← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 120

Sashe 35

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

To shin hakan zata kasance kuwa?
Wace hanya zatabi dan mallakar gwarzan shekara kuma dodonsu É—an zaki wato Abdallah?
Me kuma Anty Nafisa take shirin ƙullawa?
Shin Abdallah zai yadda kuwa ya haɗa hannu da Bintu ? Wai ma shin meyasa yake tsoron jefata cikin yaƙin?
Wai waye mutumin da fafi yace Bintu zata haÉ—u dashi zai tai maka mata?
Muje page na gaba yanzu aka fara wasan.......

COMMENT....

More typing...

Alƙalamin.

Fatima y Adam✍🏽
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

```Page 25 ```

Bintu sai da ta gama duk abinda zatayi kana ta nufi wajen inno dake zaune tare dasu Siddiqa A falo,durƙusawa tayi gabanta cikin yanayin tsoro tace" inno zan leƙa wajen Anty Nafisa tana kirana!'inno ɗauke kanta tayi cikin halin ko in kula tace" sai kin dawo!'ƙasa ƙasa su Siddiqa suka saka mata dariyar shaƙiyanci, su atunanin su yan zu inno ko fuskar Bintu bata ƙaunar gani,daga Bintu har innon babu wanda ya kulasu tashi tayi ta fita tana musu tata dariyar yadda suka maida su mahaukata ita da innon ta,ɗan kallon ɓangaren ɗakin tayi tanaji A ranta kamar ta nufi wajen yanzu amma sai wata zuciyar tace ki bari tukun har yanzu da sauran lokaci,gaba tayi tana mai ɗaukar shawarar zuciyarta,

Can saman ɗakinta ta sameta sai kaiwa da kawowa take ga dukkanin alamu dai Bintun take ta dakon jira,tana ganin shigo war ta kuwa tayi saurin ƙara sawa ta jawo ta cikin ɗakin sosai kana ta murɗa key ɗin jikin ƙofar,shigowa tayi sosai ta gyagygyara labulayen ɗakin suma, ita dai Bintu tana tsaye tana binta da kallo har sai da ta gama tazo ta ja hannun Bintun ta zaunar da ita gefan gadon itama ta zauna, cikin yin ƙasa da murya tace"Bintu ki saurare Ni da kyau wannan karon taimakon ki nake nema,ina kuma fatan zaki taimaka min,jinjina kai Bintu tayi cike da zaƙuwar san jin taimakon da zatayi mata, Anty Nafisa tace"Bintu ciki nakeso nayi!'wata irin zabura Bintu tayi tare da zaro manyan idanunta,bakinta har rawa yake tace" ban ban gane me kike nufi ba? Anty Nafisa ta miƙe tsaye tare da goya hannayen ta A hankali take zaga ɗakin, kana cikin nutsuwa tace"Bintu ki nutsu ki saurareni banason wannan tsoron naki domin zai iya ɓata min shirina,na yadda dake ne shi yasa har zan gaya miki wannan sirrin saboda ko babu ke zan iya aikata ƙudurina,to kawai dai nayi tunanin abin yana buƙatar hannu biyu, ko Hajiya ta bata san da wannan ƙudurin nawa ba,juyowa tayi tana kuma fuskantar Bintun tace"Bintu na gaji da zaman jiran gawan shanu ban san ranar da zan samu ɗan kaina ba shiyasa naga ya dace na fara shiryawa rayuwata abinda zai amfane ta,Bintu baki sake take bin duk inda Anty Nafisa tayi da idanu so take taji ƙarshen labarin domin ita A ɓangaren ta labarine ko kuma tatsuniya,Anty Nafisa ta cigaba da cewa Bintu zan ƙirƙiri cikin ƙarya!'bintu cikin mamaki tace" idan kika ƙirƙiri ciki shima ɗan ƙirƙirar sa za kiyi ko yaya? murmushi tayi nasamun Bintu da tayi mai dabara da fikira,kana tace" Bintu ai cikin ba zai zo da rai ba balle a ƙirƙiri ɗan! cikin tarin mamakin dake shinfiɗe saman fuskar ta ta kuma cewa to meye amfanin ƙirƙirar cikin idan baza a haifi ƙirƙirar ran ɗa ba? good kinyi tambaya mai kyau Bintu,haɗe fuskarta tayi sosai kana tace" Bintu kafin a haifi ɗan za akashe uban ɗan!'wata irin miƙewa Bintu tayi cike da tsananin razana duk da bata gama fahimtar maganar ba,Anty Nafisa kiyi min bayani dan Allah ban gane komai ba ban fahimci komai ba ban san inda maganar ta dosa ba,dafa kafaɗarta Anty Nafisa tayi tana cewa ke dalla ki nutsu sai kace wadda nace ke za'a kashe,ina so ki fahimceni sosai Bintu wannan hanyar ce kawai zata samar min da abinda nakeso,manufa ta ta kashe uban ɗa kafin na haifi ɗan ba rai kuwa shine dole ɗan cikina ya gaji dukiyar ubansa, idan aka haifeshi bai zo da raiba dukiyar ɗana ta zama tawa,kinga kema daga nan zaki samu duk irin kuɗaɗen da kikeso,

Tabbas alokacin nan da za'a tsaka jikin Bintu to kuwa baza asami jini na gudana ba ko mai nata ya tsaya cak hatta da numfashin ta da sauri da sauri yake fita tamkar ana fizgoshi, Anty Nafisa ta cigaba da cewa taimakon kuma danakeso kiyi min anan shine kece wadda zan bawa kwangilar kashe uban ɗan Bintu ke zaki kashe mijina!'waiyo masu karatu zan so kikaga yadda mutuniyar taku tayi a wannan lokacin,da ana mutuwa adawo to da sai nace Bintu mutuwa tayi ta dawo,idanunta ne suka tafi luuu kafin kace meye ta zube a gurin sumammiya,batare da wata fargaba ba Anty Nafisa ta shiga banɗaki ta ɗebo ruwa tazo ta sheƙa mata a fuska,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai buɗe idanunta tare da fatan ace duk abinda yake faruwa da ita mafarki ne zata buɗe idon ta ta ganta gata ga fafi ɗin ta da ummin ta tare da Baffa Jauro suna ce mata Bintu tashi daga wannan dogon baccin ya isa haka,amma kuma sai hakan bata samu ba dan tana buɗe idanunta sai caraf akan fuskar Anty Nafisa,tashi tayi da sauri tana ƙara murza idon amma dai still Anty Nafisa ce A gabanta ba fafi ba,wani irin kuka ne taji ya taho mata da sauri tasa hannu ta toshe bakinta, Aunty Nafisa ta zuba mata ido tana watsa mata wani mugun kallo tare da watsa mata tambayar da ta saka ta cikin tashin hankali tace" da kika damu haka ko ubanki nace ki kashe? duk da Bintu bata san waye ubanta acikin gidan ba amma sai da taji tambayar tamkar haka ne a cikin ranta sai takeji kamar uban nata akace ta kashe, katse ta tayi da cewa Bintu ki sani dole ne ki aikata abin da nasaki saboda kin riga kinji sirrina dan haka shawara ya rage naki ki aikashi ko kuma na kasheshi kema na kasheki sai ki zaɓa!'girgiza kanta take yi cike da tashin hankali mara misali, Aunty Nafisa tace" kije Ina jiran amsarki daga yau zuwa gobe,duk wanda kika gayawa wannan maganar shima zan haɗa dashi duk na aikaku inda ba A dawowa,cikin kuka Bintu tace" meyasa ke bazaki aikata ba tunda kuna tare a guri ɗaya? Anty Nafisa tayi wata shegiyar dariya kana tace"kema gashi kin faɗi dalili saboda muna guri ɗaya za ai zargina amma idan daga wani gurine babu wanda zaiyi zargina kuma kema ba wanda zai zargeki,ki sani mijina yana yawan cin masa a wajen Hajjah dan haka duk ranar da zai ci Ni zan sanar miki zan kuma baki gubar da hannuna kije can ki zuba ki gudu kinga babu wanda zaiyi zargin ki tun da ba zuwa ɓangaren Hajjah kike ba,idan kuma akayi zargin Hajjah fa? wannan babu ruwan ki tunda ke dai kinsha babu abinda yay miki zafi da wanda za azarga,maza ki tashi kije kar inno taga kin jima abinda kika zaɓa kiyo min test ba sai kinzo ba!nuna mata banɗaki tayi tare da cewa maza shiga ki wanke fuskar ki karki sake ki bar wata alama da zatai nuni da damuwarki!'cikin sanyin jiki Bintu ta tashi ta shiga banɗakin bata jima ba ta fito,batare da ta cewa Aunty Nafisa ko mai ba ta buɗe ƙoafar ta fice daga ɗakin,da wani irin murmushi tabita tana ji kamar burinta ya gama cika...

Tun da tashiga ɗakin ta tarufe kanta take kuka har sai da ya saukar mata da mummunan ciwon kai,ko kiching bata jin zata iya shiga, )su Oga Abdallah yau fa sai haƙuri dan baza ka samu haɗaɗɗen girkin Bintu ba)shin yaya zatayi da wannan babban tashin hankalin da ya kuma dannowa cikin rayuwar ta? gaskiya A wannan karon bata da wata dabara ko mafita dole tana buƙatar shawarar wani,to tayaya kenan? bayan ta yi mata gargaɗin kar ta faɗa wa kowa,to hakan yana nufin duk wanda na gayawa shima sai ta kashe shi? runtse idanunta tayi yayin da hawaye suka ƙi dai na zuba mata,ita kanta tasan tana cikin tsaka mai wuya,domin baza ta taɓa iya kashe koda kiyashi ba balle mutum sukutun guda,idan kuwa hakane dole tayi gaggawar neman wa rayuwarta mafita,harma da wanda Anty Nafisa take shirin cutarwa.

Ranar yini tayi A É—aki tana fama da tunani da matsanan cin ciwon kai.

Inno duk ta shiga damuwa ta rasa yadda zatayi ta duba Bintu, can sai wani dabara ya faɗo mata duban su siddiƙa tayi waɗanda suke ta buga game cikin ƙwarewa da nishaɗi yayin da Taufiƙa take can tana zurfafa tunani akan neman cikar muradinta,cikin haɗe fuska inno tace" dasu Farida wai ina yarinyar nan ta shiga ne ban ji alamar tafito shiga kiching ba? Siddiqa ta taɓe baki tana cigaba da sha'anin gabanta,Farida tace"yo inno kika sani ko yajin aiki ta tafi,yau tana muradin ɓatawa Yah Abdallah rai,miƙewa inno tayi ranta A ɓace ta nufi ɗakin bintu,dariya Farida da Siddiqa sukayi har da tafawa,
Chapter 35 · 0% Book details