← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 109

Sashe 107

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma ta rantse nan duniya ba za ta
ara wani auren ba idan ba shi ba.

Haka take waya su gaisa da Umma, tun tana ro
onta akan ta sa baki ta dawo
akinta har ta ha
ura don Barr Dawud ya ce ma Umma kar ta sake ta
ara yi mishi zancenta.

Wannan babban dalilin, da kuma tonuwar asirin cewa da Momin Mu'az suke yawon gidan bokaye ya sa gaba daya Momin Mu'az ta tsorata ta kuma tuba ta yi al
awarin ba za ta
ara ba.

Ita ma dai sai da ta
ana ku
arta don har girkinta daina ci Abban Mu'az ya yi a
arshe kuma komai ya wuce ya yafe mata da manyan sharu
ai.

A yanzu haka Jannat tana auren wani hamsha
an siyasa suna zaune a Abuja, haihuwar Zaituna yasa ta zo takanas da yarinyar da take goyo Hidaya.

Tsakaninta da Haulatu babu komai face zumunci.

Fa'iza ma ta ha
ura tun sadda Khaleefa ya auri Zaituna, itama ta samu mijinta
an Katsina, tana aure da zama a garin.

Haka Haulatu ke ta tunanin rayuwa har ta samu wuri ta zauna ta yi shiru ba tare da ta kula ma da wanda ke gefenta a zaune ba.

"Haulen Hajja, ko abin ya zo ne?" Ta
an waiga, ganin Anti Mabruka da Maama ya sa ta sakin fuska da murmushin ya
e, shakka babu tana
an jin ciwo sai dai bai yi
arfi ba sosai.

"Lafiyata kalau Anti, Maama, ban ga Ashraf ba tun
azu."
Ta maida akalar zancen ga Maama.

"Ya bi Babansa, kinsan shi har yanzu ba son zama a taro yake ba.

Gwara su yi gaba na samu na huta nima."
"Ke dai Maama kina ban mamaki, a duniya na kula bakya son raino.

Kuma naki kike yiwa haka, amma
an kowa zai rayu hannunki lafiya kalau." Fa
in Anti Mabruka kenan tana kokarin bu
e murfin robar ruwa bayan kammala cin abinci.

"Nawa nake raina, Ashraf naku ne, ku ya kamata ku ji da shi."
Fadin Maama kenan.

Murmushi Anti Mabruka ta yi.

Haka suka hau hirarsu, Haulatu na kallonsu tana murmushi, hamdala take a
asan ranta na yanda su biyun suka ha
e kansu tun rasuwar mahaifiyarsu Inna, tsohuwa mai ran
arfe, ta sha jinya kafin lokaci ya yi.

Tsirarta da Nene uwargidan Baba Dakta shekara
aya.

Anti Mabruka ta yi aure har sau biyu, auren farko ta ci ba
ar wuya a hannun mijin wanda ya zo mata da
arya ya nuna shi
in mai arziki ne, nan duniya ta
i amincewa da za
in da su Baba Alhaji suka yi mata ta ce ita wannan take so.

Da yake ba sa yiwa kowa dole sai aka yarda aka aura mata shi.

Tun daga gidan da aka kai ta ta ji hankalinta ya tashi, gida ne duk sumunti wanda aka
an yi ado da broken tiles a tsakar gidan.

Kujerunta sun
i su ci falonta hakanan aka koma da wasu.

Ciki da falo ne
aya sai fallen
aki guda.

Sai wani ban
aki a tsakar gida sai ko kicin
inta.

Kunyar duniya suka kama Anti Mabruka, ta buga tsalle kan ba za ta zauna ba.

Baba Alhaji ya zuciya ya ce bata isa ba, haka ta soma rayuwa marar da
i.

Miji kuwa ta ki ba shi ha
in kai, fa
a suka yi kaca-kaca, karshe ko sati ba ta cika ba cikin dare aka shigo tana wani mugun bacci da ba ta san ya aka yi ya
auke ta ba, aka sace duka kayan lefenta da ma suturu da gwala-gwalan da ta taho da shi.

Koda ta farka ta ga miji na bacci ta waiga ta ga alamar an shigo dakin ga shi nan a wangale yasa da sauri ta hau bincike, nan fa sabon rikici ya
alle inda ta rantse ta
ara akan cewa mijinta na da hannu a wannan satar.

A sannan ya kama ta ya yi mata lis da igiyar wuta, sai da ya ga ta daku sosai sannan ya rabu da ita.

Tun daga nan ya ma hana ta fita don dama an kwace wayarta, kusan kullum sai ya jibgeta duk sadda ta masa rashin kunya.

Kuma hakan bai hana ya kusance ta ba duk cizon da za ta yi da yakushi.

Maama ta taimaka mata sosai don a ranar da ta kai mata ziyara ta ga halin da take ciki da yanda ta koma, ta
aura damarar kwatar mata ha
inta.

A sanadin Maama ta ku
uta daga azabar wannan bawan Allahn, don har
arin ciki ya sa ta yi sanadin duka amma bai fa
awa kowa ba, ita ma mugun halinta ya ja babu wani nata da ke kawo ziyara gidanta.

Taimakon da Maama ta yi mata yasa ta ji kunya sosai ta kuma yi nadama tsantsa.

Da
yar Baba Alhaji ya iya yafemata.

Koda ta kammala iddarta babu jimawa ta samu miji, tana zaune lafiya da shi, matansa biyu ita ta uku amma kowa da
angarensa.

Ba shi da kudi sosai sai rufin asiri, amma suna zaman su lafiya.

Yanzun hankalinta kwance.

Hawaye ya tahowa Haulatu ta yi azamar juyawa ta share su.

Hamdala ta kara yi a zuciyarta na yanda komai yake sauyawa daga marar kyau zuwa mai kyau.

Le
anta ta
an ciza sakamakon mararta da ta
ulle, can kuma yana saki ta mi
"Ina za ki je?

Ki dinga zama kina hutawa fa." Fa
in Maama tana kallonta.

Ta yi murmushi.

"Maama wurin su Radiya zan je."
"Toh." Ta amsa.

Suhail ne ya taho a guje yana
wala mata kira, Mami!

Mami!!

Ta juyo gami da dakatawa tana kallonsa da alamar gajiya.

"Ya aka yi Suhail?" Ya ri
o hannunta ya
an soma ja.

"Ki zo wani ne ke kiranki, wani gurgu a waje muna wasan keke da su Yaya Affan, Buzu Maigadi ya hana shi shigowa sai kuka yake yi."
"Haulatu, wai wani ne ya zo yana nemanki ke da Umma."
ara jin muryar Radiya a gefenta, kafin ya farga ta ga Umma ta nufi bakin
aton
yauren gidan ita da su Malama da Momi Nuratu.

Ga kuma su Safina a can,
irjinta ya shiga bugu da sauri-sauri, ta zare hannunta daga na Suhail ta nufi hanyar gate
in.

Kar dai wanda ta ke yawan mafarki ne ya zo?

Kai a'a, ya mutu, Hindatu ta ce mata ana zargin ya mutu.

Don haka ba shi ba ne, amma kuma waye?

Ta kasa ba kanta amsa, a hanyar Radiya ke ce mata wai gurgu ne a saman keke sai wani
an matashi dake faman tura shi.

Ita dai tuni ta
ara sauri, kafin ma su karasa
an gayyar suna sun cika wajen.

Daidai lokacin su Khaleefa da Sadauki suka taho, sun zo ne don yin hotuna kamar yanda Zaituna ta nema da magiya akan ita su zo a yi a ajiye tarihin sunan
an biyu.

Suna hango cincirindo a
ofa ya sa Muhsin mijin Safina fadin.

"Toh, lafiya kuwa?"
Babu wanda ya amsa sai
arasawa da suka yi wurin.

Umma ce ta soma tozali da shi kuma ta gane ko waye, a duk irin sauyin nan da ya yi na ba
i, rama da fita hayyaci, ga kuma yagalgalun kaya ba za ta kasa gane ko waye ba.

"Ibrahim?

Kai ne haka?" Ta yi furucin cike da
umbin mamaki.

Jin sunan da Umma ta ambata ya sa Haulatu da ke kokarin ture jama'ar dake gabanta ta shiga ta ja baya tana ji kamar kafafunta na kasa
aukarta.

Wato shi ne ya zo?
an Mutuwa ne?

Ji ta yi an ri
ugunta sadda take shirin kai wa
asa sakamakon jiri da ciwon da take ji a mararta.

Ido hu
u suka yi da mijinta.

Su Khaleefa ne suka bu
e hanyar suka ce kowa ya matsa gefe.

Hakan ya ba Haulatu damar ganin mahaifin nata zaune a keken guragu, ga dai
afafun amma da alama sun samu wata matsalar.

Ya yi wata iriyar rama sai karan hancin tamkar biro da suka
ara fitowa tsabar babu tsoka a jikinsa.

Cikin muryar kuka yake fadin.

"Ni ne Na'imatu, wallahi ni ne
an Mutuwa ne.

Kin ga yanda rayuwa ta maida ni ko?" Umma da hawaye suka wanke fuskarta ta juya da sauri ta ratsa mutane ta bar wurin duk kuwa da irin kiran da
an Mutuwa ke mata yana furucin ta yafe masa amma ba ta ko juyo ba.

Haulatu wacce Sadauki ya tallafe yana kokarin barin wajen da ita, sai ta ji ba ta son tafiya.

Tunda take a duniya ba ta ta
a ji har cikin
on ranta ta tausayawa Babanta ma irin na yau.

Ta ji zuciyarta ta yi wani irin karyewa ga ciwon marar dake
ara gaba.

"Ba..ba." Ta furta da muryar da ya ratsa kunnen Sadauki tunda shi ke kusa da ita.

Ya
an kalle ta, hawaye take yi, ta dafe mararta da hannunta na dama.

Ita ma shi take kallo.

Nan da nan ya dubi Mu'az.

"Ku shigar da shi ciki, ku kai shi wurin Baba Alhaji."
Mu'az zai yi magana, Sadauki ya tamke fuska, ba shiri kuwa ya juya don bin umarni.

Kowa ya koma ciki, ba
i na mamakin faruwar lamarin nan.

Wato dai duk sharrin da ake yi da kananan magana akan Haulatu ba ta da Uba, ashe dai akwai?

Kuma yana raye?

Haka suke ta tattauna, a baya kam sanadin Momin Mu'az da Mamin Khaleefa wata gulma ta ya
u wai Haulatu ba ta da Uba.

Shegiya ce kawai Umma ta zo gidan da ita.

Ta hanyarsu magana ta ya
u na zargin kamar ma tana da cutar
anjamau, duk a dabararsu na cusawa mutan gari da yan uwa tsanarta.

Sai dai ha
ansu bai cimma ruwa ba a lokacin haka suka ha
ura.

Ba wanda ya
ara bi ta kan
an Mutuwa, Sadauki dai ya ja matarsa
angaren Hajja zuwa
aki, so yake ta kwanta ta samu hutu amma ta
i, gaba
aya ita dai burinta ta je ta ji me ya maida mahaifinta haka.
Chapter 107 · 0% Book details