← Book details Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 109

Sashe 93

Fitar Tsiro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba Alhaji ya ce idan kin dawo yana nemanki."
Jin haka ran Mabruka ya
aci, Haulatu dai tuni ta ficewarta don ba ta ga dalilin da zai sa Anti Mabruka ta lalata mata farin cikinta na wannan rana ba.

Ita kuwa Mabruka tana shiga Baba Alhaji ya rufe ta da fa
a sosai ya kuma rantse muddin ba za ta bar yawace-yawacen gidan
awaye da bokaye ba shi zai yi maganinta.

Nan da nan ta zaro ido ta dafa kirji.

"Ni?

Baba ni ke bin bokaye?"
Ya kalle ta kawai, Safina ta ba shi labarin abin da ya faru kafin auren Maama, ya yi shiru ne kawai bai ce komai ba tare da addu'ar Allah ya shiryamasa
iyar, amma ya kula abin nata nema yake ya fi
arfinsa don har sanyawa ya yi ana bibiyarta a ga inda za ta je, a nan ya gano ba ta sauya zani ba, ya so yiwa yayyunta zancen amma ya sani matakin da zasu dauka zai fi na sa tsaru dalilin kenan da ya za
i fara gwada nasa ikon tunda dai ba ta fi
arfinsa ba.

"Na san da komai da kike aikatawa Mabruka, kin maida kanki kamar jahilar da babu arabi balle boko.

Kon kasa yarda da kaddararki, a hakan ki ke tunanin za ki samu mijin aure?

Maza nawa suka fito suna sonki amma tsabar raina arzi
insu da ki ka yi, ki ka wula
anta su?

Yanzu kuma madadin ki bar wa Allah komai ko rungumi kaddarar da ya rubuta mako har mijin aurenki ya fito amma kin gwammace ki yi shirka ko?

To ba a gidan nan ba, wallahi kin ji na rantse maki muddin ki ka cigaba da bibiyar gidajen bokaye don yiwa
ar uwarki mugun abu ko kuma don wata bu
ata ta kanki, sai na yanke hukuncin da ba ki ta
a zaton zan ba a kanki."
Ita dai Mabruka ji ta yi kamar ta saki fitsari a wando.

To waye yake fa
awa Baba Alhajin abin da take shukawa?

Kuma tun yaushe ya sani ya yi shiru bai ce komai ba?

Nan da nan ta shiga zufa duk kuwa da sanyin Ac da
ya mamaye falon.

"Baba waye ya soma zuwa ya yimin sharri a wajenka?

Ni kuwa Mabruka me ya yimin zafi da zan bibiyi boka ak.."
"Ya isa hakanan, tashi ki je, ni dai na garga
eki, ki kiyaye don idan babu wannan rayuwar, akwai wata.

Idan ba ki koyi aikin da zai nisantaki da wuta ba, hakika za ki fa
a mawuyacin hali a gaba.

Komai ki ka yi hakuri kika bar wa Allah idan rabonki ne sai ya taddo ki a inda ki ke."
Nan dai ya yi mata doguwar nasiha mai ratsa zuciyar duk mai imani, amma Mabruka jin sa kawai take, sai ta ga ma kamar ai raina mata hankali aka yi kawai, komai ace ita ke da laifi, an kasa a cikin manyan abokan yayyunta wani ya samar mata mijin aure ya ha
a su, kuma shi kansa Baban ai yana da yaran abokansa da har gobe suke zuwa gaishe shi, manyan mutane amma bai ta
a cewa zai ha
a ta da kowa ba, sai yanzu da aka ga ta tashi tana fafutukar yanda za ta samu miji ake nema a tauye ta.

Har ya sallame ta ta mi
e ta fice a dakin ba ta ko ji
arr na tsoron lahirar da kwanciyar kabarin da yake ta kirari ba.

Baba Alhaji ya bi ta da kallo, shi ya haife ta, ya kuma fi kowa sanin wace ce ita, don haka ya girgiza kai zuciyarsa na
aci, sam bai ga alamun saduda ba a tattare da ita.

Yanzu kuwa ya yanke zai tara yayyunta su taya shi nema mata mijin aure, idan har auren ne a gabanta gwara a yi shi da koma waye muddin ta amince za ta zauna.

Momi Nuratu ta yi shiru bayan gama sauraron bayanan da suka fito daga bakin Mijinta Alhaji Ridwan.

"Ya na ji kin yi shiru?

Ko ba ki yi farin ciki da za
insa ba ne?" Alh Ridwan ya tambaya.

Ta girgiza kai gami da yin murmushi.

"Ko kusa, akan me zan
i Haulatu?

Na ji da
i kuma ina fatan Allah ya sa su zamewa juna silar dukkanin alkhairai, Allah ya sa albarka a ciki.

Sai dai na samu waya daga Hajiya Rahma (Mamin Khaleefa), wai don Allah na ro
i yaronka ya zo su yi hira da Jannat ko Allah zai sa su fahimci junansu.

Har take cemin yarinyar ta tada hankalinta akan ita fa lallai shi take so.

Toh ni dai nace mata ta yi hakuri dai har sai na mishi magana tunda yaran yanzu ba a gwada yi musu dole abin ba ya dadi.

Akan hakan dai har sa
ani muka samu don gani ta yi wai na goyi bayan
anka."
"Ikon Allah, ita Jannat din ke son Sadaukin Alhaji?

Toh zan kira shi
in na ji ta bakinsa."
Daga haka ya ce a bar batun, dama Momi ta sani, idan har Sadauki ba ya so ba zai ta
a takura masa ba.

Ita
in ma hankalinta sam bai kwanta da Jannat ba, ta san wace ce Hajiya Rahma tun ma zamanin
an matancinsu, kasancewar sun je makarantar kwana guda, ta san irin azabtarwar da ta yiwa juniors da kuma bin malamanta ita da mahaifiyarta duk a fadi tashin neman mijin aure mai hannu da shuni.

Sam ba ta hanyarta ta ha
u da yayanta Barr Dawud ba, can suka hadu a wani biki har Allah ya kaddara aure.

Ita dai ba ta ce komai a kanta ba har aka yi auren kuma ta samu kar
uwa a cikin dangi.

Ba ta iya ta
ata mutum ba, amma kuma da
in da
awar samun kwanciyar hankalinta, bai wuce cewar Yayan nata mutum mai yawan ibada da kuma kamewa ba.

Ta sani har abada da yardar Allah, Mamin Khaleefa ba za ta ta
a nasara a kansa ba kuma hakan ce ta tabbata don har yau ta kasa mallakar shi yanda take so, Barr Dawud ya
i tan
waruwa.

Sai dai kuma wasu lokutan rigimarsu ta fi tasiri ne akan tarbiyyar yaransa da take neman lalatawa, ba ta damu da suturun da zasu sanya su fita ba, ba kuma ta damu da zuwansu islamiyya kan kari ba.

Wataran har cewa take yi su yi zamansu a gida kwakwalwarsu ta huta tunda an sha karatun bokon an dawo a gajiye.

Duk tana da labarin komai, ita din ita ce babbar aminiya ta shawarar yayanta Barr Dawud, ta sani hakuri kawai yake yi da Mamin Khaleefa sai dai babu yanda ta iya mishi tunda ya ce shi sam babu ra'ayin kara aure a rayuwarsa ballantana kuma rabuwa da uwar yaransa Rahma.

"Nuratu!" Kiran sunanta da Daddy Ridwan ya yi har sai da ya sa ta
an yi firgigit.

"Na'am?

Magana ka ke yi?"
Ya girgiza kai da mamaki ya ce.

"Tunanin me kike yi haka ne?

Zancen da ku ka yi da Rahma ki ka sa a rai har ta kai haka ko ya ya?

Ban gane ba."
Ta wayance da
aukar gorar ruwa ta hau kokarin bu
ewa.

"Babu komai.

Kawai dai wani abin ne ya
auki hankalina.

Allah ya nunamana, ya sanya albarka a aurensu."
Ba don ya gamsu da maganarta ba ya share ya na mai amsa addu'ar da amin.

Barr Dawud, mutum mai cikar kamala da dattako.

A kallo
aya tak idan ka gan shi za ka gane shi ya haifi Khaleefa saboda tsabar kamanninsu.

Tsawon, farin, har ma da
irar jikin babu wanda ba iri
aya ba.

Idan ka cire shekaru ba su sa bambancin a zo a gani.

Yana zaune a falonsa yana kallon labarai a tashar NTA.

Shigowar Mami kamar wacce aka jefo ya sanya shi dubanta lokaci guda yana
aukar remote ya
an rage murya.

"Rahma, lafiya?"
Ta nemi wuri ta zauna fuskarta a tur
une ta ce.

"Ina fa lafiya Dawud?

Yanzu fisabilillahi kana kallon
arka a cikin mugun yanayi akan abin da kake da iko da shi za ka iya magance mata amma ka gwammace ka yi shiru ka zuba idanu rayuwarta ta lalace?"
Kansa ya
aure, yau wace kalar rainin wayo Rahma ta zo da shi?

"Kin san me kike cewa?

Ki shigo min falo ba sallama, ki zo ki hau yi min maganganun shirme da shiririta?

Me na cewa ita Jannat
in?

Ban ce ta ha
ura ta fawwalawa Allah lamarinta ba?

Ita ba ta san tawakkali ba?

Yaron nan ba fa sonta yake ba, kuma ke kin fi kowa sanin ba zan kai
iyata hannun wanda ba ya kaunarta ba."
"Na ji na ji Dawud, fito kawai ka cemin Ridwan da Nuratu sun fi
arfinka.

Ba za ka iya nemawa
iyarka auren
ansu ba saboda
ansu ba ya so.

Shikenan, ni da kaina zan je na samu Alhaji Ridwan din na yi mishi batun Jannat ko..."
"Kar ki fara!

Kar ki kusa ki fara."
Ta wurga masa wani kallo mai kama da harara sai kuma ta ja tsaki ta fice ta bar shi da jin ciwon wadannan
abi'u nata.

Wai shi Rahma ta raina har haka, tsaki, harara, ba
ar magana da ma nuna bai isa ba babu wanda ba ta gwada mishi.

Idan wasu lokutan ya yi nasarar tan
wara ta, wasu lokutan takan nuna masa fin
arfi.

Ya sauke ajiyar zuciya gami da girgiza kai.

"Allah ya ganar da ke." Iyakar furucin da ya yi kenan daga haka ya cigaba da abin da yake.

Ya yanke zai
ara kiran Jannat ya bita da nasiha da kwantar da hankali, gwara ace ta ha
ura gudun abin da zai je ya dawo.

Washegari kiran Baba Alhaji ya sanya duka yaransa maza suka isa gidan.

Barr Dawud sai da ya fara shiga
angaren Baba Dakta suka gaisa sannan ya nufi na Hajja.

Da sallamarsa ya shiga falon, Hajja na sama a lokacin ba ta kai ga saukowa ba.
Chapter 93 · 0% Book details