← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 120

Sashe 87

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin hawayen da suke ci gaba da wanke mata fuska ta ɗago da kanta tana kallon fuskar Abdallah da ya zuba idanun sa akan fuskar mutumin da yake jin wata iriyar faduwar gaba akan sa,kama hannun sa tayi ta jawo shi zama yayi gefan ta batare da yace kala ba,sai dai kawai yabi sawunta na jeruwa akasan gadon da mutumin yake kai,kamar saukar aradu haka yaji muryar Bintu nayi masa amsa kuwa yayin da take cewa Yahh Abdallah wannan shine Dadyn ka farin cikin ka burinka alfaharin ka wanda kake kwana dashi kake tashi kake kuma mararin san ganin sa da ganin bayan wanda ya sace maka shi ya hanaka jin daɗin mahaifanka!'ta ƙare maganar da zuba masa jiƙaƙƙun idanun ta,bakin ta kawai yake kalla sai ya koma ya kalli fuskar mutumin da Bintu kira da mahaifinsa,ya rasa da bakin da zaiyi magana,ya kuma kasa tan-tance halin da yake ciki tsakanin farin ciki da ɓakin ciki,to idan yace farinciki zaiyi ta yaya zaiyi farin cikin bayan ga mahaifin nasa a kwance bashi da maraba da gawa,idan kuma ɓakin ciki yace zaiyi ta yaya zaiyi shi bayan ga mahaifinsa agabansa wanda ya dauki shekaru yana faman neman inda yake,kawai sai ya kifa kansa ajikin Dady Abubakar yana fidda wani irin numfashi mai haɗe da wani irin zazzafan huci,yana kuma haɗiye wani abu mai girma da ya daɗe tokare amaƙoshinsa,shuru su kayi gaba dayan su,sai bayan wasu ƴan daƙiƙa ne Bintu ta samu kanta da ɗora hannun ta saman tattausar sumar sa tana shafawa cikin yanayin lallashi da tausayin kan su tace"yanzu me zamuyi agidan nan?ba tajira amsar saba ta ci gaba da cewa nayi tunanin muje mu kaishi gurin malam mu ajiyeshi,kaga za ayi masa magani sannan kuma ya samu tsaro, dan nasan tabbas sai yabi sahun mu,kuma ina ga mukai shi yanzu a cikin daren nan!'ta faɗa tana ɗan bin bangon ɗakin da idanu dan lalubo agogo,lokacin ta ga har ya tura ɗan yanzu baifi saura awa ɗaya akira assalatu ba,dawo da duban ta kan Abdallah tayi wanda har yanzu bai ɗago kan sa ba tun ƙifawar da yayi ajikin mahaifin sa,sai kuwa da yanzu maganar Bintu ta san yaya masa zuciyar sa tunanin sa kuma ya dawo kan hanya, kallon ta yayi idanun sa cike da wani ruwa wanda nake zaton ƙwalla ce ya hanata fitowa saboda tsananin bayaso yayi kuka agaban Bintu,yace"bari na kira su Safwan suzo su kaishi!'to me yasa mu baza mu kaishi ba?zuba mata ido yayi yana ganin yadda take cije bakinta har da wasu tarin ƙwallan da suka cika ƙwayar idanun nata,kamo hannun ta yayi babu zato ko tsammani saiji tayi ya kifa ta akan kafar sa da ya miƙeta, kafin ta gama tunanin abin da zaiyi mata kuma ta tsinci hannun sa kan gadon bayanta inda rigarta ta ƙone har ya shafi fatar jikinta,me yasa kike ɓoyewa?ya tamabeta cikin muryar sa da ta kuma yin ƙasa yana kuma zagaye yatsan sa agurin,cikin jin zafin ƙunar tace"na fiso mu gama da lafiyar Dady kafin tawa tunda ni mai sauƙi ne!'a gurin ki ko?ya faɗa yana zaro wayarta dake aljihun sa,cikin sakanni ya turawa su Safwan test saboda yana da tabbacin dai yanzu sun dawo Abuja,yana tura test ɗin ya tashi ya fara haɗa kayan wanke ciwo zuwa yayi ya wanke mata sai dai a wannan karon baƙaramjn dauriya tayi ba,ko dai dan taga ba allura bace,yana gamawa su Safwan suka bashi tabbacin sun ƙara so gidan cewa yayi su shigo,fita yayi dan buɗe musu ƙofa,yana bawa Bintu umarnin, ta shiga toilet zasu shigo su ɗauki Dadyn,daga haka ya fita daga ɗakin,jim kaɗan suka shigo gaba ɗayan su, yaji daɗi da bai samu Bint a ɗakin ba,kama Dady Abubakar su kayi tare da fita dashi,har cikin mota suka sakashi tare da gargaɗin Abdallah da kuma kiyayewar da yakeson suyi.

A zaune ya same ta ta haɗa kanta da gwiwar ta,yanzu sun gama da ɓangaren Dady sai kuma mahaifiyar ta da fafinta Allah yasa suna cikin lafiya,fatan ta ke nan a kullum,shigowar sa ce yasa ta ɗago kanta,dukbdavba kallon shi take yiba amma dai tana kallon saitin da yake,tahowa yayi gabanta tare da kamo hannun ta miƙar da ita tsaye yayi,kana yaja ta zuwa toilet,cikin matuƙar kula yace"zaki iya wanka?daga masa kai tayi idanunta nasan fitar da ruwa,girgiza mata kai yayi yana cewa a'a Ni fa ba kuka nace kiyi ba, Bint meyasa kuka baya yi miki wahala ne?ya faɗa cikin yanayin zolaya duk dan san yaga ta saki ranta,ɗan tura bakin kuwa tayi zatayi magana ke nan ya ɗora bakin sa kan nata,sanyin harshen sa tare da ƙamshin da ya zauna da'iman acikin sa,yasa ta lumshe idanun ta,bata kuma yi ƙoƙarin ƙwace kanta ba ta saki jikin ta suna tanɗe bakin juna,saida suka dau tsawon mintuna biyu a haka kana ya janye yana mai kashe mata ido tare da cewa, Bint kin kuma ko?kallon sa tayi da alamun tambaya,dan langaɓe kan sa yayi tare da turo mata jajayen lip ɗinsa yace"kin kuma cinye min baki bayan ban rama wan can ba!'ai tana jin haka ta juya masa baya tare da rufe fuskar ta da tafikan hannun ta.wani dan murmushi ne ya suɓuce masa ganin yasamu abin da yake so sai juya zai fita,juyowa tayi ta zubawa bayan sa idanu,karaf sai gashi ya juyo,da sauri ta kawar da kanta,yace"ya dai ko nazo nayi miki wankan?kukan shagwaɓa tasa masa tana buga ƙafar ta aƙasa,fita yayi tare da ja mata ƙofar.

Bayan fitowar ta shima shiga yayi yayo wankan,a bakin gadon ya same ta duk tabi ta kanannaɗe jikinta da bedsheet ɗin saboda babu abinda zata ɗaura towel kuwa tana ganin idan ta daura abinda ya faru ranar zai kuma maimaituwa,shi yasa taga kamar zama da bedsheet din yafi mata sauki,har ya gama abinda yakeyi yasaka kayan bacci bata motsa daga nan inda take ba,ɗan daga banta yayi kana yace"Bint kinji anfara Kiran sallah ina fata dai kin yi alwala? daga masa kai tayi,fita yayi daga ɗakin jim kaɗan ya shigo da sallaya da kuma doguwar jallabiyar sa wadda ta ɗan ɗage masa,miƙawa Bintu yayi tare da bata umarnin ta saka,tana daga zaune ta zura rigar san nan ta tashi tsaye,duk da cewa tayi masa kaɗan rigar amma saida tayi wa Bintu yawa,sabon tawul ya bata mai girma yace"maza rufe kanki muyi sallah!'karɓa tayi ta rufe jikin ta kana suka tayar da Sallah.

Duk da matsanancin rashin hankalin da yake ciki amma haka ya daure ya ɓoye bai nuna wata damuwa akan fuskar sa ba,yabi ayarin da suke shiga sallah shima ya shiga yayi kamar yadda suka saba shida sauran ƴan uwansa,yana fitowa ya bar gidan dan yasan tabbas za ayi maganar ƙonewar dakin kuma bayaso ya tsaya ganin takaici,kamar yadda yayi zato don kuwa haka ce ta kasan ce,duk inda ka gifta zancan ƙonewar dakin akeyi,wasu dayawa basu ɗakin ya ƙone batare da sun san abinda ke cikin saba shekara talatin da ɗoriya,Alhaji Baba da kansa sai da yayi tu ajjubin Al'amarin.

Bacci suke yi baccin da basu samu sunyi shi a daren jiya ba,idan kuga yadda Bintu da Abdallah suka cure guri ɗaya sai abin ya baka mamaki da da dariya ga kuma sha'awa, Bintun ce cikin jikin shi ya kanannaɗeta kamar wani zai ƙwace masa ita,wayar da ya karba a hannun Safwan ce ta fara ringin wanda shine dalilin farkawar sa daga baccin da yake yin sa ba tare da wani dadi ba,saboda mafarkan da suka da baibaye baccin marasa daɗi,da sauri ya dauki wayar dan kar ƙarar ta ta tashi Bintu,daniyal ne ya kira shi bayan sun gaisa daniyal yake cewa Oga nayi ta kiran wayoyin ka wasu suyi ringin wasu kuma akashe shine na sanar da Safwan ya bani wan nan layin!'Abdallah cikin yanayin bacci yace"haka ne Daniyal me ya faru? daniyal yace"Oga ka manta da tafiyar mu cikin suleja?cikin sauri Abdallah ya miƙe har saida Bintu ta farka a razane,yace"daniyal na sha'afa amma yanzu ka shirya kazo gidan nan na gari ka same Ni!'daniyal ya amsa cikin girmamawa kana suka ajiye wayar,Bintu da gaba ɗaya hankalin ta yana kansa cikin tsoro tace"me ya faru Allah yasa dai ba Dady bane!'ta faɗa cikin sanyin kuka,yace bashi bane amma dai yanzu mu shirya da akwai inda zamuje,bari nayi waya Safwan ya samo miki kaya ya bawa daniyal ya taho dasu,

Sorry no edittin
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 50 ```

Ba tace dashi komai ba amma dai gani take kamar wani abun yake ɓoye mata,ba'A fi mituna goma ba sai ga kiran daniyal,ba tare da ya ɗauki wayar ba ya tashi ya fita daga ɗakin,jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata leda,miƙawa Bintu yayi tare da cewa sauri ki saka zamu tafi!'tashi tayi tana ƙoƙarin shigewa toilet sai taga ya juya ya fita daga ɗakin hakan ne ya bata damar saka rigar tare da yana mayafin ta asaman kanta,fita tayi falon gidan wanda suka ci karo da Abdallah shima ya fito cikin shigar sa ta ƙananun kaya wadda sukayi masa matukar kyau suka kuma fito da zallar kyawun jikin sa,ɗan kallon sa tayi kana ta ɗauke kai,yayi mata kyau sosai amma ita yanzu tsoron kallon sa ma takeyi dan kar yayi mata wata fassarar,

Sarai ya gano ta amma bai magantu ba,fita sukayi tare, Daniyal yana ganin su yayi saurin buÉ—e motar suka shiga baya,ya rufe tare da komawa mazaunin drever,a hankali ya fara jan motar har suka fita daga gidan,fita yayi ya rufe get din kana ya dawo suka dauki hanyar zuwa gidan Hajjo.
Chapter 87 · 0% Book details