← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 109

Sashe 25

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To watakila ma ta ta
a ganin nata amma ba ta san wace ce ba.

Malama ta kar
e su fuska a sake, Haulatu dai daga gaisuwa ba ta
ara cewa komai ba sai shiru da ta yi tana
arewa falon kallo yayinda suke ta hira da Maama.

"Kinga fa yarona na zo gani ba ke ba.

Ya dage na zo akwai magana."
Malama ta
an ta
e baki cike da takaici.

"Au, kenan ke ya kira ki taushe ni ko?

Aikuwa dai ina nan akan bakana.

Ke kam kina son biyewa shiriritar yaran nan naki."
Maama ta yi turus.

"Toh kinga dai ban san komai ba, amma kin
auko hanyar fesamin.

Wani abun ne ya faru?

Ko kuwa bai kai girman da Zaid ya
ago ni ba?"
"Aa, ai ba kya ji a bakina ba.

Wa
a a bakin mai ita ta fi da
i.

Ki dai je yana can wajen nasa tunda shi ya nemi ki zo.

Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, duk za ku zo ku same ni."
Dariya Maama ta yi tana mai mi
ewa.

"Allah ya kyauta toh.

Har na matsu ma na je na ji meke faruwa.

Haulatu ki jira ni."
Ta amsa da toh kawai, bayan ficewar Maama daga falon Malama ta
an girgiza kai tana duban Haulatu ta ce.

"Ke kam kin huta da alama ba ki da surutu ko?

Koda dai gidan nawa ne ba abokan hira da yawa.

Yarana duka ukun maza ne, mace
aya ce za ki iya ba ta shekaru biyu zuwa uku, ta jw makaranta amma nan kusa za ta dawo."
Murmushi Haulatu ta yi, wai ita ake cewa ba ta da hira.

Lallai, don dai Malamar ba ta dan wace ce ita ba.

"Kina zuwa makaranta a can inda kike?"
Tambayar da Malama ta kara yi ya fahimtar da Haulatu dagaske hirar ta ke so, kuma ga dukkan alamu matar ba ta da girman kai, tun soma zancen fuskarta ma a sake take.

Aikuwa ta gyara zama ta shiga labarta mata yanayin karatunta, hatta da irin hantarar da ake mata idan ta fita ana kiran gidansu gidan karuwai babu irin abin da ba ta kwashe ta fa
awa Malama ba.

Sosai tausayinta kuwa ya mamaye zuciyar Malama Safiyya.

Ta kuma karanci abubuwa da dama a kan Haulatun.

Yarinyar tana bu
atar nusarwa akan wasu daga cikin
abi'u da ladabin magana.

A yanayin da ta ke ba ta labarin tamkar da wata sa'arta, kamar misali takan yi amfani da 'Hum, ke na ga rayuwa fa.' Ko kuma ta ce 'Ke ba za ki fahimta ba.' Da dai sauransu.

A shekaru da wayewa irin na Malama Safiyya sam ba ta ga laifinta ba duba da yanayin rayuwar da ta taso a ciki, itama mahaifiyarta ba lallai ta samu wadataccen ilimi ba da kuma wayewar mu'amala da mutane ba.

Sai ta ji inama za'a yi mata kyautarta koda na watanni
alilan ne, ita kuwa za ta yi iya yinta don ganin ta gyara koda kaso sittin ne cikin
ari na daga
abi'unta.

Tun zuwan da suka yi gidan, sam ba ta taka ta je ba saboda ta jima kwance ba lafiya, kwanakin nan ne ta
an samu ta warware.

Amma ta ji labari daga yan uwanta cewa Haulatun ba ta da kunya, wai kowa ya je tana dubansa ne ta maida mishi magana.

Haka ta yi ta kula da
abi'un Haulatun, ita kuwa ko a kanta, bilha
i take ba ta labari amma ko kusa ba ta ce ga mummunan sana'ar da Mahaifinta ke yi ba don tuni Umma ta kwa
e ta da furtawa wani, ba kuma ta sa dalilin rufamasa asirin da Umma ke yi ba.

Tana dai kokarin nunawa Malama yanda ta tsani
anMutuwa a rayuwarta.

"Allah ya shirye shi idan mai shiryuwa ne.

Sai hakuri, abin da ya faru da ku, kaddara ce.

Ki saka a ranki haka ya tsara maku.

Kin ji ko?" Fa
in Malama Safiyya kenan a
arinta na datse zancen iyaka nan ganin hirar ma babu da
in ji ga
arancin ladabin magana da Haulatun ke da shi.

Aikuwa jin abin da Malama ta fadi yasa Haulatu yin wata dariyar.

"Aikam mun ga rayuwa.

Tab din!

Ai wallahi Hajja ta rufawa kanta asiri ma da ta kar
e mu idan ba haka ba wallahi daga nan har gidan rediyo."
Ita dai Malama ta cika da
umbin mamaki, shakka babu akwai tarin gyara da yarinyar ke bu
ata.

Ta yi shiru ba ta
ara uffan ba, ba kuma za ta ce wai ta ji wani tsana ko haushin Haulatu ba face ma tausayin da ta ba ta.

Ta san wahalar tarbiyya, ta yi msta uzurin kalar gidan da ta rayu a cikinsa.

Murmushi ta yi kafin ta mi
"Bari dai mu yi haramar sallah, na ga lokacin Magriba ya gabato.

Tashi muje na nunamaki
akin Auta ki yi alwala."
Ta amsa da to, daidai sadda wata yar yarinya mai shekaru sha uku ta shigo da sallamarta ranga
au.

Suka dube ta, tana sanye da kayan islamiyyarsu.

Yarinya ce
arama amma fa akwai
iba masha Allah.

Ba ta da hasken fata, sai karen hanci da hasken idanu.

Ta shigo tana nishi gami da wurgi da jakar hannunta.

"Mama yunwa nake ji wallahi." Ta furta kamar ta yi kuka.

Sai ma a sannan ta ankara da Haulatu, sai ta washe baki.

"Lah, Anti Mimi, yaushe ku ka zo Katsina?"
"Ba ita ba ce Bebi, wannan sunanta Anti Haulat, maza raka ta
akinki ta yi alwala ki zo ki ci abincin.

Ki dauke jakarki kuma."
Ta amsa da toh kafin ta dauki jakar tana
ara satar kallon Haulatu wacce itama ta ke tsaye tana jiranta.
***
Zaid El-Yakub.

Matashin saurayi son kowa
in wacce ta rasa.

Allah ya mishi baiwa ta iya lafazi da kuma ilimi na boko da arabi don idan Zaid ya juye harshe yana larabci kai kace balaraben
asar Saudia ne, kusan kaf a jikokin gidan maza, su biyu kacal Allah ya ba wannan baiwar ta jin harshen larabci sosai, Zaid da Abeed (Sadaukin Alhaji).

Uwa uba kuma ga kyawun fuska ga kuma na gidan rana da Allah ya ba shi.

Da murmushinsa kawai, sai ya narkar da zuciyar mace.

Mutum ne da ya iya tausar mace musamman idan tana cikin yanayi na fushi da zafi.

Sai dai duk da wannan nagartar tasa bai ta
a tara shirgin
anmata ba.

Ba ya kuma ba da fuskar da ma zancen soyayyar za ta ha
a ku, komai ala
arka da shi muddin ya fahimci daga
an uwantaka ka fa
a kogin kaunarsa to fa zai ja baya da kai ya sauyamaka baki daya.

Ko Zaituna
ar malaysia da ta yi mutuwar sonsa, daga sabo na zumunta ne ya juye a wurinta ya koma so
in.

A duniya kuwa ba abinda ya tsana sama da auren zumunci, sam ba ya burge shi.

Wannan na
aya cikin dalilan da ya sanya shi kawo maganar abokiyar karatunsa Jalilah, har a yanzu ta kai su ga aure.

Sosai ya yaba da nutsuwarta tun ma zamanin da suke tare a makaranta, tana sonsa sai dai koda alama ba ta ta
a furtawa ba.

A karan kansa ya gane hakan.

Bai kuma
ara tabbatarwa ba sai da ya fara zuwa gidansu da sunan zance.

Ga shi a yanzu ta kasance mata a gareshi.

"Mutanen Abuja."
ago kai daga saman laptop din ya dubi
ofar, lokaci guda ya saki murmushi gami da shafar sumar kansa da ba ta da yawa.

"Maama, bismillah."
Bayan ta zauna ya gaishe ta cike da girmamawa.

Kafin ta tambaye shi Jalilah.

Anan yake sanar da ita ta je gidansu.

Ba su wani
ata lokaci ba yake fa
amata
udurinsa na tafiya da Bebi can Abuja wanda Malama ta ce sam ba ta amince ba.

Harararsa ta yi kafin ta ja guntun tsaki.

"Ga ka nan dai wani lokacin idan ka yi abu kamar kai ne Autan ba Bebi Ayyush ba.

Yanzu Zaid akan wannan ka sanya ni zuwa fisabilillahi?

Wannan ai magana ce da a karan kanka ka san ba mai yiwuwa ba ne, Malamar ka ke son ta zauna ita
aya a gida?"
Ya yamutse fuska.

"Maama ta ina za ta rayu ita daya, ga Jafar, Nabeel duka, itama Juwairiyya gobe za ta dawo daga Malumfashi.

Sannan ba fa hakanan zan tafi da Bebi ba, zaman shirun ne babu dadi, Jalilah na damuwa tunda idan na fita tun safe ba na dawowa sai Magrib.

Aron Bebi da za ta ba ni na kwanaki ka
an ne kafin su yi resuming school.

Ina ce ma biki za'a yi nan kusa?"
"Hakane, to Islamiyyar fa?"
Ya yi murmushi.

"Zan koyar da ita a gida."
Maama ta girgiza kai.

"Da ace na san wannan dalilin ka sanya ni zuwa Zaid, tun a waya ba zan amsa maka ba.

Ni ka ga tafiyata kafin Haulatu ta
osa."
Ya yi saurin ri
e gefen mayafinta yana mai narkar da wuya.

"Please mana Maama.

Wace ce kuma haka da ba za ta iya jira ki taya ni wannan ya
in ba?"
Takaici ya cika Maama.

"Tsakanin Khaleefa, Mu'az da Sadauki na rasa wanda ya fi wani mayar da ni abokiyar wasansa.

Ni fa har yanzu ban dauki wannan magana da muhimmancin da za ka kira ni na zo ba.

Wato kai mai mata ko?"
an ha
e fuska.

Ta kuma san dalilinsa bai wuce na ha
a shi da Sadauki da ta yi ba.

A duniya ta rasa dalilin rashin jituwar Khaleefa da Mu'az, haka Sadauki da Zaid.

Idan ka ga kowannensu a wuri guda to tabbatar abu ne na dole babu yanda suka iya kowa cikin zuri'ar na wurin.

Amma fa idan an hadun za'a gaisa.

Magana mai karfi zai wahala ta shiga tsakaninsu dai.

Zaid da Mu'az ke
asawa saboda barkwanci irin na Mu'az, Zaid kuwa na son ababen ban dariya.

Khaleefa da Sadauki kuwa tasu ta zo
aya idan an ha
u za su yi ta tattaunawa akan abin da ya shafi matsalolin rayuwa da gwamnati.

Kowa dai da nashi za
in.

Alhaji ya yi nasihar da fa
an, amma ina.

A cewarsu su fa lafiya suke zaune da juna kawai dai halayyar ce ta bambanta.
Chapter 25 · 0% Book details