Sashe 17
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallama sukayi afalon Alhaji baba, sai da ya amsa kana inno ta kutsa kai tana mai cewa da bintu shigo mana kidena dar dar nan ma gidane kamar kowane irin gida!' Alhaji baba dake kashingide cikin kujerarsa, yana kallon labaran duniya yace" ke dawa ne haka kike ta surutu!'inno ta zauna akujerar dake gefensa tana nunawa bintu wajen zama,tace aiko ma meye yanzu zakajishi, ni sarkin surutu kai kuma sanjin zance!'murmushi yayi yana maida dubansa kan bintu da kanta ke sunkuye, yayin da kuma ita kadai tasan halin da zuciyarta take ciki, ahankali ta kuma yin kasa da kanta cikin matukar girmamawa ta gaida Alhaji baba,shi kuma ya amsa cikin mutuncinsa da karamcin da yasaba yiwa duk wani wanda yazo gareshi, inno ya kalla da san karin bayani, ganin haka yasa ta dan muskuta, sannan cikin nutsuwa ta zayyana masa takai taccen tarihin zahra wanda nafisa ta gaya mata, cikin tsananin tausayawa yace" da zahra zonan fadima 'yar albarka na shafi kanki!'matsawa bintu tayi tanajin wata 'yar nutsuwa na shigarta, ayayin da tasamu karramawa ta mutumci daga wannan kamilin dattijo,dora hannunsa yayi akanta yashiga sharara mata addu'a, sai da ya gama kana ya dubi inno yace" kibata daya daga cikin dakunan dake gefanki sannan kuma fadimatu ba 'yar aiki bace rukon maraya yana da matukar alfanu garayuwar dan Adam, dan hakan zamu riketa tsakani da Allah zan sanar da abdallah komai!'duban bintu yayi ya dafa kanta tare da cewa fadima kema 'yace kamar kowa agidan nan amma zan rokeki wata alfarma, inaso zaki dinga dafawa jikana abinci sai kakarku da Zaki dinga taimakawa kina kama mata wasu aiyukan, inno gatanan azaune!'bintu wani nauyi ta dinga ji azuciyarta da gangar jikinta yana da baibayeta, yanzu dama irin wadannan mutanen akeso tazo tashiga jikinsu dan ta cutar dasu?yanzu kenan wannan mutumin mai tsananin kirki da karamci akeso ta cutar?shin sun san adadin mutane nawane suke amfanuwa ta karkashinsa?ko sun san adadin mutanen da sukeci sukesha akarkashinsa? dan basai anfada mataba wannan mutumin uban marayune da marasa karfi da rashin galihu irinsu,to ta yaya za ai ta iya cutar da mutumin da ya amsheta amatsayin jika dan butulci,muryar inno ta tsinkaya tana cewa zahra ko dai bazaki iya ba kikayi shiru, idan bazaki iya ba ki fada kanki tsaye karki damu sai asamo wata!'Alhaji baba ya dora da cewa abinda yasa bazan ce anemo wataba saboda nasan halin abdallah yana da tsantsani sosai kuma kinga ke kina da tsafta, Ina ji lallai zai iya yarda da abincin ki saboda kina da tsafta!' girgiza kai bintu ta shigayi alokaci daya tana cewa, wallahi ko abinda yafi girkine sau dari zan iyayi muku, dan hakan kudena tunanin bazan iyaba zanyi biyayya ga dukkanin umarninku!'Alhaji baba yace masha Allah fadima Allah yayi miki albarka, ya baki nasara acikin rayuwar ki!'cikin san rike kukan dayake makogoran ta take amsawa da amin,yace" da inno kutafi ta kwanta ta huta zuwa gobe!'inno ta amsa da Allah ya nuna mana goben, tare da riko hannun bintu tana cewa, tashi muje fadima kinji!'
Kai tsaye dakin dake gefan nata ta kai bintu,dubanta inno tayi tace" yauwa zahra ga nan bathroom kiyi wanka ki huta zansa su rahima sukawo miki kaya!'bintu tace" na gode inno!'inno tace karki damu bari na kawo miki abinci!'ta fada tana fita daga dakin,
Juyi kawai takeyi bisa dan ma daidaicin gadon da ayanzu ya zama nata, babu abinda zuciyarta takeyi sai kaikawo da tunanin mafita, jin ko Ina nata takeyi a daddaure tarasa makama, haduwarta da wadannan dattawan kirkin yasa taji tanason taimakon su,sannan ga tata matsalar yanzu yazatayi?shin zata gujewa mutanen da suka karbeta amatsayin jika ne ko kuma zata tsaya dan taimakon su?to idan ta tsaya fafinta kuma da mamanta fa tayaya zatayi ta samosu?ga kuma asalinta zatayi ta zama ahakane batare da ta damu da yin rayuwa da danginta ba?acikin wannan yanayin wani wahalallan bacci yay awon gaba da'ita.
Maza-maza dije kizo kisameni ainda muke haduwa Ina bukatar ki cikin gaggawa karki zauna lusaranci kuma ki kula da hagunki da damanki ki tabbatar babu mai ganinki(Amma dai Allah na ganinku ehe)
kashe wayar tayi tana cigaba da sunturi awajen, ita kadai tasan irin tashin hankalin da take ciki, hannu tasa ta gyara nikabin dake fuskarta.
tsawon minti arbain saiga dije ta bullo ta wata hanya daban, da gani dai hanyar boyayyiyace, cikin sauri matar ta fizgo hannun dije saida suka dan bada ta zara da inda suke duk da bawai mutanene awajen ba, taja ta tsaya tana kallon dije cike da tashin hankali, duk da ita dijen ba ganinta takeyi ba dan haryanzu bata taba bari taga fuskarta ba,ahaka suke duk tsawon lokacin da ta dauka tanayi mata aiki, koda ace bata hada mata da barazanar idan ta fadawa wani zata kasheta ita da alhlin ta ba,bazata iya fada ba, to dame zata kwatanta ta? ko kwayar idanunta bazata iya kwatantawa ba,
Matar ta girgiza dije cikin tsawa da tashin hankali tace" dije bakya jina wai Ina magana!' dije tayi firgigigit tace inajinki ranki ya dade!'zagaye gurin ta shigayi tare da cewa, dije aiki ya dawo min baya nasa anbinciko mun komai akan Alhaji jafar da abdallah abinda akasanar dani shine, Alhaji jafar aiki ya turo abdallah yayi masa, kuma suna cikin yan adawarmu yaki suka shirya yi damu kuma suna da kyakykyawan shiri akan hakan niyarsu duk abinda na shirya su kuma su rushe, duk da nasan cewa bani kadai bace nake laluban duniya,akwai wasu hadamammu Irina sai dai bakowa nasani ba,shiyasa kikaga bana zaune akan neman burina, ada hankalina ya tashi amma cikin yan mintuna nasamo mafita, kuma wani abun burgewa shine zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya!'wata mahaukaciyar dariya ta saki, kana ta dubi dije tace"ankawo mun nama adai-dai lokacin danake bukata, dije nifa shu'umace yadda bakya zato,basu san komai dasukeyi idanunta na kansuba, sun lullubo yarinya sun kawota dan tai musu aiki amma sun fake da cewa, sun samowa inno da abdallah mai aiki ne, to ni suka kawowa mai aiki, dije na kuma samun tsanin aiwatar da abinda nakeso, ke zaki fake abayanta, kawo kunnanki wannan bazan bari Fatima taji ba dagani saike,,rada tayiwa dije wadda akalla tadaukesu kusan minti goma tana tsara mata bukatarta,daga nan tayi mata umarni da ta wuce tatafi gida.
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ¼*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page 14 ```
Baffa hashir ya dubi Abba salisu yace"yanzu Salisu har yanzu babu wani bayani akan labarin Abubakar?nifa abunnan yana matuƙar ɗaure mun kai ni burina nasan suwaye suke da alhakin ɓatar dashi, idan ba hakaba kuwa tabbas muna cikin ruɗani baza kuma mutaɓa cimma burinmu ba, sanin mutanen nan shine samun mafita agaremu tunda kuna ganin dai yadda muke tufka ta baya tana warwarewa,Abba salisu yaja wani dogon numfashi kana yace" Baffa yanzu kafin na karaso nan maganar da muka gama da Alhaji na kenan (Alhaji nasir)kuma munyi maganganu dashi masu muhimmanci, akwai shirin da mukeyi A ƙasa, nasanar da yaya Nura komai dan haka kubamu lokaci!' Baffa Hashir yace to shikenan hakan yayi zamu saurareku muna fatan muji kyakkyawan sakamako!'daga haka sukayi sallama.
Sun kasance suna yin mitin duk ƙarshen wata,manyan mutane ne masu faɗa aji,suna yin mitin ɗin ne saboda matsalolinsu da base ankai su gaban dodo jack ba,ko kuma idan sun sami nasara A wani aikin, sai su haɗa ƙwarya-ƙwaryar liyafa dan taya junansu murna, kamar dai yadda sukayi yanzu mitin ne me haɗe da liyafa don taya junansu murna sabida wata gagarumar nasara da suke ganin sun kusa cimmawa.
Sai dai wani abin mamaki babu wanda zaka gani batare da face Mack ba duk rabin fuskar su A rufe take, ikon Allah wato abinda na fahimta kamar dai sunyi haka ne saboda sun san ina laɓe dan gano su waye daga cikin su ƴaƴan Alhaji Balarabe dan nazo nafesawa fans ɗin ƙudurar Allah, bayan Ni kuma suna tunanin da A kwai wanda zai'iya yi musu leƙen Asiri, gaskiya waɗan nan mutane sun iya takunsu.
Wani ne daga cikinsu, ya fara magana cikin salon nau'in maganar su da bazaka taɓa iya gane muryoyinsu ba, yace" ya kamata ku saurara muyi Abinda ya kawo mu kar lokaci ya tafi!' tsit falon yayi,kana cikin nuna muhimmancin maganar da zaiyi yace" yanzu dai kowa A nan yana cikin farin ciki na kasancewar nasarorin da wasu daga cikin ƴan'uwan mu suke samu na daga manyan burukansu, to gaskiya muna matukar farin ciki da wannan lamari, kuma muna fata zamu ga ƙarshen lamarin cikin nasara!' yana direwa gaba dayansu suka ruɗe da shewa da wasu maganganu na nuna farin cikinsu,sai da kowa ya nutsu, kana wani ya ɗora da cewa lallai dole ne mu kasance cikin tsananin farin ciki kamar yadda abokina ya faɗa,kamar yadda kuka sani ne A kwai muhimman Abubuwan da mukesan haɗawa A cikin matakan aiyukan mu,wanda muka daɗe muna jira har muke ganin kamar hakan bame yiwuwa bane kuma muke ganin kamar rashin nasara ne yake tun karan mu, sai dai kuma da temakon dodo jack lamarin ya sauya daga faduwa zuwa nasara,dan A halin yanzu komai ya kammala sai aiwatar da aikin wanda shine mataki na biyu da zamu shiga, amma fa karku manta wannan aikin da muke shirin tunkara yana da matuƙar wahala zamu shiga ƙalubale masu yawa A kwai yiwuwar tonuwar asiri A kwai kuma yuwawar samun nasara, amma mun fi raja'a akan samun nasarar sai dai kawai wahalar aikin, dan yaran sarrafa su shine babban haɗarin da zamu fuskanta to amma munyiwa hakan kyakkyawan shiri kuma zamu cigaba da yin shiri!'gaba falon ya daɗa ɗaukar sowarsu, nan dai aka fara ciye-ciye da shaye-shaye, basa tare da wata damuwa bare kuma tunanin makomarsu.