← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 109

Sashe 4

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta shige ciki, yaran su uku suka bi bayanta da kayan suka sauke, sai da Umman ta sallame su ta ba su abinci da kudi sannan ta dawo kan Haulatu.

Rai a
ace ta ce "Kin yi sallar Azahar da La'asar?"
Ta turo baki ka
an.

"Yanzu fa na tashi daga bacci, shi zan yi."
Cike da takaici Umma ta girgiza kai.

"Ki ji tsoron Allah Haulatu, wannan rayuwar da ki ke yi na rashin sauke ha
in Allah a lokacin da ya kamata babban kuskure ne.

Kina tunanin matsalolinki za su warware alhalin kina yiwa Allah yanda ki ke so?

Wato yau ma ba ki yi ko tunanin zuwa Islamiyyar ba ko?

Kin kyauta, ki cigaba, nidai Allah na gani ina iyakar bakin
ar.."
"Kai Umma, nifa ba cewa nayi ba zan yi ba.

Haba don Allah, wannan masifar ma da kike ta yi ai sai ya
ara cinye lokacin."
Umma ta saki baki kawai tana kallonta har ta cika ruwa a buta ta shige ban
aki tana
uni, yanke ta idan tana cikin magana wannan ba sabon abu ne a wurinta ba, amma kalmar tana masifa ya yi mata ciwo
warai.

Haulatu sau da dama idan ta yi magana kamar an bu
e masai tsabar rashin sanin abin da ya dace ta fadi.

Sam, ba ta iya tauna harshe kafin ta furzar ba, komai ya zo mata hakanan ta ke jinsa daidai a wajenta.

"Allah ya shirya." Abin da ta iya fadi kenan zuciyarta babu dadi sannan ta shiga tattara kayan, tun a kasuwa ta saka yaran sun wanke komai, maida su ta yi kawai kicin ta adana, abincin da ta rage musu da zasu ci, shi ta juye cikin madaidaitan kwanuka sannan ta shige daki don rage kaya ta watsa ruwa.

Koda ta fito daga dakin, ta iske ta a tsakar gidan ta tayar da sallah bayan ta zura dogon hijabin Umman dake ajiye saman tabarmar.

Ita kuwa bokiti ta
auka ta cika ta shige.

Haka Haulatu ta yi sallolinta kafin ta mi
e ta dauko faranti, kai tsaye ta dibi shinkafa da waken ta sanya kabeji da mai a samansu.

Tana cikin ci Umman ta fito, cikin sakin fuska Haulatu ta dube ta.

"Lah Umma yau dai kin yi sa'ar mai, babu warin nan irin na rannan."
Ganin yanda ko kallonta ba ta yi ba ta shige
aki sai ta sha jinin jikinta.

"Ita kuma wannan ita da wa?" Ta yi tambayar a fili babu mai amsa mata, sai kuma ta ja guntun tsaki tunawa da ta yi mai yiwuwa rashin zuwa islamiyyarta ne ya yi wa Umman ciwo.

Hakan yasa ta mi
e duk abincin ma ta ji ya fice a ranta don ita fa ba ta kaunar ta ga ko alamar
acin rai a fuskar mahaifiyarta.

"Umma ni ce ko?

Ban je makaranta ba, kiyi hakuri na dawo kaina na ciwo.

Amma zan je ran Lahadi tunda gobe juma'a." Kasancewar makarantar hutun juma'a da asabar ake yi.

Umman dai ba ta ce uffan ba ta zura doguwar rigarta ta shan iska, ganin dagaske dai ba za ta kulata ba yasa hankalinta tashi.

Nan fa ta shiga ban hakuri har da su hawaye, Umma ta dube ta, dagaske ita laifinta
aya ta ke hangowa kanta, wato na
in zuwa makaranta, a ganinta shi ne dalilin fushinta.

Ta
an yi shiru tana nazarin wannan wauta na
iyarta.

Can kuma ta numfasa gami da soma magana.

"Shikenan, amma ki sani kalmar da kika yi amfani da ita na ina masifa, ba daidai ba ne yiwa babba ita.

Ba ma wannan ka
ai ba Haulatu, ko ka
an bai kyautu ace babba na magana ka katse shi ba, wannan yana nuni da rashin ladabi gareshi.

Sannan ba sau
aya ba, na sha nunamaki illar wannan tsakin da kike yawan yi ga babba balle kuma ni da nake mahaifiya gareki ba daidai ba ne, na lura ya riga ya zamar maki jikin da yanzu da kuma nan gaba zai iya haifar maki da tarin matsaloli, koda ace ba a wurina ba, za ki iya samun matsala da gidan da za ki je nan gaba."
Cikin rashin fahimta Haulatu ta ce.

"Gida kuma?

Ni zan je?

Wayyo Umma kin amince kenan mu bar masa gidansa?"
arashe a
okance tana jin nesa ta matso kusa, burinta zai cika sai dai kuma girgiza kan da Umman ta yi ya sanya ta yi kamar ta ja tsaki sai kuma ta tuma ta saita le
an da ta turo gaba da farko.

Sosai ta lura da abin da ta yi niyyar yi, ta sani yarinyar sai a sannu za ta gyara.

"Umma wane gidan zan je na bar ki?"
Ta katse mata tunanin da ta tafi.

Ta numfasa.

"Ita mace ai ba ta zama ba ce, dole wataran ki tattara ki je gidan wanda Allah ya
addara shi ne mijinki."
Dariya sosai Haulatu ta sanya.

"Kai Umma kina magana kamar a irin Indiyarnan mai fassarar Hausa.

Aure manya.

Ai fa, Iro dai zai ga wacce zai kai gidan wancan tsohon
warton mai sa..."
"Haulatu!" Tsawar Umman ya dakatar da ita.

A zafafe ta cigaba da magana.

"Meyasa kika da taurin kai da kunnen
ashi ne?

Mahaifinki kike kira da wannan banzan sunan wai Iro?

Na fadamaki duk lalacewarsa shi din Uba yake a wurinki!

Kar ki kuskura ki kai ni ma
ura!

Aure kuma ai dole wataran ki yi shi!

Kin fi kaunar ki zauna kina rayuwa cikin wa
ancan
an daban masu shirin farautarki a kowane lokaci?

Idan ke har yanzu ba ki san meke maki ciwo ba, ni na sani!"
Umman na kai wa nan ta fice daga
akin.

Dagaske sosai Haulatun ta sha jinin jikinta, ko mene ne ta aikata, tana da tabbacin wannan fa
an ba iyaka nan ya tsaya ba, akwai wani abin da ke ran Umman da ta kasa fahimtarsa.

Kusan ta mance rabon da ta ga bacin ranta irin wannan.

Wannan yasa duk ta rasa sukuni.

Da
yar da su
in goshi ta shawo kanta har ta sake bayan ta mata nasiha akan gyara kalamanta ko don gaba musamman ma na wannan sunan da ta sanyawa mahaifinta daga Ibrahim zuwa Iro.

Haulatu dai ta amsa da toh za ta gyara don komai ya wuce amma har a zuciyarta ba ta jin yana da wani sunan bayan Iro, ko a makaranta ma da Muhammad take amfani matsayin sunan Uba.

Umma ba ta hana ta ba tunda dai ana jika, ita ta san sunan mahaifin baban Haulatun ne sai kawai ta rabu da ita.

Ya yi shiru yana juya cokali cikin kofin ruwan shayin dake ajiye saman teburinsa a ofis.

Numfashi yake ja gami da furzarwa tamkar wanda ya ci gudu.

Can kuma ya cire hannun ya
an bugi tebur har
ruwan shayin na
ata wasu takardun dake ajiye gefe.

Hakan ya
an tsoratar da mutane biyun dake zaune a ofishin tare da shi.

Babu wanda ya samu damar cewa uffan a cikinsu har sai da uban gayyar ya soma magana don kansa.

"Kai
an Mutuwa!

Ba fa zan yarda da wannan soki burutsun naka ba!

Ya kake
arin haramtamin abincin da Allah bai yimin iyaka da shi ba?!

Ka fito kawai a mutum, kai tsaye ka cemin ba za ka iya auramin
iyarka ba kawai!"
Mutumin da aka ambata da
an Mutuwa cikin ma
urar ladabi ya soma magana.

"Haba Yalla
ai, na rantse ka fi
arfin dukkan wata alfarma.

Ni ko Na'imar ka gani kake so ai zan iya sakarta ka aura ballantana kuma abin da yake
ashin ikona?

Kawai dai akwai babbar matsala ne."
arashe murya a
asa da tunanin
aryar da zai shirgawa Ciyaman ya samu su rabu lafiya.

"Wace irin matsala ce kai kuwa
an Mutuwa da har za ka kasa biyawa Yalla
ai bu
atar da ba ta fi
arfinka ba?" Cewar wani kakkauran mutumin dake zaune a kujera suna fuskantar juna.
an Mutuwa ya sauke ajiyar zuciya, ya kula gaba
aya hankulansu na gareshi wannan ya sanya shi ha
iyar yawu da
yar.

"Mata maza ce."
Abin da ya tsinci harshensa da furtawa kenan, babban burinsa wannan ta kawo
arshen zancen, ya kasa ha
a idanu da su duka.

Kirjinsa na bugawa tamkar zai fito.

Kalaman Haulatu
iyartasa ke amsa kuwwa a dodon kunnuwansa cewar da ta yi za ta fallasa dukkan sirrinsa.

Toh kuwa da fashewar ru
wan nan baragurbi, wanda warinsa zai shafi mutane da dama, ai ya gwammace ya yi wa maganar auren kisan gilla ko ta wace hanya.
*FITAR TSIRO*
Rufaida Umar*
Paid book: 500
Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar.

FCMB
Phone number: 09034973645
Free page 3
an Mutuwa, ni za ka kawowa wasa?"
Cikin dakiya ya girgiza kai gami da
ara narkar da fuska kamar muminin da ya tuna kwanciyar kabari.

"Wane ni na zo maka da wasa Yalla
ai?

Wa ya
akinsa da
wan jimina?

Ai bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne.

Tunku, ya san jibar da yake yiwa kashi, ba irinku ake zuwa gabanku da
aramar magana ba."
Jin haka sai kuwa jikin Ciyaman ya yi sanyi, komawa ya yi ya jingina da kujerar gami da
an rufe idanu.

Tabbas dole ya yiwa abin tufka kafin wankin hula ya kai shi dare.

Bai so ace wai Haulatu, mace ta uku cikin wadanda ya so aure amma ba a dace ba.

Ga dai tafarkin da bokansa ya
ora shi a kai, ruwansa ne ya yi gaggawar aure nan da sati lafin guguwar siyasa ta motsa, ruwansa ne ya yi fatali da zancen ya ci karo da sakamako mafi muni a rayuwa.

Sharu
a biyu bokannasa ya ba shi,
aya shi ne ya nemi matashin namiji su aikata alfasha,
ayan kuwa shi ne ya nemi budurwa marar kowace nakasa ta kowane
angare ya aura, wato sabuwa dal a leda wacce aka yi mata kyakkyawar shaida ta kamun kai.

Muddin ya cika wa
annan sharu
an bayan layu da ya sa aka binne a sabon gawa, to babu abin da zai hana shi cimma nasara da yin tamola da abokan hamayyar kujerar takararsa na
an majalisar dokoki na Jaha.

Budurwar farko ya samu rahoton tana shaye-shaye, ta biyu kuwa tana biye-biyen maza.
Chapter 4 · 0% Book details