← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 109

Sashe 96

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me ka yi min?

Rayuwar da ka za
arwa kanka kenan akan soyayyar mace, ka yi duk yanda ka so Zaidu.

Amma ina maka rantsuwa ko bayan raina ka auri Haulatu ban yafe maka ba!

Shashasha marar tawakkali.

Iliminka ya tashi a banza kenan!

Ai alhaki kwuikwuiyo ne, da ace ba ka da saurin mantuwa, da ka tuna alhakin Zaituna ke cinka a yanzu.

Kuma a gobe ka tattara ka koma Abuja.

Ban yafe maka ba idan koda wasa ka cutar da Matarka."
Tana kaiwa nan ta mi
e a fusace da zummar wucewa
aki sai dai ba ta ko yi taku biyar ba ta zube a wajen.

A gigice ya kira sunanta.

"Umma!" Kafin ya yi wurinta yana salati, hakan ya yi sanadiyyar shigowar samarin
annen Zaid din.

Nan da nan ya mi
awa mai bi masa mu
ulli akan ya kunna mota, shi kuwa ya cicci
i Malama ganin ya zuba ruwa amma ba ta farfado ba suka fita.

Gaba daya suka shiga motar, Juwairiyya da Bebi ya ce su zauna a gida bayan Al'amin dake gefe ya kar
i hijabinta da Juwairiyya ta kawo.

Kai tsaye asibitin Baba Dakta suka nufa, ba ya nan sai Khaleefa suka iske tare da wata Dr Aisha.

Nurses suka kar
i Malama da gaggawa a ka shiga da ita
akin duba marar lafiya.

An yi sa'a bayan dabaru na likitoci ta farfa
o daga doguwar suman da ta yi.

A
arshe dai bincikensu ya tabbata da jininta ne ya
an hau dalilin damuwa da
acin ran da ta shiga.

Abin sosai ya motsa zu
atan yaran tunda ba su ta
a sanin mahaifiyartasu da hawan jini ba.
annen suka dinga jin zafin Zaid har suna
aure masa fuska don sun sani silarsa ne komai ya faru.

Shi kuwa wata irin nadama sosai ta shige shi, jikinsa ya yi sanyi.

Malama kuwa ta dage akan ba za ta kwana asibiti ba dole suka sallame ta bayan ba da shawarwarin a kara kula sosai.

Khaleefa har mota ya rako su yana kara yi mata sannu.

Sai da suka tafi sannan ya koma bakin aikinsa.

Daren ranar Zaid bai iya bacci ba, ya dinga nafila da addu'o'i kan Allah ya cire masa wannan soyayyar da ke wahalar da shi da ma makusantansa.

Har ya yi sallar asubahi bai runtsa ba, yana idarwa kuma ya ha
aramar jakarsa ya shiga suka yi sallama da Malama wacce a farko kallonsa ma ba ta yarda ta yi ba.

Sai da ya dinga magiya da neman gafara tare da al
awarin daga ranar yau ba za ta
ara jin makamancin haka a kansa ba.

Ya ha
ura da Haulatu, a nan ne ta iya dubansa har ramar da ya yi ta ba ta tausayi.

"Na yafemaka, Allah ya yi albarka.

Ka yi ta addu'a sannan ka ji tsoron Allah gun sauke ha
in da ya rataya a wuyanka na matarka.

Allah ya tsare ya kai ka lafiya."
Har wata ajiyar zuciya ya saki na samun sa'ida.

Ya jinjina kai.

"Ameen Umma, in sha Allahu na maki al
awarin kiyayewa.

Allah ya
aramaki lafiya."
Da haka ya mi
e ta bi shi da kallo har sai da kwalla suka cicciko mata.

Addu'ar neman sau
i da rangwame daga Allah ta
aga hannu ta shiga yi wa
an nata.

Garin Kano an wayi gari da saukar ruwan samu, misalin
arfe goma da mintoci Khaleefa ta
arasa shiga cikin garin da motarsa Land Cruiser ba
a wulu
mai gilasai masu duhu sai she
i take yi sakamakon wankin da ta sha, ga kuma ruwa da ya
ara wanke ta tas.

Da kansa yake tu
in, kai tsaye bai zarce ko'ina ba sai Bristol Hotel inda ya yi amfani da google map har ya
arasa.

Nan Ango El-Mu'az
araye ya fito tarbarsa shi da wani abokinsa sun sha babbar riga.

A lokacin ruwa ya tsaya sai dai har a sannan garin bai washe ba, ga kuma ni'imantaccen sanyi.

Ya fito suka yi musabaha da raha da komai, Khaleefa ba ma'abocin yawan magana ba ne da hira, El-Mu'az ya fi shi wannan sakewar, koda kuwa bai yi niyya ba, idan an ha
u sai an sanya shi magana da darawa.

Bai wani jima ba suka
unguma zuwa masallacin Umar Ibn Khattab inda anan ne za'a
aura auren.

Koda aka kammala kai tsaye reception aka tafi aka yi
aramar liyafa sannan aka wuce gidan Amarya.

Nan ma hotuna ne aka yi ta
auka bayan gaisawa da iyaye.

Sai da Khaleefa ya huta sosai a masaukin Otal
in har
arfe hu
u da kusan rabi ya buga, kiran Hajja ne ya fargar da shi tunawa da aikin da aka rataya a wuyansa.

"Ya Salam." Ya furta gami da juya akalar motar ta koma hanyar da za ta sada shi da filin jirgin na Malam Aminu Kano.

"Khaleefa, ka
auko
anwar taka?"
Ya runtse idanu.

"Afuwan Hajja, saura ka
an na
arasa shiga Airport
in.

Abu ne ya
an ri
e ni."
"To ba damuwa.

Na maka uzuri tunda kai ne, da Mu'azu ne cewa zan yi da biyu ya yi."
Murmushi kawai ya yi sannan suka yi sallama.

Can kuma ya ji shigowar sa
o, Umma ce ta turo lambar Zaitunar.

Kafin ya ajiye ta kira shi.
ana, ga lambar
anwartaka na nan, da shi ta yi kiranmu yanzu ba jimawa."
Ya amsa da toh gami da godiya suka yi sallama.

Bai gwada ko kiranta ba sai da ya
arasa ya nemi wuri ya yi parking.

Daidai sadda ya rufe motar ne ya ji ta
aga wayar da sallama cikin harshenta da ya ha
u da larabci da yaren Malay ga kuma Hausa.

Sai sallamar ta fita daban da irin na cikakken Bahaushe, ta yi dadi.

Ya amsa mata.

"Khaleefa Dawud ke magana, ki fito ina waje."
Ta amsa da toh, ba jimawa ba, yana tsaye yana kallon
ofar sai ya hango tana fitowa, wani
an matashi yana jan trolley
inta.

Khaleefa daga nesa ya
are mata kallo tas.

Riga ce ta yadin Abaya kalar ruwan
asa mai V shape a jikinta, tsawonta har ya zarce gwuiwa sosai, ta
an kama ta ka
an daga
irji daga
asan kuwa ta bu
e, sai dogon wanda ba
i da ta sanya sai ko high heel ba
i da ke a
afarta.

Ba
in mayafinta
arami sai ta zagaye fuskarta da shi.

Sai ko ba
in sunglasses da ta rufe idanunta da shi.

Ta sha hoda da jan bakinta da ya fiddo tsantsar kyawunta.

Komai na Zaituna cike yake da burgewa ga uwa uba yarinya ce mai aji da iya gayu.

Hannunta babu komai sai wayarta da
aramar ba
ar jaka da ta ri
Khaleefa ya kauda kai bayan kallon da ya
are mata.
an bakinsa ya ta
e.

Ba laifi ta iya kwalliya.

Sai kuma ta ba shi haushi ganin kamar kowa a wurin kallonta ya ke yi.

Har ta
araso bai kalle ta ba, sai ma ya juya ya nufi motarsa ya bu
e boot, matashin ya sanya jakar a ciki bayan ya tambayi Zaituna ko shi ya zo
aukarta ta amsa da gya
a kai cike da jin babu dadi na yanda ko gaisuwarta Khaleefa bai amsa ba.

Shi kuwa sallamar matashin ya yi ya tafi sannan ya bu
e motar ya shiga, da hannu ya bu
e mata gidan gaba ganin ta kai hannu za ta shiga bu
ofar baya ta shiga.

Sai da ya
auke farar babbar rigarsa da ke jikin kujerar ya maida baya sannan ta shiga ta zauna da bismillah a bakinta ta rufe ta
aura seatbelt.

Kafin ta
ara dubansa tana fidda gilashin ta mayar saman goshinta.

"Yaya Khaleefa, barka da yamma."
Kallonta ya yi fuskar ba yabo ba fallasa.

"Yauwa, daga yau kar ki
ara kwalliya idan za ki biyo hanya.

Babu amfanin kina mace ki yi ta abubuwan da za ki
auki hankulan maza."
Zaituna ranta ya sosu, nan da nan sai ga
walla sun cicciko mata, Khaleefa da tuni ya maida kansa ga tu
i yana
arin yin ribas bai
ara kallonta ba.

"Abu Affan, wallahi ban yi kwalliyar da wannan manufar ba.

Bari na goge."
Ya nanata sunan da ta ambace sa da shi,
an kallonta ya yi ganin ta zuge jaka ta fiddo tissue wanda ke zuwa
aramar leda da nufin goge bakin.

A sace ya kalli le
an ya kauda kai.

"Ni ban ce ki goge ba.

Bar kayanki."
Kallonsa ta yi sai ta sauke ajiyar zuciya ta maida tissuen cikin jaka.

Katafaren wurin abinci da kayan ma
ulashe na Albaik dake kan titin Kurna ya yi parking
in motarsa.

Ta dubi gidan abincin, eh tana jin yunwa don ba ta iya cin komai a jirgi amma fa ta fi
okin ta gan ta a gida.

Ba dai ta ce komai ba, ya ce ta jira shi sannan ya fita.

Ta bi bayansa da kallo, dogo cikakken namiji, babu macen da ba za ta yi fatan Khaleefa a matsayin mijinta ba sai dai marar sa'a da rabo.

Ita tunda take da shi ma ba ta wani tsayawa
are mishi kallo, yau
in ma don yana nesa da ita ne kuma babu damar da zai gan ta tunda ta waje duhu ne.

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ciro wayarta tana dannawa.

Murmushi ta yi ganin sa
on murya daga Haulatu ta whatsapp, bu
ewa ta yi ta kunna.
ar uwata kun taho kuwa?

Allah ya kawo min ke lafiya, na matsu ki
araso."
Ta maida mata da sa
on muryar ita ma.

"Ni kaina haka my sister, amma fa na ji ance ki na gidan Maama ai."
Koda ta amsa ganin bai shiga baki
aya ba ne yasa ta fahimci datar a kashe sai kawai ta sauka ita ma.

Ta
an ci mintuna kusan biyar kafin Khaleefa ya fito hannunsa
auke da ledoji.

Yana shiga ya mi
a mata, kar
a ta yi gami da furta Thank you.

Daga haka ya sanya seatbelt ya yi ribas ya hau titi.

Ita kuwa gudun kar ya ji babu dadi ya sanya ta bu
e ledar, shinkafa ce da ta ji kayan ha
i sai kaza,
ayar kuwa lemu ne da ruwa sai youghurt.
Chapter 96 · 0% Book details