← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 109

Sashe 100

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahima kuwa tun da yamma ta koma gidansu bayan mahaifinta ya zo Baba Alhaji ya roki alfarmar ya janye batun aure, ya dai amsa da toh amma babu wanda ya san meke ransa.

Da kansa kuma ya yi umarnin ta shirya su tafi.

"Yaya Sadauki sannu da zuwa.

Ina yini." Fadin Zaituna da ke zaune a gefe fuskarta a sake.

Shima da sakin fuskar ya amsa mata.

Yana tambayar ko su Mama sun iso.

"Sun ce suna dab da shigowa Katsina, nasan nan ba da jimawa ba za su karaso."
Ya jinjina kai.

"Allah ya kawo su lafiya."
Suka amsa da amin.

Zaituna ta kula dai hankalinsa na ga benen da Haulatu ta haye, kafin ta ce wani abu sai ji ta yi Hajja na fadin.

"Ka ji kuma wani tsohon gulma wajen yarinyar can, ta ishi mutane da zancenka amma yanzu ka zo ta wani kama hanya ta gudu.

Ke Zaituna maza kira ta su gaisa."
Ta fadi ne don ba ta ga dacewar ya hau ba, ko babu komai a yanda Haulatu ta dauki wannan kyawun da hasken, zai kara zama hatsari a ke
ewarsu a rumfa haka.

Shi kuwa dama haka yake so, don haka sai ya yi shiru, Zaituna ta mi
e da sauri ta nufi saman.

A lokacin Haulatu na falo ta yi shiru hankalinta gaba daya yana
asa, ta ga ya yi kyau abinsa amma kuma duk ya rame.

Ganinsa da ta yi ya
ara haifar da sabuwar
aunarsa a ranta.

Koda Zaituna ta zo mata da batun ta je su gaisa, turo baki ta yi ta nuna ita ba ta son ganinsa.

Zaituna ta dungure kanta.

"Ji gulma, matar da ke kwana kallon hotonsa.

Malama umarnin Hajja ne, ko za ki nunamin ba ta isa da ke ba ne?"
Idanun Haulatu cike da kwalla ta dube ta.

"Yanzu Sis, apart from duk abinda ya yi min, kina ganin ya dace na manta da komai da wuri har haka?"
Murmushi Zaituna ta yi karo na ba adadi.

"Ki yi hakuri, ya maki laifi.

Amma ki duba ki gani, yanda ya ce mana fa, yanzun shigowarsa garin kenan ko
angarensu bai
arasa ba.

Kuma ni na tabbata don ke ya shigo nan
in.

Shi ma fa an masa laifi, an hana shi ganin abin da zuciyarsa ke so na kwanaki da dama, don Allah ki manta komai ki je.

Ni na tabbatar komai zai wuce kin ji ko?"
Da wadannan tausasan kalaman na Zaituna ta mi
e ta shiga daki, hijabinta mai kyau wanda Zaituna ta kawo mata matsayin tsaraba daga Malaysia, da kadan ya wuce gwuiwarta, hawa biyu ne da shi, dogo da kuma
ara iyaka kirji.

Fari
al.

Ta fito ta sauka
asan.

Ganin Hajja kadai ya sanya ta ji har ranta ya
an yi babu dadi.

Kafin ta tambaya ko ya tafi ta ji Hajja na fadin.

"Ki je yace ki same shi inda ku ke hira tunda kin kwace min miji."
Ta yi gaba kawai ta bar Baba Saude wacce ba ta jima da shigowa falon ba da dariya.

Ta iske shi zaune a rumfa sama kujera a farfajiyar gidan, hasken fitilu suka haska musu fuskokin juna tun ma kafin ta
arasa gare shi.

A hankali take takawa har ta kai gefensa ta nemi wuri ta zauna.

Kallonta kawai yake yi kamar ya samu waya a hannu.

Sallamar da ta yi mishi ce ya sanya shi numfasawa sannan ya amsa.

Shiru ya
an biyo baya kafin ya ce.

"Kawai ki ce shirin zautar da Abeed Malumfashi ake yi, shi ne dalilin yi min rowarki?

Bebi kar ki
auki alhakina.

Ina sonki ina sonki, idan ya fi haka akwai matsala."
an runtse idanu ta yi kanta a
asa, tunda suke da Sadauki kalmar ina sonki ba dai ya firta ba amma kuma duka kalmominsa masu nuni ne da tsantsar so
in da
auna.

Yau ga dukkan alamu dagaske ya je ma
ura.

"Ki yafemin, ni mai laifi ne.

Na ji zafin hana ni ganinki da Maama ke yi, sai aka zo ke ma madadin ki ji tausayina, sai ki ka biye mata.

Tunanina ya ba ni ko dai ba ki wani damu da ni ba ne?

Sai na ji ke kanki kin ban haushi, na yanke hukuncin mu zauna haka babu wayar ko tuntu
ar juna zuwa lokacin da kaf duniya babu mai cikakken iko a kanki sama da ni.

Amma ba zan iya ba.

Na kasa, ba zai ta
a yiwuwa ba.

Ki yi hakuri kin ji?

Ko na dur
usa?"
Ta kalle shi, idanunsa sun ka
a, muryarsa ta narke gaba
aya, ya yi wani irin taushi fiye da baya.

Ba
arya duk abin da ya ce ta yarda har cikin zuciyarsa hakan ne.

Don haka ta girgiza kai.

"Aa my heartbeat, ni ba na bu
atar ka durkusa min.

Na yarda da duk abin da ka ce.

Na yafe maka na hakura, ni ma ina ro
on hakan daga gareka."
Ya yi murmushi.

"Ba kya laifi.

Naki da nawan duka na ha
e su ya zama ni kadai ke da laifin.

Bebi kyau kike ko babu kwalliya.

Kin sauya, anya ba ki fi
arfin Abeed ba?"
Ta harare shi kadan, ya lumshe idanu yana shafar sumar kansa.

"Ki bari."
"Na bari." Ta amsa tana kauda kai.

Sai a lokacin ta gaida shi da tambayar ko ya iso lafiya?

Ya amsa mata ba tare da ya iya kauda kai daga dubanta ba.

Dakyar dai ta lalla
a suka rabu ya wuce don ya huta, babu sallah a kansa face sallar isha'i da ake kira yanzu.

Har sai da ta shiga gida kafin ya juya ya fice shi ma.

Babu jimawa da rabuwarsu, su Maman Zaituna suka iso gidan.

Murna ya kara
e a
angaren Hajja, Umma ma a sannan sun dawo.

Ranar dai kwanan farin ciki Haulatu ta yi ga waya da suka sha da Sadauki kamar za su cinye juna.

Biki na ta matsowa, ana sauran kwana uku ne ba
i daga Malumfashi suka iso da yawa.

Ga mutanen Kaduna da Kano kamar ba lokacin karatu ba don yara ba su yi hutu ba.

Amma an taru sosai, masu yaran kanana kuwa sun bari sai juma'a ranar da za'a fara bikin za su iso.
inkunan fitar biki babu
aya da ya fita daga hannun Umma, Abba Ridwan ne ya dauki wannan nauyin, shi da Momi Nuratu, sam ba ta yiwa Haulatu kallon suruka sai
arta.

A sannan tuni an kawo lefe na gani na fa
a, saiti uku da kayayyakin ga kuma na Uwa da aka yi daban.

Komai na cikinsa abin burgewa.

Sadauki a zuwansa Dubai ya
ara yo siyayyar abayoyi da sar
a sai jakunkuna, ya kaiwa Maama bayan Momi Nuratu ta gani ta sa albarka.

An yiwa Haulatu komai a fannin jere, babu abin da ba'a zuba ba, nata kawai shiga gidan.

Momin Mu'az da Mamin Khaleefa ko Allah ya sanya alheri na lefe ba su shigo sun yi ba.

Akan hakan sai da Hajja ta yiwa mazajensu tas kan su ja wa matansu kunne kar su kawo rarrabuwar kai a zuri'a don ko yaransu ma ba su shigo ba idan ka cire mazan da ba su ko damu ba.

Aikuwa kowaccensu ta kwashi kashinta a hannu don Baban Mu'az har kusan sakin Momin Mu'az ya yi akan furucin da ta yi mene ne ya yi saura da zai burge ta a bikin
ar bariki.

Wannan ne ya yi sanadin da ya ce ta tafi gida amma bai kai ga sakinta ba.

Ita kuwa Mamin Khaleefa da yake ba ta saba ganin
acin rai sosai daga Barr Dawud ba, sai ta yi shiru da ta ga ya rufe ta fa
a ganin kamar tana neman zagin Hajja wai tana ha
a husuma tsakanin mata da miji.

Dole ta ja baki ta tsuke tana tunanin ya aka yi har ya iya
agamata murya?

Kada dai aikin da take a kansa ya bar ci kwata-kwata?

Biki Buduri....
ara hakuri, in sha Allah ko post biyar ba zai kai ba.

Labari ya na dab da
araye.

Ranar Alhamis aka sanya Haulatu a lalle.

Umma har hawayen farin ciki ta fitar.

A nan farfajiyar babban gida aka yi komai da yammaci aka
are.

Sosai Amaryar ke fama da ciwon kai, kwanakin ba
aramar gajiya ta yi ba.

Zagayen zuwa
unshi da kuma gyaran gashi ga kuma wani gyara na musamman da Maama ta zo takanas aka yi mata wanda dama shi an bar shi ne sai dab da biki.

A wannan daren duk yanda Angon ya so su yi magana bai samu ba, bai takura mata ba.

Da wuri ta shige
akin Hajja inda babu mai takura mata ta kwanta bayan ta sha magani, ai kuwa ko mintuna biyar ba ta yi ba ta yi bacci.

Ba kuma ita ce ta farka ba sai washegari da Asubahi.

Nan ma Hajja ce ta tayar da ita domin yin sallah.

Sai a sannan ne ta ji kan nata ya saki, babu wani ciwo.

Ranar kuwa
aurin aure ne da yini.

Wannan yasa tana kammala yin kari, aka ce ta fa
a wanka.

Kamar ta yi kuka ta dubi Maman Zaituna.

"Mama ba sai anjima ba?"
Maman Zaituna ta yi murmushi.

"Wane anjima kuma Haulatu?

Ke da yau za'a shafa fatiha?

Aa, je ki maza ki yi wanka ki fito ki yi shiri.

Mai maki make-up ta fi awa da zuwa."
"Au, sai ma an lalla
ata za ta yi?

Toh kodai a fasa ne a
aura da ni?"
Cewar Hajja dake zaune a falon wanda cike yake da iyaye, sai ko ita Haulatun da Maman Zaituna ta sa a gaba ta yi kari a kusa da ita.

Aka yi dariya.

Ita kuwa sai ta mi
e don yau babu baki balle ta rama zolayar Hajja.

Tana shiga
akin nan ma ta ha
u zolayar su Safina, wai sai wani murmushi take yi baki ya
i rufuwa duk murnar
aurin aure.

Ita dai ba ta ce musu uffan ba ta
auki babban tawul
in wankanta ta shige ban
aki.
Chapter 100 · 0% Book details