← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 109

Sashe 67

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ba ta ce uffan ba duk da a
asan ranta ta ji da
in rashin ba sa fuskar da Haulatun ta yi, ko ba komai ta fi kaunar su tsira da mutuncinsu.

Sam ba ta kaunar abin da zai
ara ha
a su da Momin Mu'az.

Ranar Alhamis ana gobe za'a fara azumin goman farko na Zhul-Hajj.

Kasancewar babu islamiyya, Radiya da Safina da kuma Haulatu suka shirya don ziyartar Maimuna jikar Hajja
iya ga Haj Hadiza don su duba
iyarta dake fama da malaria.

A hanyar fita daga babban gate zuwa inda Gali Direba ke jiransu a waje suka ga Zaid ya fito a motarsa.

Da sauri Haulatu ta kauda kai ta cigaba da tafiya yayinda Safina da Radiya suka gaishe shi ganin ya nufo su.

"Noor."
Jin sunan da ya ambaci Haulatu da shi har yake bin ta a baya duk da ta
i tsayawa ballantana ta gaida shi ya sa Safina da Radiya kallon juna baki sake kafin su maida kansu.

Haulatu kuwa ranta ya
aci, fuska
aure ta dube shi bayan ya shiga gaba ya hana ta nufar gate.

"Lafiya?" Abin da ta furta kenan.

Zaid ya
an numfasa, rabon da ya gan ta ba zai ce ba.

Ta
ara kyau da haske.

"Idan na aikomaki sa
o ba kya reply, kin ji ni shiru, ba ki damu da sanin halin da nake ciki ba.

Rashin kaunar ta kai a yanke ala
a koda ta zumunci ne?"
Ta dube shi a fisge ta kauda kai, ya
an rame.

"Sauri muke yi, Malam Gali yana jiranmu."
Abin da ta furta kenan cikin bagarar da wancan zancen nasa ganin su Safina sun ma fice daga gate din zuwa waje.

Duk sai ta ji ta tsargu, wato Yaya Zaid ya shirya yi mata tonon silili, abin da take
oyonsa yake son bayyanawa duniya a yanzu.

"Ba wannan zancen nake son ji ba Noor..."
"Please suna na Haulatu.

Kar ka
ara kira na da wata Noor."
Ta na kai wa nan ta
ara yun
urin tafiya sai dai ya kuma dakatar da ita ta hanyar ri
e gefen mayafinta.

Ta fisge mayafinta.

"Kar ka
ara ta
a ni Yaya Zaid.

Na ce maka ka fita hanyata amma na ka ke yi ka shigemin hanci da
udundune.

Da alama ka shirya da
awa kanka wu
a, shikenan mu zuba, ga fili ga mai doki."
Ta na kai wa nan ta banka masa harara ta fice.

Sam ba ta ganinsa da wani girma ko ka
an a yanzu.

Kallon mutum mai mugun son kansa ta ke mishi.

A motar duk yanda ta yi zaton jin wani abu daga Safina da Radiya ta ga ba haka ba, sun share batun kamar ba su kula da komai ba, sai ma hirar duniya da suke yi suna kallon tiktok su na gulma.

Ganin babu mai yi mata zancen a cikinsu sai ita ma ta saki jiki ta watsar da zummar daga baya za ta fayyace musu komai idan sun dawo.

Sun samu tarba daga wajen Maimuna, dama ita ba ruwanta kamar ba Haj Hadiza ce ta haife ta ba.

Ta bambanta da Ihsan da Fahima.

Yarinyarta guda mai sunan Hajja da ake kira Husna.

Ita ke fama da
yanda.

Gidanta tsaf, mijinta ma'aikacin gwamnati ne.

Daidai gwargwado asirinsu a rufe, sun sha hira da dariya.

Ta yi musu girkinta mai dadi sun ci sun yi nak.

Sai bayan la'asar suka yi shirin tafiya, tamkar kada a rabu, har bakin
ofa ta yi musu rakiya Husna na ta kukan sai ta bi su ta je wurin Hajja.

Sai da dabara sannan ta ha
ura.

Zaid kuwa wannan karon ma Hajja ba ta wani sakar masa fuska ba, suna gaisawa ta kunna rediyonta ta na jin shiri.

Umma ce dai ta sakar masa sosai amma duk jikinsa a sanyaye ya mi
e ya fita da zummar
arasawa ciki.

Bayan tafiyarsa Umma ta dubi Hajja.

"Hajja don Allah ki yi hakuri haka ki yafewa yaron nan.

Ni tausayinsa nake ji.

Gaba daya ya kasa samun sukuni, ke kuma duk sadda ya shigo ko ya kira ba kya wani sakar masa.

Tun da dai abu ya wuce mai afkuwa ta afku ba shikenan ba?

Sannan mutum fa ba ya aurar matar wani."
Hajja da tun soma maganar Umma ta rage sautin rediyon dama hararar Umman take tana jira ta kai aya kafin ta tanka.

"Na'imatu kenan.

Ke dai ki kalli mutum kawai.

Amma ni tsakanina da Zaidu, hum.

Na dai yi shiru.

Wa ya fadamaki ya wuce kuma?

Toh idan ba ki sani ba ki bu
e kunne ki ji ni dakyau, har gobe Zaituna tana mutuwar sonsa.

Ni na rasa hasken fatar ke kwasarta ko kuwa wannan tsawonnasa marar
ira kamar mace."
Umma dai ta girgiza kai ba tare da ta ce uffan ba amma ha
a ta ji ya soma ba ta tausayi.

Fatanta Allah ya daidaita lamura komai ya wuce.

"Ni gani nake ma wannan sunne kan da ya ke yi da biyayyar nan duk ta dole ce da sa kai, na fi tunanin ba banza ba.

Watakila dai an yi dace uwarsa ta ci galaba wajen tan
wara shi, wata
ila kuma mutuwa ce ta kusanto shiyasa ya gyara hali."
Maganar Hajja ya sa Umma dariya, ba tare da ta ce komai ba.

Wayarta dake gefe ta yi
arar shigowar sa
o ba ta ko damu da bu
ewa ba don ita dai idan har sa
o ya shigo wayarta bai wuce na kamfanin layukan dake kan wayar.

Cike da mugun ka
uwa Maama ta saki baki tana kallon Zaid.

Ta ma kasa fitar da harafi ko guda
aya.

Daga yanayin duban da ta ke masa sai ya
ara jin babu dadi.

Kada dai a nan ma ba zai samu goyon baya ba.

Sallamar Sadauki ce ta sa nan da nan Zaid ha
e girar sama da ta
asa, meyasa bai za
i lokacin shigowa ba sai da ya riga shi zuwa gidan?

Sadauki shi ma ganin wanda ke zaune ya maida murmushin da ya shigo da shi ciki.

Hakan kuma bai sa ya ha
ura ya fasa sanyo kai falon ba.

Maama ta amsa sallamarsa tana duban Zaid sannan ta maida kallonta ga Sadaukin.

Sam ba za ta so su
ora maganar a gabansa ba.

Zai fi ta takawa abin burki tun wuri.

Zama ya yi ya gaida Maama ta amsa tana
an murmushin ya
e.

Ta maida duba ga Zaid.

"Ba ka gaida
an uwanka ba."
Ya ji kamar ta watsa masa ruwan zafi, sai dai Maama ce, dukkansu ba sa tsallake umarninta.

Ba tare da ya kalli inda Sadaukin ke zaune ba ya ce.

"An wuni lafiya?"
Shi kuwa Sadauki ganin yanayin gaisuwar sai ya yi kamar bai ji ba.

Sai da Maama ta yi magana kafin ya ce.

"Oh, lafiya."
Abin ya yiwa Zaid zafi
warai don haka ya mi
"Maama bari na je mu gaisa da Baba Alhaji, ma
arasa maganar idan na fito."
Hakan ya yi wa Maama dadi don haka ta amsa masa da toh shi kuma ya juya ya fice.

"Sadauki, ba a haka, girma ku ke yi, bai kamata ace kai a matsayinka na babba ba ku na yiwa zumuncinku ri
on sakainar kashi ba.

Ni ban ga amfanin wannan rashin jituwar taku ba."
an murmushi Sadauki ya yi.

"Maama kin fi kowa sanin halayyata.

Ba ni da ri
o, shi ne dai mai wannan banzar halin.

Kuma ace abubuwa da suka faru tun
uruciya ba su wuce ba?

Sannan ko yau ko gobe ya
ara yin wani laifin bai fi
arfin na yi mishi fa
a ba."
Maama ta jinjina kai, babban abinda a baya ya sa Zaid
ullatar Sadauki bai wuce don kama shi da ya yi yana shan sigari ba, lokacin
uruciya da tashen balaga ne suka kwashe shi ya buga wannan wautar kuma a bayan gida.

Sau biyu Sadauki ya kama shi ya kuma garga
e shi, a na uku ne ya je ya sami Baba Alhaji ya sanar da shi.

Ai kuwa Zaid ya fuskanci hukunci sosai, wannan shi ne babban dalilin da ya sa har gobe ya kasa ganin mutuncin Sadauki.

Shi ma kuma a hali na rashin yarda irin ta Sadauki, ya sa sam Zaid ya sire mishi.

Ya sha yi mishi rantsuwar ya bari amma sai ya tarar ya na yi.

Yanzun ne ba shi da masaniya tunda ba wuri
aya suke rayuwa ba.

"Shikenan.

Ina fatan ba wata matsala ce ba yanzu?"
in Maama kai tsaye.

Ya shafi sumar kai yana murmushi.

"Ko
aya.

Toh wai ma shi ke nan ba zan zo ganin uwata ba sai da matsala?"
Ta yi dariya ganin yanda ya yi maganar a shagwa
"Ai fa kam ban ga laifinka ba."
Daga haka kuma suka shiga hirar da ta shafe su har Zaid ya dawo, ganin Sadaukin ya ja guntun tsaki
asa-
asa, wannan ba zai bar shi ya yi abin da ya ci
amarar yi a yau ba kenan?

Sadauki kuwa kamar ya san ganin bai mishi da
i ba, ya
ara kishingi
a ya hau danna waya saboda Maama ta maida hankali ga tambayar Zaid har ya fito?

"Na fito Maama, sai mun yi waya kawai."
Ta gya
a kai.

"Shi ke nan toh, ka gaida mutan gidan."
"Ok, za su ji." Daga nan ya yi gaba, jin Maama ta sauke ajiyar zuciya ya sa Sadauki dubanta ba tare da ya ce komai ba.

"Abeed, ajiye wayarnan mu yi magana."
A duk lokacin da Maama ta kira sunansa na yanka ya sani ko mene ne zai fito daga bakinta to fa mai muhimmanci ne."
Wannan magana ta Maama ya fa
a kunnen Mabruka da ta soma saukowa daga matattakala sai dai ba ta riga da ta kawo inda za su hangi fuskarta ba.

Wannan ya sa ta ja ta tsaya da zumu
in so ta ji me zai fita a bakin Maama.

Maama kuwa duban Sadaukin ta yi a nutse ta fara magana.

"Ina tunanin lokaci ya yi da za ka fito a mutum ka nunawa yarinyarnan kana sonta.

Tunda dai kana gani jami'a za su shiga, ba ka san mai gaba za ta haifar ba.

Gudun samun kowace matsala."
Ya murmusa.
Chapter 67 · 0% Book details