Sashe 28
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fans ɗin ƙudurar Allah ina godiya da addu'ar ku gareni Allah ya ƙara mana zumunci da so da kauna,love U kwando kwando
```Page 21 ```
Yau gaba É—aya jikin Bintu A san yaye yake kasan cewar tun safe mutanen nata suka haÉ—a dabar hira A falon inno, wani abin takaicin ma har da mazan suka gayyato,kuma ba komai ne yasa sukayi hakan ba sai dan kawai yau sun shiryawa Bintu buhu buhun rashin mutunci, saboda tun sassafe suka ga fitar do don nasu,yau kwana biyu da faruwar wancan abun, dan haka yau dama suka samu.
Bayan ta gama jigilar kaiwa da kawowa tayi musu girkin dasuka buƙata, sai da ta jera musu komai na buƙata A gabansu kana ta wuce dan ƙoƙarin ta na barin falon,Sayyid ne yace"ke dawo nan uban waye zai savin ɗinmu? Farida ta yatsina fuska kana tace"Ni kije kisake min sakwara dan bazan ci wannan abincin ba!ita kuma Siddiqa tace" Ni kuma kiyi min danbun shinkafa! Bintu cike da takaici take duban su ta kasa cewa komai saboda mamakin ɗabi'ar su Hauwa'u ce tace"dalla Malama kije kiyi musu abinda suka buƙata kin tsaya mana akai yawa tsohuwar maiya!' juyawa tayi har ta fara ta fiya sai kuma ta ɗan da kata tare da juyowa jin Siddiqa na cewa banzar yarinya dama ai wan can uban shishshigi shine kwarin gwiwarta, ranar har da wani zagewa tana sheƙa mana mari to yau zakici ubanki idan kina dashi!'A hankali ta buɗe bakin ta tana son cire tsoronsu dake dan kare A ranta dan Allah ya gani Bintu tana tsoron taɓa lafiyar jikinta dan tasan zasu iya naɗa mata na jaki, amma badan haka ba sam batajin zata iya raga musu ta ɓangaren ragargaza musu magana ko wace iri ce, cikin san jawo ƙarfin gwiwa tace" to shikenan bazanyi girkin ba tunda aibaku kuka ɗaukeni aiki ba kuma ba asaminku A cikin albashi na ba balle kudinga wahalar dani kamar baiwarku,ta faɗa A yayin da take shirin bawa ƙafarta iska,dan tasan tsaf zasu naɗa mata duka,kamar ta sani kuwa Farida mai jiran ƙiris ita ta miƙe tayi wani irin tsalle ta sha gaban Bintu,da sauri Bintu ta matsa baya cikin yanayin ta na nuna firgici ,Nabil yace"ke Farida meye haka ne? Hauwa'u tace"idan bataya mu dukanta zakayi ba kayi shuru da bakinka inno bata nan tana ɓangaren Alhaji Baba Dan haka zaneta zamuyi la ada waje!' Sayyid yace" malam ka rabu dasu su zane bakin tsiwar duk da mugun sanda nake mata hakan ba zai hana nayi mata rashin mutunci ba!'Bintu tace"Ni dan Allah ku rabu dani babu ruwana daku,kuma ai gaskiya na faɗa ba aikinku nazoyi ba da haka sai ku rabu dani!kan ta rufe bakinta Siddiqa tasa hannunta ta doke bakinta,aiko Bintu taji zafi tuni idanun ta suka kawo ruwa wata zuciyar tace"da ita karki sake ki bari suga hawayenki daga nan zasu ƙara rainaki, dan haka sai tayi ƙoƙarin shanye hawayenta,A hankali ta shammace su ta angije Farida ta hankaɗata tayi ƙasa bata tsaya wata wata ba ta arta ɗakinta tasaka key, Farida ta lailayo wani uban ashar ta dan ƙara mata, Sayyid yace" kuzo kuji wani abu wannan duk ba mafita bace!' gaba ɗayan su suka zo suka haɗa kai yayi musu ƙusƙus, Siddiqa ta yi wata shewa tare da cewa lallai yarinya kin ɗauko ruwan dafa kanki kin shiga uku a gidan nan!'dariya suka saka gaba ɗayansu suka shiga ɗibar garar girkin Bintu maisa kunnen oga Abdallah motsi.
Taufiƙa ce ta samu Bintu A kiching tana yiwa Abdallah abincin dare sai dai bata jima da ɗorawa ba saboda tsoron kar ta fito su haɗu su casata, Taufiƙa tace" Bintu me kike dafawane haka? batare da ta bata amsaba ta zuba mata ido cike da mamakin yadda tayi mata magana cikin kwantar da murya, murmushi Taufiƙa tayi tace"ko yau kin kurmance ne? girgiza kai Bintu tayi kana tace" yau tuwon semo nakeyi masa da miyar ɗanyan kubewa sai farfesun kifin ruwa!' Taufiƙa ta riƙe baki cikin mamaki tace" wai shi kam dan Allah Bintu meyasa yakeson irin wadannan abincin? Bintu tayi dariyar ta me kyau har kumatunta na loɓawa kana tace"wallahi Ni ma bansani ba kawai dai kowa kinsan da abinda ya fi burgeshi A rayuwarsa to shi dai yana san abincin mu na gargajiya!' Taufiƙa tace" kuma hakane fa maganarki!' yanzu dai ki kawo nayi masa girkin nan yau inaso yaji irin baiwa ta nima saboda nan gaba!' ɗan jim Bintu tayi cike da tunanin ta bata ko kar ta bata,Taufiƙa tace" Bintu bazaki bani ba?kinga dolene na koyi duk irin abibcin da yake so saboda gaba yadda nake mafarkin zama matarshi kinga hakan shine dai dai ko?Bintu cike da mamaki take bin bakin Taufiƙa da kallo kai wannan irin wawanci haka, sai yanzu ta gane manufar ta na yadda ta can ja mata lokaci ɗaya ashe ita da manufarta wato ashe ita ma ta faɗa komar soyayyar Oga Abdallah,tab amma lallai sun gamu da wahala in dai Oga Abdallah ne, Bintu tace to shikenan muyi tare!' Taufiƙa tace" Ni dai ki tsaya kawai ki tayani da hira har na gama sai ki ɗiba kikai masa!' Bintu tace Tom shikenan,amma fa ranta cike yake da tsoro kawai dai ta bayarne saboda kar ta jangwalo wa kanta wata rigimar bayan ta ɗazu da tasan ba ƙyaleta su Farida sukayi ba,
Sunayi suna hira har Taufiƙa ta gama komai aka zuzzuba cikin kuloli, daga nan ta koma ɗaki sai da tayi sallar isha'i kana ta fito ta ɗibi kayan abincin ta nufi falonsa,bayan ta jera komai kamar yadda ta saba ta fito tashiga wajen inno suka fara taɓa hira.
Sai da ya gama komai na aldarshi da yasa ba na yau da kullum kana ya nufi dining ya zauna ya fara savin ɗin kansa. lomar farko da yayi kasa haɗiye wa yayi sai da ya nufi sink ya zubda kana ya kuskure bakinsa ya koma ɗakinsa ya shiga yayi brosh,zama yayi cikin kujerarsa ya haɗa hannayen sa biyu ya rufe fuskarsa, yunwa yakeji sosai danshi bai cika san zama da yunwa ba, tun daya saba bawa cikinsa haƙƙinsa, wayar sa ya ɗauka ya dannawa inno kira,bayan sun gaisa yace" inno yarinyar nan tazo!'daga haka ya maida wayar ya ajiye,inno suna tare da Bintu har lokacin,duban Bintun tayi dan tasan ita yake nufi sanin cewar babu wanda yake shiga ɓangaren sa idan ba itaba,tace" tashi kije saraki na kira wataƙil wani abun yake buƙata!' dum,haka ƙirjin Bintu ya buga cike da fargaba ta tashi ta tafi tana fatan Allah yasa ba ganewa yayi ba ita tayi girkin ba.
A hankali tayi sallama tare da ƙara sawa gabansa ta duƙa,kana tace" Barka da dawowa wani mugun kallo ya fara watsa mata kafin yace" wa kika bawa yayi abincin can? yana maiyi mata nuni da kan dining table,kallon gun tayi kana cikin tsoron abinda zai biyo baya tace" Ni nayi!' ɗan wara idonsa yayi akanta gami da cewa ko? gyaɗa kanta ta kumayi a tsammanin ta ya yadda, miƙewa yayi yace" zo nan!'tashi tayi tabi bayansa har zuwa dining ɗin, sai da ya zauna kana yayi mata nuni da itama ta zauna,A ɗarare ta ɗosana ta zauna gaba ɗaya idanunta sun fiffoto waje saboda tsananin tsoro,nuna mata wanda ya faraci yayi yace" oya maza kicinye su duka,zaro idon ta kumayi da sauri ya kawar da nasa,cikin ransa yace" yanzu zata fara firgita mutane da waɗan nan shanyayyun idanun,fuska ta kwaɓe tana shirin sakan mai san gar tattun hawayen ta,yayi saurin ɗora hannun sa kan laɓɓansa yayi mata alamun tayi mai shiru,haka nan ta haɗiye kukanta ta sanya hannu ta gutsiri tuwan tare da kaiwa bakinta,kasa haɗiyewa tayi tafara ƙoƙarin furzo shi,zaro mata manyan idanunsa yayi wanda suke da wani irin maganaɗisu acikinsu, ga wani maiƙo- maiƙo dake cikinsu tamkar manƙuli aka ɗiga musu,tuni ta kuma rikicewa dama ga yanayin da take shiga a duk lokacin da ta kasance tana shaƙar numfashi akusa dashi,sai ya kuma haɗe mata ya dinga bata wani irin yanayi mai wuyar fassarawa har wani sanyi sanyi take ji A can cikin ƙashushuwa da ɓargon ta,ƙasa tayi da kanta tana haɗiye tuwan daƙyar,haka ta dinga cusa tuwan cikinta tana kuma zabgawa Taufiƙa Allah ya isa saboda ita tajawo mata wannan tashin hankalin,bata taɓa zatan bata iya abinci ba ita A tata wautar tayi zatan kowa ya iya abinci mai daɗi shiyasa ta bata batare da tayi tunanin haka ne zata kasance ba, A nata yaritar kawai tunda bai gani ba ai bazai gane ba ita tayi ba.
Sai da ta cinye wanda ya faraci, da ƙyar,kana ta ɗan saci kallonsa yana ta danna wayarshi hankalinsa kwance,cikin san rushewa da kuka tace" na cinye cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta mai fitar da wani sauti mai daɗin sauraro,kallo ya bi ɗan karamin bakin na ta dashi wanda bakowane zai fahimta ba sai ƙwararren munasiri (amma fa bani ba) A hankali yace" sauran fa? fashewa tayi da kukan da yake ta cin ranta,maida kansa yayi yajinginar tare da lumshe idanunsa yayin da zara zaran eye lashes ɗinsa sukayiwa idanun runfa,jin sautin kukan yake har can cikin ƙasan zuciyarsa,muryarta yaji tana cewa,Ni dai kayi haƙuri wallahi ita tace" sai na bata tayi maka saboda ta saba!' buɗe idanun yayi ya ɗorasu kan rigimammiyar fuskarta kana yace ita wace haka? Taufiƙa!' ta bashi amsa kai tsaye abinta, ya tsina fuska yayi danshi har yanzu bai fahimci shirman nata ba,batare da ya nemi ƙarin haske ba,yace" da ita kije ki samomin wani abu da zanci yanzu saura ki kuma bawa wata tayi min jagwalgwalo!' da sauri ta miƙe cikin share hawayen da ya ɓata kyakykyawar fuskarta,tace" me zan dafa maka? komai!' da ga haka ya miƙe ya barta tsaye tana faman tura ƙaramin bakinta.