← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 120

Sashe 31

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin kuka Rahima ke zaiyanawa Hajiya Babba dukkanin abinda ya faru, ta ƙare da cewa, Hajiya Babba yaza ayi Bintu tayi min haka? nakasa mantawa ina sonta sosai tausayinta nakeji wallahi!'Hajiya Babba ta shafa kan Rahima kana cikin nutsuwa da taushin murya tace"Rahima bakyason Bintu!'da sauri Rahima ta tashi zaune tare da cewa kamar ya bana sonta Hajiya? yanzu fa na gama gaya miki amma sai kice banason Bintu!'Hajiya Babba tayi murmushin su na manya masu hangen nesa tace"Ai da kinason Bintu da bazaki yadda da abinda ya faruba, domin Hausawa sunce so hana ganin laifi koda an aikatashi kuwa,dan haka ko Ni ɗin nan nafiki son Bintu tunda ban yadda da abinda A kace ta aikata ba,ko da kuwa A hannunta A kasamu sarƙar, kinga Ni ba tare nake da ita ba zuwa kawai takeyi shima zuwan ba sosai ba amma nayi mata yaddar da koke banyi wa ita ba,tana can ina nan amma da ita nake kwana nake tashi,inno bata kyauta ba in dai har ta yadda cewa Bintu zata iya yi mata sata,saboda watannin da tayi tare da ita yaci ace takaranci halayyar Bintu,wanda A cikin abinda nasani dan gane da ita nasan imaninta bazai iya barinta ta ɗauki abin wani ba Abu na biyu tausayinta san nan tsoro,dan haka Rahima ki je ki koyi yadda ake aminta ta gaskiya da amana kafin kiyi ƙawance da Bintu domin nasan idan itace baza ta taɓa yi miki haka ba!'daga haka bata kuma cewa komai ba ta maida hankalinta kan casbahar da takeja,Rahima kuka tasa tana mai jin tsananin kunyar haɗuwa da Bintu bata san da wane baki zata bata haƙuri ba, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga ɗakinta tana mai jin nadamar abinda tayi.

Nafisa wai meye amfanin ki A cikin gidan nan indai har kina kallo wasu banzaye daga can gefe zasu wargaza mana shiri,kin riga da kin san dai Bintu itace idon mu yanzu A gidan nan tun ba mu cimma abubuwan da mukesan cimmawa ba a keson A koreta!'Anty Nafisa tace"nifa Hajiya ban san meke faruwa ba saboda nima kwana biyu bana jin daɗi ban shiga ɓangaren inno ba dan haka bani da masaniya A kan komai dake faruwa!'Hajiya ladidi tace"shike nan amma inaso daga yanzu kisaka mana idanu akan masu kawowa burinmu farmaki!'Anty Nafisa tace"to Hajiya nayi miki alƙawarin bazan bari ƙananan maƙiya suyi tasiri A kan Bintu ba har sai mun cimma burinbu!'suna A jiye wayar Aunty Nafisa ta miƙe daga saman gadon ta, A fili tace"dole shirina bazai tafi yadda ya kamata ba sai da sa hannun Amintacce, kuma ba kowa bace sai Bintu ita kaɗai ce zan iya haɗa wannan al amarin da ita batare da fargaba ba, saboda Ni nakawo ta gidan nan Ni na buɗe mata ido, dan haka babu wadda ta can canta da Bintu ta zauna a ƙarƙashin ta face Ni, kuma tsari na baze yuwu Ni kaɗai ba dole sai da sa hannu dan haka yanzu lokaci yayi Bintu da zakiyi min amfani, bani da shakku akan ke ɗin zaki rufan asiri duk da tarin tsanarki me zafi ta dake ƙunshe cikin raina amma babu yadda zanyi dole na danneta A wannan karon.

A hankali ta zauna gaban inno dake kan sallaya hannunta riƙe da ɗan ƙaramin ƙur'ani,Bintu ta zuba mata ido har ta ida karatun ta kana ta ajiye shi gefenta cikin nutsuwa,ƙara matsawa gabanta Bintu tayi tare da ruƙo hannunta cikin san haɗa ido da innon tace" inno kiyi haƙuri nasan ban kyauta miki ba da nakasance ɓarauniya A gareki duk da tarin halaccin ki A gareni!'hawayenta ne suka gangaro daga cikin idanunta tanajin zafin karɓar laifin da bata aikatashi ba, amma kuma tana ganin haka shine mafita A gareta,A hankali inno tasa hannu ta share mata hawayen, kana cikin taushin kalami tace"Bintu meyasa kike bani haƙuri? meyasa kika zaɓi karɓar laifin da baki aikata shi ba?da sauri Bintu ta kuma runtse hannun inno dake cikin nata,inno ta ciga da cewa,ba komaine yasa nakasa duban ki ba Bintu abu biyune, dalili na farko shine banaso na nunawa waɗanda suka saka miki sarƙa A cikin ɗakinki ban yadda ke kika ɗauka ba domin yin hakan shi zai basu damar cigaba dayi miki ƙullin da kowa zai iya tsanar ki koda kuwa Ni na yadda dake A banza wata rana abun zaiyi girman da ko Alhaji ba zai saurara miki ba,na biyu kuma shine tsananin kunyar ki kasancewar A cikin ahlina A kasamu waɗan da suka shirya miki wannan tuggun,amma wallahi Bintu ban taɓa zargin ki da zaki aikata wa wani ma mugun hali ba balle kuma Ni,Bintu ina ji A jikina ke ɗin wata fitila ce da tazo daga wata duniya dan haska mana abin da mu bama gani, dan haka ki saki ranki da zuciyar ki kici gaba da walwalarki Allah Ubangiji yana tare dake,sai dai ina mai sanar dake zaki ga canji A tare dani indai muna cikin jama'a saboda kawar da idon maƙiya A kanki!'wata kyakykyawar runguma Bintu tayiwa inno ta shiga sun batar ta tako ina tana cewa inno ilove U ina sonki da yawa ina yi miki son so inno, Allah ya barminke nasan idan ina tare dake bazaki bari hawayena su zubaba kece farin cikina garkuwa ta Allah Ubangiji yaja min kwananki domin kika ga ƙudurar Allah da idanunki!'A hankali inno tasa hannu ta sharewa Bintu hawaye itama tayi dabara ta goge nata ƙwallar kana tace"tashi kije Allah yayiwa rayuwarki Albarka!'Buntu ta amsa da Amin tana mai kuma sunbatar hannun inno,bayan ta fita inno tabita da kallon tausayi tana mai addu'ar Allah Ubangiji ya dafawa rayuwar Bintu baiwar Allah.

Kafin wani lokaci Bintu ta shiga walwalarta tare da ƙwarin gwiwar inno mace da babu kamarta A wajen ta sai dai kuma can ƙasan zuciyarta tana jin A kwai sauran abinda ya daƙile farin cikinta na samun yardar inno, tana jin kamar hanyanzu A kwai sauran yaddar datake nema, zuciyarta ce ta rayamata Rahima, a'a ba ita bace ta kuma canja tunani,can kuma ta kuma yin wani tunanin Hajiya Babba tabbas tasan Rahima ta gayawa Hajiya Babba komai dan haka dole taje ɓangaren Hajiya Babba ko dan gano matar datake matuƙar ƙauna,
cikin nutsuwa ta ɗauki ƙatan hijabinta ta saka har ƙasa kana ta nufi ɓangaren Hajiya Babba...

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 23 ```

Lokacin da tashiga falon inno babu kowa dan haka kai tsaye ta nufi hanyar ɗakinta,tana dab da shiga ɗakin taji daga bayan ta ance, wata satar kikazo ki kumayi A nan?da sauri ta juya Sayyid ta gani tsaye da alama yanzu shima ya shigo kamar ma ita ya biyo,ya tako ya ƙara so inda take, kana cikin san cimma wata manufa yace" dama zuwa kikayi na taimaka miki, da ki dinga yawan bin ɗaukar sarƙoƙin kakannin mu dan nasan yanzu ma zuwa kikayi ko zaki dace A nan tunda ta can ta suɓuce miki!'Bintu kallonsa kawai takeyi tana aiyanawa A ranta anya kuwa Sayyid baya daga cikin annobar gidan nan? to idan ba haka ba me tai masa meye haɗin ta dashi? meyasa ya uzzurawa rayuwarta? to lallai kuwa ya jawa kansa matsala domin tasaka masa ayar tambaya, tabbas da A kwai abinda zata iya samu ta ɓangaren sa Sayyid bai kai yayiwa kansa wani tanadi ba sai dai ayi amfani dashi haƙiƙa A kwai wani abu A ƙasa kuma da sannu zata bincikosa,yatsan sa yasa ya ƙyasta mata A kan fuska,bin hannun nasa tayi da wani irin kallo tamkar A cikinsa zata gano amsarta,murmushi yayi kana yace"kina tunanin yadda zaki samu kuɗi A gurinane? to indai wannan ne karki damu Ni ba matsala bace A wajena!'daddagewa tayi ta tattaro duk wani miyau dake cikin bakinta ta tofa masa A fuska tare da jan wani ƙaƙƙarfan tsaki tayi shigewarta ɗakin Hajiya Babba ta barshi tsaye yana binta da mugun kallo yana mai raya mugayen manufofinsa A kanta wanda babu wanda ya san manufar sai shi sai mai ƙudura da irada.
Chapter 31 · 0% Book details