← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 109

Sashe 92

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kuma ci alwashin duk inda maganin zubar da ciki yake sai ta nemo shi ta gwada iya yin ta.

A ganinta da haihuwar abin da zai fa
a hannun matsafa gwara ta yi
arinsa ya bi rariya.

Da wannan
udurin ta shirya tsaf ta fita zuwa unguwa a motarta.

Kai tsaye tsohuwar unguwarsu ta nufa, ba ta mantawa akwai wata Nos da har haihuwa ta ke kar
a a gida a layin nasu.

Kai tsaye wajenta ta nufa, a yanda idanunta suke a rufe ta gwammace duniya ta yi mata dariya da dai ta cigaba da rayuwa
ashin inuwar mutum irin
an Mutuwa.

Sai dai a rashin sa'arta, ta tarar ba ta gida tana wurin aiki don haka ta yiwa yaran nata alheri da kuma kar
ar lambar wayarta, bayan fitowarta daga layin nasu ne zuwa titi ta hangi wata kamar Bahijja makwafciyar su Haulatu tana tsaye gefen titi, koda ta
arasa ta ga dagasken ita ce, nan da nan ta saki fuska, ta jima ba ta ha
u da wata idon sanin ba a dai cikin
an unguwar su Haulatun.

Bahijja dake tsaye ganin mota mai ba
en gilasai ta tsaya a saitinta sai ta
an ja baya.

Lura da hakan ya sa Hindatu sauke gilas suka ha
a idanu.

Ganin tana niyyar matsawa ne ya ba Hindatu tabbacin cewa Bahijja ba ta gane ta ba.

Ita kuwa Bahijja tuni ta gano ta a ganin farko saboda tana bin ta a shafukan sada zumunta, duk bidiyoyin da ta ke
orawa na ta har ma a wasu bidiyoyin da na mijin nata babu
aya da ba ta gani.

Ta dauki aurenta na cin amana, ta kasa yarda da Haulatu wacce ta ce mata Hindatun ba ta san mahaifinta ba ne, a ganinta ku
i babu abin da ba ya sanyawa.

"Bahijja, na san ba ki gane ni ba ko?

Hindatu ce fa, Big Mama aminiyar Haulatun Umma."
Sam ba ta san ma ta fito ta biyo ta ba sai da ta ji muryarta a gefe.

Ta ja ta tsaya tana wai murmushi bayan ta bi ta da kallon
asa zuwa sama.

"Oh, sannu fa Hajiya Hindatu, ashe kin yi sauyin da talaka ba zai iya ganeki ba ko?

Uhum."
Hindatu sai ta yi sak, a sanyaye ta ce.

"Kamar ya Bahijja?

Kada dai ke ma irin kallon nan ki ke yimin?

Na wacce ta yi auren ku
i?"
Wata dariya Bahijja ta yi.

"Kar ki
atamin lokaci domin ina da abin da ya fi sauraronki a yanzu.

Ai ke da a auren ku
in ka
ai ma kika tsaya da ba haka ba, aikin banza kawai, wacce ba ta san darajar aminta ba, kin auri mahaifin Haulatu ki zo kina wani
atu na banza.

Mts."
Daga haka ta ka
a kai za ta tafi, Hindatu ta yi saurin riko hannunta.

"Waye baban Haulatu?

Ban gane ba, waye baban Haulatu?!"
Ta karashe cikin daga murya mai nuni da yanayi na ru
ani.

Bahijja ta kwace hannunta tana kallon mutanen da hankulansu ya kai garesu.

"Malama kar fa ki taramin jama'a.

Kina nufin ba ki san mijinki
an Mutuwa shi ne mahaifin Haulatu ba?

Mijin Umma?"
Sai da Hindatu ta dafe
irjinta saboda tsananta bugun da ya yi, har wani jiri ta ji ya na neman kwashe ta, da wannan damar Bahijja ta samu ta tsaida napep ta bar ta, ganin yanda zufa ke wanke ta ga kuma jama'a duk wanda zai wuce sai ya kalle ta yasa ta komawa cikin motar da sauri, da
yar ta sanya seatbelt tana ambaton sunayen Allah.

"Alhaji Ibrahim
an Mutuwa?

Shi ne mijin Umma?"
Hannu na rawa ta dauki wayarta ta dannawa Haulatu kira sai dai a kashe, ta mance shaf Umma ta ce mata ta sauya layi kuma ba ta da layin, ba ta son kiran Umma, wani irin nauyi da kunyarsu duka ya mamayeta.

Ta yi kuka sosai kafin a karshe ta ja motar ta soma tafiya sai dai duk rabin tu
in a tunani ya ke tafiya.

Cikin iko na Allah, wani hatsari ya faru inda motarta ta bugi motar dake gabanta da
arfi don ta lula tunani ba ta ma san an tsaida su ba a danja, ita kuwa tu
i kawai take ya yin da motar dake gabanta ke tsaye.

Kanta ya bugi da sitiyari har sai da mararta ta yi waki irin azabbaben
ullewa, kafafunta duka sai da suka bugu sosai, tuni ta suma.

Motar dake gabanta kuwa ba karamin lahani ta yi musu ba, da ace akwai rai a bayan motar zai wahala ya fito a raye.

Tun zuwan Haidar ya sanar da ita kiran Baba Alhaji take cikin fa
uwar gaba.

Jikinta gaba
aya ya yi sanyi, ta san dalilin kiran amma kuma ta kasa gane meke zuciyar Ummanta.

Ita ba ta
ara zancen ba kuma ba ta sauya mata a komai ba.

Hajja tuni ta samu labari daga Umman, kuma
ari bisa
ari ta ji dadi ta goyi bayan al'amarin.

Ganin Haulatu ba ta da niyyar tashi ta wuce ne ya sanya Hajja kallonta.

"Ke Haule, kiran ne ba za ki ba ko me?

Ji min
a?

Za ki tashi ko sai na zo inda ki ke?"
an saci kallon Umma wacce ko kallonta ba ta yi ba tana aikin shafawa Hajja man zafi a kafafu sakamakon kafafunta da ke mata ciwo.

Ganin dai Umma ba za ta ce komai ba sai ta mi
e a sanyaye ta yafa gyalen da ta fita da shi makaranta da safe sannan ta fice.

Bayan tafiyarta ne Hajja ta dubi Umma dakyau.

"Wai ni Na'imatu kodai bakya son lamarin Sadaukin Alhaji da Haule?"
an mamaki Umma ta ce.

"Hajja me kika gani?

To ai ban ce komai ba."
an murmushi mai hade da dariya Hajja ta yi.

"Na'imatu kenan, ai koda ace ban yi zama dake a farkon rayuwa ba, yanzu tsawon lokacin da muka
auka tare ya ci ace na fahimceki.

Damuwar dai tun ta farko ce da ki ka yi
orafi a kai ba ta sake ki ba."
Umma ta yi shiru tana maida murfin man ta rufe.

Sadda ta samu Hajja da batun Haulatu da Sadaukin, ta yi ne don ta nunawa Hajjar abin bai kwanta mata a rai ba gudun abin da zai je ya zo, Hajjar kuma ta fahimce ta sosai amma ta nuna mata hakan duka ba hujja ce mai
arfi da zai sa ta dakatar da yaran ga samun farin cikinsu ba.

"Na'imatu, ki bar wa Allah komai ki taya
arki neman za
insa.

Sadaukin Alhaji a kaf matasan nan idan ka
auke Dakta (Khaleefa) ya fi su nutsuwa da sanin ya kamata.

Ban ta
a jin inda aka koka da halayyarsa ba, don haka kar ki yarda ki sanya damuwar komai a ranki.

Ballantana ma ina da tabbacin Nuratu da Ridwanun da ki ke tunanin ba za su amince da Haulatu ba, sai sun fi ki murna da wannan ha
in.

Ki cire damuwar nan a ranki mu aurar da Haulatu, kema fatan samun miji nake ta maki don in sha Allahu ba zan zuba idanu da
uruciyarki ki tsofe a gida ba sai dai kawai idan Allah bai nufeki da auren ba."
Tsam Umma ta tashi, an zo darasin da ba ta so ta ji Hajja ta
auko shi, Hajja ta yi dariya tana bin bayanta da kallo.

"Ka ji min wani shirme?

Au auren ne ba kya so a tayar da zancensa?

Ai shikenan."
Ta yi zaune gaban Baba Alhaji shi kuwa sai da ya ja ta da hirar makaranta kamar koyaushe har ta
an saki ranta sannan ya yi gyaran murya.

"Haulatun Hajja,
an uwanki ne ya zo min da wata magana shi ne mai dadi sai dai ban yanke hukunci a kai ba na fi son jin ra'ayinki tukunna."
an yi shiru yana
an tari.

Dama ita ta san inda zancen ya kwana, ya
ora maganarsa da jefamata tambaya.

"Ke kika amince da Sadauki ya fito neman aurenki?"
Kunya ya sanya ta murmushi kawai kanta na
asa, ya kula da hakan, a matsayinsa na babba kuma ya fahimci amsarta sai dai zai fi
aunar ji daga bakinta ta amsa.

Don haka ya ce.

"Haulen Hajja." Ya furta kamar yanda ya saba idan yana cikin raha.

"Na'am." Ta amsa.

"So nake ki ce min eh ko a'a.

Ni yau suruki kika maida ni ne?"
Ta girgiza kai tana murmushi.

"To ki fa
amin, kin amince da Sadaukin Alhaji, kin ba shi damar ya fito neman aurenki ko kuwa shi ma irin wadancan ne na baya ne, ba da yawunki ya zo ba?"
ara girgiza kai sannan ta yi magana murya a
asa.

"Na amince Baba Alhaji."
Tana fa
in haka ta yi saurin rufe fuska da tafukan hannuwanta.

Ya yi dariya.

"Ja'ira, yau ni kike jin kunya kuma?

Toh Alhamdulillah.

Na ji dadin wannan amsa taki kwarai, dama can na maki sha'awar miji irin Sadaukina, ban bayyana ba ne don kar ya zama na so kaina da yawa, ba na son tursasawa kowa, na fi so ace ban yiwa kowannenku dole ba a jikokina don dukkanku tsatso guda ku ka fito.

Allah ya za
a abinda ya fi alheri, tashi ki je, zan yi magana da iyayen naku."
Ba musu Haulatu ta mi
e ta fito, sai ta ji gaba daya zuciyarta ta yi wani sanyi, duka wannan fargabar ta kau, ta sani Umma kawai damuwa ce ta sanya a rai amma ba za ta
i aurenta da Sadauki ba.

Kuma ta tabbata idan da Ummanta ce, nan ba da jimawa ba komai zai wuce a ranta.

Kici
us suka yi da Anti Mabruka wacce shigowarta gidan kenan, yanzu ba ta zama kusan kullum sai ta fita, yau
in ma ta sha kwalliya kamar wacce ta dawo daga yawon gidan biki.

Ta gaishe ta, ita kuwa ta bi ta da kallon sama da
asa kafin ta ja tsaki ta maida duba ga
ar dattijuwar dake kuma da mahaifiyarsu.

"Inna ta yi bacci?" Ta amsa mata da eh , za ta wuce ta dakatar da ita.
Chapter 92 · 0% Book details