← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 109

Sashe 7

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare misalin
arfe tara tana kwance saman
ar katifarta ta yi shiru gami da zubawa rufin kwano idanu.

Dagaske Hindatu itama tsoronta take ji?

Ashe ita ce kawai ke zaune da ita da zuciya guda?

Kodai ta yarda da abin da mutane suke yi mata
azafi a kai ne?

Ta juya tana fuskantar tagar
akin, idanunta fes akan
farin watan da ya hasko su.

To idan ma hakan ne, ai bai kamata ta ga laifinta ba, komai da ke faruwa a rayuwarta silar tsatson da za ta fito ciki ne.

Nan da nan hawaye suka wanke mata fuska.

Ba zato ta ji hannun Ummanta a kan
afafunta.

"Haulatu, tashi zaune mu yi magana."
Ta share hawayen gudun kar Umman ta gani sai dai tuni ta makara, zama ta yi jikinta duk a mace ta
urawa ledar
akin idanu wanda duk ya cinye ana ganin
asar dake a
asa.

"Tun da yamma da na shigo gidan nan na fuskanci akwai abin da ke damunki amma
arin nunamin kike babu komai.

Kina da wacce ta fi ni ne?"
Ta girgiza kai, kukan da ta ke dannewa a
irjinta kawai ta saki gami da fa
awa jikin Umma.

Ba ta hana ta ba, sai da ta yi mai isarta ta yi shiru kafin Umma ta
ago kanta.

Cikin murya ta rauni irin na Uwa ta ce.
amin meke faruwa?"
Ta labarta mata yanda Hindatu ta yi mata
oyon sabon saurayinta har tsawon sati biyu, da kuma nunawa Umma abu ne da ba su yiwa juna.

Ita komai da ya dangance ta Hindatun ta sani.

Ta
ara da fa
"Umma na soma zargin ko dai itama tana guduna ne saboda
azafin da jama'ar unguwa ke yimin wai nima yar bariki ce zan musu
wacen miji ko saurayi idan naga fuska.

Ko dai shi ne dalilin da Mominta ba ta ta
a nuna tana kaunar ala
armu da ita ba?

Umma zuciyata na zafi idan na tuna wai iyayena ba ku da asali.

Dagaske ne a bariki ku ka ha
u kamar yanda ake fa
a?

Don Allah ki taimaka yau ki fidda ni a duhu."
"Haulatu, kenan dama duk zaman da nayi da ke na baki tarihin aurenmu da mahaifinki bai gamsar da ke kin yarda cewa ni
in ba ni da wani aibu ba?

Ban fadamaki ban san inda mahaifiyata take ba?

Duk bayanan da nayi maki bai gamsar da ke ba?" Umman ta yi maganar cikin nuna dakiya a zahiri, amma can
asan ranta ita ka
ai ta san ba
in cikin dake dun
ule a ciki.
ara duban mahaifiyarta fuska cike da rauni ta ce.

"Ai ban ce
arya kike yi ba Umma, kawai dai so nake na
ara sanin wani labarin dangane da rayuwarki.

Yanzu ace ko sunan dangin mahaifiyarki, babanki bai ta
a sanar da ke ba?

Anya zan yarda da wannan?"
Ran Umma ya
aci da irin kalaman Haulatun.

Magana idan ta furta shi gareta kai ka ce da
awarta Hindatu ta ke yinsa.

"Kalmar
arya da kika ambata a maganata da ke kuskure ne, kar ki sake ki
ara gangancin furtawa ga wani ma ba ni ba.

Ina jiyemaki yanda kike furta kalamai gatsal ga kowa, don Allah ki yi kokarin koyon magana, duk abin da na hane ki na kuma ci gyaranki a kansa, ki dinga matukar kokari wajen kaucewa maimaici a zancenki na gaba.

Kin ji ko?"
Ta gya
a kai kawai don ita fa ba ta ga abin zafi ko wani abu da ta furta ba daidai ba cikin maganarta.

Ta fi tunanin kodai Umma ba ta son zancen ne ta wayance da cin gyaranta.

Sai can kuma ta tsinci muryarta cikin sanyi ta soma magana.

"A rayuwa sai kin kauda kai kin kima koyi toshe kunne.

Ba komai ne mutum zai yi ya dameki ba, kar ki sake ki kasance cikin masu zargi, ki kyautatawa
awarki zato tunda ba ki ta
a kama ta da laifi makamancin wannan ba.

Kuma mene ne ciki idan ta yi maki
oyon samarinta?

Komai ne ya zama dole ki sani na rayuwarta?

Ko kuwa dole ne ta san komai dangane da ke?

To me za ki amfana da shi idan kin san labarin saurayinnata?

Ki koyi kauda kai a duk abin da ba'a nemi ki sa baki ciki ba."
Umma ta
an numfasa sannan ta
ora zancen ba tare da ta ba Haulatun damar cewa kanzil ba.

"So kike na yi ta maimaita maki ba
in tarihina?

Mene ba ki sani ba a kaina yanzu?

Kin san mahaifina Kalangu shi ne sana'arsa, mahaifiyata kuwa an ce tun ina
arama ta maido ni hannunsa ba ta
ara waiwayata ba.

Kauna tsantsa, babu irin wacce ban gani a hannunsa ba, ya yi iyaka kokarinsa na ganin ya tsaremin mutuncina bai bar ni na fa
a hannun
an barikin da ke farautana ba koyaushe.

Haka na taso ya sanya ni makaranta boko da arabi, ban yi nisan kirki ba iyakata sakandire ya cire ni ya aurar da ni ga Mahaifinki.

Abu uku na sani game da mahaifiyata, na farko sunanta Asma'u, na biyu kuwa, ya cemin daga babban gida ta fito, alokacin za'a yi mata auren dole.

Ya kuma ce
ar Katsina ce.

Bayan wannan abu ukun, babu abin da zan iya fa
i game da ita.

Shi kuma mahai..."
"Ni bana son sanin komai a kansa.

Iyaka wannan ya wadace ni." Ta katse mahaifiyarta cikin sauri da jin zafi a kirjinta, a duniya anya akwai wanda ta tsana sama da shi?

Kai ba za ta ce ga shi ba.

Umma murmushi ta yi mai ciwo, sai dai ta kasa cewa komai.

Ta tabbatar muddin za ta nunawa Haulatun hoton da ta ke
oyo shekara da shekaru wanda Babanta Mai Kalangu ya ba ta sadda yake kwance cikin ciwon ajali, to fa a taurin kai irin nata, za ta iya bazama ta ce za ta Katsina nemo mata asalinta idan ya so komai zai faru ya faru.

Tun a baya ta yi niyyar ta nunamata hoton wanda a bayansa hatta da cikakken sunan Asma'un akwai da na mahaifinta wanda ba
oyayye ba ne har a yanzun ma koda ace ba ya raye, sai dai yanda ta kula da zafin
iyayyar yarinyar akan Uban nata sai ta fasa.

Ita kuma a ranta ta riga da ta
ullaci mahaifiyarta Asma'u da har za ta iya yin watsi da lamarinta har haka, ta tafi ta bar ta a bariki saboda kawai son zuciya irin nata.

Ba ta ta
a muradin zuwa inda take ba har a yanzu da take jin zai wahala ace tana nan a raye ciki duniyarnan.

Wasu lokutan takan fiddo hoton ta zubamata idanu idan Haulatun ba ta gida, ta yi hawayen ta share sannan ta mayar ma'adani, har ma ta tsinci kanta da sanya ta cikin addu'a.

Babu yanda ta iya tunda wannan na daga cikin ha
in iyaye akan yaransu.

Ba ta fasa yi ba.

Yanda uwar ta zurfafa cikin tunani, hakanan Haulatun ke fidda hawaye tana tunanin ba
abi'un mutumin da ya kasance uba a gareta.

Bugun gidan da ake yi ne kamar za'a
alle
yauren shi ya fargar da su.

Eani guntun tsaki Haulatu ta ja gami da komai katifarta ta runtse idanu tana jin wani ra
i a kirjinta, bugun da yake yiwa gidan ji take inama za ta iya zuwa ta
auki mataki a kai, sai dai inaa, ta san hakan ba mai yiwuwa bane.

Tana jin fitar Umma daga
akin ta
ara jan zani ta rufe fuskarta.

Ya dube ta sama har
asa, ta kauce ya shigo ta rufe gidan.

Shigewa ya yi bai ce mata komai ba
auke da
ullin ba
ar leda a hannunsa ko sannu da zuwan da ta yi bai amsa ba.

Ba wannan ne farau ba.

Ita dai duk sadda ya shigo ba a buge ba ta sani akwai dalili babba.

Har za ta koma
aki ya dakatar da ita.

"Ke, ki zo ina son ganinki."
Umma ta ji zafin kalaman sosai, ta tabbatar
iyarta sai ta ji.

Juyowa ta yi ta amsa.

"Ina zuwa."
"Kina zuwa?

Har in ce maki ki zo ki cemin kina zuwa Na'ima?

To ban baki iznin shiga
akin nan ba, ki zo ki shige yanzu." Ya fa
i cike da jin isa.

Dama tun can Ibrahim
an Mutuwa bai iya wani abu wai lalla
a ta ba, ta ga dai yana yiwa
an barikinsa hakan don kafin ta haihu har gidan yake kawo su, idan ta yi magana ta sha jibga.

Zuciyarta zafi take yi sosai, wai ace mutum ba ya tashi tunawa da kai sai idan ya ga dama?

Ko kuma ya nemi
an barikinsa ya rasa?

A cikin rayuwar aurensu babu abin da ta fi gujewa kamar ha
a shimfi
a da shi.

Ba za ta iya zama ya goga mata cutar da za ta nakasta mata rayuwa ba.

Ta gwammace sai dai su yi wacce za su yi.

Har ga Allah ta san babu kyau juyawa miji baya, amma fa ita kam miji irin na...

Tunaninta bai kai aya ba ta ji an ha
e kanta da
yauren
akin ji ka ke kau!

Ta bugu a goshi.

Sam ba ta ji tahowarsa ba hakan yasa abin ya zo mata bagatatan.

"Don ubanki mai kalangu ni nake maki magana kina ji kika mai da ni wani banza?

Ai ko sadda na ci zamanina Ubanki ma bai isa na yi magana ya ji ya yimin kunnen uwar shegu ba ballantana kuma ke da kanki!"
Idanunta a runtse cikin jin zafi da ra
in maganganunsa.

"Ka daina zagin ubana, na fa
amaka ba ya min dadi."
Ta furta cikin dakiya, ya kuwa kai mata bugu a baya, hakan bai masa ba sai da ya zaro belt.

"Ni kike gayawa na bar zagin Ubanki?

To yau kuwa za ki ci uban naki Na'ima!

Kuma ki kwana da shiri don aure zan
aro naga uwar uban da zai hana ni!
Chapter 7 · 0% Book details