← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 109

Sashe 68

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wato ya na
aunar Maama, irin
aunar da bayan mahaifiyarsa Momi Nuratu to fa babu wata sai ita.

A farko abin da ke ransa kenan da ya shigo, ya na so ya nemi shawararta don ya kasa danne so, ba ya jin ma akwai yanda zai yi ya cigaba da
oyon abin da ke ransa game da Haulatu ba tare da ya cigaba da amayo shi ba.

Sai dai ya ji nauyin ya yi wa Maama zancen, aka yi katari ita da kanta ta furzar.

"Nima na yi wannan hangen Maama."
"Yauwa, ka yi kokarin shawo kanta, ka kuma bari sai komai a tsakaninku ya daidaita sannan ka je mataki na gaba.

Allah ya za
amaku abin da ya fi alheri."
Ya amsa da amin, Mabruka ta juya ta koma sama cike da tunanin wace ce wannan da Sadaukin ke so ake batun ya shawo kanta?

Ta sani dai ba Jannat ba ce tunda ita yanzu ma tana shirin shiga aji biyu a jami'a.

To wace ce?

'Ko a cikin
an matan nan ne masu shiga jami'a?

Ko Haulatu?'
Wata zuciyar ta jefamata tambayar, sai ta ji wani irin zafi a ranta.

Wai da ace yaran nan na ganin mutuncinta kamar yanda suke ganin na Maama, da tuni ta san wacce ake zance a kanta ba wai ta tsaya kame-kamen banza ba.

Ta ja tsaki har ta koma dakinta zuciyarta sam babu dadi, balle ma idan ta tuna nan zuwa bayan sallah mai son auren Maama zai fito a yi komai, wasu hawaye suka zubomata.

Kowa na aure har matasan yaran yan uwanta da take nan aka haifa amma ita duk wanda ya zo da zummar aure sai ya fasa kamar wanda ake kora.

Tun ba ta biyewa bin malamai har ta soma, kullum yanzu cikin zargin mutane take da daukar alhaki don wani Malami ya ce mata na kusa da ita ne ya yi mata asiri.

Sau da yawa ma tunaninta kan ba ta cewa Maama ce ta yi mata asirin.

Shiyasa nan duniya ta ke jin tsanarta kai ka ce ba ciki guda suka fito ba.

A yanzu ji take ina ma akwai yanda za'a yi wanda zai auri Maaman ya dawo da maganar kanta.

'Ke Mabruka, tsaf zai yiwu matukar kika koma wurin Malam Mai Carbi.'
Wani
angare na zuciyarta ta raya mata, ai kuwa ta yi zumbur ta dauki wayarta, kai tsaye Malamin ta kira ta zayyane mishi bu
atarta.

Ya ce zancen ba na waya ba ne, ta zo ta same shi a gidansa gobe amma babu abin da ba zai gagara ba.

Nan suka yi sallama ta ajiye wayar zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito don dadi.

Ai ko ba ta aura ba, ta rantse Maama ta gama aure ita ma a duniya.

Gwara su zauna su yi ta kallon juna.

Bayan Magriba
anmatan na zaune a dakin kwanan Safina dake faman ha
a kaya don gidansu za ta je yin babbar sallah.

Haulatu da Radiya suna taimaka mata amma zu
atansu duka ba dadi ji suke kamar su bita su tafi wurin Dakta Hashim da mahaifiyarta da ake kira Yaya.

Tana da kirki ita ma kwarai.

Ga kawaici da hakuri, ba ta ta
a nunawa duniya Safina
iyarta ce, ta maida ri
onta kacokam ga Maama.

Ita ce
iyarta ta farko,
annenta biyar cif da ita cikon shida.

Haulatu ta fisge rigar da ke hannun Safina.

"Feenah." Ta furta, sunan da sukan kira ta kenan a wasu lokutan.

Ganin sun tsaya su na dubanta ta
ora.

"Wai ma ba za ku tambaye ni game da abin da ku ka ji Yaya Zaid na fadi
azu da safe ba?"
Suka dubi juna suka sa dariya ita kuwa ta hau harararsu.

"Ah, mene na tambaya?

Kin san dai mun gane ko?"
Fadin Radiya.

Safina na
arawa da "Ai shi ne."
"To na rantse ba ku ga daidai ba.

Abin da ku ka gani ba haka ba ne."
Nan ta labarta musu duk abin da ya faru tun ma farkon sa
onnin da ake aikomata a waya har zuwa yau din."
Jikinsu ya yi sanyi.

"Amma Yaya Zaid shi ma dai ya na da mantuwa.

Yanzu duk abin da ya faru a baya ya manta da har ya ke tunanin wani zai kalle shi ya goyamishi baya akan ki?

Wane irin kuri da cika baki ne bai yi ba na nuna shi fa ba ya ra'ayin auren zumunci.

Hum, wai ma, har ya manta da Anti Zaituna?"
Radiya ta ta
e baki.

"Ke ma dai Safina kin manta su maza ba kunya suka cika ba?

Ai idan su na son abu idanunsu rufewa yake yi.

Ni kam ba na maki fatan ma mutum irin Yaya Zaid, sam halinsa na ri
o na tsana, amma idan an cire wannan ba shi da matsala."
"Hum, ai ko mene ne Radiya, ni ba zan ta
a ba shi fuska ba har abada kuwa.

Ashe ma kaunar da nake yiwa Anti Zaituna na
arya ne.

Hum, wai ma dagaske yake shi aurena ya ke so yi, bai dubi da fuskar da zai kalli Hajja ba ma?

To koda ina ra'ayin soyayyar nikam ban ga wanda zan iya so ba."
"Har Yaya Sadauki?"
Tambayar da Radiya ta jefomata ne ya sa ta jin wani irin faduwar gaba, sunansa kadai idan ta ji yana ma ta yawo a kwakwalwa ta ji ta wata daban.

Ballantana kuma idan ta ji muryarsa ko ta yi tozali da shi.

Ta kauda kai daga kallon tuhumar da suke bin ta da shi jin sun kashe mata baki, da
yar ta tattaro jarumta ta ja guntun tsaki.

"Ni wai meyasa ku ke min wannan tunanin?

Shi ya ce maku yana sona?"
"Ba fa batunsa ake ba, ke muke tambaya idan misali ya ce yana son naki, za ki amince?"
Ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba ta dauki wayarta tana
arin mi
ewa suka yi saurin dakatar da ita daga mai warce wayar sai mai ri
o hannunta dole ta fa
a gadon suna dariya.

"Banzaye, ni wallahi duk kun takuramin.

Ke ba za ki mana batun Yaya Mu'az ba."
Safina ta yamutsa fuska cike da jin wani iri a rai saboda fami da aka yi mata.

"Ni kinga na fa ha
ura da shi.

Na kula son maso wani nake yi.

Don rannan na ji yana cewa Maama wai ta baza idanu yana dab da gabatar mata da wacce zai aura kuma a family dinnan take.

Ban baku labari ba saboda ban ga amfaninsa ba tunda dai dama ni ke so ba wai ni ake son ba.

Na soma rage sonsa, a hankali ma zan daina gaba
aya."
"A family?

To wa yake so kenan?" Radiya ta cafe zancen, ita ko Haulatu sai ta ji duk ta tsargu, ko dai ta ba su labari ne?

Kai ba za ta iya ba.

Gwara idan zancen ya fito ta nuna ba ta ma san ita yake so ba sai da ya furta din.

Mutumin ma da sun bar ko waya balle tura sa
o na waya?

"Ohon masa.

Shi ya sani, in sha Allahu ma a wannan azumin na Zhul-Hajj zan dage da addu'ar neman za
in Allah."
"Hakan ya fi maki, Allah ya yi mana za
i na alkhairi." Fa
in Radiya karo na biyu, suka amsa da amin.

Wannan batun ne ya kore tambayar da suke jiran amsarta daga Haulatu, suka hau hirar saurayin Radiya wanda ya ce zai turo da zarar sallah ta wuce.

Sai wuraren tara na dare suka rabu da junansu, nan ma sai da Umma ta dokawa Haulatu kira akan ga dawo dare ya fara kafin su yi sallama da juna.

Tare suka fito Radiya ta yi nasu
angaren ita ma ta nufi
angarensu.

Tana tafe tana tunanin maganar da Safina ta yi akan wai Mu'az ya sanar fa Maama yana da wacce ya ke so a cikin family.

Kamar an ce ta
ago daga kallon
asa da ta ke yi ta hango shi ya na nufo ta.

Nan da nan ta tamke fuska ta
ara sauri.

"Wannan gujemin da kike yi, ba shi zai sa na fasa niyyata na kai maganarmu gaban iyaye ba."
Cak ta ja ta tsaya, kenan ta tabbata ita Mu'az ke nufi zai gabatar matsayin wacce ya ke so?

Ta juyo tana murmushin takaici gami da watsa mishi kallon ka yi ka
an kafin ta soma magana.

"Ni dai ka ke nufi?

Toh bismillah, ai ga fili ga mai doki.

Ina ce a gidannan ba a auren dole ko?

Kuma ba za'a fara a kaina ba Yaya Mu'az, ni na san wannan.

Ka je ka tunkari duk wanda ka so tunkara da zancen aurena."
"Me na yi maki kika tsane ni wai Haula baby?

Me ya yi zafi har haka?

Mene ne laifina don na ce ina sonki please?

Ba ki da tausayi wai?"
Ta harareshi da haushin kirata Haula Baby da ya yi.

"Haulatu ne sunana.

Daga kai har Yaya Zaid na rantse ku fita idona in rufe.

Na ce maku bana sonku, ai idan ma kai kana da tausayin Yaya Mu'az, ya ci ace ka tausayawa Safina tunda na san ko ba a fadi ba ka san tana sonka.

Mace ce mai kunya da kauda kai, hakan ya sa ka za
i nunawa duniya ba ka fahimci tana son naka ba.

Kuma ni yanzu ba na mata fatan ma ta aureka don ba ta dace da kai ba, zan fi kaunarta da wanda ya san tana sonsa kuma ya girmama wannan son."
"Wait, Safina ke sona?

Dama saboda ita ce ki ka juyamin baya?

Kuma ma wane Zaid din?

Zaid ke sonki?

Wow!"
arashe da jin mamaki da wani murmushi mai ciwo har yana
an tafa hannuwa.

"Wannan kuma matsalarka ce.

Sannan ka sani da Safina da babu ba zan ta
a sonka ba."
Tana kai wa nan ta juya a fusace ta bar shi da bin ta da kallo.

Ganin babu wani amfanin tsayuwar tasa ga su Najeeb a gefe da ke hira da musun ball daga can
ofar gidan tare da abokansu, ga dukkan alamu ma sun hankalta da su a tsaye.

Sai ya juya ya bar wurin gwuiwa a sake.
Chapter 68 · 0% Book details