← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 109

Sashe 40

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani abu ya faru ne?"
Ya yi tambayar sakamakon tsaf ya ji kuka a
azun sai dai kuma bai san waye ba sai da ya ji shiru daga bisani jikinsa ya ba shi ana kallonsa ya juya suka ha
a idanu.

Ita kuwa Haulatu sai ta dube shi jin tambayar da ya watso mata.

Ba don nasa dara-daran idanun irin nata suna dubanta ba za ta dauka ko da wani ya ke.

Ta kauda nata idanun, kai ta girgiza masa.

"Aa."
an tsaya ta ji ko zai
ara tambayar amma kawai sai sautin muryarsa ta ji ya cigaba da karatu bayan bismillah da ya yi.

Ta kalleshi baki sake, wannan Yaya Sadaukin kawai kuma don ta ce a'a ba zai
ara tambaya ba kamar yanda Mu'az ke mata naci da son jin meke faruwa idan ya ga ranta a
ace?

Kawai sai ta
aga
afa ta bar wurin tana jin dama ba ta ha
u da shi ba.

Shi kuwa sai kawai ya tsinci kansa da murmushin da ya bar wa kansa sanin dalili.

Bai tashi a wurin ba sai da ya soma jin kiraye-kirayen sallar la'asar tukunna.
***
Hajja koda ta dawo sai da Haulatu ta zayyane mata komai bayan an sha ruwa, don su Baba Saude, Umma ta hana su fa
amata, ita kuwa Haulatu ba ta ga dalilin shiru ba tunda ita an hana ta yi magana balle kuma Umman da ko za'a yi abin da ya fi hakan ba za su ce musu uffan ba.

Aikuwa sosai ta hau bambamin fa
a kamar ta ari baki.
arshe ma hannu na rawa ta ciro waya ta sanya Haulatu lalubo mata lambar Mahaifin Mu'az, Injiniya Faisal.

Nan ta hau zazzaga fa
a don ko amsa sannu da sha ruwan da yake mata ba ta tsaya yi ba.

"Lallai ka ja wa Matarka kunne idan kuwa ba haka ba zan nunamata ni
in koda ban haife ka ba toh ina da iko da isar da zan saka ka sauwa
e mata.

Da ni take zancen, ta
ara gigin shigowa ta gwada cin zarafin
iyata da jikata ta gani."
Shi dai Injiniya hakuri sosai ya dinga ba Hajja ya kuma ce zai yi mata magana ba za'a
ara ba.

Bayan sun ajiye wayar Haulatu ta kwashe da dariyar da ke cin ta a rai, Hajja sosai ta burge ta, Umma da tun dazu take zubawa Haulatu harara ta ce.

"Sai da ki ka fa
a ki ka ji dadi, burinki ya cika ai."
"Aa kin ga Na'imatu rabu da ita.

Ke mene ne amfanin yin shirunki?

Ita ma so ki ke ta zama kamar ke ta dinga yin gum tana shanye
acin rai da ba
in ciki har ya yi ajalinta ko?

Toh ba ki isa ba, ke Haule daga yau duk wacce ta
ara zuwa ko bana nan ki sanar da ni matu
ar ba alheri ne ya kawo ta ba.

Idan ma na yi nisa ga Alhaji Babba can ko Yaya Dakta."
"Toh Hajja." Fadin Haulatu zuciyarta fes kwalliya ta biya ku
in sabulu.

Umma girgiza kai kawai ta yi ba ta
ara magana ba.

Sai bayan kammala shan ruwa Umma ta dubi Haulatu bayan barin Hajja daga falo.

"Kin kuwa kira Yayanki kin masa godiyar tsaraba?"
Sai ta
an waro idanu, ita shaf ta ma mance.

Ta tuno ha
uwarsu da shi
azu da yamma, ina za ta iya yi mishi godiya a sannan alhalin ya zubamata wa
annan idanun masu kama da na mage.

"Kin yi shiru."
"Na manta." Ta fadi tana
an turo baki ka
an.

Ran Umma ya
aci.

"Amma ke dai an yi marar wayo.

Wato ni kika bari da yin godiyar kenan ke ba ki bi umarnina kin kira shi kin masa ba?

Ciro wayarki yanzu na ga kin kira shi."
Ta jawo wayar idanunta ya yi rau.

"To ai ban da lambarsa."
Girgiza kai Umma ta yi ta mi
a mata nata wayar.

"Duba za ki ga Sadauki a kai."
Ta kar
a ta
au lambar.

Yanda Umma ta tsura mata idanu ya sa a dole ta danna kira.

"Assalamu alaikum."
Ta tsinkayi muryarsa a dodon kunnenta, wannan ai shi ta dubi Umma kafin ta ha
iyi miyau ta amsa.

"Waalaikumussalam.

Barka da shan ruwa."
"Yauwa, go straight to the point, sallah zan shiga."
"Haulatu ce."
"Yes, na sani."
Ya fadi a hanzarce, ta shanye mamakin jin yana da lambarta don ta ji ya ce yana sauri ta ce.

"Dama godiya zan yi na tsaraba.

Nago..."
"No, ba godiya.

Ki gaida Umma."
Daga haka bai
ara jira ba ya katse kiran.

Ta bi wayar da kallo, ba don da kunnenta ta ji ana haramar tada sallah ba za ta ce da gayya ma ya yi mata hakan.

Ta
e baki ta yi.

"Ya ku ka yi?"
"Cewa ya yi ba sai na gode masa ba.

Kuma yana gaida ki."
"Ina amsawa." Daga nan ita ma Umman ta mi
e don
auro alwala.

Ita kuwa Haulatu sai ta
urawa lambarsa idanu, 909090 har uku a
arshenta, lambar ta burge ta sosai.

Ta adana akan waya da sunan Yaya Sadauki.

A karshe kuma ta mi
e ita ma.

Washegari Mu'az ya zo ya sami Umma ya ba ta ha
urin cim mutuncin da Mominsa ta yi, Umma ta nuna babu komai kar ya damu.

Haulatu kuwa ko kallonsa ba ta yi ba, tana tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro ko yaya tana so ya fahimci ta san darajar kanta da na Ummanta ba wai hakanan daga Momi ta yi abu ta dinga sakin baki tana washe wa yaranta ba kamar wacce ba ta san ciwon kanta ba, amma ta rantse yanzu ma suka fara zumunci da shi sai dai ba
in ciki ya kashe Mominnasa.

A na jibi sallah bayan sun dawo daga gidan
unshi ita da Safina da Radiya, Allah ya taimake ta ba ta azumi saboda wani ciwon kai da ta ke fama da shi tun safe tsabar gajiya da kuma rana, ko ruwa ba ta sha a gidan
unshin ba ma ganin wajen a cike.

Ta tarar an kawo kayanta daga wajen tela, Hajja ta yi mata kala biyu atamfa da leshi, sai ko Haj Hadiza wacce ta aiko Atamfa wai a
inkawa
iyarta.

Umma koda ta gani a lokacin murmushi kawai ta yi, fatanta
aunar da take nunawa Haulatun a yanzu ya kasance har zuciyarta.

Khaleefa ma sai da ya ba Umman turmin atamfa mai tsada ya kuma ha
a har Haulatu.

Shi ma tun a azumi na da goma ya kawo, ba laifi koda ta masa godiya a take ya amsa.

Sosai
inkunan sun yi kyau sai dai ciwon kai ya sa ko iya gwadawa ba ta yi a sannan ba sai wajen takwas na dare bayan ta ci abinci ta sha magani har ta dan samu bacci ta farka.

"Kai Umma, wallahi wannan telan ya iya
inki.

Kalli fa yanda kayan suka zauna a jikina?"
Murmushi kawai Umma ta yi, Hajja kuwa fadi take
"TubarakAllah Haule, sai kika koma kamar ni sadda ina budurwa."
Suka yi dariya har da cafkewa kamar wata sa'ar ta.

Ta dinga juyi gaban madubin dake kusurwa daban a falon Hajja, kalar leshin ma ya hau da fatarta, silver mai adon ba
en fulawa.

Ya sha adon duwatsu.

Jin sallama ba zato ya sa ta saurin waigowa, gaba daya suka dube shi.

Khaleefa ne ya shigo, ita kuwa Haulatu ganin Khaleefan ba ta wani damu ba tunda dai sutura ne a jikinta, dama
awayenta ne ba ta son su shigo su iske ta cikin kayan, ta fi
aunar ta yi musu bazata a ranar sallah su ga yanda za ta ci ado.

Shi kuwa karasowa ya yi ya zauna yana gaida su Umma sai dai fa wani abu na jan sa ga kallon Haulatun.

Ta gaida shi ta kwashe sauran kayan da aka kawo ta wuce
aki.
akin ma sai da ta
arewa kanta kallo a madubi kafin ta yi sauri ta sauya kaya, dama leshin ka
ai ya rage ta gwada, ta maida su ta ajiye cikin sif, tana da takalmi da jaka sabbi, hatta da mayafi wanda zai hau duka Hajja ta sa an siyo mata su tun daga Kano.

Shigowar su Safina da Radiya ne ya sa ta juyowa bayan ta rufe sif din.

"Inyee, masu ciwo an wartsake.

Ai gwara ki mi
e haka kurum ba za ki kashe mana zumu
in zuwa idi ba."
in Radiya dake ri
e da leda a hannunta.

Ta harare ta tana dariya.

"Ai na rantse da ko fatalwa sai na maku na hana ku sakat, kuma
afata
afarku sai dai mu mutu tare.

Hum um, na mutu kawai na bar ku kuna shanawa?"
Suka yi dariya gaba daya.

"Dallah can, kema ai a lahirar kina aljanna in sha Allahu." Fadin Safina.

"Eh na ji din, amma ba yanzu ba.

Allah dai yasa mu cika da imani."
Suka amsa da amin.

"Ke kina ta wani rungume leda, ki ba wacce aka ce mu kawo wa mana."
Fadin Safina tana yarfa hannu.

Haulatu ta bi ledar da Radiya ta mi
o mata da idanu.

"Ke hijabai ne fa, Yaya Sadauki ne ya kawomana kala bibbiyu.

Fari da ruwan
asa.

Kuma dukkanmu iri guda.

Wallahi kamar ya auna tsawonmu.

Amma na ji Maama ta ce a shagon wannan
awarta ta Anti Laila ya siya.

Kin san hijabai da suturu ta ke siyarwa."
Ai kuwa ta zazzage ledar, hijaban an sanya su cikin farin leda an li
e.

Da zumu
i ta ce.

"Bari na nunawa Umma, ina zuwa."
"Eh ki dawo ki nunamana tsarabarki ta China." Cewar Radiya.

A falon har lokacin Khaleefa yana nan, ta ga ya auna bp din Umma da abin gwaji, sai ta dan tsaya, bayan sun kammala ta ji yana cewa Umma komai yana tafiya daidai sai dai a
ara kiyayewa.

"Ke kuma kin fito kin bar
awayen naki?"
Fadin Umma tana kallonta.

Ta karasa tana murmushi gami da mikawa Umma hijaban.

"Umma kinga wai Yaya Sadauki ne ya siyo mana mu uku.

Kowa kala bibbiyu."
Fara'ar Umma ta
aru, shi kuwa Khaleefa ya tsinci kansa da bin hijaban da kallo.

Kyauta daga Sadauki?

Saraki dai da ya sani?

Eh yana da kyauta, amma meyasa Haulatu?
Chapter 40 · 0% Book details