← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 109

Sashe 65

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kawo karshen auren wancan azzalumin da mahaifiyarki."
Sai ta yi saranda don ita ta mance wane ma azzulumin da kuma wani batun auren Umma sai kuma lokaci guda ta tuna.

"Wai Mijin Umma?

Ya mutu ne?"
"Uhum, ina fa,
an Mutuwa bai mutun ba, kwanan bai
are ba.

Har nan gidan ya shigo ya furta sakin
warara har uku rak!"
Mamaki sosai wannan karon Haulatu ta ji, kafin ta
ara wata tambayar Hajja ta shiga warware mata zare da abawa, hawayen farin ciki suka sulmiyo daga idanun Haulatu, ta rungume mahaifiyarta.

Ba
in ciki ko damuwar da suke tunanin za ta yi sai suka ga ko alamarsa babu duk da dai ta danne ainahin damuwar a
asan ranta.

Kowace
iya za ta so yau a nuna mata mahaifinta a mutumin kirki, ta yi mishi kyakkyawan zato da tunanin zai shiryu koda ba sa tare, sai dai da
aryar da ya zo har ma da kudaden da ya mallaka a yanzu wanda ko shekara ba'a rufa ba ya tabbatar mata nata Uban ba zai fasa halinsa ba duk muninsa kuwa.

Murnar rabuwar Umma da mutum irinsa ya shafe wannan damuwar nata.

Tana kuma da ya
inin yanda a baya bai ci galaba a kansu ba, gaba ma babu abin da zai ta
uka.

"Umma shi ne ki ka yi kuka har fuskarki ta sauya?

Don Allah kar ki
ara zubarmasa da hawayenki.

Kansa ya yiwa ai."
in Haulatu kafin ta mi
e zuciyarta wasai don ji take kamar an raba ta da wani nannauyan dutse.

Hajja ta bi ta da kallo tana fadin "Yauwa
ar albarka, ke dai ki nusar da mahaifiyarki.

Duk ta bi ta saka ranta a damuwa."
Haulatu ta yi murmushi tunano da kalaman da Yaya Sadauki ya yi mata wanda a lokacin ta yi musu kallon marar dalili.

Umma kallonsu kawai take yi.

Ita ta san Hajja ta fahimci damuwarta saboda ga duk mai hankali ya san mutum irin
an Mutuwa ba mugu ne kuma babu tsoron Allahn da zai yi sanadin dakatar da shi ga aikata wani mummunan abin, shi ne babban dalilin Hajja na tausarta da
ara yi mata nuni da babu abin da zai faru.

Tabbas ta sani, yanzun ma addu'a ce ta yi nasara a kansa har ya zo ya yanke igiyar aurenta uku dake kanta, ta kuma sani a gaba ma addu'ar ce za ta yi tasirin da in sha Allahu ba zai cutar da ita da
iyarta ba.

Damuwarta me zai yi?

Wane matakin zai
auka?

Ta san shi a zaman shekara da shekarun da suka yi da juna, mutum mai kafiya da shegen taurin kai wanda babu gurbi na yafiya a zuciyarsa kwata-kwata.

Ai shi ba ma ya yafe laifi sai ya yi ramuwa a kai.

Ga kuma mamaki na wannan uban kudin da ya tara da take da tabbacin ba halaliyarsa ba ce, ko ta wace hanya ya bi ya tara?

Gefe
aya kuma tausayin aminiyar
arta ta ji, ha
a ta jefa kanta a hannun baragurbi wanda nan gaba za ta yi dana sani.

"Ke Na'imatu, ki fita idona na rufe.

Wato duk
atun da nake yi ashe ya tashi a banza?

Ina nunamaki gabas kina tafiya yamma?

Tunanin uban me ki ke yi da nake ta magana ki ka yi shiru?"
Maganar Hajja ta maido Umma duniyar da ta bari na lokaci, Haulatu wacce ta fito daga ban
aki tana gyara zaman hannun rigarta da ta na
e don yin alwala ta dubi Umma a raunane ta ce.

"Don Allah Umma ki cire komai a ranki, abin fa mu godewa Allah ne.

Hajja kusan kullum ina yawan kama ta cikin dare tana addu'a tana kuka.

Ni na san kuma addu'arki ce Allah ya amsa ya kawo mana waraka har gida."
Daga nan ta saka hijabi ta shimfi
a darduma ta bar Hajja na
orawa daga inda ta tsaya.

BAYAN KWANA BIYU...

KANO...

A yau ce ranar zuwa taronsu na
ungiya wannan ya sa ya kasa yin wani baccin kirki ba don komai ba sai don
oki da ya ke yi da ma
aguwa da ya yi ya je su yi magana da Uban Dodo don a san matakin
auka game da Na'imatu.

Ya rantse ba zai bar rayuwarta ta zauna cikin aminci ba har sai ya salwantar da ita, ya kuma aika mugun abu wanda zai hana ta sakat a duniyar da ta za
a madadinsa.

Har garin saurin ya fice taro ya mance bai fesawa Hindatu hodar da ya saba sha
a mata ba mai sa bacci.

Ita kuwa
arfe biyu da mintoci na dare ta farka daga bacci don yin fitsari.

Ganin ba ya gefenta ta yi tunanin ko ban
aki ya shiga don haka ta
an zauna tana aikin murza idanu gami da jiran ya fito ta shiga, gajiya da zaman ya sa ta fice zuwa ban
akin dake falo ta yi ta dawo, har ta kwanta na ta ji alamun fitowa daga ban
aki ba sai hakan ya sauya tunaninta, to ko dai ba ya ciki ba?

Ta mi
e da sauri ta hau buga
ofar, jin shiru ta bude, babu alamun mutum, ta fito ta rufe gami da fita zuwa sashinsa.

Nan ma wayam, ga dai kayansa na bacci da ya saka
azun ya cire su ya bar su a saman gadon, bandakinsa ma ta le
a ba ya nan.

Kamar mahaukaciya haka ta shiga duba dukkan
akunan gidan sai dai ba ta sauka
asa ba saboda tsoro.

A
arshe ta dawo
akinta ta fiddo wayarsa ta kira nan ma a kashe.

Ta yi saurin bu
e labule ta le
a farfajiyar gidan, motarsa da ya fita da ita
azun, ba ta nan.

"Na shiga uku." Ita ce kalmar da ya fito daga bakin Hindatu yayinda wani tsoro da firgici suka mamaye zuciyarta lokaci guda.

Ina Alhaji Ibrahim ya tafi toh?

Ita ce tambayar da ba ta da amsarta.

Wani wawan
ara Uban Dodo ya saki kafin ya zaro ido ya dakawa
an Mutuwa dake dur
ushe a gabansa tsawa mai firgitarwa.

"Kai!

Ai mu ba'a zuwar mana nan da wasa!

Me na ce maka?

Ban ce ka bi komai a hankali ba?!

Ka san irin ranar da Na'imatu za ta yi maka a gaba?!

Shi ke nan, yanzu ka sake ta!

Har abada kuma ba za ta dawo gidanka ba!

Dama na fa
amaka!

Idan ba ka bi a sannu ba za ka yi nadama."
Gumi ya tsirfowa
an Mutuwa, ya sani ba nadamar rabuwa da Na'imatun ake nufi ba don yana sonta, sai don wani babban mu
ami da girma da Uban Dodo ya hango masa samun shi nan gaba muddin bai rabu da ita ba.

Uban Dodon bai sanar da shi wannan labarin ba sai a ha
uwar da suka
ara yi a wannan daren.

"Tuba nake Jagorana, a yafemin.

A taimake ni a haskamin wata mafitar."
arya kake yi!

Ni Uban Dodo ba na magana biyu.

Tun da har ka rabu da ita, wannan rabo wuce ka.

Abu na gaba, ina maka albishir da cewa matarka na
auke da juna biyu, wanda ya kasance mallakinmu ne.

Ranar da abin da aka haifa ya fito duniya, ko wanka bamu yarda a yi mishi ba, ka kawo mana shi har mabiyarsa.

Wannan al
awari ne da ya zame maka dole ka cika mana."
Da girmamawa ya amsa da toh ya yi godiya kafin ya bar gaban Uban Dodon wani ya maye gurbinsa da na sa kalar bu
atar.

Koda suka fito a hanya
an Mutuwa sai huci yake furzarwa na takaici ya ma kasa magana duk da irin ruwan masifar da Hajiya Adama ke surfawa wai meyasa bai ji shawararta ba ya kwantar da kai har ya samu ya
ara shawo kan Na'imatun?

Ta
ara da fa
"Ni jikina ya ban tunda har ka ji Uban Dodo ya ce ka bi komai a sannu, toh dama akwai abin da ya hango.

Yanzu shikenan, watakila ma rashin sa'a da ba
in jini za ka yi kici
us da shi a harkokin siyasar da ka ke son tsunduma saboda rashin Na'imatun."
Ran
an Mutuwa ya
ara
aci, ya dube ta a fusace.

"Au, kin san da hakan shi ne ba ki ankarar da ni ba sai bayan ta faru ta
are?

Ina zan san cewa wani abin ya hangar min tunda ba saninsa na yi ba sai yanzun?"
Haj Adama ta ja tsaki.

"Aikin gama ya riga ya gama, yanzu dai ka yi kokarin cika al
awari da zarar lokacin haihuwar Hindatun ya yi kar ka kusa ka bari kowa ya ra
e ta, kuma ka zuba idanu a kanta."
Sunan Hindatun da ta ambata ya tunatar da shi bai fesa mata hoda ba.

Ya
an bugi sitiyari.

"Kash, kin sa na tuna fa.

Yau garin sauri na fitowa mu ha
u ban sumar da ita ba.

Ina da tabbacin za ta iya farkawa koyaushe cikin daren nan ta bincika ko'ina da zummar nemana."
ara jan tsaki karo na biyu.

"Wannan kuma matsalarka ce.

Sai ka san me za ka yi.

Tun farko ai sai da na shawarceka da koyamata
an korawar nan, da tana yi ko yaya ai da wata
ila yanzun ta kai Habasha."
Ya jinjina kai.

"Ni ma ina son ta iya harkar nan, sanadinta mu samu customers.

Kin ga idan ta koyawa wasu matan musamman wadanda suke cikin damuwa da tabon
a namiji, za su dinga sadaukar da ku
ensu wajen siya.

Ba ma su ka
ai ba, ina son har matasan
an mata su tsunduma wajen siya, yanzu samarin sun fi ba da ha
in kai yanda ya kamata.

Wa
annan duk
ananun matsaloli ne, yanzu babban takaicina shi ne damar da ta su
ucemin sanadin wautana.

Amma ba kya tunanin idan na saka wani ya aure ta kuma ya sakarmin ita ni kuma na ka na aure ta, damar ba za ta dawo min ba?"
Haj Adama ta yi dariya sosai kafin ta girgiza kai.

"Ni ban san wace irin kwakwalwa gareka ba wani sa'in, ban da wauta irin taka, waye zai
ara kallonka a mutum a cikin zuri'ar su Na'imatu har a
ara yarjemaka da batun aurenku karo na biyu?
Chapter 65 · 0% Book details