← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 109

Sashe 74

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun sha dai dariya kamar cikinsu zai ciwo, don idan mutum ya na tare da Dakta Hashim to fa ba zai kamu da hawan jini ba, ko ya hau ma zai sauka.

Bayan kwana biyu...

Malama ranta a
ace ta ke duban Zaid dake tsugunne gabanta, a dazun ne Baba Alhaji ya kira shi ya ce ya yi hakuri kar ya
ara tayar da zancen Haulatu tunda yarinyar dai ta nuna ba ta sonsa, kuma karatu za ta yi to kar ya matsa mata.

Ita kuwa Malama, Hajja ce ta kira ta ta yi mata tas tace Zaid ya rainata ba shi da kunya har ya iya kallon idanun manya ya ce yana son jininta, to idan har ta isa da
anta, ta gaggauta taka mishi burki.

Har ta ke ikrarin ba lallai Malamar ta iya hakan ba tunda ba ta tilasta mishi auren Zaituna ba, to wannan ma ba za ta iya ba.

Don haka ita tana can tana jiran ranar da Zaidun zai kwaso jiki ya shigo mata gida.

Maganganun dai sam ba su yiwa Malama dadi ba, ta yarda Hajja matsayinta na Uwa a gareta komai ma ta iya fa
a, kuma ba laifin kowa ba ne sai Zaid mai masifar kafiya da naci idan ya sa abu a gaba.

"Me kuma ya kawo ka wurina yanzu?"
Wannan ita ce tambayar da ta watsa masa, dama tana son magana da shi, amma ganin yanda ya kawo kansa har ya dur
ushe ta kyautata zaton wani abun zai ce.

A iyakar sanin da ta yiwa
anta ya kasance mai kafiyar da ba ta jin ha
uri ya zo bayarwa mai nuni da ya bar maganar Haulatun.

Aikuwa ya tabbatar mata da tunaninta sadda ya karya bille ya soma magana.

"Na yi maki laifi ne, kin ce na ha
ura amma na kasa har na fiddo zancen ga Maama, sai dai ba ni na kai maganar ga Baba Alhaji ba.

Ki yi hakuri, ina kaunar Haulatu, ki taya ni ba Baba Alhaji da Hajja hakuri, su bar ni na..."
"Zaidu!"
Yanayin
agawar muryar da ma kaushinta ya sanya shi dakatar da zancen gami da amsawa.

"Na'am."
"Idan har ni Safiyya na isa da kai, idan na isa na ba ka umarni kuma ka bi.

Koda wasa ka
ara shiga rayuwar Haulatu sai na sa
a maka.

Har zuwa yaushe ne za ka daina jazamin abin magana?

An
are da wancan yanzu kuma ka ke neman jawo min wani?

To ni ban ma amince ka yi babbar sallah a nan ba, ka tattara iyalinka ku koma Abuja."
Tana kaiwa nan ta mi
e ta bar masa falon, shi kuwa ya ji kansa ya wani irin sarawa, dama kwanakin duka ba shi da sukuni.

Batun ya bar Haulatu ma bai taso ba, ya san ba zai iya wannan ba zai dai nemi hanyar da zai lalla
a Mahaifiyarsa da ma Hajja.

Haulatu kam zai bi umarnin Malama da Baba Alhaji, ba zai
ara nemanta a waya ba.

Amma haka ba wai yana nufin ya ha
ura ba.

'Za ka iya jurewa?' Wani
angare na zuciyarsa ya watsamasa tambayar wanda ba shi da amsarta.

Haka ya mi
e jiki duk a sanyaye ya bar falon.

Ana saura kwana hudu babbar sallah, Uncle Abba autan Hajja ya zo da iyalinsa Katsina.

Haulatu sam ta tsani matarsa don ba mace ce mai son mutane ba, shi kuwa Uncle Abba ba ruwansa mutum ne mai son jama'a don halinsa
aya da Maman Zaituna, Haj Nafisa.

Da
in da
awa ma sai ga Fahima, wai ita ma a nan za ta yi babbar sallah.

Sai gaba daya ma
angaren Hajja ya rage yiwa Haulatu dadi, ga shi sun yi hutun islamiyya.

Lesson din da take zuwa ma sai bayan sallah za'a cigaba don haka wurin Maama ko Radiya ta ke tafiyarta.

Ita ma Fahima
afar yawo ba zama take yi ba, sashin su Sadauki take gudu abin ta dab da shan ruwa za ta ci ado ta fice.

Abin dai na ba Haulatu mamaki.

Ana gobe sallah kuwa, suna zaune bayan kammala shan ruwa, yinin ranar dama kowa ibada ya shiga idan ka cire Fahima mai afkin kallo a waya, matar Uncle Abba, Anti Haseena da
an ukun yaranta ba sa nan sun je ziyarar wata yayarta.

Bayan gama shan ruwa Haulatu na zaune su na hira da Safina ta whatsapp, ita kuwa Fahima na gefe Hajja na jan ta da tambayar yanzu shikenan sai wata shekarar za ta sake jarrabawa amma tana amsa ciki-ciki don gaba daya ba ta so ma Hajja ke zancen nan gaban Haulatu ba, ta kula ma dariya Haulatu ke yi sai ta yi tunanin
ai kawai ma da ita take.

Wayar Haulatun ce ta yi
ara, ta dan yi jim ganin sunan me kiran, Yaya Sadauki ne.

Ba ya ta
a kira sai idan da kwakkwarar dalili don haka ta amsa gami da sallama, bayan ya amsa mata ta gaishe shi.

Jin ta ambaci sunan Yaya Sadauki hankalin Fahima duka ya koma kanta.

"Idan bakya wani uzurin, ki fito ina nan parking space, ina son ganinki."
"Toh." Shi ne abin da ta ce kafin su yi sallama.

Ta mi
e ta ja hijabinta da ta yi sallar magriba da shi, daga ita sai doguwar riga mai
aramin hannu.

Ta dubi Hajja don Umma tuni ta haye sama.

"Hajja, bari na je Yaya Sadauki na kirana."
Ta fadi ba ta ko kalli gefen da Fahimar ta ke ba, Hajja ta amsa da toh sannan ta fice.

Hankalin Fahima idan ya yi dubu to ya tashi.

Yaya Sadauki har kiran wayar Haulatu yake yi?

Abin da tunda take ko bisa kuskure ne bai ta
a kiran wayarta ba?

To ai ba ita ba, ko yayyunta ma ba nemansu yake a waya ba, sai wanda ya kira don ya gaida shi, yakan
auka amma kuma amsar a ciki-ciki.

Ita kuwa dama koda wasa ba ta gigin kiransa, ta sani ba ya son a dinga kiransa babu dalili.

"Ke ina magana kin lula wata duniyar, yanzu kenan shi ubannaki aure zai maki ko kuwa haka za ki zauna jiran shekara ta zagayo ki
ara zana shi jam din."
Fahima ranta a
ace ta mi
e tana turo baki.

"Ni ma ban sani ba." Daga haka ta fice, bayan Haulatu ta bi jikinta har rawa ya ke, gwara ko mene ne ta gane wa idanunta.
*LITTAFIN FITAR TSIRO NA KUDI NE.

DUK WACCE TA FITAR MIN TA KWANA DA SANIN TA DAUKI HA
INA.

BIYA KI KARANTA HANKALINKI KWANCE. 9034973645 OPAY.

IBRAHIM RUFAIDA UMAR.*
Sassanyar iskar da ke ka
awa sakamakon wani ha
en hadari har yana
ugi, da ya kewaye sararin samaniya lokaci guda kuma a na zuba wal
iya, alamu ne na kowane lokaci ruwa kan iya sauka idan Allah ya
adarta.

Hakan bai hana Haulatu takawa ba a sannu ga iskar dake
an ka
awa tana
an manne hijabin a jikinta, wasu lokutan kuma ta yi kokarin
aga shi sama wannan ya sa ta za
i takawa cikin nutsuwa tana kare jikinta gudun kar wani sashin ya bayyana.

Tun daga nesa ta hango shi zaune saman motarsa ya tan
washe
afa guda a gefe kuma wayoyinsa ne a a ajiye yana kur
ar lemun kwali na Chi Exotic a sannu-sannu.

Sanye yake da tshirt ruwan
asa,
irarsa ta
arfi ta fito kasancewar ba dogon hannu ba ce, sam bai mishi muni ba sai ko ba
in wandonsa mai jikin cotton.
afafunsa madadin
an silifas na zaman gida sneakers ya sanya, ga dukkan ma alamu shigowarsa gidan kenan don motar ko shigar da ita rumfar adana motoci bai yi ba, dama kuma ya fi adana motarsa can gidansu akan nan
in.

Tana tafe ta gama
are mishi kallo tsaf, shigar sosai ta haskaka shi.

Ganin ya maido hankalinsa kanta ya sanya ta sunkuyar da kai, har ta
araso bai iya
auke
wayoyin idanunsa daga kanta ba.

Ta yi mishi sallama, ya amsa.

Saukowa ya yi daga saman motar ya kasance suna tsaye da kafafunsu su duka.

Cikin yanayin lumshe idanu sakamakon iska da ke ka
awa tana kwashe-kwashe ta dube shi.

"Yaya gani."
Ta furta tana
an murza idanu, ya kalli yanda hadarin ke ha
uwa, don haka ya kwashi wayoyinsa ya ce ta biyo shi.

Ba musu kuwa ta bi bayansa zuwa cikin rumfar adana motoci, a nan sai suka samu sa'ida kadan daga iskar da ke kwaso musu
ura.

Duk wannan budurin da suke yi, Fahima na daga can gefe jikin wata
ar bishiyar dogon yaro tana hangensu, ga dai iska na barazanar raba ta da
an yalolon mayafin da ta yafa a kanta.

Har wasu hawaye ta ga sun taho mata, babban ba
in cikinta yanda ta ga sun jera kamar wasu masoya sun nufi
asan rumfa.

Me za su tattauna, me ya faru?

Oho, duk babu
aya da ta sani.

Can kuwa Sadauki ya dubi Haulatu cikin nutsuwarsa ya soma magana.

"Hadari zai hana ni yin doguwar hirar da na yi niyyar yi."
an yi shiru ita kuwa Haulatu tunani ta shiga to wace kalar hira ya yi niyya din?

Sai ta
ara tsintar muryarsa.

Na ji dukkan abin da ya faru a baya, don na daukesu matsayin past, ba na fatan a gaba na ji makamancinsu.

Karatu shi ne babban burinki na yanzu, please ina so ki maida hankali ga abin da ki ke so domin cikar wannan muradin naki.

Taya wanda kake so cikar burinsa muddin bai sa
awa shari'a ba, shi ne babban abin da ya fi kyautuwa.

Da ace sun taya ki so da kwa
ayin cikar wannan buri naki fiye da son zu
atansu, hakan zai yi min dadi.

Kar ki ba ni kunya, ki nutsar da hankalinki wuri guda kuma kan abu guda.

Ni dai na sani zai wahala idan kina soyayya.
Chapter 74 · 0% Book details