hayewarta sama da gudu-gudu, gudun kada a zarge ta.

"Sannu, garin yaya haka?" Fa
in wata dattijuwa cikin ba
in Malumfashi.

Ita kuwa mi
ewa ta yi.

Hawaye ta soma, ba na komai ba sai na ba
in cikin wannan abu da Fahima ta yi mata, ita ta sani da gayya ne, amma kuma fa
ar ba shi da ma'ana tunda ba lallai a wasu su yarda ba musamman mahaifiyar Fahima Haj Hadiza wacce ta dage ai shegen iyayin Haulatun ne ya sa ta fadi, har da cewa wata
ila ma danna waya take yi.

Ita dai ba ta ce uffan ba, Umma ma dake zaune ko mi
ewa ba ta yi ba ballantana a ce ta yi wani abin.

Maimuna wacce ta samu zuwa bikin bisa iznin mijinta, sai sannu take jero mata.

Tsabar ba
in ciki tana wanke bakin amma hawayen bai bar zuba ba, da
yar jinin dake fita a le
an ya tsaya amma bakin nan ya kumbura.

Ranta ta ji yana zafi, ta rantse Fahima sai ta yi kuka fiye da wanda ta sanya ta.

Abincin ma fasa shiga ta
iba ta yi, Hajja sai sannu ta ke jerowa, har da yiwa Baba Saude fa
a akan ta yi sauri ta kammala gugan, ba ta bi ta kan wayarta ba ta wuce ta koma sama.

A falon sama ta iske Fahimar zaune tana danna waya.

Suka ha
a idanu Fahima ta
yace da dariya sai ta wayance kamar mai yin voicenote a whatsapp ta ce.

"Ke, wani abu na gani ya tunamin da Shrek.

Hum, ina ganin salo a gidanmu, ai ina fa
amaki Yaya Sadauki dai ya fi
arfin mutum, kuma duk yanda aka
wallafa rai a kansa ake mishi tallar ciki da waje ba'a ishe shi kallo ba."
Tsaf ta gane inda maganar ta dosa, rufe
ofar
akinsu ta yi bayan ta shiga, tabbas akwai ranar ba ta amsa, akwai babbar ramuwa tana zuwa.

Ba kuma a yau ba.

Ba ta jima ba sai ga Maimuna ta shigo da sallama, ta amsa mata, abinci ne a faranti ta kawo.

"Ga abinci Hajja tace a kawomaki."
Kamar ta ce ta
oshi amma sai ta ji ba za ta iya ba don dagaske yunwar dai take ji, godiya ta yi mata.

Maimuna ta zauna tana mi
a mata wayarta gami da furta.

"Wannan ta ci screen."
Ta kar
a ta ga wani far far yake yi, sai kawai ta ajiye a gefe.

Duban Maimuna ta yi.

"A nan za ku kwana?"
"Aa fa, yana hanya ma yanzu zai
araso mu tafi."
Ta jinjina kai, da
yar ta ke sa abincin a baka da cokali saboda ra
in da le
an ke mata.

"Ki yi hakuri, na san Fahima ce da wannan aikin."
Maganar Maimuna ya sa ta dubanta da mamaki.

Ta jinjina kai.

"Na gan ta, zan shiga kicin ajiye kofi, na ga sadda ta saka maki
afa ta gudu.

Don Allah kiyi hakuri."
an murmushi Haulatu ta yi, kamar ta tambaye ta dalilin da ya hana ta fa
i amma sai ta share.

"Bakomai, kar ki damu.

Kanta ta yiwa."
"Hakane, ban fa
a ba ne saboda ba na so ya jawo abin magana, kin san yadda Hajiyar tawa take."
Wato Haj Hadiza mahaifiyarsu, Haulatu dai ba ta tanka ba ban da wani murmushin.

Wayar Maimuna da ya yi
ara ne ya sanya ta mi
ewa.

"Kin ga har ya zo ma, bari mu wuce sai da safe.

Allah ya
ara sauki."
"Amin, sai da safe nagode."
Ta na ba ta amsa ma kafin ta kai aya ma Maimuna ta wuce, ga dukkan alamu daga yanayinta mugun shakkar mijin nata take yi.

Ta maida hankali ta ci abincin ba wani sosai ba, ko wayar ba ta son kallo tsabar ba
in ciki don wani ba
i ta yi daga tsakiya har ba ka iya ganin fuskarta sosai.

Fita da abincin ta yi ta maida
asa ta rufe a kicin sannan ta dawo ta yi kwanciyarta bayan ta kashe wayar gaba
aya ta jefa a dirowar gefen gadon.

Nan kuma ta tsunduma tunanin Sadauki, ta manta da dukkan wata damuwa, kalamansa suka shiga dawowa tiryan-tiryan a kwakwalwarta yayinda
aunarsa ke
aruwa a birnin zuciyarta.

Sai ta ji tana kewar muryarsa da ganinsa, kamar ma sam a yau ba su ga juna ba haka ta ke ji don soyayya da shau
i.

Da
yar ta samu dai ta yi addu'ar kwanciya bacci ta kwanta, kafin Umma ta shigo tuni ta yi nisa a baccinta.

Kano....

Mummunan labarin da ya ris
i Haj Adama na tashin gobara a makeken store
inta dake a ke
antaccen wuri a daji wanda ba kowa ya sani ba, ya jefa ta cikin ka
uwa da tashin hankali marar iyaka don har suma ta yi saboda tsabar firgici.

Nan da nan ta baza tare da mu
arrabanta don zuwa ganewa idonta.

Sai dai babu wani kayanta da ya tsira, wuri ya shafe ya zama toka.

Ai sai ga Haj Adama na maganganu kamar zararriya.

Fadi take.

"Allah ya tsinewa
an Mutuwa, Allah ya isa!

Sai na ga bayansa!

Na rantse sai na zama ajalinsa!

Da ni Adama ya ke zancen!

Ni na san babu wanda zai min wannan aikin sai shi!

Dama ya ci alwashin ramuwa!

Ashe ta nan ya
ullo!"
Sai kawai ta shiga kururuwa da ihu ana ri
e ta.

Da
yar ta iya shiga mota tana kuka wiwi da majina suka bar wurin.

Babbar asara ce na kayyakin da ba nata ita
aya ba.

Ta sani idan kowa ya mata uzuri ya ba ta damar ha
a wasu kayayyakin, to fa ban da Major Musbahu, ba shi da mutunci ko ka
an.

Ko yau wuraren hudu na safe sai da ya dokamata kira akan a fito da kayansa a biyo hanyar Lagos, har ta ji haushi ta rufe shi da fa
an na fa tsoronsa take ba, har da cewa ita daga wannan ma ba za ta
ara ha
a harka da shi ba.

Suka yi zage-zage, ya kuma ci alwashin muddin ba ta aikomasa kaya ba zai yi maganinta.

Ashe kuwa kayan da ba za su aiku ba kenan.

Sai ta
ara fashewa da wani gunjin kukan.

Wayarta dake ruri ta duba, gabanta ya yi mugun fa
uwa ganin sunan Major Musbahu na yawo saman screen.

Hannu na rawa ta mi
awa
ar amanarta Yakura.

"Kashemin wayar gaba
aya."
Abin da ta ce kenan, ba musu Yakura wacce ta sha man bilitin fiskarnan kamar
anyen nama ga hudan hanci da bai mata kyau ba, ta cika umarnin Uwar
akinta.

Haka suka koma cikin gari Haj Adama na sa
e-sa
en matakin
auka.

Hindatu ta zubawa Mominta dake rawar jikin ha
a kaya idanu.

Ba na komai ba ne sai na tafiyar da Momin za ta yi Dubai a satin don yo mata siyayyar haihuwa wanda
an Mutuwa shi yake shiryamata komai na tafiya.

Duka hakan kuma don ya
ara wanke kansa a wurin Hindatun ne don a tunaninsa rashin ta idon da ya yiwa Mahaifiyarta ne ya sanya ya chanza.

"Momi." Kiran sunanta da Hindatun ta yi ne ya sa ta
agowa ta dube ta fuskarnan cike da annashuwa ta amsa.

"Na'am
ar Mominta.

Shalele mai goshin arzi
i, ta Alhaji Ib..."
"Momi don Allah mana, ni bana son duka wadannan abin, ba na son dukiyarsa hatta shi
in ma ya ficemin a rai.

Ni ki maida masa komai a raba aurenmu."
Ai ba ta san sadda ta saki
aramin akwatin
an kunnen da sar
a da take
arin jefawa a jakar tafiyar da
oki ya sanya ya fara shiri tun wuri ba.

"Eh??

Me ki ke cewa?

A raba aurenki da Alhaji Ibrahim?

A'a ina jin ban fahimci zancen ba.

Hindatu, auren nan ki ke fatan a raba?"
Cikin zubar hawaye Hindatu ta gya
a kai tana kallonta.

"Eh Momi, ba na son auren nan."
A harzu
e Momin ta amsa tana nuna ta da yatsa.

"Kin yi ka
an, ke ban ma yarda ke ce ba, na rantse ture aka yi maki.

Ni dai na shiga uku na lalace!

Yanzu
iyartawa ma ta yi aure ma
iya da mahassada shi ne suka sako min ita a gaba?

Burinsu a yi ta
irga maki aure?

To ba zai yiwu ba!

Lallai
aukar mataki ya zame min dole.

Ina na jefa wayata?"
Daga haka ta shiga laluben waya, Hindatu ta yi shiru sai hawayen dake fita, cike da ba
in cikin jin wacce Momin ta kira, wato sabuwar aminiyarta Hajiya Tani, ta sani bai wuce batun zuwa wajen
an tsibbu ba don haka ta fice daga
akin.

A kujerar falo ta zube ta hau kuka sosai, wannan ne karo na farko da ta ji kewar mahaifinta da
an uwanta, da ace yau tana hannunsa, tana da tabbacin abubuwa da dama ba za su faru gareta ba.

Aurenta tun daga na farko har na biyu babu wanda aka nema a dangin mahaifinta, Mominta ita ta yi ki
a da rawarta tare da wasu tsirarun
an uwanta maza wa
anda suke da hali irin nata na zalama da ha
amar abin duniya, da babu hakan a gabansu, ko kallonsu bai kamata su yi ba tunda Momin ba ta nemansu idan ba kasuwar bu
atarta ce ta tashi ba.

Ganin kukan ba zai mata magani ba sai ta share hawayenta, ba ta da wata aminiya sama da Haulatu, za ta yi shawara da ita don jin abin da za ta ce, sai dai ko giyar wake ta sha, ba za ta iya fitowa ta fa
amata abin da ta ji da kunnuwanta mijinta ke fa
i ba.

Wayarta ta jawo ta kira ya fi sau uku sai dai duka amsar guda ce, a kashe.

Haka ta gaji ta koma kiran ta Umma, ta ci sa'a kuwa ta shiga.
Chapter 87 · 0% Book details