← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 120

Sashe 69

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani mudubi ne a gaban sa yake kallon duk abinda suke yi, amma Abdallah yana fara yiwa Bintu Addu'oi sai hotan su ya ɓace masa kamar walƙiya,dariya yayi tare da cewa,duk abin da zakayi nasara na gareni tunda har nayi nasara a kan matar ka to kai ma bazaka gagari dodo jack ba!'juyawa yayi ya dubi Alhaji Abubakar dake cikin wani irin yanayi na sihiri,yace"na gaya maka Abubakar sai nayi nasara akan ku,sai naga ƙarshen ku kaida duka zuri ar ka,wani shu'umin murmushi yayi tare da shafa ƙeyar shi da ita kawai nake gani yace"Bintu banyi niyar biyo miki ta haka ba ke kika jawo,saboda kina son ganin ƙarshe na kina son ganin bayana,koshi Abdallah baya ƙoƙarin kai kansa wannan ɗakin amma ke kullum burinki ki tona sirrin dake ɗakin,bayan kuma shine rayuwata shine garkuwa ta,bankaɗa ɗakin nan tamkar bankaɗa sirrina ne,tabbas duk ranar da nabarki ki ka samu nasara akan ɗakin nan to kamar kin samu nasara a kaina ne,wanda Ni kuma bazan taɓa baki wan nan dama ba,dan haka zan saka rayuwarki cikin wasi-wasi da halin razana, wannan tsoron da nasa miki shi ne zai rage miki ƙwarin gwiwa da tunanin tun karar ɗakin,ya kuma ƙyalƙyalewa da wata mahaukaciyar dariya yana cewa yarinya baki san wuta ba sai kin taka Ni ƙi gudune maganin sa gudu,murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya,ƴan jakar uba kwayi kwa gama rana ta tana nan zuwa,ranar da zan ganni gani ga burina a hannu na,Hhhhhh.

" A ɓangaren Anty Nafisa kuwa tana cikin halin ƙaƙa niƙayi,ta kasa zaune balle tsaye,burinta gari ya waye taji abinda Bintu zata kawo mata,sai dai fargaban ta ɗaya,bata so Bintu ta kuma yi mata batun san jin mafarin al'amarin tana tsoron jin hakan daga gareta,lallai wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan hanya,wani ɓangare na zuciyar ta yace"to meye ne idan kin gaya mata abinda kika sani, bake kika ce kin yadda da ita ba,ai kamar babu wani abu dan kin sanar da ita ɓoyayyen sirrin ki wanda babu wanda yasa Ni daga ke sai ALLAH da ya halicce ta,zama ta ɗan yi tare da tallafe fuskar ta,wata kuma zuciyar nayi mata gargaɗi da aikata wannan gangancin,to ita dai tafi yadda da ɓangaren dayake mata gargaɗin sanar da Bintu ɓoyayyen ƙullin da ta ƙulla tsawan shekaru batare da ta kwance shi ko warware shi ba,to amma dai yan zu bari ta jira Bintu dan jin abinda ta yanke akan shawarar da ta nema ɗin.

Tunda ya gama karanta littafin babu abinda yake yi sai tasbihi da ƙara kaɗaita Allah assamadu,tabbas ya shiga cikin ruɗani da wani irin tausayi me tsanani na gaba ɗayan su ahlin,tun daga kan Baffan sa Umar da mahaifiyar Bintu Laila da fafi da iyalan sa,sai uwa uba Bintu wadda yakejin tausayin nata har kamar zai saka shi kuka,kallon fuskar Bintun yake da take ta shaƙar baccin ta,ganin yadda take ta ɗan yatsine fuskane ya tabbatar masa da ba wai daɗin baccin take ji ba, addu'oi ya kuma tofa mata kana ya tafi duniyar tunanin yadda zaiyi ya nemo kakar Bintu wato Hajjon su Laila ita da iyalan fafi,wanda kuma yasan hakan ba zai taɓa yiwuwa ba har sai da tallafin Baffan nasa saboda ya riga ya tabbatar da cewa a yanzu haka Baffan sa Umar yasan inda suke, saboda bashi da wata hanya da zai iya sanin abinda ya faru da su Lailan sai ta hanyar su Hajjon,to ta yaya zai yi hakan batare da shi Baffan nasa yasan komai ba?wata zuciyar tace"dashi haba Abdallah sai kace" ba aikin ka ba, wannan ai ƙaramin aikine a wajen ka koda baka bi ta hanyar Baffa Umar ba zaka iya lalubo inda su Hajjo suke,da izinin mai duka da wannan tunanin ya samu ƙwarin gwiwa,to su kuma su fafin suna ina? A hannun wa suke?tunda dai ga dukkanin alamu suna raye,to ko suna wajen wannan tsinan nan da yake batun wai ba dan ba da ya faɗa musu inda su Lailan suke,lumshe idanun sa yayi yana mai jin kansa na sara masa saboda tsabar yawan tunani,cikin nutsuwa ya zame Bintu daga jikin sa ya tashi ya shiga toilet ya ɗauro al wala,har zai tashi Bintu sai kuma kawai yaji gara ya barta taɗanyi bacci,shimfiɗa sallaya yayi tare da fuskantar alƙibla dan kaiwa Allah ƙadiran ala manyasha'u kukan sa domin ya jiɓanci dukkan lamuransa na zahiri da na baɗini, Allah kabamu dacewa duniya da lahira.

Tunda ya tasheta tayi sallar asuba tana cikin yin azkar bacci ya kuma surarta,a haka ya dawo daga masallaci ya same ta,É—an tsayawa yayi akanta yana kallon ta cike da tunanin abinda yakamata yayi,ya fara tunanin ko dai asibi zasuje aduba lafiyar ta É—an tabbas yana tunanin akwai matsala cikin wannan sabon Al'amarin na Bintu,da wannan tunanin ya nufi toilet da tsaf tace jikin sa,

Tayi kiran wayar sau ba adadi amma duk abu ɗaya dai wannan matar ke sanar da ita,lambar bata yin aiki,cikin ɓacin rai Hajiya ladidi ta jefar da wayar can gefe tana cigaba da zabga tsakin da tayi shi yafi sau goma,yau kimanin kwana goma ke nan tana kiran mutumin nata wan da yayi mata bad da bami amatsayin wancan shu'umin mutumin,ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun shi a waya,sai yanzu ne take ganin waw tar ta na kasa sanin komai akan sa,sai waya da nomber da ayanzu bata da wani amfani a gurin ta,to wai ita tun farko ma mai ya shiga kanta ne da ta kasa yin abinda yake daidai har ta bari wani ƙato can yana sarrafa tunanin ta?gashi ko Nafisa bata san komai akan tarayyarta da ɗaya daga cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba,anya kuwa batayi shirme ba? ita da take neman dukiya sai gashi bata samu ko doki ba, tana nan daga zaune duk abin nan da tayi yana son tashi a banza,anya kuwa zata yadda ta tashi atutar babu?babu wan babu ƙanin,taɓ ai kuwa hakan ba zai taɓa yiwuwa ba dolene Nafisa ta cigaba dayi musu yaƙin neman dukiyar cikin ESTATE ɗin nan,tunda dai tana ji tana gani wan nan damar ta kufce mata, yanzu kuwa dole saban lale za a sake tunda suna da Bintu a hannun su,da wannan shawara ta ɗauko wayarta dan kiran ƴar tata dan su tattauna.

A hankali ta zare ta gumin da Ammin nata ta rafka,tare da zama a kusa da ita tana kuma ƙoƙarin san taga sun haɗa ido,sai dai ina hakan bai samu daga gurin Hajiya zulaihat ba,ɗan shuru Rahima tayi tana kallon yadda Ammin ta haɗe mata girar sama da ta ƙasa,ta san ba dan komai takeyin hakan ba sai dan tayi garkuwa daga manyan tambayoyin da tasan zata yi mata,ƙara matsawa tayi kusa da ita kamar zata koma Cikin ta,abin da ya fusata Ammin ke nan,cikin hasala tace"waike kam Rahima meke damunki haka? gotai-gotai dake kin zo kina neman komawa ciki!'ta ƙara sa maganar amatuƙar fusace,dan so take ta kaucewa tambayar da Rahiman take son yi mata a duk lokacin da ta risketa cikin wannan yanayin,cikin marairaice fuska Rahima tace"kai Ammi ke ko irin kewan nan nawa bakyayi,tunda kika korani gurin Hajiya Babba baki taɓa cewa Rahima na ina kewarki yau kizo min mana ko kwana biyu kiyi min sai ki koma ,Ni kuma na gaji da kewarki da rashin ki nazo amma nazo kina korata da hantara!'ta faɗa tana mai goge hawayen da suka zubo mata akan fuska, Allah sarki uwa,sai kuma duk Ammi taji rashin daɗin abinda tayiwa autar ta ta,cikin sanyin murya tace"haba auta ya za ai nace bana kewarki,kema kin san faɗa ma ɓata bakine kawai dai inayin nesa dake ne dan bana son damuwata ta shafeki har ta sakaki cikin wani hali!'ta karasa maganar tare da jin tasowar wani ɗaci mai haɗe da zafi dake ƙunshe cikin zuciyar ta,kama hannun ta Rahima tayi tare da cewa,Ammi idan damuwarki bata saka min damuwa ba to rashin ki zai sa tabbas nima A rasani,domin tabbas kikaci gaba da ɓoye abinda yake ranki tare da baiyana damuwar ki to wataran sai dai nazo na tarar da babuke,yawan damuwarki ya kai mizanin da komai zai iya faruwa dake, Ammi Ni ban ce sai kin faɗa min damuwar ki ba,dan tunda na san bakya son faɗa min na haƙura, amma dai ina so ki rage yawan damuwar ko da ba duka bane nasan lafiyarki zata iya inganta!'murmushi Ammi tayi mai matukar ciwo kana cikin tausayin kanta da ɗiyar tata,tace"wallahi Rahima na rage damuwa tuni na fauwalawa Allah dukkan lamurana,dan da ace ban daina ba da bazan kai yanzu ba,to amma na riga nayi tawassali da tsarkakan sunayen Ubangiji na kuma san cewa ƙaddara jarabawar rayuwace,ta wani tafi ta wani ta wani bata kai ta wani ba, haka kuma ta wani kyakykyawa ta wani kishiyar hakan,dan haka ki daina damuwa,nima na daina damuwa tunda nasan Allah baya bacci yana ji yana kuma gani,kuma na roƙe shi cikin bacci na roƙe shi cikin ido biyu na roƙe shi da rana da dare da safe,haka kuma na roƙe shi cikin sakanni da mintuna da awowi,dan haka ina nan ina jiran Ranar da ƙudurar sa zata haɗu da irada,ranar da zaice ta kasan ce ita kuma ta kasan ce,domin nayi yaƙini tuni addu'a ta ta riga ta amsu sai jiran lokacin da zata baiyana!'Alhamdulillahi alakullin halin,da yayini a musulma na tashi cikin musulun ci kuma ya tsarkake zuciyata daga bin wanin sa ya bani kyakykyawar zuciyar da na kaɗaita shi shi ɗaya na kuma dogara da shi,cikin ma bayyanin farin ciki da samun nutsuwar zuciya Rahima tace"Allah ne abin godiya A ko da yau she!'daga nan Ammi ta zarce da yiwa Rahima nasiha tare da tunatarwa wanda suke shiga jinin jikin ta da ƙwaƙwalwar ta suna zagawa tare da samun wajen zama.
Chapter 69 · 0% Book details