← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 120

Sashe 34

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taufiƙa tana ganin zai fito tayi sauri tabar bakin ƙofar,sai da taga ya shige ɓangaren sa, kana ta shiga ɗakin,samun Bintu tayi tana kukan allura,tsayawa tayi A kanta tana fidda wani irin huci na tsananin kishi da tsana,tace" yanzu me zaki iya cewa game da wannan? sabo da sabon iskanci yau har sai da kikayi kisisinar da yashigo ɗakinki,wai Bintu me kike nufi da Yahh Abdallah ne?ɗan ranƙofawa tayi kana cikin tabbatar mata da abinda zata iya aikatawa taci gaba da cewa, Bintu idan har bakya son shiga tashin hankalin da baki taɓa tunanin zai kusan ci rayuwarki ba to lallai kar kibari zuciyar Yahh Abdallah ta fara sonki,san nan karki bari taki zuciyar tayi gangancin son Yahh Abdallah,wannan kashedi ne da nake miki saboda tsira da farin cikin ki, wallahi Bintu bantaɓa faɗar abu na karya shi ba muddin kika bari Yahh Abdallah ya soki to ki tabbatar da cewa zan iya saka wuƙa na yanka wuyanki, batare da nayi na dama ba,gara gara ma taki zuciyar tasoshi wannan ke zaki zauna cikin wahala,dan haka ina fatan zaki kiyaye!'daga haka ta fita ta bar Bintu sake da baki da wani irin maɗaukakin mamaki,meyasa wai bata gama da wani al ajabin ba wani yake danno kai, wai mace matashiya ce da irin wannan kaifin harshe,to wai shin gidan nan me yasa ɓara gurbin cikin sa sukayi yawa? meyasa mutanen kirki basu da yawa? wai waye silar gurɓacewar ahlin ALHAJI BALARABE ne,tabbas wannan shi ake kira da wata sabuwa,to amma ita ina ruwanta da Oga Abdallah meyasa take tunanin zai sota koda ita taso shi tabbas Oga Abdallah ba zai taɓa santa ba saboda babu gami babu alama wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa,miƙewa tayi ta ɗauro alwala ta fuskanci alƙibla domin miƙawa Allah kukan ta da kuma neman kusanci da shi.

Washe garin ranar kuwa garau ta tashi sai dai al amarin da yake ɗan cizan zuciyar ta har yanzu shine mamakin Taufiƙa,tabbas taga matuƙar ƙoƙarin ta tare da ƙarfin halinta, haƙiƙa sai tayi hankali da waɗan nan mutane huɗu Taufiƙa Siddiqa Farida da kuma Oga Sayyid,dan tabbas ta fahimci mugayen marasa mutunci ne,kuma zasu iya kawo mata cikas gurin aiwatar da aikinta,da wannan tunanin ta ta fito daga ɓangaren Oga Abdallah,wanda kwata kwata basu haɗu ba dan sai yanzu taji ta na matuƙar kunyar haɗuwa dashi,saboda ta gano ya gane abinda yake damunta jiya,tunda gashi ya bata magani da allura kuma taji sauƙi,wato dai yana nufin yadda yake gane halin da mutum yake ciki, shima haka yakeso A dinga gane yaransa, na kurame,ai ko baze yuwu mutum da bakinsa yaƙi yin magana ba wannan kam sai shi Oga Abdallah.

Tana shiga ɗakinta ta ji wayar ta na ƙara,da sauri ta ƙarasa inda ta ajiye wayar a ƙarƙashin fulo ta ɗauka,sunan Aunty Nafisa taga yana yawo saman fuskar wayar,ɗagawa tayi tana tunanin me kuma ake shirin ƙullawa dan dukkan kiran da Hajiya ladidi zatayi mata ko Anty Nafisa,kirane na sabuwar buƙata na baƙar manufa,batare da Anty Nafisa ta saurari gaisuwar ta ba tace"lallai ina buƙatar haɗuwa dake yau dan haka kizo ɓangare na kisameni!' ido Bintu ta waro tare da cewa lafiya dai ko? ba tambayar ki nake buƙataba ganinki nake buƙata dan haka ina jiranki!'sauke wayar Bintu tayi daga kunnen ta tare da cewa Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu sai na roƙi Allah ya bani ikon juriya akan sabon Al'amarin da zaki zomin da shi dan ina da tabbacin ba Alkhairi ne yasa kike nemana ba...

Anty Samira ta dubi oga Abdallah tace"na kammala dubawa yanzu dai sa hannun sir Adebayo muke buƙata da sa hannun Babban sakataren kungiyar Dss,daga nan sai mu shiga bincike ka in da na'in!'Abdallah ya cire na urar dake saƙale A kunnensa,kana cikin tsurawa computer dake gabansa ido yace"duk bamu da matsala da wannan tunda munsami babban sahannu daga manyan su wannan ma ba zai gagara ba tunda duk muna tare dasu,yanzu abinda ya kamata muyi shine,inason hada mitin ɗin sirri wanda acikin sane nakeso na tace waɗanda basu can canta da wannan aiki ba saboda ina tunanin an samu ɗan leƙen asiri acikin mu, ma ana dai wanda yake fitar da sirrin mu saboda jiya ankawo min hari har cikin gida, A yadda tunani na ya bani tabbas an fitar da wani shirin mu shiyasa har aka fara shawarar kasheni,kuma daga haka zasu iya canja wani tsarin, dan haka tunda nasan yanzu sun san abinda muka shirya musu to mu kuma zamu canja namu tsarin binciken,dan haka zamuyi mitin yau sai anjima duk zanyi muku test ɗin a ina kuma ƙarfe nawa, Aunty Samira Dan Allah ki kula da kanki saboda A kwai haɗari cikin wannan aikin duk abinda kikaga baki yadda dashi ba kiyi gaggawar sanar dani'zaki iya tafiya kisanar musu da maganar mitin ɗin cikin kula!' shike nan insha Allah zan kiyaye, Allah ya bamu nasara!' Amin Ya furta A saman laɓɓansa..

Alhaji Nasir cikin tashin hankali yace" abinda na gaya muku tun farko shi ne yake san tabbata kunga dai wannan damar ta kufce mana dolene mutashi tsaye yaƙi biyune ya samemu kunga dai gashi nan mun tsaya wasa mu ba ga cimma burinmu ba,kuma baga tsira da rayuwar mu ba tunda gashi an fara bibiyar mu za adinga yi mana ɗauki ɗai ɗai!'ya dire maganar sa yana sakin wani zazzafan huci,Baba Nura ya ɗauki xan cen da cewa Baba Nasiru karka ta da hankalin ka yaƙi ne fa tsakanin mu dasu kuma idan ya tserewa wannan farmakin kana da tabbacin zai iya tsererewa na gaba? Alhaji Salisu ya ɗan ja numfashi kana cikin ta raddadi yace"nifa ina mamakin yadda akayi yaran nan ya mamayemu haka da sauri ashe kwantan ɓauna yayi mana!'Baffa Hashir da tunda aka fara maganar baice komaiba ya ɗan numfasa kana cikin yanayinsa nagirma yace"duk Habibu ne ya cuce mu da ya kawo mana jafar cikin ahlin mu,abunda ya ke ɗauren kai kuma bai wuce abinda ya haɗamu da wannan yaron ba ban san dalilin da yasa yake son tona mana asiri da kuma ƙoƙarin san yaga ya dakatar damu daga cikar burinmu ba,Alhaji Kabir da shima har lokacin bai ce komai ba ya ɗan gyara zaman sa kana yace"Ni ina ganin sashi akayi saboda idan kukayi la akari da cewa bamu kaɗai ne masu nema A duhu ba A kwai waɗanda mu bamu san su ba wata ƙil kuma su sun san mu kuma sun fimu shiri shi yasa suka haɗa da hannu da wannan shu'umin yaron!'amma kana ganin Abdallah zai iya amincewa A haɗa baki dashi dan cutar da BALARABE? cewar Alhaji Nasir kenan, Baba Nura yace kun san tunanin da nayi? duk suka zuba masa ido suna sauraran sa,ganin sun bada hankalin su gareshi yasa yace" bakwa zargin da haɗin bakin Habibu cikin wannan al'amari? Baba Nura yace tabbas ka kawo zance mai ma'ana kasan kuwa irin kallon zargin da Habibu yake yawan yi mun idan zama ya haɗamu?kuma ina zargin Habibu yana bibiyar mu dan duk cikin ƴaƴan Baba Alhaji yafi nuna masa tattali da ƙauna,kuma shi kaɗai ne halinsa yake daban da sauran ƴaƴan Alhaji Baba,dan ina ganin daga Abubakar sai Habibu A yaran sa masu tsananin ƙaunarsa da nuna kulawa A kan sa,dan haka babu haufi idan ance Habibu yana ƙoƙarin ganin ya kare mahaifinsa daga komar maƙiya!'dukkan su sun gamsu da wannan bayani na Baba nura kuma suna ganin A kwai ƙamshin gaskiya,Alhaji Salisu yace yanzu dai mu jira bayani daga wajen ɗanleƙen asirin mu idan yaso duk bayanan da ya bamu sai mubisu mu shirya tsari na gaba!' da wannan shawarar suka samu matsaya A tattaunawarsu,

Tsaye take ta juya bayanta, fuskarta kamar ko da yaushe sanye take cikin liƙabi,magana takeyi amma kana jin maganar kasan ba itace ainahin Muryar mamallakiyar me maganar ba,cikin kaushin lafaxi take jaddada rantsuwarta ga Dije, wallahi wallahi Dije duk ranar da kika sake na kamaki daniyar cin amanata ko ƙoƙarin to na min asiri sai na yi miki mummunar illa A rayuwarki, bazance zan kasheki ba domin kisa A gurina ba hanyace ta ɗaukar fansa ba idan na kasheki kin samu salama to amma dai ina miki fatan kar hakan ta kasance!'cikin mugun tashin hankali Dije tace" ranki ya daɗe kin sameni da makamancin hakane?wani shu'umin murmushi tayi kana tace" Dije kar fa ki manta kifi naganin ka mai jarkowa,kina tunanin zakiyi wani motsine bada sanina ba? to indai kuwa hakan zata faru to lallai burina bashi da wani amfani da mahimmanci kuma bancika shu'uma ba, inaso ki sani Dije duk inda zaki shiga ki fita ina biye dake kuma!'Haɗuwar da kukayi da Bintu duk da tsarina ne amma kema dana ki tsarin A kwai abinda kuke shiryawa ke da ita wanda bakwa so nasani,shiyasa nake yi miki gargaɗi tun yanzu saboda duk abinda ya faru kiyi kuka da kanki, aiki kawai nace kiyi min ba fallasa ba!'daga haka bata ƙara magana ba ta wuce ta bar Dije san ƙame cikin matuƙar razana da tsinkewa da al a marin wannan shu 'umar mata kamar yadda takira kanta,to amma fa hakan baisa taji zata iya karya alƙawarin dake tsakanin su da Bintu ba sai dai dole zasu canja salon tafiyar,tasan Bintu tana da kaifin basira A sannu zasu haɗa ƙarfi da ƙarfe dan binciko wacece wannan mata,

Kwance take tayi ruf da ciki gaba ɗaya tunanin ta ya tafi kan abinda ta gani daren jiya bata taɓa tunanin cewa Yahh Abdallah zai iya bawa wata mace kulawa ba,sai gashi ta gani da idonta yadda ya ta rairayo Bintu A jikinsa,duk da tana tsammanin tausayine kawai da kuma matsayinta Na mai dafa masa abinci,yasa shi kulawa da ita,to kuwa indai har zai iyai wa mai aikinsa haka to matarsa fa? wani irin filling ta dingaji yana ratsata tare da wani irin so mai girma ji take inama ita yayiwa haka ba Bintu ba, tabbas indai har tana san mallakar Yahh Abdallah sai ta tashi tsaye dole tayi wani abu domin samun farin cikin rayuwarta,domin Abdallah da ita kawai ya dace ko ƴar uwarta Hauwa'u bata jin zata ƙyale in dai A kan soyayyar Oga Abdallah ne, Taufiƙa,tayi shirin mallakar Abdallah ta ko wane irin hali..
Chapter 34 · 0% Book details