← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 109

Sashe 46

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Hafsat dake falo tana chatting jin shiru bai fito don ya ci abinci ba dai ga ta kamar an jefo ta
akin babu ko sallama.

"Wai Khaleefa mene ne haka?

Kwanaki nawa ka jera ba ka cin abincin gidannan?

Haka za mu yi ta rayuwar ka
i ci sai dai ka je waje ka cika cikinka?

Salon ka cigaba da jawomin zagi wurin yan uwanka a ga kamar kana cefane ba'a girkawar?"
Duk yanda ya kauda kai ya yi banza da ita sai da maganarta na
arshe ya sa shi
ago kai ya dube ta.

"Ina gargadinki, ki kiyayi harshenki da fa
amin duk abin da ya fito daga bakinki.

Kaf cikin
an uwana babu sa'an yin ki.

Stay within your limits."
Yanda ta ga yanayin fuskarsa da kaushin da muryarsa ta yi ya sanya ta turo baki kawai ta fice daga dakin, ta san halinsa, tabbas sau daya ta ta
a kuskuren fa
in wata magana akan Umminsa aikuwa a ranar ba ta kwana gidansa ba don dai Ummin da kanta ta je biko ta nuna lallai ya yi hakuri tunda ita aka yiwa ita ma ta yafe to shi ma ya yafe mata.

Shi ne dalilin da yasa take takatsantsan amma abin na mata zafi.

Ai koda ba ita ke girkawa ba a ganinta wulakanci ne ya ci abinci a gidansu.

Akwai sadda ta ji har wurin Hajja yake tarewa yana cin abinci daga bakin Fahima don ita din
ar gidanta ce sosai.

Fahima
awa ce ga
anwarta.

Wannan ne dalilin sabon su.

Takan zo gidan tare da
anwar Hafsat din su wuni ana hirarraki.
an Mutuwa cike da walwala ya dubi Hajiya Adama.

"Sai fa a soma shiri, aurena za'a yi shagalin da ba ku taba haskowa ba."
Ta yi dariya bayan ta mi
a masa wayarsa inda ya bu
o mata hoton Hindatu wanda musamman ta je ta
auka kala-kala a gidan hoto ta turamasa.

"Ba laifi, ta gaban mota ce.

Ina fatan ka yi wa komai tufka gudun samun matsala?"
an Mutuwa ya yi dariya.

"Kar ki damu Hajjaju, ai nan zuwa anjima zan je ba ga mahaifiyarta.

Komai na tafiya daidai.

Ganin farko kar ki so ki ga yanda uwar ta ru
e a kaina.

Idanunt fes ya ke."
Suka sa dariya.

"Ai irin su an fi cin riba a kansu.

Kai dai a wannan ganin da za ka yiwa Uwar ka tabbatar ka ji
a ta yanda ta dace."
"Ba sai kin fa
a ba, gida na siya mata ma, zan kai matar takardun gidan.

Daidai da ma'aikata zan zuba mata."
Hajiya Adama ta yi wata shewa.
an Mutuwa shegen kaya.

Ko tsinanne haka ya gan ka ya
yale."
Suka yi dariya kafin ya
an tamke fuska.

"So nake na shigar da batun Na'imatu da wancan shegiyar yarinyar gaban mai alfarma."
Ta jinjina kai
"Hakan daidai ne.

Amma me zai hana ka bari ka gama da babin auren nan da ka cicci
o.

A gani na gwara koda zuwa wajen Na'imatun za ka yi, ta gane cewa ba zaman jiranta ka tsaya ba.

Na gaba ya yi gaba.

Ai ni zan fi kowa farin cikin maido Na'imatu rayuwarka.

Koda kana da kyau ka
ara da wanka nake gayamaka,
iyarnan taka babbar kadararka ce.

Ka samu ka aurar da ita ga wani mai fa
a a ji
in.

Ko nan gaba sai ka ga an ci gaba da damawa da kai fiye da haka.

Za kuma ka
ara shiga cikin manyan mutanen da ba ka ta
a kawowa a kai ba."
Haka ta ci gaba da rura wutar lamarin a wajen
an Mutuwa har sai da ya gamsu ya kuma yi amanna da dukkan hu
ubobinta.

A Katsina kuwa, washegarin ranar da su Zaituna suka iso garin.

A yammacin suka shirya don zagayawa sakamakon Zaituna da zaman
akin ya ishe ta.

Tafe suke da Haulatun don zuwa
angaren Daddy Ridwan, Zaitunan ce zasu gaisa da iyalansa da kuma na Baban Kowa, iyakacinta dama wurin Baba Dakta da Baba Alhaji sadda suka zo gidan.

Safina ba ta nan sun fita kasuwa da Maama ita kuwa Radiya tana
angarensu.

Hajja ta dube su tana washe baki.

"Inyee, ke Nafi dube su kamar dama can sun san juna."
Haulatu da Zaituna suka dubi juna gami da yin dariya.

"To ai Hajja haduwar jinin kenan.

Allah ya
ara ha
a kawunansu."
in Maman Zaituna, Umma da su Hajja suka amsa da amin.

Hajja ta dubi Fahima
wacce ta zo gidan kenan sai bayan biki.

"Ke ba za ki tashi ku je yawon tare ba?

Ke meyasa kike da ba
ar zuciya ne irin na ubanki?"
Fahima dake kwance tana danne wayarta wacce Sadauki ya maida mata ita bayan Haj Hadiza ta saka baki, gaba daya sai ranta ya
aci da batun Hajja.

Dama can ba wani jituwa ta ke yi na sosai da Zaituna ba, don ita Fahima a duniyarta ta tsani koda
awance ne da wanda ya fi ta kyau, ta fi kaunar inda ta fi mutum ta yanda za ta wula
antaka son rai.

Ha
ewae kansu da Haulatu tun zuwansu ya tsayamata a ma
oshi sai da ta ji kamar ta arce ta koma gidansu amma Haj Hadiza ta yi mata jan ido.

A cewarta ta ina za ta saka idanun ta kula da takun Haulatun da Sadauki idan har ta
i zama ta koma?

A dole don tasan tana son Sadaukin yasa ta danne ta ha
ura.

Yanzu kuwa maganar Hajja sai ta ji ranta ya yi zafi har ta kasa
oyewa a fuska.

"Haba Hajja,
ila dai ba ta son hayaniya ne.

A
yalemin
iyata ta huta."
in Umma kenan cikin son nuni da goyon bayan Fahimar, ita kuwa Haulatu ta ji inama Umma ba ta saka baki ba a shigarwa wacce ba ta san
imarta ba.

Aikuwa Fahima ta
ara jin zafi na don me Umma za ta kira ta da
iyarta?

Kawai sai ta mi
e tana tura baki ta yi
asa, gwara ta fice daga sashin Hajjar ta ba su wuri.

Zaituna ta yamutse fuska tana mai zaginta cikin yaren Malay
asa-
asa yanda ta san Mamarta ba za ta ji ba.

Haulatu dai ba ta san me ta furta ba, suka kama hanya suka sauka.

Zaituna na mata mitar dama sam Fahima ba ta da hali.

Tun can wai ba su jituwa.

Ita ta rasa ma dalilin da yasa har mamarsu ba su kwanta mata a rai ba.

Wai kamar ba jinin
an gidan ba.

Halayyarsu ta sha bamban.

Ita dai Haulatu murmushi kawai take yi tana duban wayarta ganin missedcall din Hindatu.

Daidai lokacin da suka isa ga
ofar fita daga falon, a lokacin shi kuma ya sanyo kai da sallama.

Gaba
aya suka yi turus, Haulatu ta
an yi saroro, ta kalli wancan ta maida idanunta ga wannan.

A hankali kuma ta ga Zaituna ta sauke kanta
asa.

Gaida shi ta yi da harshen larabci, shi
in ma cike da basarwa ya amsa mata yana tambayar yaushe suka iso.

Ta ce jiya.

Daga nan ta ja hannun Haulatu wacce ita gaisuwar ma ma
ale mata ya yi a fatar baki suka gifta shi suka fice daga falon.

A hanya ta kula kamar Zaituna hawaye take fitarwa don haka ta ce su karasa bayan gidan wajen rumfa su zauna.

Aikuwa suna isa Zaituna ta ci kukanta, abin ya
an daki ran Haulatu, sai kuma ta tsinci kanta da jin tausayi da haushinta lokaci
aya.

Namijin me?

Akan me za ta tsaya tana zubda hawaye kan wanda bai
auke ta komai ba?

"Ki yi ha
uri." Kalmar da Haulatu ta iya furta mata kenan, ta ma rasa ta ya za ta rarrashe ta.

Zaituna ta jinjina mata kai kafin ta share hawayen fuskarta, abin ka da farar fata tuni fuskarnan ta yi jazur ga idanun ma sun
an sauya kala.

"A duniya idan akwai wanda na so kuma nake so har gobe, bai wuce Zaid ba.

Na kaunace shi tun ban san ma me nake yi ba.

Kaf a
an uwan Mamina babu wanda na sha
u da shi kamar shi a zamana a hannun Hajja, don a nan na soma karatun secondary.

Allah ya yi ni da son zaman Nijeriya, duk
in Abeena da haka, saboda son da yake min ya ha
ura ya bar ni wajen Hajja.

Muna chatting sosai da Zaid koda ba ya kusa, hakanan idan ya zo babban gida muke hira sosai, zai
auke ni mu je wurare masu kyau mu sha ice cream da sauransu.

Wautar da na yi, ina yiwa hakan kallon so, ashe
uruciya da hauka su ke fa
amin
arya.

Hum, Zaid bai ta
a sona ba, ban fahimci hakan ba sai da na kasa ha
uri na furta masa.

Ya fututtuke ya sauyamin jin da ya yi na furta da bakina ina kaunarsa kuma da aure.

Ya tabbatarmin shi ba ya kallona da hakan face
anwarsa wacce ya ke ji da ita.

Ke tun fa daga lokacin ya sauyamin.

Ban iya soyayya ba Haulat, haka na yi ta bibiyarsa da kuka da ro
o, na kwanta ciwo.

Sanadin wannan ciwon ya sa kowa ya gane halin da nake ciki don har suma na dinga yi.

Hajja da kuka wiwi ta ce ita fa kawai a daura auren koda Zaid bai amince ba.

Shi kuma a gaban su Baba Alhaji da su Baba Dakta, Zaid ya rantse ba zai aure ni don bai ta
a sona ba kuma shi ba ya kaunar ma auren zumunci sannan har abada ba zai yi shi ba.

Sannan fa ina dab da zana jarrabawar fit daga sakandire amma komai ya ficemin a rai.

Anan ne Hajja ta zo wuya, ita ma tace duk wanda ya
ara ro
on Zaid ya aure ni Allah ya isa ba ta yafe ba.

Haka suka yi baram-baram da Zaid da Hajja.

Tun daga nan jikina ya yi sanyi, na gane dagaske Zaid ba ya sona kuma kamar yanda ya furta har abada ba zai aure ni ba ya sanya ni ha
iyar maganin
era amma Allah ya so ni da rahmarSa ban mutu a wannan yanayin ba.
Chapter 46 · 0% Book details