← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 109

Sashe 108

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A baya ta tsane shi sosai, daga baya da kuma ta ji har a rai ta yafemasa komai, koyaushe addu'a da fatan shiriya take masa kafin mutuwa, wasu lokutan kuma idan tunaninta ya ba ta ko ya mutu ne, sai ta hau nema masa gafara da rahmar Allah.

"Please, ban son musu.

Ki kwanta ki huta kin ji?

Ko kina jin ciwo ne?"
Ta yi murmushin ya
e don a sannan ciwon ya lafa.

"Aa, amma don Allah ka bar ni na je gurinsa."
arashe tana
ara
ora hannunta na hagu kan hannayensu da ya sar
e wuri guda.

Bai sha mamakin saukowarta ba don dama ya san tuni ta sauko daga dokin fushin da ta hau na mahaifinta.

Ya sha kama ta tana zabga addu'o'i cikin dare.

"Shikenan.

Amma ki bari zuwa anjima, yanzu kinga akwai ba
i a gidan."
Ta narkar da fuska za ta
ara saka wai kukan.

Da sauri ya sumbaci le
anta kafin tace.

"Naji, na ji, tashi muje.

Kinsan kuka na tsana ai."
Ba musu ya taimaka mata ta mi
e.

Ba su kai ga fita ba suka yi karo da Ihsan
ar Haj Hadiza da ta taho da sauri don kiranta zuwa falon Baba Alhaji kamar yanda Daddy Ridwan da su Barr Dawud suka bu
ata.

Kai tsaye suka
unguma can.

A babban falon Baba Alhaji babu kowa sai zuri'arsu.

Aka rufe
ofar.

Baba Alhaji na daga
aki, su Daddy Ridwan ke falon tare da
an Mutuwa wanda aka ba ruwa ya sha, ga kuma abinci a gefe,
an matashin da ya rako shi, shi ya samu sararin ci, shi kuwa ba wannan ke gabansa ba, babban burinsa neman gafarar Bayin Allahn nan da ya ba
antawa a rayuwa ko zai ga haske can gaba.

Shigar Haulatu da sallama a bakinta, da Sadauki a gefe yana
an ri
o kafa
unta tana takawa ahankali ta shiga ciki.

Idanunta a kan
an Mutuwa.

Su Umma da su Haj Hadiza da Maman Zaituna suna daga gefe suna kallo.

Umma hawayen itama take yi, ta
arasa ta zauna.
an Mutuwa ya bi ta da kallo, yarinya
aya da ya mallaka a duniya.

Ba shi da uwa balle uba, amma ya kasa nunamata soyayya.

Karshe ma ya nemi jefa rayuwarta cikin u
uba da kuma
ata.

Bayan bu
e taro da addu'a ne Abba Ridwan ya nemi
an Mutuwa ya fa
i abin da ke tafe da shi.

Kamar jira yake ya soma magana da raunanniyar murya.

"Ba komai ya kawo ni ba sai na ba ku ha
uri na kuma nemi gafarar Na'imatu da Haulatu.

Ku yafemin, sanadinku na ga ishara kala-kala a rayuwata.

Ban kasance miji nagari gareki ba Na'imatu, na tabbata ba na daga cikin Uban da
iya za ta yi alfahari da samun sa."
Sai da ya
an tsaya ya
auke hawayen da suka zubo masa ya cigaba.

"Na ha
u da masifu iri-iri bayan kaucewa hanyar da Allah Ubangiji ya yi umarni a bi, na shiga
ungiyar asiri, ni ne safarar yara mata kanana da manya zuwa
asar waje don su aikata alfasha su turomana ku
i tare da Haj Adama.

Ni ne siye da siyarwar miyagun
wayoyi.

A
arshe da na rasa komai da na samu ta
atacciyar hanyar
ungiyar asiri, na ha
u da ciwon shanyewar
arin jiki, inda komai nawa ya bar aiki.

Mutanen da na ri
a matsayin yarana
an amana, su Duna da
an Aljan, sun bar ni a asibiti yashe.
arshe da ku
in magani da aiki ya gagara aka sallame ni a asibiti.

A sannan bakina ya bu
u ina iya magana kuma ina amfani da hannayena.

Da magiya da kuka da komai, na samu wani mai tausayi cikin Alhazawan dake zuwa asibitin ya bani dubu goma ya kuma siyamin keken Ruwa, iska, sanyi, rana, haka nake yawo a titi neman abin sadaka da kuma abin da zan sa a cikina.

Tun ina barar babu mai kallona, ko kuma na tara,
ata gari su yimin wayo su kar
e.

Da Allah ya so ni da shiriya, sai ya ha
a ni da dattijon kirki, kakan wannan yaron da muka zo tare.

Su ma da bara suka soma kafin su samu jarin siyar da ruwa a bakin titi.

Kakansa kuwa na siyar da goro a faranti.

Mukan zauna mu yi hirar rayuwa, a hankali kuma aka saba, yasan ina da
a sai dai ban ta
a ba shi labarin komai nawa ba.

Shi ya taimaka min da wajen kwana.

Mukan je masallaci tare, mu yi sallah mu saurari tafsirin Alkur'ani Mai Girma sannan mu dawo.

Daga nan na soma sha'awar daukar karatu.

Dattijon ya ji dadi sosai, ya kai ni wurin Malaminsa na zaure.

Na soma zuwa, ina
aukar karatu ina kuma kara nadamar abubuwan da na shuka.
arshe ina kuka na zayyanewa Malamin komai.

Bisa shawararsa da na dattijon na samu kwarin gwuiwar tunkararku don a duniya idan akwai wadanda na zalunta matsayina na marayan da bai ri
e maraicinsa ba ya biyewa abokai
ata gari ya lalace, toh su biyo bayan Na'imatu da Haulatu.

Ku dubi girma na Allah..."
Kuka ya hana shi
arasawa, falon kowa jikinsa ya yi sanyi.

Da
yar ya iya cewa.

"Ku yafe min.

Na tuba, wallahi nayi tuban da ba zan
ara waiwayar munanan aikin da na yi a baya ba."
"Na yafemaka Baba." Wannan furuci da ya fito daga bakin Haulatu sai da ya sa kowa kallonta da tsantsar mamaki musamman Umma, dama za ta iya yafe mishi lokaci guda haka?

Shi kansa
an Mutuwa sai da ya
ago kai yana dubanta.

Mi
ewa ta yi da wani irin
arfin hali don bata bari Sadauki ya ri
e ta ba ta
arasa gareshi ta dur
usa ta ri
e hannunsa.

Sai kawai ta fashe da sabon kuka wanda ya ba mutane tausayi.

"Na yafemaka Baba, ka
untata min sau ba adadi, amma wallahi na yafemaka.

Nima ina ro
on gafararka."
Wani sanyi da dadi ga kuma hawaye lokaci guda suka dirarwa
an Mutuwa.

Ya dafe kanta.

"Nagode Allah ya yi maki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya."
Ta amsa da amin, shi da ita kusan lokaci guda suka dubi Umma.

Ta kauda kai ta maida duba ga Barr Dawud mijinta.

Alama ya yi mata da idanu akan ta ha
ura mana, sai ta sauke ajiyar zuciya.

"Na yafemasa.

Allah ya yafe mu baki
aya."
"Toh Alhamdulillah, dama haka ake so, duk wanda ya yi maka ka manta ka yafemasa.

Ya kamata ku mata ku koma ga taronku, kar ya kasance an samu
ofar kananan magana duk da ba a raba ku da shi ko?"
Alh Yusuf baban kowa, mahaifin Radiya ya yi maganar yana karashewa da
ar dariya.

Nan kuwa duka aka mi
e har Umma, Haulatu na kokarin mi
ewa ta ji mararta ta kulle.

"Ya Allah!" Ta firta da
arfi gani da komawa ta zauna.

Nan da nan aka yi kanta, Sadauki ya tallofa ta a ru
"Haihuwa ce fa ina ji." Fa
in Khaleefa.

Duk sai kowa hankalinsa ya tashi.

Aka
auke ta zuwa mota.

Dan Mutuwa ya ce zai bi aka ce ya yi hakuri ya zauna.

Su Umma dai suka koma ciki ta yi kara saboda ganin kowa na son zuwa.

Abba Ridwan ne yace Maman Zaituna da Momin Mu'az ne ka
ai za su bisu.

Aikuwa haka kowa ya ha
ura.

Suna zuwa babu jimawa ta haifi
iyarta mace.

Labari na zuwa gidan aka hau sabon murna.

Zaituna ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta je asibitin.
an Mutuwa kuwa yana ji ya shiga hamdala.

Washegari kuwa aka sallamota bayan an ga komai lafiya.

Falon Hajja ya cika da mutan gidan zallah ana kar
ar jaririya, shi kuwa Sadauki sai shan murr yake yi wai a dole ba a kyauta masa.

Haka ya je inda Khaleefa da Mu'az har Zaid (wanda aikinsa ya dawo Katsina) suke tsaye, fa
i yake.

"Kai ni fa Allah zai min sakayya tsakanina da wacce ta fara kawo shawarar wankan gida a rayuwar Malam Bahaushe.

Haka nan muna zaune da matata a wani raba ni da ita wai wankan gida.

Toh na rantse wannan karon fa a gidana za ta yi jegon.

Bari su ga yanda zan
aukemusu ita."
Su Khaleefa suka kwashe masa da dariya wanda ya
ara sha
ar da shi.

Aikuwa kamar wasa da daddare ya shiga
angaren Hajja, nan ya ga Zaituna zaune da Khaleefa sun wani saka
an biyunsu a gaba suna kallo jikinsu a ha
e.

Harararsu ya yi yana kiran shi ba zai yi abin kunya ba, ya haye saman ya bar su da yi mishi dariya.

Ya iske Maman Zaituna zaune a
akin tana lalla
a Haulatu kan ta daure ta ci abinci ko yaya ne.

Bayan sun gaisa ya
an saci kallon Haulatu, ta kauda kai, ta san me ya kawo shi ba kuma ta so ya yi rashin ta idon a gabanta don haka ta
i kallonsa, da ace ma za ta iya mi
ewa ta bar
akin da ta yi.

"Mama, amma dai ba anan za ta zauna ba ko?"
Maman Zaituna ta fiddo ido.

"Idan ba nan ba ina kake son ta je?

Ai tana nan gidan sai ta gama wanka za ta tafi.

Wa zai kularmin da ita a gidan naka?"
Wani abu ya soki zuciyarsa, kamar yace ni zan kula da abina, ai da kai da kayan duka mallakar wuya ne, sai kuma ya yi shiru ya ha
iye.

Yana wani cin magani ya fice ya bar
akin Maman Zaituna na ka tsaya ka ga
iyarka amma ya ce sai gobe.

Gaba
aya Haulatu ta ji wani iri, hakan ba ya daga cikin
abi'un Maman Zaituna, mace ce mai faram faram da komai, sai kawai ta ji ta saka dariya.

Da sauri ta dube ta.

"My daughter, na iya acting ko?

Kar ki damu kin ji ko?

Kin zauna ne saboda surukarki kuma mamanki tace a bari ki yi wankan koda na sati ne sai ki koma gidanki.

Ba don haka ba kin fi kowa sanin bana son harkar wankan gidan nan, ita ma waccan yayartaki don su Na'imatu sun goyamata baya ne.

Amma tunda an yi suna dolenta su tattara su koma."
Murmushi kawai Haulatu ta yi.
Chapter 108 · 0% Book details