← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 109

Sashe 97

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abu Affan, ba za ka ci abincin ba kai?"
Yana so ya ce mata ba ya son sunan da ta ke ambatonsa da shi, amma kuma ya kasa, haka kawai tana wani maida shi tsohon
arfi da yaji, eh ya haifi Affan, amma meyasa ba za ta kira shi da Yayan ba kamar yadda sauran
annen ke fa
i?

Bai kalle ta ba a can
asa ya amsa.

"Alhamdulillah.

Ki ci."
"Toh."
A nutse ta ke cin abincin kamar yanda shi ma ke tu
in a nutse.

Yana yi ne gudun kar ya yi takun da zai sa ta kasa cin abincin.

A hankali ya ke satar kallonta, komai cikin nutsuwa ta ke yi.

Ta ci sosai sannan ta rufe ta maida leda, ta yi amfani da tissue ta goge hannun wanda garin cin kazar ta
ata, ta kora ruwa ka
an saboda ba ta son ta fitsari ya kama ta a tsakar daji.

Jingina kai ta yi jikin kujerar a hankali kuma tun tana bin hanya da kallo bacci ya sure ta don a kwanakin sam ba ta samu ta runtsa sosai ba tsabar zumu
i da kuma yawon shiga kasuwa siyayya.

Khaleefa jin shirun ya yi yawa ne ya sanya shi
an waigo kansa.

Fuskarta na kallon saitinsa, bacci take yi cikin kwanciyar hankali abinta.

Ta cire gilashin ta
ora bisa cinya, ya maida kai ga kallon titi sannan ya
ara juyowa ya dube ta.

Ya maimaita hakan har bai san adadi ba, shi kansa bai san me ke
aukar hankalinsa ga kallon ba, amma kuma duk sadda ya dubi fuskarta yakan ji ba ya kaunar ya daina kallo.

Sallar Magriba ce ta sanya shi tsayawa a wani masallacin gefen hanya cikin wani
auye.

Jin tsayuwar motar ya sanya Zaituna farkawa, dubanta ya yi.

"Ina zuwa, zan yi sallah ne."
Ta gya
a kai sannan ya fice.

Wurin akwai jama'a sosai, kamar ma kasuwa ce, kowa dai harkokinsa yake.

Wayarta ta fiddo a jaka ganin tana ta ringing.

Hajja ce.

Tambayarta take ko sun
araso, ta ce mata sun dai kusa kawai don ba ta ma san ina ne nan ba.

Suka yi sallama bayan ta musu fatan isowa lafiya.

Ba ta koma baccin ba har Khaleefa ya dawo.

Sai bayan ya cigaba da tu
in, wani baccin ya
ara kwashe ta.

Suna isa cikin garin Katsina, nan ma ba ta farka ba har sai da ya shiga cikin gidan nasu ya tsaida motar, ya kula dagasken gaske bacci ne a kanta.

Farfajiyar gidan babu kowa an tafi masallaci gabatar da sallar isha'i.

Zaituna kuwa jin kamar a tsaye suke ya sanya ta farkawa bakinta
auke da sunan Allah.

Idanuwanta cikin na Khaleefa suka fa
a, ta yi saurin mi
ewa zaune tana rarraba idanu, ba ta son yin doguwar magana saboda ta san zai wahala bakinta idan ba ya
an tashi sakamakon bacci da ta yi don haka ta kauda kai.

"Ashe mun iso?

Abu Affan ba ka tashe ni ba."
Madadin ya ba ta amsa sai kawai ya bu
e motar ya fita, ganin haka ita ma ta fito.

Shi kuwa akwatin kayanta ya ciro.

Har a sannan sallah ake suna ji daga masallaci ba a idar ba, zagayowa ta yi ri
e da ledojin abincin da ya siya mata da zummar kar
ar akwatin, don a ganinta ba girmansa ba ne ya ri
e akwatinta.

Fuska a
aure ya ce.

"Ki je ciki, zan taho da shi."
an kalle shi tana murmushin da har gefen kumatunta na lotsawa, Khaleefa ya sauke ajiyar zuciya.

A zuciyarsa ya furta masha Allah.

"Nagode sosai Abu Affan."
Daga nan ta juya ta yi gaba ta bar shi da bin ta da kallo kafin ya numfasa ya rufe motar shi ma ya shiga ciki.

Ya kula ma kamar da gayya take fa
in sunan da bai wani yi mishi armashi ba.

Umma da Hajja baki ya
i rufuwa suka tarbi Zaituna da murnarsu.

Khaleefa kuwa ko zama bai yi ba bayan ya kawo akwatin ya yi musu sallama ya wuce.

Zaituna sai da ta yi wanka ta sauya audugar mata dake jikinta kafin ta sauko
asan tana yin video call da Haulatu inda take yaba kyawun da ta ga ta yi, fadi take.

"Sis kin sauya baki daya, har wasu kumatu na ga kin yi."
an farr da idanu Haulatun ta yi mata.

"Ka ga Mrs Abeed Ridwan Malumfashi."
"Yes, ita ce."
Suka yi dariya, Zaituna cikin sauri ta maida fuskar wayar ga Umma da Hajja da ke zaune, ai tuni Haulatu katse kiran baki
aya.

Umma murmushi kawai ta yi gami da girgiza kai.

Hajja ko cewa take.

"Ja'ira, wato kam Sadaukin Alhaji ya sauya min ita ko?"
Umma ba ta amsa ba sai Zaituna dake kare
ar uwarta.

Momi Nuratu ta zubawa takardar idanu tana karancewa ganin babu wani abin tashin hankali a saksmakin gwajin ya sanya ta murmushi gami da sauke ajiyar zuciya lokaci guda tana mai godiya ga Allah.

"Alhamdulillah.

Na ji da
in hakan.

Ni dama ba ni da kokwanto, sai dai ka sani, tunda har Rahma ta soma haka, gwara a yi abin da zai toshe bakinta da
ananun magana.

Koda dai, nasan ko hakan ma ba a tsira ba."
Sadauki ya yi murmushi yana mai amsawa da hakane.

Ita kuwa Momi Nuratu ta saka a rai duk radda Mamain Khaleefa ta
ara zuwa da wani batun to fa ba za ta
yale ta ba.

Tunda ba ta san kara ba.

Washegari tun da wuri Zaituna na kammala shiri ta shiga
angaren kowa a gidan aka gaisa, kowa ya gan ta dai ya hau murna da washe ha
ora.

Yarinya ce mai shiga rai tun a baya, ba ta da girman kai ko ka
an.

Sai da ta yi dagaske kafin ta samu kanta a
angaren Momi Nuratu don ita ma gwanar son hira ce.
angaren Baban Kowa nan ne
arshen inda ta shiga, sun gaisa, Radiya ma ta fito ta hau ihun murnar ganinta suka rungume juna.

Ranar ba zata shiga makaranta ba hakan yasa Zaituna ro
on alfarmar ta yi mata rakiya gidan Maama.

Khaleefa ya tamke fuska sosai yana kallon Jannat da ke kwance tana wani nishi kamar mai na
uda ya yin da Mami ke tsaye a kanta gaba daya ta ru
e, fa
i take.

"Ka tsaya kallonta kamar ba jininka ba, matsayinka na likita ba za ka yi kokari ka auna ta a san matsalarta ba?"
Bai ko kalli Mamin ba, idanunsa a kan Jannat wacce Nos ke tsaye a kanta tana
an tatta
a hannu da goshinta.

"Ku je waje Mami, bari na duba ta."
Ba musu Mamin ta fita, Nos ta bi bayanta.

"Tashi zaune ko na karairayaki." Ya fa
i murya a kausashe.

Jannat duk da irin ru
ewar da ta yi, sai da ta daure gudun kar a gano
arya take yi, ta
ara wani juyi da ri
e kai.

"Wash!"
"Za ki tashi ko sai na wanka maki mari?"
Ai bai kai ga
arasa zancen ba ta yi zumbur ta mi
e zaune tana
uni.

"Don ba ki da mutunci akan
a namiji ki ke tayarwa da tsohuwarmu hankali?

Toh na rantse maki matu
ar ba ki bar wa
annan shirme da shiriritar ba sai kin koma gidana da zama na maki hukuncin da ba ki ta
a zato ba.

Banza kawai da ba ta san ciwon kanta ba.

Ni na sani babu uwar abin da ke damunki, tsabar kin raina mutane ne ki ke wannan
ananan iskance-iskancen.

Daga yau kika
ara bari na ganki a asibitin nan saboda mutumin da ba ya ta taki sai na maki allurar mutuwa kowa ya huta."
Ai fa nan ta hau rarraba idanu, hawayen suka wanke fuskar.

Dagaske yake babu ciwon komai tattare da ita, ta yi ne don Mamin ta gane ba za ta iya rayuwa babu Sadauki ba.

Hakanan Abbanta wanda sam ya
i goyamata baya.

Ganin hawayen sai kuma ya
an ji tausayinta, zama ya yi a gefe ya shiga yi mata nasiha da nuna mata illar auren wanda ba ya sonka.

Jikinta ya yi sanyi, har wani
aci
aci take ji a ma
ogwaronta, dagaske dai ta rasa Sadauki?

"Yaya, Allah ya ban wanda ya fi Yaya Sadauki." Ta na kaiwa nan ta fashe da kuka sosai, ya
an rungume kafa
arta yana rarrashinta.

Son maso wani ciwo ne babba, ta kuma ji har a ranta ta
ura da shi
in.

Khaleefa ya fi kowa a gidan kusanci da Sadauki, tunda har ya rantse mata akan cewa Sadauki ba zai aure ta ba, ta ji ta yarda kuma za ta ha
ura da shi.

Amma fa ko bikin ba za ta iya zuwa ba ko don su Fa'iza da za su yi mata dariya.

Har abada kuma ba ta ga zumuncin da za ta yi da Haulatu ba, a cewarta.

Ya dai cewa Mami ciwon kai ne kawai sai damuwa, ya rubuta magunguna suka fito tare tana lalla
iyarta har tana mata ra
a a kunne kan cewa kar ta wani damu, ta san idan an yi gwajin nan Momi Nuratu ba za ta amince
anta ya auri Haulatu ba don tana ji a jikinta yarinyar na da cutar
anjamau.

Ita dai Jannat ba ta ce uffan ba, ba za ta
ara biyewa Mamin ta dinga kwa
aita mata abin da har abada ya fi
arfinta ba don haka ta yi gaba zuwa mota ta bar Mami tare da Khaleefa.

Zaituna sakin baki ta yi bayan sun gama murna da farin cikin ganin juna da Haulatu, ta yi wani kyau, fatar nan sai she
i take yi, ga wani
amshi dake tashi a jikinta duk inda ta gifta koda kuwa ba ta shafa turare ba.

Ko'ina ya
ara cika dam dam.

Duban Maama ta yi murya a shagwa
e ta ce.

"Ni ma Maama ke zan sa ki kira a yi min gyaran jiki idan aurena ya zo."
Maama ta yi dariya, idan da sabo ya ci ta saba da rashin ta idon Zaituna, sam ba ta mata kallon uwa sai wata abokiyar kuka da dariya.

"Magana ta
are
ata, yanda ki ka ce haka za'a yi.
Chapter 97 · 0% Book details