← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 120

Sashe 64

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Buɗe idanun ta tayi lokacin da taji yana ƙwala mata kira,cikin yanayi na tashin hankali tare da karanto duk wata addu'a data zo bakin sa,cikin ikon Allah yana ɗaga ƙafar sa sai gashi Allah ya bashi ikon shiga wajen, cikin wani irin hanzari na ƙarfaffan namiji ya finciko hannun Bintu da ake shirin turata cikin ɗakin nan,tare da ce mata maza kiyi addu'a,amma ina tuni ai Bintu ta sume masa saboda tsananin razana da tayi da wannan al'amarin,ɗaukar ta yayi cak tare da fita daga ɓangaren,yana ƙoƙarin saka Bintu a mota yaji muryar Dady Mansur yana cewa kai kam ka zama wahalalle kai kenan ɗaukar mace"a bainar jama'a,to ai ba sai ka nuna mana Kai ɗin dan zamani bane, tuni mun riga mun sani dan duk wasu alamu sun nuna atare da kai!'tsayawa Abdallah yayi tare da zubawa fuskar Dady Mansur ido,yayin da tunanika sukabi suka da baibaye zuciyar sa tare da zargi mai ƙarfi akan Mansur ɗin,me yasa yake yawan ganin sa ta wannan ɓangaren ne?me yake yi a wajen?meye kuma haɗinsa da wajen?meye ne kake kallo na haka kamar zaka cinye Ni Ni dai na fi ƙarfin duka a wajenka babu yadda zakayi dani,Tom kuma ina mai sanar da kai idan har dasa hannun ka cikin ɓatan ɗana to kayi gaggawar sakar min shi idan ba haka ba duk abinda ya faru kayi kuka da kanka!'yana gama faɗar maganar sa yayi ciki tamkar zai tashi sama,saboda fushi da kuma sauri.

A hankali Abdallah ya saka Bintu cikin motar, yana shirin shiga sai ga Anty Nafisa cikin sauri ta ƙara sa gaban sa tana cewa kamar Bintu na gani anan? me yasame ta?daƙyar kamar mai ciwon baki yace da ita,ta ɗan tsorata ne,shine ta suma!'da sauri Anty Nafisa tace"to ai ba sai an kaita asibiti ba ko ruwa aka zuba mata ya wadatar!'yahya ne yayi saurin miƙa masa gorar ruwa saboda alamar da yayi masa,ɗan zura kansa yayi ya yayyafa mata ruwan,bata wani jima ba kuwa ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya sai dai amma a tsorace take,ganin haka yasa shi shiga cikin motar tare da tallafo kanta saman cinyar sa,shafa kanta ya shigayi A hankali, tare da ɗan hura mata iska saman fuskar ta,buɗe idanunta da suke rufe tayi,ta zubasu kan kyakkyawar fuskar sa,sai kuma ta ɗan maida su ta lumshe saboda yadda wasu maganaɗisu ke fitowa daga cikin idanun nasa suna shigewa cikin nata idan.

Anty Nafisa kuwa tana daga waje tana kallon sarautar Allah,ko tace wata iriyar ƙauna,wadda bata taɓa ji ko gani ba A tarihin rayuwar ta,ga kuma mamakin daya rufeta wai dama wannan muskilin mutumin zai iya tarairayar mace irin haka?to gashi dai ta gani da idanunta ba wai labari aka bata ba, duk da ta fahimci kamar Abdallah bai san da wannan zazzafar ƙauna da yake yiwa Bintu ba,fitowar Abdallah da Bintu ne ya katse mata tunani,bin su ta kuma yi da wani kallo saboda yadda taga Bintu tana wani narkewa Abdallah,shi kuma sai wani rirriƙeta yake duk da fuskar sa A haɗe take amma hakan bai hana damuwar halin da Bintu take ciki baiyana asaman fuskar tasa ba,ganin yana ƙoƙarin wucewa da Bintun part ɗin inno yasa tayi saurin ɗan matsawa kusa dasu tare da cewa,i can help her,ta faɗa tana duban Abdallah sama-sama batare da ta iya haɗa ido dashi ba,ci gaba yayi da tafiya batare daya kulata ba,ganin haka yasa Bintu ɗan dakatawa tare da duban sa tace"ka tafi kawai zamu ƙarasa da Anty Nafisa!'wani irin kallon yake mata wanda har saida ta kasa jurewa ta shige cikin jikin sa,ƙasa-ƙasa cikin miskilar maganar sa yace"kin tabbatar zaki iya babu wata matsala?ɗaga kanta tayi tana mai zamewa daga jikin sa,sakin ta yayi kana ya ɗanja da baya batare da ya ɗauke idonsa akanta ba,Anty Nafisa datayi mutuwar tsaye daƙyar ta iya ɗaga kafafunta tare da kama hannun Bintu suka fara tafiya dan shiga falon inno, Anty Nafisa ta shiga tsananin mamaki da irin wannan soyayyar da ta hango cikin idanun Abdallah da Bintu,anya kuwa soyayya zata bari Bintu tayi mata abun da ya dace akan wannan al'amari?to amma dai bazatayi saurin karaya ba tunda wannan tunanin tane ba tunanin Bintu ba,da haka suka dan gana har zuwa cikin ɗakin Bintu batare da kowa ya gansu ba saboda basu tarar da kowa A falon ba, inno tana sashen Alhaji Baba ita kuma Taufiƙa sun ƙule cikin ɗaki tana nemarwa kanta mafita,shi yasa suka shigo ba tare da kowa ya gan suba.

Suna shiga ɗakin Anty Nafisa ta maida ƙofar tare dasa mata key,zama tayi gefan Bintun wadda ta shiga duniyar tunani, gaba ɗaya tunaninta yana kan wannan ɗakin itafa tasha alwashi ko zata rasa rayuwarta sai tagano sirrin ɗakin nan, wannan abin da akayi mata ba komai bane ba kuma ba zai sa taji ta karaya ba,ji tayi ma tamkar an zaburar da ita akan al'amarin,dafata Anty Nafisa tayi tare da cewa Bintu wai mai yafarune? tun ɗazu nake jiranki ganin bakizo bane yasa na biyo bayanki!'Buntu tace"ba wani abu bane ba fa Anty, A hanyar zuwa wajenki ne fa na ɗan samu tsautsayi,sauri tayi ta kawar da zan cen da cewa Anty Nafisa me yake faruwa ne kike nemana haka da gaggawa?take fuskarta ta sauya saboda motsuwar abinda yake ranta,cikin kama hannun Bintun tace"haƙiƙa ina cikin tashin hankali mara adadi,a hankali ta shiga zaiyanawa Bintu duk abinda ya faru ta ɗora da cewa,tashin hankali na bai wuce yadda zanyi nasan abinda Umar yake shiryawa ba,ban san me yake nufi da mallakawa, gaibu dukiyar sa ba,na shiga matuƙar ruɗani tare da duhun da naka sa ganin haske ko yaya yake!'tun da Bintu ta fahimci inda labarin Anty Nafisa ya dosa ta manta inda take saboda ruɗewa da tunani,me yake shirin faruwa ne?ba dai mijin Anty Nafisa shine mahaifin ta ba?wata irin zufa ce ta shiga keto mata,yayin da ƙwaƙwalwarta ta cigaba da yin zagaye tana auna abinda sa hannun yake nufi da labarin rayuwar ta,da kuma sunan mahaifinta da fafi ya gaya mata cikin labarinta wanda duk ta mantasu Abaya sai yanzu komai yake dawowa cikin ƙwaƙwalwar ta,ga sunan da ta ambata yayi dai dai da sunan da mutumin nan ya ambata, hakan yana nuni kenan mijin Anty Nafisa ita ya mallakawa dukiyar sa?to yasan da ita ne?kuma waya bashi labarin an haifeta,?tunanin tane ya kai kan matar Baffan ta fafi da mahaifiyar su,to ko mahaifinta ya same su dan ta hanyar sune kaɗai zai iya samun labari akan su ta hanyar sune ka ɗai zai san cewa Laila ta haifa masa ɗaya mace,to hakan yana nuni da cewa suna raye?idan suna raye to suna ina?Bintu fa ta ruɗe lallai tana buƙatar waɗan nan amsoshin a kusa,to amma ai zata iya samun wasu amsoshin wajen Anty Nafisa duk da tasan baza ta gaya mata ko mai ba,amma tabbas tana da yakinin Aunty Nafisa tasan wani abu akan mahaifiyar ta Laila,idan ba haka ba me yasa ta tashi hankalinta, saboda sa hannun?wata zuciyar tace Bintu ki nutsu kar Nafisa ta ganoki dan agurinta zaki samu,rabin amsoshin ki dan kuwa tasan abinda ke baki sani ba wanda kuma zai iya kasancewa wani ɓoyayyen sirri da batason kowa yasani,tabbas dole kiyi ƙoƙarin binciko wannan sirri, Anty Nafisa ta zaman miki tsanin hawa wanda zaki taka dan cimma kyakkyawar manufarki, da wannan tunanin ta juyo tana daɗa fuskantar Anty Nafisa wadda ta zuba mata ido ba tare da ta katse mata tunani ba dan atunanin ta ita take lalubowa mafita, ɗan numfasawa Bintu tayi tare da cewa"gaskiya wannan al'amari yana buƙatar dogon nazari!'cikin yanayin damuwa tace"haba Bintu Ni da nake ta sauri dan zuwa gareki ki bani shawara amma sai kice sai Anja lokaci,idan wani can shawarar baibgagareki ba me yasa wannan zai gagareki?kai tsaye Bintu tace"saboda ban san makamar zaren ba,bani na fara labarin ba dan haka ƙarƙareshi zaiyi min wuya!'cikin tashin hankali Anty Nafisa tace"me kike nufi Bintu?kai tsaye ta kuma cewa ban san ko mai akan batun yarinyar da aka mallakawa dukiya ba,ballantana nabaki shawarar yadda zaki ƙwaci dukiyar da A kasa hannu domin shaidar ta zama tata!'

Wani irin gumi ne mai tafe da wani irin yaji ya shiga sauko mata tako ina,gaba ɗaya miyan bakinta ya ƙafe har wani ɗaci-ɗaci take ji saman harshen ta,hannu tasa ta ɗan share gumin kan goshin ta,kana cikin sarkewar da harshen ta yayi tace"yanzu kina nufin in dai zaki warware min wannan matsalar sai na gaya miki wani abu daya dan ganci yarinyar?jinjina kanta Bintu tayi cikin bata tabbaci,Anty Nafisa ta kuma cewa to idan kuma ban san komai ba fa?wani irin kallo Bintu ta wurga mata a fakaice,kana tace"ai nasan ba zai yiwu ace baki sani ba,kinga fa Anty Nafisa Ni taimakon ki nake yi kuma ina nema miki hanyar da zaki samu abinda kike nema batare da kinsha wahala ba,idan kina ganin wannan ba hurumi na bane babu wata damuwa sai mu canja shawara!'ta faɗa tana mai fargabar kar ta ɗauki maganarta ta ƙarshe,ai kuwa cikin sauri Anty Nafisa tace"gaskiya Bintu gwara mu canja shawara,saboda Ni kaina ban san komai game da wannan al'amari ba,kawai ki taimaka ki kawo shawarar yadda zan ɓullawa Umar ya faɗa min wani abu da yake ɓoyemin!'Bintu dai ba dan ranta ya soba Amma tasan a sannu zata samu abinda take so gurin Anty Nafisa,kuma ko ba komai itama samun bayanai daga wajen Abba Umar ɗin zaiyi mata amfani,dan haka cikin nutsuwa tace"shike nan amma ki ɗan bani nan da zuwa gobe,gaggawa bazai mana amfani ba a wannan gaɓar amma kiyi haƙuri zuwa goben idan Allah ya kaimu!'Anty Nafisa dai ba dan ranta yaso ba haka ta haƙura...
Chapter 64 · 0% Book details