← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 109

Sashe 35

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Alhaji ma ya yi alkawarin muddin jarrabawarmu ta fito zai sa a nema min admission a Al-Qalam na cigaba da karatuna.

Ke dai ki taya ni addu'a kin ji?"
Ita ma Umma murmushin ta yi tana mai kauda kwallar da ta cika idanunta ba tare da ta yarda sun zubo ba.

Idan wasu lokutan ta dubi wannan sauyi na rayuwar da suka samu, sai ta
ara fahimtar a rayuwa ba a fidda rai da rahmar Ubangiji.

Komai kuma yana da lokaci idan bawa ya yi ha
uri to fa babu wani abu da ba zai zama tarihi ba.

Babban burinta na gaba a duniya bai wuce ta ga auren Haulatu ba.

Shirye-shiryen azumi ya kankama, ana gobe za'a
auki azumi, Haulatu na zaune sashin Baba Dakta suna hira da Maama da Safina sai Radiya da wasu yan mata su biyu na gidan wadanda ba wani sabo ta yi da su sosai ba sai dai a wannan ranar sun dan sake koda sun tsoma baki a hira takan amsa idan an sanya ta ciki.

Batun ankon
anne da yayyu mata suke yi da aka fitar na bikin su Raudha,
ayar mai suna Saddi
a ta na aikin kushewa a cewarta sam kalar atamfar bai mata ba.

Kowa dai na fa
in ra'ayinsa a haka suka ji sallamar sa ya shigo falon.

Gaba daya suka waiga suna masu amsawa.

Haulatu suka ha
a idanu ta yi saurin kauda kai.

Ita kam ta shiga uku, me kuma ya kawo wannan mai nacin kallon garin a yanzu?

Tana ji ya karaso ana gaishe shi amma kallonsa ma ba ta yi ba.

Kusan shi ne ya kula da ba ta gaida shi ba don duka baki suka ha
a wurin gaishe shi, a zaton Maama, har da ita.

Maama ta kalle shi fuska a sake daidai sadda yan matan ke mikewa su duka a kokarinsu na fita a falon.

"Mutanen Abuja, dama kana tafe ba sanarwa?

In ce dai lafiya?"
Zaid ya yi murmushi, ya dakatar da yan matan.

"Kai ina za ku je?

Ku yi zamanku."
Suka
an dubi juna jin abin wani banbarakwai, sam ba su saba da zama a wuri idan yana nan ba, kusan kamar wasu dodonni haka suke ganinsa shi da Khaleefa da Sadauki, gwara Mu'az yakan sake idan ya ga dama.

Idan kuwa sun kula ranar babu walwala tattare da shi, to fa sukan kama kansu su ja baya daga shiga sabgarsa.

Haulatu kamar ba ta ji ba ta yi gaba yayinda su kuma suka dawo wajen zaman su.

"Ke, ba ki ji me aka ce ba?"
Ya yi maganar cikin dakiya don ba ya son fallasa abin da ke ransa.

"Haulatu ina za ki je?

Zauna mana ku cigaba da hirar ku." Fadin Maama.

"Maama zan je ne lokacin shan maganin Umma ya kusa, ni ke tunasar da ita."
"Toh, je ki idan kin ba ta kya dawo."
Daga haka ta juya ba tare da ta
ara kallon Zaid ba wanda ta ji a jikinta ita ya ke kallo.

Gaba daya sai ya ji ransa ya
aci, ya bi ta da idanu har ta fice a falon.

Shi kam ba abin ya bi bayanta ba saboda Hajja, bai ga me zai sa ya shiga
angarenta ba.

"Are you ok?" Ya ji tambayar Maama a tsakar kai, lumshe idanunsa ya yi kafin ya dube ta yana mai
alo murmushin da bai kai zuci ba, tsaf ta karanci akwai wata damuwar binne a zuciyarsa, sai dai kuma me nene?

Ba ta da masaniya, har Safina ta kawo ruwa da lemo da kofi a tray ta ajiye a gabansa bai ce uffan ba, ganin haka sai Maama ta dube yaran ta ce su ba su wuri.

Dama su hakan ya fi musu dadi don ba wani sabo suka yi da shi ba.

Da sauri suka mike suka yi
aki.

"Meke faruwa?

Ko wani abu ya faru tsakaninka da Jalilah?"
'No Zaid, you have to control your feelings, zai zama abin kunya wani ya ji kana son jikar Hajja.' Wani
angare na zuciyarsa ya kwa
e shi.

Nan da nan kuwa ya saita kansa gami da wayancewa da bude gorar ruwa yana murmushi.

"Ko
aya Maama, kawai dai na gaji kaina ke
an ciwo.

Haka yau na tashi da shi."
Maama ta bishi da toh gami da tambayarsa ko ya sha magani don ita kam ba ta wani gamsu da abin da ya ce ba.

Ai ba ta jin ko iyayensu sun yi musu karatun da ita ta yi musu.

"Yau ka shigo garin amma ko?

Don jiya da dare ma mun yi waya da Malama ban ji ta ce kana hanya ba."
"Eh yau na shigo, anj
ima zan bi jirgi na koma, akwai wasu bayin Allah da nakan sallama a wani
auye kusa da Malumfashi duk sadda azumi ya kusa, nakan yi musu alheri haka, wannan karon na mance da batunsu shi ne silar zuwa na ba shiri.

Amma har na je na dawo."
Ya fadi hakan ne don Maama ta yarda babu wani abu da ya faru wanda ya yi silar zuwansa ba sanarwa, ya kuma ci sa'ar ta yarda da wannan don daga yanayin fuskarta da furucinta na cewar yanzu ta ji batu yasa ya gane.

Shi kuwa dai ya sani
arya ce kawai don tun a na saura sati guda ma ya yi waya da wani yaronsa dake
auyen, ya aikamasa komai ta asusun banki, sun kuma tabbatar masa matashin ya kai musu kayan masarufi na azumi har suka dinga godiya sai da ya katse kiran.

Zuwa ya yi musamman don ganin Haulatu kuma ya gan ta din amma ba irin ganin da yake so ba.

Ya na so ya fa
i abin da ke ransa sai dai ya gwammace ya yi shiru gudun zubewar girmansa.

Ba ya son raini sam.

Sun
an ta
a hira da Maama ka
an kafin ya yi mata sallama ya tafi don samun zuwa ya yi shirin komawa a nutse.

Ya fito ya kai duba ga sashin Hajja, ya ji zuciyarsa na neman raunana, wai wannan wace irin jarrabawa ce haka yake fuskanta?

Yarinya kamar wacce ta yi masa wani aikin, daga gani sau
aya shikenan ya bi ya susuce?

To ko dai ya samu Alhaji fa
amasa komai?

"No, ba zai yiwu ba." Ya ba kansa amsar a fili.

Haka ya bar gidan da sa
e-sa
en zuci.

Kano...

Ranar da duniya aka wayi gari da azumin Ramadhan, a wannan ranar ce
an Mutuwa ya shiga Kano ba tare da ya
au azumin ba kamar yanda Hajiya Adama ta yi masa kashedi.

Koda ace ma ba ta yi ba, ta sani bai damu da ibada ba amma gudun ma kar a yi din ya sa ta yi wa abin tufka.

Daidai lokacin kuwa da bayin Allah suke haramar zuwa masallaci don yin sallar isha'i bayan an kai azumi na
aya, a wannan lokacin suka shiga shirin tafiya can wani
ebantaccen wuri a dajin Allah don gabatar da uzurorinsu na duniya.

Wuri ne mai nisa da zai kwashe su awanni uku zuwa hudu, hakan ce ta sa
an Mutuwa ke tu
in sai Hajiya Adama a gefensa sai kuwa wata aminiyarta
ungiya, Zulaihatu.

Suna tafe su na
ara kwa
aitawa
an Mutuwa irin alfarmar da zai samu da kwarjinin da zai dinga yi wa mutane nan da wasu lokuta.

Shi kuwa ban da washe baki babu abin da yake yi.

Hajiya Adama ke ta nuna masa hanya har suka soma keta daji, sai da suka kai ga wani gida tafkeke mai
aton
yaure sannan tace ya yi hon, motarta da aka gani bai sa an bude ba sai da ta sauke gilashi wani jibgegen
atti su biyu masu gadin
yauren suka zuro kai, ganin ba
on fuska yasa su dubanta.

"Kar ku damu, mun samu
aruwa ne."
Suka
yace da dariya idan ka cire sannan suka karasa aka wangale
yauren, suna shigewa da motar aka maida aka rufe ta gam har da manyan padlocks.

"Ka cire takalmanka ka bar su a mota." Fa
in Hajiya Adama cike da nutsuwa, zuwa sannan gaba daya hatta a fuska ta sauya, wani irin ladabi ta soma kamar tana gaban Uban Dodon.
an Mutuwa ya amsa da toh.

Har zai fita ta ce.

"Ba a
aga murya, ba kuma a shiga da wayoyi, ba ka isa ka
aga kai ka kalli sararin samaniya ba.

Ladabi, ladabi, ladabi."
Tana kai wa nan ta ajiye mayafinta, dankwali, da jaka da wayoyi, ta cire takalminta ta fito a sannu sannu.

Yanda ta yi, haka
awarta Haj Zulaihatu ta yi.
an Mutuwa ya cire takalmi shi ma ya fito, ya ga ba ma su ka
ai ne a farfajiyar wurin ba, manyan mutane da jallabiyoyi wasu kuwa da manyan riguna sai masu sanye da coat haka suke tafe suna nufar cikin gidan.

Madadin ya ga falo, sai ganin wani babban fili ya yi a tsakar wajen da wani
aton wuri zagaye kamar rijiya an jera kyandir masu ci sai fararen
yallaye da kuma ja da ba
i an yiwa kyandiran ado.

Hajiya Adama suka tsaya can wani
angare mai
an tudu, zai bi bayansu aka dakatar da shi.

Da wata murya marar dadi aka ce.

"Kai!

Koma can baya!

Ba ka da darajar zuwa wurin can!"
Ba musu ya ja baya ya koma can gefe, sai ga jikinsa yana rawa, bai san yana da tsoro har haka ba a duniya.

Wani ihu suka fara yi suna kiran sunan Uban Dodo, can haya
inya turnu
e wajen sai kuma a hankali wani bango daga kusurwa ya soma bu
ewa, wani mutum ne ya fito jikinsa duk gashi babu kaya, zirr yake.

Sai wasu mata su ma tsirara su na take mishi baya har gaban wannan wuri mai kyandira.

Gani ya yi ana zubewa ana kai goshi
asa ana kwasar gaisuwa, ba musu ya yi irin yadda suka yi.

Sai
an Mutuwa ya ga wasu
atti tsirara sun shigo ri
e da wata
atuwar
warya sun ajiye gaban Uban Dodo, can kuma wasu yan mata suka soma zuwa su na rarrabawa kowa wani jan
yalle ana
orawa a saman goshi.

Ana zuwa kansa Uban Dodo ya ce a dakata.

Da kakkausar murya ya ce.

"Adama!
Chapter 35 · 0% Book details