← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 120

Sashe 99

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A zaune kan sallaya ta tarar dashi kamar yadda ta tafi ta barshi,zama tayi a gefan gadon har ya shafa addu'a itama ta shafa, cikin nutsuwar sa ya juya ya dubeta kana yace"sun dawo?tace"sun dawo amma alamu ya nuna a kwai wani abu da suke ɓoyewa a junan su!'nan dai ta gaya masa yadda sukayi da su Bintu,ta ɗora masa da cewa, wallahi Alhaji haka nan nakeji araina kamar da wani gagarumin abu dake shirin faruwa acikin gidan nan,kuma zuciya ta tafi raya min Alkhairi shi yasa nakejin wani irin farin ciki!'murmushin su irin na kamilan mutane yayi,kana yace"kice munyi ɗaya dake amma Ni dai farinciki na baya rasa nasaba da irin mafarkan da nake yi da Abubakar wanda nake ganin sa cikin halin jinya amma duk kwanan duniya idan na kumayin mafarkin to sai na ga samun sauki da lafiya a tare da shi, kuma inaji ajikina ya kusa dawowa garemu,sai dai kawai mu cigaba da tsananta addu'a akan lamarin!'Hajiya Babba tace" hakane Allah ya shige mana gaba!'...

Turus tayi ganin Dady Mansur zaune a falon ta, ya zuba ta gumi kana ganinsa kasan yana cikin damuwa matsananciya,
cikin sanyin jiki ta ƙaraso cikin falon sai kuma duk taji damuwa da tausayin MANSUR ɗin ya kamata,tasan damuwar da yake ciki bata rasa nasaba da halin da ɗan uwansa ya shiga,to yake nan zaiji idan yaji cewar uwarsa ma tana daga cikin waɗan nan mutanen masu matukar san zuciya da san abin duniya?wane irin hali zai shiga duk ranar da ta bayyana cewa mahaifiyar sa munafuka ce mai fuska biyu?kai ina bata ma fatan zuwan wan nan rana, baza ta taɓa bari hakan ta faru ba,duk yadda zatayi zatayi dan rufuwar asirin ta,baza ta bari ta tozarta gaban mutanen da suke matukar ganin girma da darajar ta ba,zama tayi a kusa dashi tare da dafa kansa cikin san cire damuwa da fargabar da suke san rufeta tace"Mansur ya haka da zama mai makon kaje ka kwanta ka huta sai kazo ka zauna anan, ko kana nufin kwanan zaune zakayi?wata irin ajiyar zuciya yayi cikin sanyi jiki da murya yace"Hajja bazan iya bacci ba,ba na yau kawai ba har da na gobe da jibi,abun nan bazai taɓa fita daga raina ba,na dade ina tuhumar kaina dalilin da yasa ina ganin ana aikata ɓarna amma bazan iya kataɓus akan hanawa ba,Habibu ya cuceni ya cutar da ƴan uwan taka yaci amanar zumunci!'ya faɗa wasu zafafan hawaye na zubowa daga kwarin idanun sa, cikin mamaki Hajjo tace"kana nufin tun tsawon lokacin nan kasan abinda Habibu yake aikatawa kuma kasan ABUBAKAR yana hannun sa?jinjina kansa yayi tare da cewa tabbas Hajjo Ni ganaune kuma jiyau akan dukkan abinda Habibu yake aitawa,sai dai kuma sanin nawa bai da wani amfani tunda baiyiwa ɗan uwa na ABUBAKAR rana ba!'Hajjah tace"meye dalilin ka na rufawa wannan bugun asiri?cikin damuwa da tsananin takaici yace"Hajjah ban sani ba,amma yanzu na sani,nasha yunƙurin zuwa dakin nan dan fito da Abubakar amma sai hakan ya gagara,wanda nasan hakan baya rasa nasaba da ƙarfin sihirin dake tare dani ko nace tsafi dan yanzune nake da tabbacin Habibu tsafaceni yayi,nasha yunƙurin zuwa gurin, wanda tasanadin haka da yawa mutanen gidan nan suke zargina da alaƙa da wannan ɗakin,ranar da aka sace Sayyid ma nayi tunanin shine ya ɗauke shi saboda yasha min kashedin idan ban daina yunƙurin zuwa dakin nan ba to zai kashe min Sayyid,hakan ta farune agaban matata shi yasa ita ma take min kallon wanda ya sadaukar da rayuwar ɗan ta akan wata buƙata,Hajja Habibu ya sakani acikin haɗarurruka da dama,ranar da naga gobara a ɗakin da Abubakar yake baƙaramin tashin hankali na shigaba dan atunanina Abubakar ɗin ne ya ƙone, sai kuma ƙonewar ɗakin nan tamkar shine tashin rayuwa ta,da baibayin da aka yiwa bakina da zuciyata duk ya kama gaban sa,wanda kuma tun daga ranar na saka idanu sosai akan duk wani motsi da Habibu zaiyi saboda ina son tona masa asiri,na rasa da wanda zan hada kai domin ya zamar min shaida,sai kawai Alhaji Rufa'i ya faɗo min dan haka na tare shi da maganar ban sha wuya ba ya fahimceni muka haɗa hannu,daga nan shi ya bani labarin su Abdallah da binciken da suke akan wanda ya ɗauke Abubakar, duk da nayi mamakin hakan sai dai kuma da nayi tunanin shifa jami'i ne sai na daina mamaki, A hankali muka cigaba da bibiyar Habibu har muka gano abinda yake shiryawa na sace Bintu na kuma gano Abubakar yana gurin su Abdallah,shine dalilin da yasa naje wajen Alhaji jafar dan yasanar dani inda su Abdallah suke, tunda na tabbatar a ranar Habibu zai sace"Bintu amma sai yaƙi bani haɗin kai daga ƙarshe ma ya fito ya nuna min zargin da yake min akan Abubakar,Ni kuma hakanne yasa na rabu dashi ba tare da na gaya masa shirin da Habibu yake ba,daga baya ne na tabbatar Habibu ya sace"Bintu kuma na bibiyi Abdallah nasan cewa zai kai masa Abubakar kamar yadda suka shirya,duk da nasan wata ƙil da akwai wani shiri da sukayi a ƙasa, amma hakan baisa nayi kasa a gwiwar isa wajen ba,duk da kema kin so ki ɗan bani matsala gurin tafiyata gurin!'ya tsaya da maganar shi daidai nan,yana ɗan ajiyar numfashi,alamun dai yaji daɗin fidda abinda ke cikin ranshi shekara da shekaru,Hajja dai jugum tayi tana al ajabin yadda ɗan ta ya yaudareta,domin duk mugun halinta taso ace yaran ta sun kasance na arziƙi ko zata iya cin albarkacin su ranar lahira,amma yanzu ma ai ga Mansur nan,wata zuciyar tace da ita"ai kuwa kin san barewa bazata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba,halin ki ne sak Habibu ya ɗebo sai kuma yace kauce ki ban guri,tashi tayi tana cewa Mansur dan Allah in dai na isa da kai kaje ka kwanta ka ɗan yi bacci kafin kiran sallah!'shima tashi yayi yana cewa shike nan Hajja amma dai yanzu bazanyi ba sai nayi salla tunda kinji har har n fara kiran farko,idan na kwanta zan iya makara dan haka sai nayi sallah!'daga haka ya fita daga falon zuciyarshi sawai ta rage mugun nauyin da tayi masa, sai dai kuma tunanin inda Hajja ta kai Abubakar yake wanda yana sane dashi azuciyar sa,kawai dai yayi shurune yaga abinda Hajja zata shirya akan fitowa dashi, yasan wata ƙila ta kaishi wani gidan daban dan akula da lafiyar sa kafin dawowar sa gida.

A ɓangaren Anty Nafisa kuwa, A cikin daren ta yiwa Hajiyarta waya tasanar da ita ta shirya tarbar ta tare da arzikin da zata zo mata dashi,Hajiya ladidi da ta haƙura ta saduda ganin babu hanyar samun arzikin gidan Alhaji Balarabe,tace"me kike nufi nafisa? maimakon ta bata amsa sai kawai ta sheƙe da wata irin dariyar farin ciki kana tace"Hajiyata labarin mai tsayi ne abin da yasa ma bazan ce gobe zaki ganni ba saboda ina so sai jibi zan fasa kukan mutuwar sa daga nan na haɗo kan dukiyata nayo gaba!'ita dai Hajiya ladidi jin Nafisan take kamar almara wace irin kukan mutuwa kuma zata fasa?kafin ta samu damar yiwa Nafisan tambayar afili tuni ta katse wayar tare da kasheta gaba ɗaya,takaddun da take ta haɗawa na kadarorin Abba Umar su taci gaba da haɗawa,wanda daƙikiyar ƙwaƙwalwar ta tabata tabbacin cewa na gaske ne,sai da ta gama haɗa su tsaf kana ta tashi ta koma ɗakinta tayi kwanciyar ta tana juyin farincikin samun sabuwar rayuwa..

Kai tsaye É—akin sa ta nufa,shiga tayi tare da Æ´ar sallama saman fatar bakinta,zaune ta ganshi kan sallaya da alama dai sallolin da baiyiba ya rama,wuceshi tayi ta shiga toilet É—in itama,wanka tayi mai rai da lafiya wanda ta daÉ—e tana durzar fatarta,dan ji take kamar ta shekara ba tayi wankan ba,dan haka ta zage ta dirji fatar jikin ta da gashinta,har sai da fatar ta ta fara zafi ga jan da ta farayi abunka da farin mutum,alwala tayi ta É—auro towel mai dan girma ta fito,wadrob É—in sa ta bude wanda take da tabbacin ba zata rasa guntun kayanta anan ba,ilai kuwa ta samu wata doguwar rigar bacci mai santsi har da hijab dan haka ta É—auka ta zura tare da saka É—an turare kana ta zura hijab É—in itama taje bayan shi ta tayar da sallar,saida sukayi sallar asuba kana suka koma biyan bashin baccin da suka ci...
Chapter 99 · 0% Book details