← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 109

Sashe 30

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gigice ta dube shi, duba na tsantsar tsana.

Yau ita namiji ya mara?

Tabbas ta sani, duka halinsu guda ne.

Hajja kira take "A'a A'a Sadauki amma ina!

Sai da ya aiwatar da marin.

Sam a farko bai yi niyyar hukunta ta ba, ya ji zafi da mamakin maganganun da suka fito a bakin Fahima, sai dai yarinyar ta nunamasa ba ta da kunyar dagaske.

Ransa a tsananin
ace yake dubanta.

Murya a kausashe ya ke magana.
aryarki, kin ci
arya ki zo gaban jama'a kina rashin kunya a zuba idanu a kyale ki.

Har ana dakatar da ke kina botsarewa?

Wannan koda ba mahaifiya take gunki ba sa'arki ce?"
"Ai bari fa
i ma, mahaifiyarta ce ita ta haife ta." Umma ta sunkuyar da kai jin amsar da Hajiya Hadiza ta bayar.

Zuciyarta a cunkushe, wai yaushe Haulatu za ta nutsu ne ta koyi ha
uri a rayuwa.
ace ki bani wuri." Ta dube shi tana ha
iyar yawu mai
aci kafin ta juya da sauri bayan ta saki wayar a tsakar falon ta fice
aki cike da zafin rai.

Safina da sauri ta sa hannu za ta dauki wayar ya dakatar da ita,
auka ya yi ya jefa a aljihun wandonsa, ganin haka ta juya ta bi bayan Haulatu
aki.

Fahima kuwa kallo ya watsa mata kafin ya ba ta umarnin fita waje ta yi jiransa.

Sai kuma ya dawo daidai tamkar ba shi ba.

Hajja ta cika ta yi fam tana mitar don me zai mari wacce aka zalunta alhalin ba ita ke da laifi ba ta
o ta aka yi, bai ko biyewa
orafin Hajja ba ya maida hankali ga Umma ya gaishe ta a mutunce.

Ta amsa tana murmushin da ta saba yi na danne damuwa wanda ya zamo
aya cikin
abi'unta.

Koda ya yi musu sallama ya fita, Hajja mi
ewa ta yi ta nufi
akin don rarrashin Haulatu
"Allah yasa kar ta ba ki kunya." Cewar Ihsan tana dariya don ranta ya yi haske da marin da aka wanke Haulatu da shi.

Umma dai ba ta ce uffan ba.

Fahima kuwa wayarta yasa ta koma ta
auko ya kar
e kafin ya kuma rantse muddin ya kuskura ya ji labarin ta ri
e waya sai ya yi mugun sa
a mata.

Wannan hukuncin ya yiwa Fahima tsauri matu
a, dama mahaifinta mai shegen tsaurin bala'i da ya ya bata wayar?

Sai da ya bi ta da ruwan kashedi iri iri na muddin ya kama ta da wani laifin to fa babu ita ba ri
e waya sai a dakin mijinta.

Ballantana kuma ya ji Sadauki ne ya
wace, ai kuwa ta shiga uku, zai dau lamarin ba na wasa ba tun da ya yiwa Sadauki farin sani.

Haka ta koma falon Hajja tana kuka wiwi, Hajiya Hadiza ranta ya
aci da wannan hukunci na Sadauki.

Hajiya Fatima ke fadin ai gwara da hakan ta faru tunda ita ba za ta iya saita bakinta ba.

Umma dai ba ta tanka ba.
angaren Haulatu kuwa, kuka wiwi haka ta dinga yi, har Safina ta shigo tana aikin rarrashi amma ko kallonta ba ta yi ba.

Ita a ganinta ai wannan son kai ne da son zuciya.

Ta ya ya ita aka yiwa laifin kuma zai
au hanu ya mare ta?

Ita tun ganinsa da ta soma yi dama ta fahimci ba
in azzalumi ne da ba ya
aunarta.

Da ace ya san yadda ta tsani namiji mai bugu da bai yi kuskuren
ora yatsunsa a sama fuskarta ba.

Hajja itama ta shigo ta hau rarrashi da sababin ita Sadauki bai kyauta mata ba.

Yanda ta dinga nuna fushinta a kai har tana ikrarin za ta kira shi ta yi mishi tas tunda dai ko ubansa bai isa ya ja da ita ba.

Sai abin ya
an yiwa Haulatu dadi a rai, ba ta kuma ta
a ji Hajja ta burgeta ba sai yanzun.

Kiran da aka shigo yiwa Hajja kan cewa ta yi ba
i yasa ta fice daga dakin, lokacin hayaniya sosai ya kaure a falon ga dukkan alamu an
ara yawa ne a gidan.

"Ki yi hakuri ki tashi muje
asa ki ci abinci."
Jin abin da Safina ta ce yasa Haulatu mi
ewa zaune cikinta har yana
ara amma damuwarta da
acin ran sun shafe wancan.

"Don Allah Safina wai rashin kunya na yiwa Umma?"
Safina ta
an yi jim, ita kuwa Haulatu wai wace iri ce ne?

Yanzu ba ta ga irin katse zancen Umma da ma
aga muryar da ta yi mata ba?

Can ta dube ta dakyau cikin sanyin murya ta amsa.

"Gaskiya har ga Allah kin
aga wa Umma murya.

Ta kuma nuna
arfin iko da isa a kanki ta hanyar dakatar da ke daga maganganun da kike yi sai ki ka nuna ba ta isa ba.

Ba zan
oyemaki ba ni kaina yanayin da kika yiwa Umma magana bai min dadi ba Haulatu.

Wannan kuskure ne babba.

Ki yi hakuri da marin da Yaya Sa..."
"Ni ba maganarsa nace ki yimin ba.

Na yarda na yiwa Umma laifi.

Wallahi na ji babu dadi, ta ya ya zan ba ta hakuri?

Ni na sani Umma yanzu ranta ya
aci da lamarina.

Wallahi ni ban san ma sadda na
aga muryar ba."
Sai ta fashe da wani sabon kukan mai nuni da tsantsar nadamarta da dana sani.

Shigowar Umman ya sa suka dube ta.

Fuskarta a sake ta dubi Safina.

"Safina, maza je ki wajen Baba Saude ki kar
o muku abinci, an kammala."
Ta amsa da toh kafin ta mike ta fita.

Umma ta shigo dakin sosai, da sauri Haulatu ta mike tsaye ta ma kasa kallonta, ta rasa me za ta yi?

Sai kawai gani ta yi Umman ta ri
o hannunta ta zaunar a gefen gadon.

"Ba ki kyauta ba ko kadan Haulatu.

Me kika son ki nunawa mutanen gidan nan?

Ni uwar banza ce?"
Har a sannan murmushi mai ciwo Umma ke yi, Haulatu ta girgiza kai sai ta
ara karfin kukanta.

Fuskarnan ta yi ja, ga kuma shatin hannun Sadauki kwance a gefen kumatunta.

"Wallahi ban san na yi ba.

Ki yafemin don Allah Umma.

Ba zan
ara ba."
"Ya wuce.

Amma ki
ara hankali da rayuwa da kuma zaman duniyarnan Haulatu.

Idan ba ki iya zama da mutane ba, za ki wahala a rayuwarki.

Yanzu dai kusan a farko ke aka yiwa laifin, amma me?

Sai ki ka nuna gajen hakuri har kika dauki matakin da ya haifar maki da dana sani.

Da kin yi shiru da bakinki, kina tsammanin Fahima za ta sha ne a hannun mutanen da ke falon koda kuwa ni ban yi magana ba?

Don Allah ina ro
onki ki koyi hakuri da kuma danne zuciyarki.

Kar ki sake kuma ki ce za ki tsani
an uwanki don ya mareki, gyara ya yi maki.

So yake ya ga kin fahimci kuskurenki.

Kullum ina
ara fahimtar da ke yanayin rayuwa, idan ba ki koyawa zuciyarki hakuri yanzu ba, sai yaushe?

Akwai namijin da zai dauki wannan sakarcin naki?"
Ta turo baki ka
an jin Umma ta sako batun wani namijin.

"Ki yi hakuri." Ta
ara maimaitawa karo na biyu.

Sai a sannan Umma ta yi murmushin da ya fito tun daga zuciyarta.

"Ya wuce.

Allah ya shiryamin ke, ya yi maki albarka."
Cike da jin dadi ta yi dariya tana mai amsawa da amin gami da rungumar mahaifiyarta.

Dawowar Safina dakin dauke da faranti na abinci har da flask na ruwan shayi ya sa Umma mikewa ta bar dakin zuwa falo.

Nan suka shantake suka shiga hira ran Haulatu ya yi fari
al tamkar babu wani abu da ya faru don a yanda ta zuciya ta rantse ma ko wayar ya maido ba za ta kar
a ba tunda ta ji Safina ta ce wai ya dauke wayar bayan ta bar falon.

Su na kammalawa, Safina ta dube ta.

"Zo mu tafi kiga Anti Raudha, suna can gidan Abba."
Zuwa sannan ta gane waye Abban tunda yana shigowa su gaisa da Hajja, kuma ta gan shi mutum mai sakin fuska, koda ba ta falon to fa sai ya tambaye ta.

Alhaji Ridwan kenan mahaifin Sadauki.

Wannan ne ba ta sani ba.

Ta yamutse fuska.

"Da wannan yatsun da suka kwantamin a fuska na wancan mugun kike tunanin zan fita a samu abin magana?"
Safina ta dubi fuskar sosai.

"Lah, wallahi ko kadan ba a ganewa gaba daya ya goge sai
an ja da wurin ya yi kuma shi ma nasan zuwa anjima za'a nema a rasa.

Don Allah taho mu je ki gan ta."
Jin haka Haulatun ita ma ta mi
e, sai da ta
arasa gaban madubi ta ga dagasken ba lallai a gane ba kafin ta yarda da fitarsu.

Falon Hajja a cike ba ta ko kalli kowa ba ta fice ta bar Safina na aikin gaishe-gaishe tunda dai ita ba sanin su ta yi ba duka ba
in fuska ne.

Gidan Alhaji Ridwan a cikin kewayan babban gidan yake, shi ne kalarsa ta bambanta da na su Hajja da Alhaji.

Ba ta ta
a shiga ba, ko sadda Hajja ta kai Umma gidajen yaranta da na yan uwanta koda wasa ba ta yi yun
urin bin su ba don a lokacin sosai take jin haushin Hajjar.

Tun daga farfajiyar gidan da suka shiga
aton
yauren, ta ga ya sha bamban da duk gidajen da ta ta
a sa
afarta ciki tun zuwanta Katsina.

Baki ta bu
e tana kallon yanda aka
awata shi har da wani gefe na
aramin garden da aka zagaye da wani gajeran katanga an yi shuka mai kyau da burgewa a cikinsa ga wani kujera mai lilo, a iyakar hangen Haulatu dai ta tabbata wajen akwai abubuwan burgewa a ciki.

Idan yamma ta yi zai fi dadin zama.

Ba ta
ara tsinkewa da tsaruwar gidan Alhaji Ridwan ba sai da suka shiga wani babban falo da ya ji kayan
awa iri-iri masu tsada koda kuwa ba a fadi, inda anan ne suka ji tashin wa
a da kuma muryoyin yanmata wadanda suka iya wa
ar su na bi muryar kowa a sama, ga rawa su na ti
a abin su.
Chapter 30 · 0% Book details