Sashe 56
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun ranar da Laila ta gaggaya mata maganganun nan masu zafi da nusar da ita abinda ta manta, bata ƙara samun nutsuwa ba gaba ɗaya hankalin ta atashe yake, tabbas ta amince da maganar Laila basu ya kamata ta tsare akan wani ƙaramin dalili ba ko da yake shima wani jigone sanin wannan mugun mashirikin na cikin ahlin ALHAJI BALARABE to amma ita Laila da ɗan uwanta sun ƙi bata haɗin kai su sanar da ita ko waye wannan mutumin dan sanin sa shima yana da matukar muhimmanci dan tana da tabbacin zai iya sanin inda aka ɓoye Abubakar, duk iya takunta a wannan karon ƙwaƙwalwarta bata aiki duk wanda zata yi tsammanin yasan inda Abubakar yake ba sannan inda zata lalubo shi ba bayan wannan dai shi umin da takasa gano waye duk iya binciken ta kuwa, da hakan ta jinjinawa taƙadirancin sa,ta riga ta sani kamar yadda ta iya takun ta haka suma ragowar masu neman suka iya nasu takun,babu wanda ta iya ganowa sai ƴan tsirarin mutanen nan su Alhaji Nasir da kuma Hajiya ladidi,to amma kuma yanzu duk bata tasu take ba dan ta riga ta gama bincikenta akansu tasan suma har yanzu lalube suke,shine dalilin da yasa ta kuma riƙe wuta gurin su Laila dan tayi yaƙinin sun san mutumin nan sai dai ta rasa dalilin su na ƙin gaya mata ko wanene,iska ta fesar daga cikin bakin ta dole Sayyid ya kamata ta kira tunda shi yayi mata binciken Bintun da waɗanda suka kawota gidan ta dalilin hakane yasa ta gano Hajiya ladidi da ƴarta Nafisa,wani shu umin murmushi tayi yayin da ta tuna shikansa Sayyid ɗin bai san fuskarta da Muryar ta ba balle ya gane WACCE ITA,dole shi zata saka yasawa ubansa ido cikin hikima zata sashi yayi mata aiki akan ubansa,har yanzu da akwai ragowar ƙwarin gwiwa atare da ita kuma baza ta taɓa sarewa ba har sai taga abinda ya turewa buzu naɗi,
Ta ɓangaren su Alhaji Nasir tare da tawagar sa su Baffa Hashir sun miƙa cikin binciken kishiyoyin su, kamar yadda Samira ta tunatar dasu sai dai kuma basu manta da ci gaba da neman inda mukullin samun sirrin su yake ba wato Alhaji Abubakar,haka kuma sun kasa ɗauke ido daga kan Abdallah saboda suna matuƙar tsoron sa,kowa nema yake yi ido rufe, yayin da ta gefe Samira ta cika da ɗaukin san Alhaji Sama'ila ya sanar da ita wannan sirri,kamar dai yadda suka saba yauma sun haɗu a mahaɗar da suke haɗuwa,Samira cikin yanayin jimami tace"har yanzu babu wani da kuka samu wanda kuke tunanin yana da hannu cikin yaƙin nema,ɗan shuru yayi kana ya ɗan numfasa tare da cewa a kwai wanda muke zargin ana sashi bibiyar mu da kuma saka mana ido a dukkan al'amarin mu!'wani irin bugu zuciyar Samira tayi tare da zaro ido waje,Alhaji Sama'ila ya cigaba da cewa abinda yasa nace miki saka nace miki sakashi akayi shine saboda bai san komai akan wannan sirrin ba sai dai idan faɗa masa akayi,cikin zaƙuwa da kuma fargaba Samira tace"to waye wannan?kai tsaye yace" da ita Sayyid ɗan gidan Mansur!'wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta saki dan da atunanin ta ko ya gano wanda Oga Abdallah yasa shi aiki akan su ne,cikin mamaki tace'Sayyid kuma? tare da ƙara duban wayarta adabarance dan ta tabbatar bata kauce daga kan recording ɗin da take yi ba,yace"Sayyid shine wanda nake zargi abinda bansani ba kawai shine Mansur ɗin ne yake saka shi kokuwa wasune daban?jin jina kai Samira tayi tare da cewa shi kaɗai kake zargi yanzu?yace shikaɗaine kafin binciken mu ya kuma samo mana wani!'da kyau Alhajina yanzu zakaga komai naku yana tafiya kan tsari daga nan ma sai kuga kun samo wannan abu mai mahimmanci da kuke nema!'yace"tabbas hakane amma kuma wani abu da ban sanar dake ba Samira shi wannan abu da muke rububin nema mutum ɗaya ne yasan inda yake kuma an sace shi kusan shekaru talatin kuma tunda aka ɗauke sa ba akuma jin ɗuriyar sa ba hatta da ESTATE babu Wanda ya kuma tunawa shi,to a yanzu dole sai mun same shi kafin mu sami abun da muke hari dan shi kaɗai ne zai nuna inda aka killace abun!'jinjina kai kawai Samira takeyi saboda Al'amarin yayi matuƙar taɓata,tace"baku san inda yake ba kenan?da mun sani Samira ai da tuni an wuce gun kuma da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba!'hakane to yanzu wane mataki kuka ɗauka dan cigaba da neman sa?Samira kenan ai baza mu zauna ba saboda duk abinda kikaga munyi dan shi mukeyi da zarar mun sami inda Abubakar yake,shike nan kakarmu ta yanke saƙa!'to Alhaji meye tabbacin ka na za a sameshi a raye?wani makirin murmushi ya saki kana yace"ai Samira Ina tabbatar miki da cewa da ankashe Abubakar da yanzu an fara kashe ƴan uwansa da mahaifin sa,Bama shi kaɗai ba duk wanda yake da ƙudurin samun wannan abu to wannan shine shirin sa na gaba koma waye ko su waye,dan magadan wannan abu su za akashe ko muma burinmu kenan,shi yasa nace miki ba akashe Abubakar ba,kuma Abubakar yana da matukar taurin kai ba zai faɗi inda abun nan yake da wuriba ba!'Samira da al ajabi yaƙi barin fuskarta da zuciyarta tace"ya akayi ku kasan da wannan abun kuma meye shi wannan abu haka da ake irin wannan ta asa akan sa? murmushi yayi tare da cewa Samira bazaki gane ba wannan amsar ba yanzu zaki san ta ba,amma,abinda zan gaya miki shine shi kan sa me abun bai san sirrin ya fita ba bayan Abubakar bai sanar da kowa ba, yadda akayi muka sani shima zaki sani nan gaba!'batayi masa musu ba saboda gudun karya ganota, wannan ma da ta samu ba ƙaramin babban nasara suka samu ba yanzu za ta kaiwa Oga Abdallah sai suji mataki na gaba da Yakamata su ɗauka,daga nan ta daure suka ɗan sha copy tare amma ji take kamar tayi tsuntuwa ta ganta office ɗin Oga Abdallah.
Babbar macece wadda zata iya kaiwa sa ar inno zaune take bakin madafa daga dukkanin alamu dai girki takeyi,amma kana kallon fuskarta zaka iya hango ɓoyyayyiyar damuwar da ta kasa bushewa daga zuciyarta,wata makiman ciyar matace ta fito daga wani ɗaki a ƙiyasina baza ta wuce talatin da biyar zuwa da zuwa da bakwai ba,da sauri ta ƙarasa gaban matar dake gaban madafi tare da cewa haba Hajjo me yasa baki bari na fito ba kin san ba lafiyar idone dake ba amma kike zuwa gaban hayaƙi!'kama hannunta tayi tare da miƙar da ita tsaye sai da ta kaita har kan tabarmar dake shimfiɗe a makeken tsakar gidan,zama tayi akusa da ita,kana cikin tausayin surukar ta ta tace"dan Allah Hajjo ki daina yawan damuwar nan bana so ciwon ki ya tashi kin ga dai yadda Alhaji Umar yake damuwa idan yaga halin da kike ciki,bayan shima ba cikakkiyar lafiya ce dashi ba, gamu nida ƴan biyu duk ba mason rasaki saboda ke kaɗai ce muke gani muji sanyi idan kika bari lalura taci ƙarfin ki tabbas zamu shiga damuwa!'wani wahalallan numfashi ta sauke kana cikin muryar da take cike da damuwa tace"Asma'u ina matukar ƙoƙarin da dauriya wajen danne abinda ke taso mun,babu yadda zanyi ne Asma'u ƴara biyu har da jika babu su babu labarin su,kema nasan dauriyar kikeyi amma ki sani Ni dake a kwai banbanci ke da ragowar ƙuruciya atare dake Ni kuma girma ya fara cim mani dole yanayi na danaki su banbanta,hannu tasa ta share hawayen da suke ta ambaliya kan fuskarta tare da cewa,kullum addu'a ta da fatana shine inga Laila da Sulaiman,fafi take nufi (afwan ban faɗi sunan fafi na asaliba sunan sa Sulaiman)ina son ganin su kafin na bar duniya!
Asma'u tace"Hajjo insha Allah burinki zai cika zasu dawo gida, kamar yadda suka tafi tare haka zasu dawo tare harma da jikallenki, ta ƙara sa maganar cikin san kautar mata da damuwarta.
Tunda ya fara sauraran recording ɗin da Samira tayi na tattaunawar su da Alhaji Sama'ila,ya rufe idanunsa yana mai ƙara tasbihi ga Ubangiji tare da gode masa da yashirya rayuwarsa ya ƙawata zuciyarsa da tsoron sa da kuma ƙauna ta masoyin da babu kamarsa Annabi Muhammad swa,jin maganar ta tsaya yasa a hankali ya buɗe idanunsa da suka sauya kala saboda ɓacin rai me tsanani da ya mamaye zuciyarsa,duban Safwan yayi tare da cewa ina so a yau din nan a kamomin Sayyid ku kaishi can gidan sirri ku ɓoyeshi,ina so ku kula da aikin ku bana buƙatar Kowa yaga lokacin da kuka ɗauke shi!' Safwan yayi salut ɗin sa tare da cewa angama Oga insha Allah baza asamu kuskure ba!'jin jina kan sa yayi tare da mai da dubansa kan Samira yace"Samira na gode da taimakon ki!'da sauri ta katse shi da cewa haba meye na godiya kar ka manta da wannan aiki na ne kuma saida na ɗauki alƙawari kafin na fara, dan haka ya zaman min dole na jajirce dan taimakon al umma!'na sani duk da haka kin cancanci lambar yabo aikinki yana kyau sosai!'godiya tayi masa kana sukayi sallama ya sallame su,shima daga nan ya kira Yahya su tafi dan yana son leƙawa asibiti.