Sashe 7
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mom abigail ce zaune tsakiyar rog capet din dake malale akasan falon,tayi kuka har ta gaji dan kanta, hawaye duk sun bushe mata,kofar falonce ta sanar da ita akwai bako wanda kesan shigowa ta hanyar wani Jan futula da yake kawo haske ta cikin falon,ahan kali ta jawo rumot din kafar ta danna nan take glass door din ta zuge, matar dake bakin door din ta shigo afuja atan kana ganin ta kasan tayi yar doguwar tafiya amma saboda bala'i naa cinta ko zama bata iya ba ta hau sababi,tace' ke abigail Ina wannan tsinan nan yaron naki? da baya ganin kan mutane da furfura maza ki fito mun dashi tun kan naci miki mutunci!' da sauri abigail ta mike tare da Jan hannun mamanta ta, cikin yanayin roko da magiya tace" mama kiyi shiru zo muje sama muyi magana fatash son yana nan kin san kuma bayasan hayaniya bare kuma irin wannan!'cikin hangame baki na matukar mamaki maman abigail tace" woo na wawoo abigail kene kika koma haka kinajin tsoran yarinyanki!'kasancewar yanzu cikin gurbatacciyar hausarta take maganar, abigail tace'"naji mama ni dai kizo muje sama zamuyi shawara dole sai mun hada da dabara kinsan halinsa yanzu fatash bazai murduba yana nan da halinsa saima wanda ya karu
dakyar mama ta yadda da shawarar abigail,suka haura sama amma taki yadda tasa komai abakinta ,sai ta samu mafita, mama ta gyara zamanta tare da kara fuskantar yar tata,kana tace" abigail Ina mafitar?cikin yanayinta na damuwa race" mama aure zanyi masa Ina ganin shine kawai abunda zai canja shi daga wannan halayya,mama ta zuba mata ido kana ahankali ta furzar da wani zazzafan iska daga bakinta,tace'"kina ganin wannan itace' mafita agaremu? kuma kina ganin zai amince da wannan' din? cikin sauri abigail tace'"akwai hanyar da zanbi,Ina ganin niomy zan fara kawowa mu gwada akanta ko zamu dace, daganan sai mu fara addu'a akansa!' mama ta sauke tagumin da tayi,sannan tace' to allah yasa karyaa karya musu yarinya, dan haukan dankin nan kullum karuwa yake!'nan da nan mom abigail ta hada rai, tare da cewa" gaskiya mama kidaina cewa fatash mahaukaci,idan kika sake yajiki kuma wallahi babu ruwana!'ta fada ta na gunaguni.
...... BAUCHI.....
Adame take kallon bakin fafi wanda yake tayi mata nasihu tun tashinsu a safiyar yau, ta fuskance shi yau kwata-kwata baya cikin walwala, duk da yanayin rayuwar dasuke ciki hakan bai hanasu walwala da farinciki ba,fafi yakance mata bintu duk wanda ya kasance me yadda da kaddara da tawakkali da jarrabawar rayuwa baya taba Bari asan damuwarshi Kuma baya bada kofar da za asan ahalin dayake ciki,shiyasa zaki ga Ina yawan janki da wasa domin kikasance me boye damuwarki aduk inda kika kasance!'
rumtse idanunta tayi adai dai lokacin da taji fafi kana kiran sunanta,hakan ya nuna mata lallai tayi nisa atunaninta,fafi yace"da ita bintuna ban hanaki irin wannan zurfin tunanin ba kina karamarki dake ?cikin dan tura baki da kuma tarin kwallar da tacika fararan idanunta tace"fafi kaine,banaso,kadaina!'to bintu me kuma nayi? fafin ya tambayeta cikin sigar lallami, cikin gab da rushewa da kukan da ya tokare mata makoshi,tace"fafi wannan maganganun ne banaso jinake kamar wasiya kake ajiyemun!'shima cikin san rushewa da kukan yace " a'a bintu kar muyi haka dake ai ba yau na fara yi miki irin wannan zantukan ba!' cikin rushewa da kukan da ta kasa rikewa tace" fafi yau na musamman ne bantaba jin yadda nakejiba ayau,inajin wata kewa na mamaye dukkan sassan jiki da ruhina,fafi bazaka gayan abinda kake boyen ba har sai mun rabu, fafi kadaina boyen komai na girma fa,kar ka tafi kabarni baka gayan yadda zan fuskancesu ba,karka tafi baka gayan wadà nda zan mamaya ba, kar ka tafi baka gayan inda zanje da abinda zanje dashi ba,fafi karka tafi baka bani tarin amsoshin tambayoyi na da suke kanka ba,kuka take sosai
tamkar zata shid'e,fafi ma kuka take, kukan kewa kukan tausayi kukan fargaba,kukan wayyo rayuwa, yana matukar tausayin bintu,to yanzu me zaice mata? tayaya zai fara gaya mata?abu daya yasan zai iya nuna mata, wanda zai haska mata hanya,ta katse masa tunani da cewa'fafi kai nake sauraro,ahankali ya kama hannunta yace"bintu ba'abinda zan iya fada miki,sai abu daya,shine kije ki nemoshi aduk inda yake,zaku haska hanyar junanku dukkanin ku kuna bukatar temakon juna!'wani guri taga ya zubawa ido yana kuma girgiza kansa,yayin da bakinsa ya sarkafe ya kasa karasa mata,cikin kidima tashiga girgizashi tana cewa"fafi menene?ka fadamun a'ina yake yaza ai na ganeshi? meye sunansa?wane gari zan nufa?amma, Ina fafi shiru da alama dai fafi....
Tofa tafi-tafi dai akwai'fa murda-murda duk inda kuke zaton al'amarin ya wuce haka,
soyayya zazzafa me cike da wani irin salo me ratsa,zuciya cin amana makirci, tausayi ga kuma curku dadden lamari.....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 7 ```
...... ABUJA.....
Pastor david ya zubawa mom abigail Ido yana sauraren tatsuniyar datake rangada masa,wai zata kawowa fatash matar aure,abin da matukar wuya,waisu mata meyasa kullum tunaninsu baya yakeyi,duba sai kace bata san halinsa ba,amma sai bai saurin gwasaleta ba,yace"yanzu kina ganin wannan mafitarce zata bulle miki?kina ganin yaron nan zai iya kallon macen da zaki kawo amatsayin matar da kikeso ya aura? abigail ina jiye miki aikin danasani akan abinda bazai amfaneki ba!'ya dire zancen da zuba mata Ido dan jin abinda zatace",
cike da karfin gwiwa mom abigail tace"tabbas zanyi duk yanda zanyi dan ganin fatash awannan karon bai bani kunya ba,mace zan kawo mai wayo da kissa, wadda duk irin tsananin murdewa da kafiya da miskilancinsa sai ya sauko yabita, awannan karon bazanyi sakeba!'ta karasa maganarta cike da confidence,david yayi murmushi me dauke da ma anoni kana yace"shike nan amma kisani duk abinda ya biyo baya karki nemeni,sannan ina da sharadi bayan amin cewata!'da sauritace"meye sharadin?yace" nima akwai abinda nake shirin zartarwa akan fatash,yanzu na bar miki filin amma indai dabararki batayi ba zanyi abinda na shirya, kuma karki sake kice dan me? idan lokaci yayi kawai ki zuban Ido kamar yadda nayi miki karkiyi mun tashin hankali, karki daga mun hankali,Ina fatan kin amince!'batare da wani dogon tunani ba tace" ta amince.
....alhj balarabe estate....
Dijee ce agurfane gaban uwargijiyarta, babu abinda take sai kakkarwa da rawar baki,hankalinta amatukar tashe yake zuciyarta tana cike da alhini da danasanin shigowarta cikin wannan ahli,cikin wata irin gigitacciyar tsawa matar tace da'ita"amma dai ke dije ban taba sanin cewa bakyasan rayuwarki ba sai yanzu, kinsan kuwa abinda kika jamun?kinsan tashin hankalin da kika jefani?ko da ike dama naga take-takenki bakyasan wannan aikin da nasaki,to ki sani yadda aka fara dake to tabbas dake za'agama,kinriga kinsan sirrina ayanzu baki da fita dolene kisawa bakin ki linzami ko dan rayuwar yaranki, kuma dolene mu gyara wannan bar nar tare,dan haka yadda nake cikin tashin hankali dole kema ki dandana kiji ya'akeji!'daga nan tayi wani shu'umin murmushi tare da jefawa dijee wayar hannunta tana ci gaba da wata dariyar mugunta,da sauri dijee ta kawar da fuskarta daga kan allon wayar dan ganin yadda wasu katti zaratan maza majiya karfi kewa danta masduk wani irin duka nafitar haiyaci,jini suke fitar masa tako ina,ita kuwa kanwarsa azaba suke mata da ruwa me tsananin sanyi dasaka mutum tafiyar suman wucin gadi,cikin wani irin rikitaccen kuka me taba zuciyar me imani tace" dan allah rankishi dade ki taimakamun kisa arabu dasu, na daukar miki alkawari duk abinda kikasani zanyi batare da kuskure ba, kiji kaina, suka dai suka ragen aduniya, sune sanyin idaniyata!'ta fada tana rike da kafar hajiyar ,fuzge kafarta tayi taja baya gami da tamke fuska, kana tace"dije wannan alkawarin dakika dauka shi kadai zai taimaki yaranki daga fadawa tarkona,dan haka kije saina nemeki!
D.A.D special hospital.shine asibitin dr abdallah (fatash) cikin takunshi na zaratan maza karfafa masuji da da tsantsar kyau da kwarjini yanufi lifter hawa na biyar inda anan office dinsa yake, yana shiga sakatariar sa me suna nabiha tayi azamar mikewa tare da tattaro nutsuwarta,tace" good morning sir!'ko gefan da take bai samu alfarmar kallonsa ba, bare ita, yana shigewa ta saki wata kakkarfar ajiyar zuciya ta tsabagen tsoro da kuma azababbiyar soyayya me cin zuciya da ruhi.
Hadadden office ne wanda yake cike da duk wani nau'i na amfanin lafiyar dan' adam,zama yayi cikin kyakykyawar kujerarshi me kama da ta sarauta,kana cikin yanayinsa me cike da nutsuwa yasa hannu ya fara duba wasu muhimman fayal, cikakkun mintuna goma da shigarsa sannan nabiha ta yi kokarin fara gabatar da marasa lafiyar dasuke ta tsumayin jiransa,
Agajiye yake taka dogayen kafafunshi akan tattausan carpet din dake malale akasan tan gameman falon,idanushi alumshe suke dan bazaka taba tsammanin yana kallon gabanshi ba,
Mom dake zaune tun misalin bakwai na mangariba tana dakon shigowarshi, tayi saurin mikewa dan tarbanshi sai dai kuma wani kallo da ya bita dashi me cike da alamun gargadi shine ya dakatar da'ita daga niyarta na kama jakar dake a hannunsa,ganin yana kokarin shigewane yasa tayi azamar bin bayanshi dan tasan indai tabari ganinsa yanzu ya kufce mata ta tafka babbar asara dan kuma ganinsa zaiyi mata matukar wuya, yana jin takunta amma sam bai kula ba, danshi magana daya zuwa biyu ma gagararshi takeyi,zama tayi afalonshi kana cikin marairai tar murya tace fatash son dan allah zanjiraka anan ka gama bukatun ka inason zanyi magana da kai! ta fada tana mai hade hannayenta alamar roko dan Jim yayi sai kuma ahankali ya gyada kanshi gami da karasa shigewa,
Rawa tayi harda juyi dan tasan tunda ya riga ya amsa to tabbas zai fito ya saurareta, danshi indai yace zaiyi abu da wuya kaga ya sauya magana yau agareta farar ranace me wuyar zuwa.