← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 109

Sashe 16

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayinda Haulatu ta baza kunnuwa tana sauraro sai faman washe ha
ora ta ke, babu ma kamar Hajiya Rabi da ta dage sai ta yi musu rakiya a goben, acewarta za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an kar
i Umman hannu bibbiyu.

"Uhm." Shi ne kawai abin da ya fito a bakin Umman.
*LATE ALH BELLO S MALUMFASHI RESIDENCE.*
Fitar tsiro
Page 13
*Late Alh Bello S Malumfashi Residence*
Haka aka rubuta a
aramin allo wanda ya sha adon ba
i da kuma ruwan zaiba da aka li
e a daidai tafkeken gate na shiga gidan.

Haulatu ta
auke kai daga saman allon ta mayar da idanunta kan gidan wanda kusan tun farkon layin har zuwa
arshe shi ne ya ci
angaren dama.

Gida ne mai adon fari da ruwan toka.

An
awata wajen da shukoki masu kyau inda aka gewaye wurin shukokin da wasu fararen
arafina sai kuwa fitilu dake jikin bangon wanda ko ba a fa
i ba idan dare ya yi su na taimakawa wurin da
awata su.

"Madams, ina zuwa?"
Hankalin Haulatu ya koma ga jibgegen
aton dake tsaye jikin
ofar shiga gidan, idanunsa akan Umma, sosai yake ganin kamanninta da mutan gidan, sai dai shigar da ta yi ko
an aiki albarka.

Hajiya Rabi cikin sauri ta amsa.

"Mun zo wajen Hajiya Babba ne."
ara duban Umma kafin ya dubi Haulatu, kai shi abin mamaki yake ba shi, to ko
an uwansu ne daga Malumfashi?
arshe dai ya ce su jira yana zuwa.

Cikin
akinsa na gadi ya koma ya danna kira
angaren Hajiya Babba.

Koda aka amsa ya yi bayanin an yi ba
i, babu
ata lokaci aka ba da umarnin su shigo.

Ya sani dama idan har
angaren Hajiya Babba ne, ba a fiye disga ba
o ba.

Matu
ar aka zo ganinta, to fa koda ace jikin girma ya hana ta fitowa wurinka, ba za ka tafi hakanan ba.

Dawowa ya yi ya yi musu iznin su shiga.

Nan fa
suka shigo farfajiyar gidan da ya kusan tafiyar da numfashin Hajiya Rabi da Haulatu.

Ita dai Hajiya Rabi tun da take ba ta ta
a shigowa gidan S Malumfashi ba sai dai ta ji ana ko
a shi a wani wurin, ga Haulatu kuwa, ta sha jinin jikinta don ba ta hangi inda za su sami matsagini a gidannan ba ita da mahaifiyarta.

Umma kuwa
irjinta ke bugu da sauri-sauri, hatta da jikinta rawa yake yi.

Ta daure ta shiga ambaton sunan Mahaliccinta.

"Kun san hanyar kuwa?" Suka ji sautin Maigadin na tambaya.

Kamar wasu
adangaru haka Hajiya Rabi da Haulatu suka shiga girgiza masa kai.

"Hey!

Siii!" Suka dubi wanda yake kira don su gaba daya yanda suka shagala da kallon gidan bai sa sun kula da wanzuwar wata halittar bayan su hu
un ba.

Wani ne sanye da irin uniform din dake jikinsa, ga dukkan alamu shi dinma abokin aikinsa ne sai dai shi saurayi ne bai kai shi shekaru ba.

"Kai su wajen Hajiya Babba."
Ya dube su, baki ya
an bu
e ganin Haulatu, da idanunsa suka sauka kan Umma kuwa, sai da ya
an fiddo idanu.

"Wai ba ka ji ba?" Cewar babban a
an fusace hakan ya sa shi soma tafiya su na binsa a baya.

Haulatu ta
irga gidaje masu kala iri guda biyar curr sai kuwa wasu gidajen a gefe guda masu kala daban.

Har suka
arasa
angaren matar da aka ambata da Hajiya Babba ba su ci karo da kowa ba kai ka ce babu kowa sai su
in.

Saurayin ya
arasa ya
wasa
ofar, can babu jimawa aka bu
e.

Wata
ar dattijuwa ce.

"Baba Saude, ga ba
in Hajiya nan.

Bismillah ku shiga."
Ya fa
i yana mai ba su wuri, Dattijuwar da aka kira da Baba Saude ta dube su, ta
urawa Umma idanu tana mai cika da
umbin al'ajabi da mamaki.

Hanya ta ba su suka shiga ciki, har sannan kallonta take yi.

"Wannan fa?" Ba ta san tayi furucin ba sai da ta ji Saurayin nan ya amshe zancen.

"Kema kin ga kamanninta da Hajjaju ko?

Ba
ar uwarku ce ba daga Malumfashi kuwa?"
Ya yi tambayar cike da son jin
waf, Baba Saude ta harareshi.

"To shaida, kai dai Bilya ban san sadda za ka shiga taitayinka ba.

Wuce ni ka ban wuri."
Daga haka ta rufe
ofar shi kuwa ya yi dariya ya bar wajen.

Su Umma kuwa da Hajiya Rabi duka su na tsaye suna sauraronsu, ba su yi karambanin
arasawa cikin falon ba.

Sai dai su na bin ko'ina da kallo, falon daidai gwargwado ya tsaru, har da wajen dinningtable a gefe, sai kuwa wani tafkeken talabijin a jikin bango dake faman aiki kai ka ce za ka yi magana na cikinsa ya amsa.

Falon sai
amshin turaren wuta yake ga lafiyayyen kafet dake shimfi
"Bismillah ku shigo ku zauna." Ba musu suka
arasa suka nemi wuri
asan kafet suka zauna.

Baba Saude ta
araso aka hau gaisuwa ita dai idanunta ya kasa kaucewa akan Umma da Haulatu masu tsantsar kama da Hajiya Babba.

"Bari na yiwa Hajiyar magana." Daga nan ta mi
e ta nufi wani
an tsukakken wuri da aka yi bene.

"Wai Allah, Allah ka yi mana arziki duniya da lahira.

Hajiya Na'ima Allah yasa kun shigo a sa'a.

Ni wallahi wannan fargabar da kike yi ne bana so, ki yi ta addu'a in sha Allahu komai zai tafi daidai.

Naga gaba daya tun zuwanmu kin rasa sukuni."
Umma dai
an murmushi ta yi wanda ya fi kuka ciwo jin maganganun da Hajiya Rabi ke yi, amma dagaske a tsorace ta ke.

Ko wace ce Hajiya Babbar nan?

Ita ce mahaifiyarta ko kuma mahaifiyarta ma ta jima da rasuwa ne?

Wa
annan tunane-tunanen su ne suka yi ta
ara jefa ta cikin fa
uwar gaba.

Hajiya Babba, tsohuwa mai ran
arfe.

Yanayi na hutun da take ciki ya taimaka
warai wurin
oye tsufanta.

Allah ya yiwa zuri'a baiwa ta kyawun jiki.

Tana zaune saman darduma hannunta ri
e da carbi bayan ta idar da sallar walha.

Sallamar Baba Saude ce ya sa ta dubanta gami da yin gyaran murya na yi mata iznin shigowa.

Ta shigo ta nemi gefe ta zauna.

Mintuna uku kafin Hajiya Babba ta shafa addu'a ta dube ta.

"Saude, akwai abin da ake bu
ata?"
Cike da girmamawa Baba Saude ta amsa.

"Ko
aya Hajiya, ba
i kika yi."
Hajiya Babba dake kokarin cire gilashin karatun da ta ma
ala a fuskarta, ba tare da ta dube ta ba ta janyo gidan gilashin ta ce.

"Su waye haka da safe?"
"To, nima dai ban gane fuskokin ba.

Ba zai wuce wasu cikin yan uwanku na Malumfashi ba don na ga kamanni."
an yi jim kafin ta amsa.

"Ikon Allah, ba damuwa, shigo da su nan."
Baba Saude ta mike bayan ta amsa mata da toh.

Ita kanta za ta so sanin su waye a cikin dangin nasu don ba ta ta
a ganin fuskar ba sai a yau.

Ta
arasa sauka gami da yi musu iznin su biyo ta.

Suka mike suka soma taka matattakalar, Umma dai
irjinta dukan tara-tara yake.

Yau ne karo na farko da za ta sadu da wani a cikin zuri'ar mahaifiyarta, ko wani irin tarba za ta samu?

Allah masani.

Sallamar Hajiya Rabi ce ta sa Hajiya Babba kallon hanya.

"Wa'alaikumussal..."
Sauran sallamar ya ma
ale a bisa fatar bakinta sadda ta ci karo da photocopy
inta sadda take Hajiya Asma'unta.

Umma ma kallonta take yi jikinta babu inda ba ya rawa, idan har wannan matar ba ta kasance Uwa a gareta ba, shakka babu jininta ce.

"Asma'u Bello?" Umma ta samu bakinta da furucin cike da rawar murya.

Hajiya Babba ta ha
iyi wani miyau ma
wat ya wuce jin sunanta
aro-
aro a bakin wannan baiwar Allah.

Ga Haulatu kuwa ta dubi Ummanta ta dubi Tsohuwarnan, hakanan Hajiya Rabi da ta yi sandar tana ganin ikon Allah.

Bambancin Na'ima da wannan tsohuwa sai fa shekaru.

Umma kuwa, ambaton sunayen Allah da ta dinga jerawa a zuciyarta shi ya ba ta damar jin
arfin gwuiwar soma magana.

"Hajiya Asma'u Bello, wajenta na zo."
Hajiya Babba ta ji kirjinta ya buga, le
anta suka yi nauyi.

Kar dai ace allura ce za ta tono garma?

Kada dai asirin da ta riga ta binne a bayanta, shi ne bai tashi tonuwa ba sai da shekaru suka mi
a har tafiya ta yi tafiya?

Wani gumi ta ji ya tsirfo mata.

Kafin ta kai ga ba da amsa ta tsinci muryar Baba Saude na fadin.

"Ai da ita kike magana Baiwar Allah.

Wannan
in ita ce Hajiya Asma'u ake kiranta da Hajiya Babba.

In ce dai lafiya?"
Jin haka yasa Umma
ara kallon Hajiya Babba da gaba daya ta ru
e.

Ta rasa me za ta yi, murna ko ba
in ciki.
angaren Haulatu kuwa, murmushi kawai take yi mai bayyana ha
ora.

Ita sosai ta ke jin wani dadi tana
ara bin gidan da kallo sannan ta maida hankali ga tsohuwar da ta kasance kaka a wajenta.

"Wace ce ke?

A ina kika san ni?" Tambayar da Hajiya Babba ta watsamata kenan.

"Ku zauna mana kuna tsaye."
Cewar Baba Saude don ganin abin na yi ne.

Bayan sun nemi wuri sun zauna ta baza kunnuwa don jin abin da zai fito daga bakin Umma.

Sai dai madadin Umma ta yi magana, kawai sai ta sa hannu ta fiddo hoto ta mi
amata tare da wani abin hannu na azurfa mai kyau da ba ta ta
a karambanin fiddo shi ba ko a baya, ta yi mishi ajiya mai nisan da ko hoton ba ta adana haka ba domin shi din sunan Asma'un ne da Maikalangu a ha
e wuri guda.

Hajiya Babba hannu na rawa ta kar
i hoton gami da abin hannun.

"Saude ina gilashina?" Ta furta da rawar baki.

Baba Saude ta cika da mamaki, da sauri ta dauki gilashin ta mi
amata, Hajiya Babba ta zura ta karanta rubutun dake jikin azurfar kafin ta kai duba ga hoton har da juya bayansa ta ga kwanan wata da kuma na gari da aka rubuta a jiki.

Shikenan, ta faru ta
are wai an yiwa mai dami
aya sata!
Chapter 16 · 0% Book details