← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 120

Sashe 51

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ɗin dai kamar yadda tasaba haka taje ta jera masa dinnar ɗin sa kana ta wuce tayi wanka tayi sallar isha tare da shafa'i da wuturi,wata kyakykyawar riga ta zura iya cinya mai shegen kyau wadda ta karɓi jikinta tamkar kasace ta ka gudu, dogon gashinta irin na fulani da sirkin Larabawa ta haɗa ta tufkeshi ya sauka kan bayanta fuskarta ce ta fito tayi fayau da ita yayin da jikinta yake wani irin santsi da ƙamshi mai tafiya da imanin mutum,wanda sam tunda ta dawo inno da Hajiya Babba basu ƙyaleta da kaye kaye ba, wannan ta bata wannan wannan ta bata wannan wai maganin baki ne da tsari, duk da wani maganin ma da ƙyar take iya sha,har ta kwanta sai ga kiran inno wai ta manta bata kaiwa Abdallah copy ba,ɗan tura baki tayi kana tace"Allah yasa dai bai dawo ba kalan naje ya kuma kamani ya wani riƙe ya sani kwana aɗakinsa dan iskanci kawai!'cikin wannan gungunin ta gama haɗa copy ɗin ta nufi falon,bayan ta ɗora doguwar buɗaɗɗiyar Abaya akan kayan baccin ta,tana shiga sai da ya tabbatar ta kai tsakiyar falon kana yasawa ƙofar lock batare da tasan lokacin da ya motsa daga inda yake ba,ƙin bari tayi su haɗa ido har ta ajiye masa cikin miskilar muryar sa yace"bani nan a hannuna!' miƙa masa tayi tana kawar da kanta gefe wanda hakan ne yasa taci tuntuɓe da ƙafarsa kawai sai jinta tayi cikin jikin shi batare da sanin sa ko sanin ta ba,da sauri ta ɗago dan tashi amma sai caraf fuskarta kan tasa hancinta na gogar nasa laɓɓanta na kan tattausan lip ɗinsa.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 33 ```

Da sauri ta miƙe tana yi masa hararar gefan ido,bai nuna ya ganta ba sai ma cewa da yayi ki zauna inason magana dake!'zaro manyan idanunta tayi cike da tashin hankali itafa bata son zama kusa dashi saboda zazzaɓin da yake sata, dan ji take wani sanyi na ratsa ƙasusuwanta har cikin ɓargonta,ɗan zama tayi daga can nesa dashi,batare da ya kalleta ba ya kuma cewa,ina wasa dake ne?girgiza kanta tayi kana ta miƙe ta koma gefan sa a mai makon ta zauna kan kujerar sai ta zauna ƙasa kusa da ƙafafunsa tare da sun kunyar da kanta sai jajjan yatsun hannunta take zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai ce mata ga kuma zazzaɓin kusancin ta dashi,zuba mata ido yayi na ɗan wasu da ƙiƙai wanda bazaka taɓa fahimtar kallon nata yake ba sai dai ita kuma a jikin ta taji alamun idanun sa akanta dan haka ta fara ɗan motsa bakinta a hankali kuma cikin shagawaɓaɓɓiyar muryarta tace"Ni kam dai bacci nakeji!'yaji ta sarai amma sai ya basar tare da ci gaba da tafa wayar sa,sai da yagama ƙulal da Bintu, kana cikin wata irin murya mai cike da nutsuwa da san nuna mata mahimmancin maganar da zaiyi yace"

Duk abinda na tambayeki ina so ki nutsu ki bani amsa ta gaskiya idan kuma kika sake kika yimin ƙarya tabbas baza kiji daɗin hukuncin da zanyi miki ba!'ai tuni Bintu ta ruɗe iya ruɗewa dan bata shiryawa tutseyan Abdallah yanzu ba kuma bata gama shawara akan duk wani batu da zai tambayeta ba, cikin marairaice murya tace"dan Allah kayi haƙuri sai Allah ya kaimu gobe wallahi bacci nakeji sosai!'cike da alamun tashin hankali ta ƙara sa maganar,ba tare da ya dubeta ba yace"ki gaya min suwaye suka kawo ki cikin estate ɗin nan da kuma dalilin kawoki? duk da ya riga yasan wannan tun lokacin da yasa akabi masa ita tare da ɗauko masa tattaunawar su ita da Dije,amma yana buƙatar ƙarin bayani daga bakinta yana so ya tabbatar kuma yaji ko zata canja magana,ita kuwa Bintu tuni ta shiga wani hali na jin tsoran sanar da Abdallah wannan lamari duk da tanason sanar dashi amma idan ta tuna kashedin da suka yi mata duk sai taji tsoro ya kamata, fuskantar hakan da yayi ne yasa a matsayin sa na cikakken me binciken sirri kuma kwararre a wannan harkar yasa ya ɗan sassauta fuskar sa tare da muryarsa cikin tattausan harshe yace"Fatimah!'da sauri ta ɗago fuskar ta wadda take cike da fargaba ta dubeshi,saboda yanayin da kiran sunanta da yayi ya haifar mata ji tayi kamar shi ka ɗai iya kiran sunanta saboda salon da yayi amfani dashi gurin ambatar sunan,ganin tana kallon sa yasa ya kawar da fuskar sa saboda maganaɗisun da ke cikin idanunta wanda shine dalilin da yasa bai cika son kallon cikin ƙwayar idanun nataba,

Cikin basar da abinda yakeji yace"ki kwantar da hankalin ki ki nutsu ki amsa tambayoyi na ki cire tsoron da ke ranki babu abinda zai faru,ko bakyason taimakon bayin Allah n da suke cikin matsala?da sauri ta kaɗa kanta kana tace"inaso mana!'yauwa to kinga dole idan haka zata faru saikin cire wannan tsoron dake addabar zuciyarki!'cikin gamsuwa da kuma samun ƙwarin gwiwa tace"Anty Nafisa ce da mahaifiyarta Hajiya ladidi sune suka kawoni, shuru ta ɗan yi kana ta faɗa mishi komai kamar yadda ta faɗa wa Dije har daga inda tazo babu abinda ta ɓoye masa labarin dai sak iri ɗaya da na Dije,yace"ki gaya min dukkan abinda ya faru daga lokacin da kika zo zuwa yanzu ina nufin har labarin gubar da aka saka min!kuka ta saka masa cikin kukan tace"wallahi ban san yadda akayi ba ban san komai ba!yace"Ni ba cewa nayi kin san komai ba kawai abinda nakeso dake ki gayamin duk wani shirin su da kuma abinda suke shiryawa da kuma bayanin da kika sani akan saka min guba da akayi!'

Cikin nutsuwa ta bashi labarin ko mai hatta da haɗuwar su da sukayi da Dije da shirin da sukayi akan yaƙar magauta sai da takuma maimaita masa sai maganar guba wanda ta gaya masa gaskiyar abinda ta sani,abu ɗaya ne ta ɓoye masa aikin da Anty Nafisa takeso tayi mata, yace"ina wayarki take yanzu? shuru ta ɗan yi kana tace"Ni tun ranar ban sa ke ganin ta ba!'yace"a kwai ragowar abinda kika ɓoyen kuma idan baki gayamin ba na gaya miki zan yi matukar saɓa miki!'cikin lumshe idanu da tsananin baccin da ke cikinsu tare da fargabar da ta cikata,tace"Ni ka rabu dani bacci nakeji, Bintu tariga tayi alwashin baza ta gaya masa sirrin Anty Nafisa ba, saboda baza ta so Anty Nafisa ta kashe Oga Abdallah ba, lamarin cikin ahlin yana matuƙar bata tsoro tunda ta ga basu ɗauki cutar da mutum a komai ba,cikin wannan tunanin baccin da yake ta lallaɓowa idanunta ya samu nasarar surar ta, Abdallah cikin ƙosawa da yawan maganar yace"ke fa nake saurare!'shuru yaji daga ƙarshe ma sai ji yayi ta Kwaanto jikin ƙafafunsa,wanda shine da lilin da yasa ya ankara da abinda ke faruwa, ɗan tsaki ya saki kana ya shiga tashin ta dan ta koma ɗakinta.

A hankali take buɗe idanunta wanda suka cik a fal da bacci,alama yayi mata da ta tashi,a hankali ta miƙe batare da ta ce komaiba ta nufi ƙofar falon a hankali ta murɗa ta fita yana tsaye yana kallon ta har ta maida ƙofar ta rufe,numfashi ya ɗan sauke kana ya kuma zama tare da ci gaba da aikin da yake cikin computer sa.

Washe gari ta tashi cikin farin ciki saboda nauyin zuciyarta da ya ragu,sosai taji nishaɗi da nutsuwa, lokacin da ta kai masa break ɗin sa ya tafi motsa jiki dan haka cikin sauri ta haɗa masa komai tare da kimtsa masa sashen nasa,cikin sauri ta fito daga ɗakin ai yanzu kuma wasan ɓuya zata dingayi dashi dan ko mai zaiyi baza ta gaya masa ba,

Tana shiga ɗakin ta tarar da Anty Nafisa zaune a bakin gadon ta, tana ta faman jijjiga ƙafa kana ganinta kasan tana tafe da rashin mutunci dan sai wani hura hanci takeyi kamar zata fashe,cikin sanyin jiki Bintu ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kanta ƙasa,Anty Nafisa ta ƙare mata kallo sama da ƙasa kana tace"kin kyauta min Bintu na gode da abinda kika yimin!' cikin zaro manyan idanunta tace"me nayi kuma?au tambaya ta ma kike yi? gaskiya Bintu wuyanki yayi kauri naga alamar kin zama ƴar gari,yanzu har kin manta da yadda mukayi da ke? tunda kin samu waɗan da sukafi mu sakin kuɗi,shikenan sai mu ki saki namu aikin wallahi Bintu kin bani mamaki saboda yadda kika iya juyamin baya amma kikaje kika yiwa wasu,to ko meye hujjar ki tayin hakan?cikin damuwa Bintu tace"wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa ta har so uku bani bace na aikata ba, kuma ban san waye ba kuma ban zargi kowa da aikatamin haka ba na barwa Allahu jalla wa'azza dan shine kaɗai yasan sirrin dake ɓoye amma ki yadda dani bani bace ban san komai ba!'zuba mata ido Anty Nafisa tayi na wasu ƴan daƙiƙa kana taja Ajiyar numfashi tare da cewa shike nan na yadda mu ajiye wannan batun mu dawo kan asalin labarin domin yanzu shi yafi ko mai muhimmanci a gurina,shin zaki yi min abinda nasaki ko bazakiyi ba? idan har yanzu kina kan bakanki to nima ina kan nawa bakan bazan taɓa ɗaga miki ƙafa ba Bintu, saboda kin riga kin san sirrina kuma nasan tun da kika sani sai wani ya sani,dan haka ina sauraren ki wanne kika zaɓa?

Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Bintu ta ko ina bata da wata mafita a yanzu wanda ya wuce ta karɓi aikin nan inyaso daga baya sai ta nemi mafita,katse ta tayi da cewa kina ɓatan lokaci ki bani amsa!'a hankali Bintu ta ɗago kanta dake sunkuye tun ɗazu tace" na amince zanyi abinda kika sakani!'daga haka ta ƙunshe kanta cikin cinyoyin ta tana fitar da wasu zafafan ƙwalla masu tsananin raɗaɗi a zuciyarta, Anty Nafisa tayi wani shu'umin murmushi tare da cewa burina yana gab da cika, Bintu a hankali tace"nima nawa yana gab da cika insha Allah!'murmushi Anty Nafisa ta kumayi batare da tasan inda furucin Bintu ya dosaba,fita tayi da sauri ranta fari ƙal ji takeyi kamar burin nata ya gama cika,
Chapter 51 · 0% Book details