← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 109

Sashe 48

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu dai tunda abin haka ne ma, na
ora maka ragamar nema mata admission."
Wani
an murmushi Sadauki ya yi kafin ya shafi sumar kai ya dubi Haulatu da ita din ma ta kalle shi don jin me zai ce wannan karon.

"Ta yi Jamb
in ne?

Sannan result din ya yi kyau?"
Haulatu ta ji ta tunzura kamar ta kai masa bugu don haushin rainin hankalin da ya ke mata.

Ita kuwa ta yi Jamb, ba ta mancewa da
yar ma Umma ta bari ta yi don a cewarta gwara ta yi aure a lokacin ta fita daga
angin rayuwar da suke ciki na gidan.
yar ta yarda ta biyamata kuma sakamakon ya yi kyau ba laifi ta fito da maki har 177.

"Ah ta yi mana.

Har nan ta zo ta nunamin.

Ni nawa ma ki ka samu?" Fa
in Baba Alhaji.

Ta yi shiru don ta cika ta yi fam.

"Ba amsa?"
an dube shi, ya
an lumshe idanu ya bu
e yana mata murmushin da ya
ara masa kyau.

"One sebin sebin."
Ta ba da amsa bayan ta kauda kai, aikuwa sai ga Sadauki na dariyar sebin sebin, wanda ke zaune a gefensa na taya shi.

Ran Haulatu ya
aci
warai, ta ma ture mamakin ganin Sadaukin na dariya sai na haushin dalilin da yasa suke mata dariyar kawai sai ta mi
e tana hawaye ta fice daga falon.

Baba Alhaji na tsaida ta amma ina, tuni ta bar musu wuri.

Bugu Alhaji ya kai wa Sadauki da carbi sai ya dube shi yana
an dariya ciki-ciki.

"Na ta
a jikarka ko?

Sorry."
Baba Alhaji ya mishi da
uwa.

"Ungo nan.

To ya ka ke so ta fadi?

Kai ai mai cin gyaranta ne ba ku tsaya daga kai har Rufa'i kuna mata dariya ba."
Sadauki da har lokacin bai bar murmusawa ba, bai ce komai ba sai kallom takardar jarrabawar Haulatun.

Gimtse dariyarsu suke yi suna duban juna, Radiya da Safina a zaune gefe
aya a falon, gefe kuwa Anti Mabruka ce tare da wata ba
uwa daga Malumfashi suna hira, sai ko yara masu tsalle tsalle a gefe.

Can dai duk kokarinsu sai da suka kwashe da dariyar labarin da Haulatu ta ba su.

Cike da takaici ta mi
e za ta bar wurin suka yi saurin ri
o ta.

"Don Allah ki yi hakuri."
Ganin hawaye a fuskarta ya sa kuma jikinsu sanyi.

Ta zauna gami da yin
wafa.

"Don kawai yana ganin ya je makarantar lilo shi ne zai tisa ni a gaba yana min dariyar kuskurena, kuma ku din da nake tunanin za ku fahimce ni shi ne ku ka wani biye masa ku na min dariyar ku ma."
"Mene ne makarantar lilo?"
in Safina don dagaske ba ta fahimta ba.

"Makarantar masu kudi mana.

Ni ai na gwamnati babu lilo.

Kuma sai mu je mu
araci zama bai fi malamai uku ne za su shiga ajinmu ba.

Mafi yawanci ma da Hausa ake koyar da mu, idan aka yi da turancin ma da yawa daga cikinmu ba sa ganewa.

Ni kam daidai gwargwado aka yi wanda bai fi
arfina ba, ko ban iya bada amsar ba, ina gane me aka ce.

Kuma na iya karantawa."
"Ki sha kuruminki.

Idan dai English ne in sha Allahu za ki iya shi.

Na yarda da ke.

Watarana sai Yaya Sadauki ya sha mamakin yanda za ki turance shi.

Akwai Antinmu ta makaranta, Malama Zuhra, lesson ta ke yi duk ran Asabar da Lahadi, dama ki yiwa Hajja magana a sanyaki wallahi, sosai ana gane koyarwar ta, ni na tabbata za ta maida hankali wajen ganin kin koya dakyau tunda tana son
an gidanmu sosai.

Tana da kirki kuma."
e baki Haulatu ta yi.

Ganin kamar ba ta son zancen ne sai suka sauya hirar har suka mantar da ita wancan.

Biki Buduri...

Ranar farko aka fara da wasan
wallo
na nisha
i tsakanin dangin Amarya da na Ango.

Su Haulatu kaf sun je filin, Najeeb da su Haidar da abokanansu su ne suka wakilci dangin Amarya don dama sun sani koda wasa manyan yayyunsu ba zuwa za su yi ba.

Haka aka yi abu cikin nisha
i da raha inda dangin angon Raudha da na Batulu suka zama team guda amma duk da haka sai da dangin
Amarya suka lashe wasan.

Aikuwa murna wajen su ba a magana.

An yi hotuna kafin kuma a watse.

A gajiye suka shigo sashin Hajja ita da Zaituna, Haulatu jiki na rawa ta
ibi duk abin bu
atarta a leda don ita kam can
angaren Baban kowa za su kwana, gidan su Radiya.

Su uku abin su sai ko wata
ar uwar Maman Radiya da ta zo daga garinsu Daura ana kiranta Munira.

Ko'ina a gidan da mutane, wasu
anmata ne tsaye na hira yayinda wata na gefe da wani daga cikin
an uwa maza tana hira sai ko yara masu guje-guje kamar ba tara da mintoci na dare ba.

Kungiyar su Najeeb kuwa suna can gefe ana buga musu akan
wallo da aka yi a ranar.

Ita dai ba ta bi ta kan kowa ba ta cigaba da tafiyarta.

Ta zo daidai
angaren Alh Ridwan inda sai ta gifta shi ne za ta
arasa na Baban Kowa, a lokacin Sadauki ke fitowa daga
ofar gidan, ta dube shi ta da sauri ta kauda kai tunano abin da ya faru jiya.

Shi kuwa tuni ya gane ta don haka ya kira sunanta.

Yanayin kiran da ta ji babu wasa a ciki sai ta juya ta tako tana kumbura fuska.

A ranta tunani take yanzu kuma me zai ce mata?

"Ina wuni." Ya amsa yana kallon ledar da ke hannunta.

Shi har ya manta ma da abinda ya faru jiyan.

"Ina za ki je?"
an mamakin tambayar ta dube shi sai kuma ganin ita yake kallo ta kauda kai tana duban
awayen Raudha da suka zo wucewa zasu nufi gidan Daddy Ridwan da duka amaren nan zasu kwana.

Su
in ma kallonsu suke yi da mamaki na ganin Sadauki tsaye da wata macen, sai kuwa suka shige ciki bayan sun gaida shi ya amsa ya kauda kai, babban burinsu su je su fesawa Jannat wacce duk wanda ya zauna da ita ko na sakanni ne sai ya san tana son Sadaukin.

"Amsa?"
Ta dube shi don ita ta tafi kallon
anmatan da suka shige suna waigensu.

Haka kawai yanayin kallon da ya bi ta da shi sai ta kasa jurewa ta kauda kai.

Ta
an yi gyaran murya.

"Gidan Baban Kowa wajen Radiya."
Ya jinjina kai.

"Ok, gobe ki kawomin results dinki na Jamb.

Idan ba ki gan ni ba, ki kira ni a waya."
"Na dauka sai bayan biki."
Ta tambaya.

Ya yi murmushi don sai a sannan ma ya tuna diramarsu ta jiya.

"No, ina son ganin score dinki na..."
Ai da sauri ta juya za ta bar wurin lokaci guda shi kuma ya ri
o hannunta ya dawo da ita baya, kusancin da har numfashinsu na cu
anya da juna.

Da sauri ta ja baya amma fa ta kasa
watar tsintsiyar hannunta da ya ri
"Kar ki damu, ba wanda aka haifa da iya wa.

Gradually, ke ma wataran za ki iya idan kin maida hankali a inda zan kai ki.

Na yarda da ke."
Daga nan ya saki hannunta yana mata murmushi, wannan murmushin shi ne Jannat ta gani da kuma kalmar
arshe da ya ce ya yarda da Haulatu.

Haulatu wacce mamakin kalmar da ma murmushin nasa ya kusan sanya ta suman tsaye, ba ta farfa
o ba sai da ta ji ya soma tafiya yana kiran sweet dreams.

Ta dube shi inaa, sai
eyarsa, tuni ya bar wurin da taku irin na wanda ya amsa sunan namiji.

"B...uban can!

Kai!!!

Kun ji kuma kun ga abin da na gani?"
Muryar wata ce a gefen Jannat, ya dauki hankalin Haulatu, a nan ne ta ankara da su, ba ta ce musu uffan ba ta kauda kai ga kallon banza da hararar da ta ga Jannat na jifanta da shi ta sa kai ta nufi sashin Baban kowa.

Ita a zatonta ma ko za su biyo bayanta ne ta nunamusu daidai take da kowacce a cikinsu sai dai kuma ta ji shiru.

A can ne ta labartawa su Safina duk abin da ya faru.

Sakin baki suka yi suna kallonta kafin su kwashe da dariya.

Radiya fa
i take.

"Kai kai kai!

Ki ce akwai kallo a gidannan.

Anti Jannat ta ganku?

Kin san irin mutuwar son Yaya Sadauki da ta ke yi?

Toh wallahi na ta haukar ina ga ya fi na Anti Zaituna.

Gwara ma ita Yaya Zaid ya san da zamanta, ita kuwa wannan Momi Nuratu ce kawai ta sani kuma ta ce ba ruwanta a cikin sha'anin."
"Ni sai na ga ma kamar sonki yake yi." Fa
in Munira tana duban Haulatu.

Haulatu ta dube ta sai ta ji gabanta ya fadi.

"Sona kuma?

Kin ga ki yi shiru ma kar wasu su ji ki.

Ni ban iya abin soyayya ba.

Duka duka ma nawa nake?"
Harararta Safina ta yi.

"Jimin ke.

Kin kusa ashirin kina batun nawa kike.

Tab, ai bana fatan soyayya ta yi maki ma irin kamun hauka na Aunties dinnan namu, ni kinga da sauki ko ba komai yawan addu'a ya sanya na rage damuwa hankalina kan shagalta da wasu abubuwan.

Amma fa son yana nan babu
arya.

Kai, ina ma dagaske Yaya Sadauki yana sonki, wallahi kun yi masifar dacewa."
Haulatu za ta yi magana kenan wayarta ta yi
arar shigowar sa
o.

Ta duba, ganin ba
uwar lamba ya sanya ta maida hankali.
_*If I could give you one thing in life, I'd give you the ability to see yourself through my eyes, only then would you realize how special you are to me.*_
(Idan ace zan iya ba ki abu
aya a rayuwa, da na baki damar ganin kanki ta cikin
wayar idanuna, a nan ka
ai za ki gane yanda ki ke ta daban a wurina).
Chapter 48 · 0% Book details