← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 109

Sashe 72

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan kun
are da Baba, ina son magana da ke kin ji ko?"
Ta amsa da toh, a nan ne ma ta
an sha mamaki, toh maganar me Maama za ta yi mata kuma?

Ko yana da dangantaka da wacce Baba Alhajin zai mata?

Ta hakura da canki-canka ta shiga falon Baba Alhaji da sallamarta.

Ya amsa yana rage
arar rediyon da ya ke ji, ya dau gilashinsa ya saka.

"Baba ina wuni, an sha ruwa lafiya?"
"Lafiya kalau Haulatun Hajja, ya ku ke ya su Umman taki suka sha ruwa?"
Ta amsa da lafiya kalau.

Ya jinjina kai gami da hamdala kafin gyaran murya ya biyo baya.

"Masha Allahu.

To dama akwai wata magana da aka zo min da ita
azun, shi ne nake son na ji ta bakinki."
Ji ta yi gabanta ya
an fadi, ta hadiyi miyau, babu abin da ta kawo a kai face Yaya Zaid.

Kenan don taurin kai da kafiya da naci irin nasa sai da ya samu Baba Alhaji da zancenta?

A ranta ta yi
wafa gami da
ara nutsuwa don jin me zai fito daga bakin Baba Alhaji.

"Babanki, Faisal.

Ya same ni da batun nemawa
ansa Mu'az aurenki, yace shi Mu'azun ya tabbatar masa kun fahimci juna kuma ku na son juna.

Duk da cewa na nuna musu a bar zancen har mu sallaci idi in sha Allahu, amma na fi son na kara samun tabbaci daga bakinki.

Kina son Mu'azu?"
Har wasu hawaye ta ga sun zubomata a fuska, kenan sharrin da Yaya Mu'az ya
ulla mata kenan?

Ta nan ya
ullo?

Sai ta ji ta tsane shi fiye da baya.

Ta girgiza kai.

"Ni wallahi Baba Alhaji babu wata soyayya tsakaninmu.

Kuma shi da Yaya Zaid ne suka ce su na sona, amma ni bana son dukkaninsu.

Ban ma san Yaya Mu'az ya zo wajenku ba."
"Ikon Allah, shi Zaidun ne ke sonki?"
Ta gya
a kai cikin muryar kuka na zallar takaicin wannan magana ta amsa da eh.

A
arshe ma sai da ta labartawa Baba Alhaji komai dangane da batun Zaid da Mu'az, ta
ara da fa
in.

"Ni fa Baba na fadamaku ba aure nake son yi yanzu ba, ni karatu nake so.

Ni sam ban shiryawa soyayya ba."
Murmushi Baba Alhaji ya yi irin nasu na manya.

"Shi ke nan Haulatu, ai magana kam an bar ta.

Kar ki damu kin ji, in sha Allahu su ma babu wanda zai
ara takura rayuwarki.

Da kaina zan ja musu kunne.

Ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu burinki zai cika ko bayan raina.

Aure kuma, sai wanda ke da kanki ki ka ji kina so, idan har mun yarda da nagartar wanda ki ka kawo, babu abin da zai hana aurenku."
Ta ji dadi sosai, ta kuma
ara jin
aunar Baba Alhaji a ranta.

Nan fa ta dinga godiya da addu'a kafin ya ce ta tashi ta je, kar ta
ara sanya damuwarsu a ranta.

Da haka ta fito ta nufi hanyar bene inda Maama ta yi.

A dakinta ta iske ta, ta rage kayan jikinta daga ita sai daura
irji za ta shiga wanka.

Maama ganinta sai ta zauna gefen gado, Haulatun ta zaune gefenta don sun yi sabon da suke mata kallon Uwa ga kuma sha
uwa da ke tsakani.

Ita ma Maama batun Mu'az din ta yi mata.

Nan fa ta
ara sanya wani kukan, ita Safina kawai ta ke tunanin ya za ta yi idan ta ji wannan zance.

Ta zayyanewa Maama daga farko har karshe, hatta Zaid mai nacin nuna mata so ba ta
oyemata ba.

Da yake Maama ta san da zaman Zaid, sai ta fi mamakin na Mu'az, ashe Haulatu ce yarinyar da yake cewa zai kawo ta gan ta matsayin wacce zai aura?

Dama abin da ya jefa ta cikin tunani bai wuce jin wai ita Haulatun ce ta amince Mu'az ya yiwa iyaye magana ba.

Yanzun ta fahimci shiri ne da kuma son zuciya irin na sa.

"Ni fa Maama yanzu Safina nake tsoro kar ta ji wannan maganar ta kasa fahimta na, ban ta
a ba su labarina da Yaya Mu'az ba.

Kuma duk saboda kar Safina ta ji babu dadi.

A zatona zancen ba zai ta
a fitowa ba."
Maama ta yi murmushi.

"Kar ki damu, in sha Allahu za ta fahimce ki kamar yanda na fahimceki.

Ni ma a farko ai kin ga ban fahimceki ba amma kuma dama ina tunanin ba lallai hakan ya kasance gaske ba, kin san zuciya da sa
e-sa
e dai.

Ku na da kyakkyawar ala
a ta zumunci tsakaninku, babu abin da zai hana ta yi maki uzuri."
Cikin narkar da murya ta ce.

"To Maama ki fadamata komai sai daga baya na yi mata magana."
Maama ta girgiza kai.

"A'a, da kanki nake son ki sanar da ita.

Idan da hali ma ki ja Radiya ku same ta har gida ku yi magana.

Na san dai Umma ba za ta hana ki ba."
Cike da gamsuwa ta gyada kai.

Maama ta ce ta kwantar da hankalinta komai zai zo da sau
i.

Daga nan suka yi sallama, Haulatu na jin kaso saba'in na damuwarta ta ragu.

Ko babu komai Baba Alhaji ya ce zai takamusu burki, kuma Maama ita ma ta
arfafa mata gwuiwa.

Tana zuwa ta ba Umma da Hajjah labarin komai har na Yaya Zaid.

Nan Hajja ta shiga zazzaga ruwan masifa.

Fadi take.

"Ni ban ta
a ganin cikakken marar kunya ba irin Zaidu, shi ya na da idon da zai dubi jikata ya ce yana so?

Eh lallai, da walakin ashe, wai goro a miya, shiyasa ya ke ta safa da marwar zuwa ya gaishe ni?

To aikuwa daidai nake da su.

Ke Na'imatu, lalubomin lambar wayar Safiyya ki bani nan, ni
anta zai nunawa iya shege?"
Umma ta
an numfasa.

"Ki yi hakuri Hajja, ai kin ji yanda suka yi da Baba Alhaji, tunda ya tabbatar da cewa zai takawa abin burki, don Allah kar ki kira Malama ki tada hankalinta.

Kuma yin haka zai sa Baba Alhaji tunanin kamar bai isa ya yi hukunci akan naki ba ne."
Hajja ta yi kwafa.

"Ashe zuciyar tasa ta banza ce, ai da sai na nunamasa ni Asma'u karr nake kallonsa.

Dama jikina ya ban ba don Allah ya ke jelar zuwarmin ba.

To ahirr dinsa, shi ma Mu'azun da ya ke wani raragefe, an
i a ba shi ita tunda ba ta so, haka kawai uwarsa ta salwantarmin da rayuwar jika?

Ke Haule ki kwantar da hankalinki, daga kaina aka bar yunkurin yiwa kowa auren ha
i a zuri'armu kin ji ko?

Yanda Yaya Usman ya fadi hakan ce za ta faru, ki maida hankali ga karatunki kamar yanda ki ke so."
Haka Hajja ta yi ta sababi ita dai Haulatu
an murmushi kawai ta ke yi, jikinta dai a sanyaye yake, har yanzu maganar na ba ta mamaki.

Yaya Mu'az ya cika mugu mai son kansa da yawa.

Shigowar Radiya ce ya sanya ta sulale ta bar falon suka yi
aki.

Ta sani, zancen ta ji ga dukkan alamu.

Dama kuma ta yi niyyar ta je wurinta.

A gefen Sadauki kuwa, wuni ya yi a waje bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i don a waje ma ya sha ruwa, koda ya zo ma
angarensa kawai ya shiga ya watsa ruwa sannan ya nufi falon Mominsa.

Su Fu'ad dake zaune su na hira ana buga musu su na ganinsa gaba daya aka nutsu suka gaida shi, ya amsa fuska ba yabo ba fallasa ya tambayi Momi Nuratu.

Suka ce tana sama.

Daga nan ya haye saman ya iske ta zaune tana waya.

Bayan ta kammala ya gaida ta.

Ta amsa tana mai jin tausayinsa a rai.

Wato dai shi ke son Haulatu amma ita ba ta sonsa?

Ko kuma dama tunaninsu ne ya ba su kamar yana sonta?

A bakin Mamin Khaleefa ta ke jin komai, takanas kawai ta kira ta da yamma ta hau ba ta labarin wai auren Mu'az da Haulatu za'a yi don magana ta je kunnen manya.

"Ya aikin?

Daddynka ya ce kun yi meeting ko?"
Cike da alamun gajiya ya yi
as da yatsun
afa.

"Eh Momi, yau na gaji sosai."
"Allah ya huta gajiya.

Bari na sa a hadomaka abinci."
an lumshe idanu kafin ya bude.

"No, ba zan iya cin abu mai nauyi ba.

Kun yi fruitsalad?"
"Ai fa, aikin kenan, ba ka son cin abinci, ba don ma jikin naka ba a ganewa ba ai da tuni ka zama kyandir tsabar siranta.

Bari a ha
omaka."
Ya yi murmushi kadan, wai shi zai zama kyandir?

Bayan ta gama waya da bayar da umarnin ha
amasa ta dube shi.

"Kana da labarin maganar auren Mu'azu da Haulatu?"
Bai san lokacin da gajiya da kasalar da yake tattare da shi ta tafi ba.

"What?

Ban fahimta ba Momi."
Jikinta ya
an yi sanyi, ko dai yana son ta?

A sanyaye ta ke fadamishi yanda aka yi.

Ta kara da fadin.

"Amma fa ban sani ba ko dagaske manyan sun ji, ni dai ban ji daga bakin Daddynku ba."
Ya rasa ma abin cewa don haka ya mi
"Ina zuwa."
Ba ta dakatar da shi ba, ta gama karantar yanayinsa, ransa a
ace yake.

Shi kuwa kai tsaye
angaren Baba Alhaji ya nufa wurin Maama.

Ya yi nasarar iske ta a falo tare da su Najeeb da Haidar yaranta.

Suna ganinsa suka gaishe shi, ya amsa yana mai musu alamar su fice da hannu.

Ba shiri duk suka mi
e suka fita, ya karasa ya zauna gefen Maama, idanunsa har sun ka
a.

Maama ta san dama za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya.

Kafin ya yi magana ta katse shi.

"Ka samu labarin abin da
aninka ya aiwatar kenan ko?"
"Maama, me hakan ke nufi?"
Haka kawai ya iya fa
i don magana na yiwa Sadauki wuya idan yana cikin
acin rai.

Haka yanayinsa yake shi.

Ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, fargabar kada ya rasa abar kaunarsa ta kau.

Ko babu komai ya samu tabbaci daga harshen da bai ta
a fa
amasa
arya ba, wato daga bakin Maama.
Chapter 72 · 0% Book details