← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 109

Sashe 81

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga ta iske yana waya yana zazzaga masifa da
ura-
uran ashariya.

Ba yau ta soma jin sa yana zage-zage ba da girmansa, abun ma kamar bai ta'azzara ba sai da ya gayyato mata wasu
an iskan
an daba gida suke kwana wai su Duna.

Bai ko kula da tsayuwarta ba sai da ya
ago ya gan ta ya ha
e rai ya katse kiran.

"Ke ya za ki shigo ki yimin tsaye ina waya?"
Hindatu ta
aure fuska.

"Ai kai zan tambaya, ta ya ya za ka shigo mana falo babu ko sallama kuma wai mahaifiyata na gaisheka tunda kai ba ka gaida ta, shi ne za ka bi mu da kallon banza ka shigo
aki?"
an Mutuwa ya saki baki.

"Ke!

Da ni ki ke wannan maganar?"
"An.."
Ai ba ta
arasa ba da ya yi wani taku da bai fi uku ba ya cimmata ya hau jigba yana ashariya, dama neman inda zai huce fushinsa yake sai Allah ya yi ta fa
o tarkonsa.

Jin ihun Hindatu ya sa Momi ba shiri ta shigo kamar an wurgo ta.

Ganin jinim da ke bin
afafun
iyarta ya sa ta sakin
ara.

"Wayyo na shiga uku!

Shikenan ka kashe ta!

Shikenan ka
arar da cikin!"
Tuni Hindatu ta sume, shi kuwa jin batun
arar da ciki sai ya tsaya cak!

Ya bi
afafun Hindatun da kallo, jinin da ya gani ya sanya shi jin wani irin fa
uwar gaba.

Kashedin Uban Dodo ne ya shiga amsa kuwwa a kunnuwansa.
_"Idan ka bari muka rasa abin da ke cikin matarka lallai ka sani za ka rasa dukiyarka!"_
Ai bai san sadda ya kinkimi Hindatu ba ya yi hanyar waje a guje, Momi ta bi bayansu ita ma babu batun
aukar mayafi balle takalmi.

Katsina...

Matashiyar
ar aikin Momi Nuratu mai suna Ummi, ta kammala ha
a komai na farfesun a wuta bayan tafasa kazar, jira ta ke yi kawai ya
arasa ta jiye a flask ta ba Fu'ad ya mi
a kamar yanda Momi Nuratu ta umarta.

Tana nan tsaye ta kafa waya a kunne tana sauraron labarin wani littafin hausa da aka tura mata audio
insa Jannat ta shigo kicin
in.

Ita a farko ma ba ta kula da ita ba sai da ta
araso sosai.

Cikin sauri Ummi ta kashe sautin gami da fadin.

"Sannu Anti, wani abun ki ke bu
ata?"
Jannat ta dube ta, kamar ta watsa mata harara sai ta danne ta jefamata murmushin ya
e don ita a duniya ba ta ta
a sakarwa
an aiki fuska, ba ma iyaka na gidansu ba, ko a nan
an aikin na gulmar irin girman kanta da ma yanayin yanda ta ke wula
anta su kai ka ce ba mutane ba ne.

"Yes, am..ku na da quaker oat a store?"
Ummi ta
an gane me take nufi tunda cimar Fu'ad ce, tana yawan dafamasa da safe.

Ta gya
a kai.

"Eh akwai."
Jannat ta kai duba ga tukunyar farfesun wacce
amshinta ya kara
e kicin din sannan ta dubi Ummi.

"Ok, je ki daukomin bari na taya ki
ora ruwan."
"Lah, ai akwai ma a kicin
innan, kin gan shi.
azu na damawa Yaya Fu'ad da safe, na mance ban maida ba."
Jannat ta ji kamar ta sha
o wuyanta.

Sai ta basar da cewa ok.

Ita dai Ummi mamaki ke
awainiya da ita, matar da tun zuwanta sai dai ta yi ta ba ta umarnin aiki kamar ita ta ajiye ta a gidan, amma kuma yau ita ke kokarin yin abu da kanta.

Ita dai ta karasa ta duba farfesunta ya yi, hankalin Jannat na kan Ummi dake kwashe farfesun tana zubawa a foodflask.

Ta kammala ta
ora saman tray ta
auraye
an bowl da serving spoon sai cokali duk ta goge ta
ora saman tray din.

"Na waye?" Cewar Jannat.

Ummi da girmamawa ta amsa.

"Na Yaya Sadauki ne."
"Kawo na mi
a masa, dama yau ba mu gaisa ba ashe ba ya jin dadi."
Kamar kar ta bayar tunda ga umarnin da Momin ta yi mata amma kuma ai ba ta isa ta hana Jannat ba.

Ba ta shiryawa cin mutuncinta ba don haka ba musu ta mi
a mata.

"Idan ya tafasa ki ha
amin kafin na dawo."
"Toh." Ummi ta amsa.

Bayan fitarta ba jimawa sai ga Fu'ad ya shigo.

"Ummi, ina sa
on Yaya Sadauki?

Ya kira yana fa
a ban kai masa ba."
"Yanzun nan Anti Jannat ta tafi ta kai."
an bugi bakin
ofar kafin ya fice yana mitar Jannat za ta jazamasa fa
an da ya fi na farko kenan, ai shi Yaya Sadauki muddin ya sanya ka aiki bai ga ka yi ba wani ya yi, to fa kawai ba ya maka uzuri sai dai ya ce dama ba ka yi niyya ba.

A
arshe kuma ya hukuntaka.

Wannan dalilin ya sanya Fu'ad sauri-sauri wajen bin bayan Jannat.

Har ya kusan cimma ta, sai ya ga ta dire tray din a hankali tana waige-waige, ganin za ta juyo ya yi saurin la
ewa a jikin ginin da ya raba corridor
in da barandar shiga wurin.

Mamaki ne ya cika shi ganin ta bu
e murfin ta kunce wani gari ta barba
a da sauri kafin ta
an gauraya ta hanyar jujjuya flas din sannan ta maida ta rufe.

Garin kuwa ta yi azamar
ullewa ta jefa a inda ta ciro.

Sosai Fu'ad ya razana, tana soma tafiya ya yi saurin
arasowa amma ya yi iyakar kokarinsa wajen shanye mamakinsa da firgicin da ta jefa sa ciki.

"Sis." Kusan a firgicen ita ma ta waigo, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya.

"Kai amma ka tsorata ni.

Sam ban ji tahowarka ba."
Ya yi dariyar ya
"Oh, ina ta sauri na cimmaki, uhm, don Allah bani na kai, na rantse idan Yaya ya ga ba ni ne na kai ba fa
a zan sha.

Yanzu ma haka ba jimawa sai da ya kira ni yana tambayar wai ina sa
onsa da Momi ta ce na kawo?

Shi ne na
arasa kicin Ummi ke cemin kin kar
a.

Taimaka please."
Daga yanayinsa ta gamsu da cewa bai gan ta ba don haka ta
an yi murmushi.

"Shikenan, kar
i ka kai.

Dama na so mu gaisa ne na ji ba ya jin dadi.

Amma idan ya shigo ciki na gaishe shi."
Ya sa hannu ya kar
a yana maida mata martanin murmushin.

"Yauwa godiya nake."
Daga haka ya
arasa zuwa
ofar
akin Yayan nasu ya
wankwasa kafin mur
a ya shige da sallama.

Sai da ta ga ya shige ya rufo
ofar sannan ta yi wani tsalle har da rawa don jin dadi, da sauri ta fice son ta sanar da Maminta a waya.
angaren Fu'ad kuwa, zaune ya iske yayan nasu a falo yana share hanci da tissue, saman hancin nan ya yi ja ga dukkan alamu yana jin jiki don ko a muryarsa za ka fahimci lallai yana fama da mura.

Bayan ya ajiye tray din ya tsaya, shi bai zuba ba kuma bai mi
e ba.

Har sai da Sadauki ya rage
arar tv dake aiki ya dube shi.

"Lafiya?"
Fu'ad bai yi nauyin baki ba ya labarta masa duka abin da ya faru.

Sadauki ya yi mamaki shi kansa, ya sani dama bai wani yarda da yarinyar ba har da zamanta a nan, sai dai bai kawo har wuyanta ya yi wannan kaurin ba.

Ajiyar zuciya ya yi.

"Dauka ka je ka ba masu gadi."
an tsorace Fu'ad yace.

"Yaya, kar ya cutar da su."
Murmushi Sadauki ya yi.

"Kar ka damu, ba abin da zai faru.

Ai ba su aka yi wa ba.

Na kuma sani, ko mene ne ba zai wuce don abu
aya ta yi shi ba.

Jeka ka kai musu, koda Momi ta tambaya ka ce ka zubamin na sha kawai."
Daga haka ya kwantar da kai, yunwa yake ji ba kuma ya jin
anon komai, amma ya gwammace ya ha
ura zuwa gobe.

"Ko a yi maka wani abun?"
Tambayar Fu'ad ta sanya shi
ago kansa ya kalle shi.

"No, kar ka damu, i'm ok."
Daga nan Fu'ad ya dauki flask din ya bi ta
ofar da za ta sada shi da farfajiyar gidan nasu kai tsaye ba ta
ayan hanyar da ya shigo ba.

Ba jimawa ya dawo ya ajiye kwanukan gami da yi wa Sadauki sallama, har zai fita ya ji Sadauki ya dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa.

Dawowa ya yi.

"Na'am." Ya amsa.

"Bana son kowa ya san zancen nan.

Koda Momi."
"Toh Yaya." Ya amsa ba don haka ya so ba domin jikinsa har tsuma ya ke yi don ya je ya sanar da Momin tasu.

Amma kuma tunda har Yayan nasu ya taka masa burki ya sani idan ya aikata zai yabawa aya za
inta.

Shi kuwa Sadauki ko bayan fitar Fu'ad lamarin ya yi ta juyawa a kwanyarsa, duka-duka nawa Jannat take da har ace ta san hanyar gidan
an tsibbu?

Waye ya koyamata?

Anya kuwa a gida an sani?

Haka ya yi ta watsawa kansa tambayoyin da rashin mai amsawa ya sa kawai ya rufe da addu'ar Allah ya shirye ta.
angaren Jannat ko, tana can cikin zullumi a falo, Zuhra na mata hira amma ita rabin hankalin ya na ga
ofa, so take ta ga shigowar Fu'ad, aikuwa yana zuwa ko zama bai yi ba ta ce.

"Ya jikin Yaya Sadaukin?

Ya kuwa samu ya sha farfesun?"
Fu'ad ji ya yi kamar ya zage ta, sai kawai ya daure ya ce eh.

"Kai Yaya Fu'ad, maimakon ma ka tsaya ya kammala ka kwasomana sauran mu sha?" Cewar Zuhra.

Harara ya banka mata sannan ya ja guntun tsaki yana mai mi
ewa lokaci guda, shi ba ya ko son kallon Jannat din.

"Au kodai tare ku ka sha ne ma?"
Zuhra da ba ta ha
ura ba ta
ara furtawa.

"Ki tashi ki je ki tambayi mai shi ba ni za ki tsaya yiwa tambayoyi ba."
Daga haka ya mike ya bar wurin don shi ko kallon Jannat din ma haushi yake ba sa.

Jannat dai dadi kamar ta yi me, ta tabbatar burinta ya kusa cika akan Yaya Sadauki.

Tabbas idan ta aure shi ta gama morewa.
Chapter 81 · 0% Book details