← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 109

Sashe 71

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safina kira take ita dai za ta bi su, amma Yaya ta ce sam tunda dai karatu za su soma da zarar sallah ta wuce.

A lokacin suka tsinci sallamar Jannat.

Gaba daya suka amsa ta shigo falon ri
e da hannun
anin Safina, da fara'a Yaya ta ke fadin.

"Wa nake gani yau a gidan?

Jannat?

Sannu da zuwa."
Jannat kuwa ta shanye borin kunyar, dama gaskiya takan jima ba ta
ullo ba, Safina kuwa tuni ta ji a jikinta ko mene ne ya kawo Anti Jannat gidan ba abin alheri ba ne tunda dai ba wani jituwa Maminta ke yi da Yaya ba.

Bayan sun gaisa da Yaya, ita ma ta gaidata.

Ta amsa fuska a sake.

Sai da aka shiga hira, Yaya ta sakar mata kamar ba ranar ce ta soma zuwa gidan ba, a karshe ta mike ta bar su da Safina da zummar shiga kicin duba girki.

Wannan damar ita Jannat ke jira don haka ta gyara zama da murmushi ta dubi Safina.

"Congratulations.

Ashe dai
awarki Haulatu da Yaya Mu'az mun kusa shan shagalin bikinsu?"
Safina ta ji maganar tamkar saukar aradu, kirjinta sai da ya shiga bugun da ba ta yi zato ba.

Har wani bibbiyu ta soma ganin Jannat din.

Ta ha
iyi miyau mai
aci.

Haulatu da Yaya Mu'az?

Wannan tatsuniya ce kawai Anti Jannat ta shirya.

"Oh, na ji kin yi shiru.

Ba ki da labari kenan?

Uhm.

Ai magana har ta je kunnen iyaye nima ta bakin nawa iyayen na ji shi, ashe wai tun zuwanta ba jimawa suka fara soyayyar, abu kamar wasa har Yaya Mu'az ne ya fa
amusu da amincewar Haulatun.

Abin dai ni ya yimin dadi, ko babu komai can gasu gada, ba ita ba tunanin lashe kurwar Yaya Sadauki."
Wani murmushi mai kama da ya
e Safina ta yi, idan ba wanda ya yi mata farin sani ba ma, ba za a kawo ya
en ba ne.

Ta dubi Jannat dakyau.

"Kema dai Anti Jannat, ki na tunanin magana za ta kai ga tsawo haka har ke da ba kusa da Haulatu ki ke ba ki ji, ni kuma na kasa ji?

Uhum, to wannan zancen tun ma kafin abu ya yi nisa muke da labari ni da Radiya.

Haulatu ta cancanci na sadaukar mata da komai, don na sani watakila labari ya riskeki cewa na ta
a son Yaya Mu'az ne a baya ki ke tunanin hakan da zan ji zai min zafi a zuciya ko?"
Ta na kaiwa nan ta yi
ar dariya.

"Ko kusa, ai babu yanda za'a yi mu
oyewa junanmu sirri.

Kuma ina yi musu murna da fatan alheri koyaushe.

Ni tuni na rufe shafin Yaya Mu'az a raina tun ma kafin faruwar lamarin.

Ke ma Allah ya sa ki gane."
Jannat tuni ta sha
a, babu ma kamar furucinta na
arshe.

"Allah yasa na gane me?

Me kike son fadi Safina?"
Safina ta yi murmushi.

"Kin san akwai ciwo son wanda ba ya sonka."
Ta kula dai abin da ta zo da shi bai samu matsuguni a zuciyar Safina ba, ta ma gane yarinyar muguwsr marar mutunci ce, wato ita za ta gasa mata magana ma?

Don haka ta mi
e ranta na suya da zummar tafiya, ya kuma yi daidai da fitowar Yaya daga kicin.

"Ah, me nake gani?

Ba dai tafiya za ki yi ba?

Ki jira a sha ruwa mana."
Da ya
e ta amsa.

"Lah, Yaya ki yi hakuri, Mami ta ce kar na kai dare.

Dayake dama unguwarku na zo gidan wata
awata shi ne na biyo mu gaisa.

Ni ba na ma azumin."
Yaya ta yi murmushi.

"Hakan ma ai kin sada zumunci.

Jira ina zuwa."
Daga haka Yaya ta wuce zuwa
akinta, gidansu gini ne flat marar bene.

Amma ya tsaru iyaka.

Safina kuwa ta fake da daukar wayarta ta saka a flight mode a fakaice yanda Jannat ba za ta fahimta ba, daga nan ta kara a kunne ta ja mintuna kamar biyu sai ta soma magana.

"Amarsu ta Ango ba da kanki a sare."
an yi shiru tana ji a jikinta idanun Jannat na kanta.

Can ta kara cewa.

"Na fiki murna rabin rai.

Ai ranar akwai kallo, ke akwai fa magana."
Daga haka ta mi
e ta dan dubi Jannat wacce ke tsaye tana cika da batsewa, murmushi ta yi.

"Anti Jannat ki gaida su Mamin."
Daga haka ta wuce zuwa
akin da ya kasance na ta wanda har kullum idan ta zo gidan nan take sauka.

Tana ba da baya kuwa sai ga Yaya da
atuwar leda.

Ta mi
awa Jannat.

"Ga wannan ba yawa kya yi adon bayan sallah tunda yanzu kam sallah ta gabato." Ta
arashe da dariya, ita ma Jannat ta yi ya
e, kar
a ta yi da godiya sannan ta fice.

A can
akin kuwa, Safina kawai gado ta fada ta shiga kuka mai sosa rai, dagaske ne abin da ta ke ji?

Duk abin da Jannat ta fadi dagaske ta ke ba wasa ba?

Ya za'a yi ta tabbatar?

Ita sam ba zafin soyayyarsu ta ji ba kamar irin yanda Haulatun ta raina mata hankali.

Ta rasa tunanin da ya dace ta yi don haka ta kunna wayarta ta kira layin dan uwanta Haidar.

Yana
agawa bayan sun gaisa ta tambaye shi ko ya ji wata magana a gida dangane da Yaya Mu'az da Haulatu?

Ya kasa magana sanin da ya yi tana son Mu'az din, sai da ta matsa sosai kafin ya amsa.

"Yes, dazu bayan Azhar na ji Maama na cewa wai Uncle Faisal ya zo wurin Baba Alhaji yake shaida masa batun soyayyarsu kamar dai yana nemawa
ansa aurenta, ya ce sun jima wai suna son juna, Baba Alhaji dai ya ce a bar komai zuwa bayan sallah kuma sai ya ji ta bakin Haulatun.

Ita ma dai Maama na ga ranta ya
aci sosai.

Sai dai na fi ganin laifin
awarki, wannan wane irin cin amana ne?

Duk zamanku tare ashe soyayya suke yi ta
oyemana?

Bayan ta san irin son da kike mishi?"
Runtse idanu ta yi tana ji
irjinta na suya, ga kukanta da ya kasa tsayawa
arshe ma ta gaji da ha
urin da Haidar din ke ba ta, ta katse kiran.

"Meyasa haka Haulatu?

Me na yi maki?"
Haka ta furta a fili cikin yanayi na kuka.

A can
asan ranta tana kokarin yi mata uzuri amma kuma ji ta yi kawai ta kasa, so ba
arya ba ne, hakika tana son Yaya Mu'az tun ma ba ta san me ake kira da son ba, tun ba ta mallaki hankalin kanta ba.

Wannan kauna ce tsaftatacciya.

Da ace wata ce ma daban ba lallai ta ji wannan zafin ba.

Hango murmushinta da kuma yanda ta ke yawan nunawa Haulatun irin matowar da ta yi akan Yaya Mu'az din kawai take, wato wannan
arfafa gwuiwar da take mata, wannan addu'ar da take ikrarin tana taya ta da shi, duk na bogi ne?

Kanta ta ke yiwa?

Kaunar da ta ke nunawa kamar tana yiwa Yaya Sadauki, duka ba gaske bane?

Ta sa a ranta har abada ba za ta cewa Haulatu komai ba, kuma za ta danne wannan
acin ran a rai, za kuma ta yi kokarin rage shiga sabgarta.

Dakyar ta saita kanta ta shige bandaki ta gyara fuskarta ta fito zuwa falon inda ta tarar Yaya da mai mata hidima suna ta aikin jera kayan shan ruwa.

Ita ma ta fada kicin din ta shiga taimaka musu, Yaya tsaf ta karanci damuwa a saman fuskar
iyarta, ta kuma ga sauyin da idanunta suka yi, shaidar ta ci kuka ta
oshi.

Ba ta ce mata uffan ba har mahaifinta Dakta Hashim ya dawo suka sha ruwa.

Tana ta kasa kunne ko za ta ji ya yiwa Yaya zancen auren Mu'az din da Haulatu tunda Jannat ta ce iyaye sun san da maganar, amma sai ta ji shiru.

Da wannan ta gane mahaifinta bai kai ga ji ba.

"First Love, meke faruwa?

Naga yanayin fuskarki kamar kin yi kuka ko?".

Fadin Dakta Hashim yana kallon Safina cike da kulawa.

Ta yi murmushin da bai
arasa zuci ba.

"Babu komai Dad.

Kawai kaina ke ciwo."
"Kina gidan Dakta ki ke zama da ciwon kai ba ki nemi magani ba?

To Sweetheart laifinki ne."
Sai ma ya ba ta dariya, shi dama ba ruwansa akwai son raha.

Yaya tun tana jin nauyin ya dinga kiranta da wannan suna gaban yara har ta saba.

Haka ya yi ta jan ta da hira har ta saki jiki, suka shiga magana game da karatunta, matsayinsa na Uba mai zurfin ilimin addini da na boko, ya yi mata nasiha sosai dangane da kama kai.

Har da daukomata labarin aurensu da mahaifiyarta, ana zuwa ga
ar Yaya ta mi
e tana fadin.

"To wannan ba da ni ba.

Ahyaan ku tashi mu je a watsa ruwa a sauya kayan nan."
Ahyaan na dariya ya mike, wato dai Yaya ba ta son su sha labarin.

Daga Safina sai shi a wajen Yaya.

"No bar su na ba su labarin irin nutsuwa da kamalar da na gani tattare da ke mana har ki ka siye zuciyata."
Ita tuni ma ta yi gaba tana murmushi da girgiza kai.

Hashim ba zai ta
a girma ba, kullum yana jin sa kamar wani matashin saurayi.

Duk wannan budurin da ke a babban gida, babu
aya da Haulatu ta ji.

Hajja ita kanta zancen bai zo kunnenta ba.

Sai bayan sallar isha'i suna zaune a na kallo, sai ga Najeeb ya shigo wai Baba Alhaji na kiran Haulatu.

Kiran bai wani ba su mamaki ba tunda a wasu lokutan musamman idan ya kwana biyu bai ji gan ta ba, yakan turo a duba masa ko tana lafiya.

Ta amsawa Najeeb kafin ta mi
e duk da tana jin dadin kallon film din hausan da suke haka ta hakura ta dora dogon hijabi saman riga da wandon da ba su matse ta ba, ta fita.

Tana shiga sashin Baba Alhaji, suka yi kici
us da Maama, kallonta ta yi bayan amsa gaisuwarta ta ce.
Chapter 71 · 0% Book details