Sashe 82
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin ya samune ta sanadin wani da ɗaɗɗen waje da Alhaji Baba ya saya domin ayi masa kamfanin robobi wajen kuma gini yake buƙata mai ƙarko,shi yasa kullum ta Allah sai Alhaji Baba yaje wajen, har aka gama ginin ma aikatar nan akazo kan hakar rijiyar da zata dinga bada ruwan amfani a cikin ma aikatar to anan ne ko mai ya faru a lokacin daga shi sai ɗan sa ABUBAKAR saboda yawanci tare suke zuwa irin wannan guraren,dama ance komai da sanadin sa sai kiga idan Allah yace da rabon ka to sai kiga sanadi ko mai ƙankantar sa ya kawo maka rabonka to hakan ce ta faru da Alhaji Baba ɗan abu ƙarami kuma mara tushe da dalili shine ya kawo masa wan nan rabon, indai ba rabo ba to haka kawai babban mutum zai zauna yana tona taɓo? haƙar rijiyar da aka fara batayi nisa ba wan nan ne dalilin da yasa Alhaji Baba tsugunawa yana taɓa ƙasar wajen yana ɗan tottonawa ramin badan wani abu ba sai dan nishaɗi,taɓo abin yayi a hannunsa hakan ne yasa ya ƙara tura hannun dan san ganin ko meye aaboda santsin da yaji abun ke dashi,abu kamar wasa sai gashi yana ta zaro abu wanda shi dai bai fahimci ko menene ba, Abubakar yace"Alhaji Baba me kake cirowa ne haka sai kajiwa kanka ciwo!'ya faɗa yana tsugunawa shima gaban ramin da bashi da zurfi, Alhaji Baba yace"ina tunanin dai wani babban dutsene kaga idan na ciro ai narage musu aiki ko? Abubakar ya kuma cewa'haba Alhaji duba kaga fa kana ciro abu da wahala kace zaka ragewa waɗanda zasu ciro shi da masarrafi aiki!' Alhaji Baba dai bai ce masa komai ba yaci gaba da tagagarin ciro mulmulen dutsen da ya kasa zaroshi saboda santsin sa,Abubakar babu yadda ya iya haka ya naɗe hannun rigar sa ya shiga taya dattijon nasa aikin da ya rikitowa kansa,kamar wasa Abubakar ya janyo wani ƙarfe dake can gefe irin na masu aikin haƙa,yace"Baba bari mu tona da wannan muragewa kanmu aikin da ka ɗauko mana!'Alhaji Baba yace"Abubakar bazaka gane ba jinake kamar wannan abun ba dutse bane saboda yana da santsi idan kayi la'kari da yadda yake saɓulewa daga hannun mu!'to bari na haƙo da wannan sai muga wane alherin ne yake kiranmu!'ya faɗa yana cusa abun dan zaƙulo abun daga cikin ƙasa,cikin sakanni saiga abun mai girma kamar ma dai dai ciyar boll,sai wani irin ƙyalli da sheƙi yake yana haske musu idanu,cikin ma daukakin mamaki Abubakar yace"Baba wan nan ai dimon ne,abu mafi ƙololuwar daraja!'sunkuyawa yayi da sauri ya ɗauke shi a hannun sa tare da nufar wajen da suka ajiye mota,cikin wani irin zafin nama yake takawa har ya isa motar ya buɗe ya saka dimon ɗin kana yace"Baba shigo mutafi da sauri!'shiga Alhaji Baba yayi tare da yiwa Abubakar ɗin wani irin kallo kana yace"bangane abinda kake nufi da wannan rawar jikin ba?sai da Abubakar ya tada motar ya ɗauki hanyar barin kamfanin kana ya ja ajiyar zuciya tare da cewa Alhaji Baba baka San akan wannan al'amarin yanzun nan sai a harbe mu ba? Ai yanzu ganin dimon ɗin nan tashin hankali ne a wajen mu dan duk wanda ya san dashi to wallahi sai an biyomu ankashe mu!'jijina kai Alhaji Baba yayi tare da cewa maganarka haka take kuma nima nasan da haka,da farko nayi tunanin farin cikin samuwar dimon ɗin agaremu ne ya hanaka nutsuwa, murmushi Abubakar yayi tare da cewa haba Baba kamar kamanta waye habunka kuma duk arziƙin da muke dashi sai na hangi wani,Alhaji Baba cikin tunanin yadda zasuyi da wannan dimon ɗin yace"ban mantaka ba habu,amma bana son samuwar wan nan abu ya sauyaka daga kan kyawawan halayyar ka dana riga na sanka da ita saboda shi wannan ɗin samuwar ƙololuwar arziƙine darajar sa ta wuce tunanin ka saboda wan nan dimon ɗin babban ne kuma kasan yanzu me shi a kullum shike neman daɗi!'baba ya akayi kayi saurin gane darajar dimon ɗin? Alhaji Baba yace"haba habu karfa kamanta kasuwan ci nane fa a baya kuma ido ba mudu ba ai yasan kima!ɗan murmushi yayi batare da ya iya cewa mahaifin nasa ko mai ba,sai can bayan sun kusa shiga estate Alhaji Baba ya dubi ɗan nasa yace"Habu bai kamata mu shiga estate batare da mun yanke shawarar yadda zamuyi da dimon ɗin nan ba!'Abubakar yace"nima abinda nake tunani ke nan amma ina ga ɓoyeshi zamuyi kar mu bari kowa yasan da shi idan ba haka ba kuwa tabbas duniya taji za a iya zuwa har gida a farmaki rayuwar mu akan sa!'Alhaji Babba ya jinjina kai tare da cewa amma kasan sai na gayawa ƴar Agadez ko!'naji Baba Amma kasan ta yadda zaka faɗa mata ba tare da ka bari wani yaji ba dan wan nan abun sirrin junan mune bayan zune lokacin bayyana shi ba,daga nan sukayiwa junan su raɗar inda zasu ɓoye dimon ɗin,babu wanda yasan inda suka ajiye shi sai su biyun nan bayan Allah da ya haccesu baki daya.
Samira taja wani gauran numfashi tare da cewa to ku kuma ya akayi ku kasan da dimon É—in? Alhaji Sama'ila yayi dariya tare da cewa,to ai wan nan ba Abune na mamaki ko wahala ba,yadda akayi mukasani kuwa shine É—aya daga cikin mune yaji wato Nura É—an Alhaji Hashir,alakacin da Alhaji ke faÉ—awa Hajiya Babba to shine yaji ya faÉ—a mana,amma ko ita Hajiya Babba bata san inda wan nan dimon yake ba,sai dai abinda ya É—aure mana kai yadda akayi kwana kaÉ—an da faruwar al'amarin aka nemi Abubakar aka rasa tare da É—an sa na biyu mai suna abdulraman,kuma tunda Aka É—auke su har rana irin ta yau babu wanda yayi kukan rashin su ko cikiyar su,sai dai Alhaji Baba da ya fara cuta wadda har ta kaishi ga kwanciyar wasu watanni a asibiti!kinji abinda ya faru kuma yake kan faruwa kuma kinji akan abinda ake ta gumurzu akan sa!'
Baƙaramar dauriya Samaira tayi ba gurin ƙoƙarin hana kukan dake idanun ta kufce mata ba,wani irin azababban tausayi ne ya cika mata ƙirji Allah sarki Alhaji Baba yana tare da maƙiyan sa bai sani ba,kalaman Alhaji Abubakar sun fi taɓa mata zuciya,wato abinda ya faɗa kuma ya guje musu tun A lokacin shine ya faru akan sa,cikin dabara ta goge hawayen da ya ɗan fara zubowa daga idanuwan ta,kana tace"gaskiya wannan al'amarin da ɗaure kai yake to waye ya ɓoye Abubakar?shi kuma ɗan nasa yana ina yanzu? Alhaji Sama'ila yace"ɗan sa dai babu labarin inda yake, shi kuma abubakar tunda muka rasa shi hankalin kowa a cikin mu ya tashi, ko da yaushe cikin nema da binciken inda yake muke ba tare da kowa ya sani ba,kuma har yau ba musamu damar sanin inda yake ba!'miƙewa tsaye yayi tare da cewa to Samira lokaci yayi bari na wuce kar suzo suna jirana!'tace"shike nan Alhaji sai munyi waya zanyi tunanin abin da ya dace!'yauwa sai mun haɗu daga haka ya fita daga gurin yana fita itama Samira ta wuce, officce ɗin Abdallah inda suke dakon jiranta..
Wannan karon Abdallah ya kasa daure abinda yake ji acikin zuciyar sa,dan haka kana kallon ƙwayar idanun sa zaka gane yanayin da yake ciki na azabar raɗaɗin zuciya,yana kuma tausayawa waɗanda suka aikata wannan mummunan kuskure ga mahaifinsa,miƙewa yayi ba tare da ya iya cewa dasu komai ba,ya tattara kayayyakin sa ya bar officce ɗin,Samira ta kalli Dady jafar tare da cewa, Dady anya kuwa babu wata matsala atare da Oga Abdallah naga yana yawan shiga tashin hankali akan wan nan aikin namu?shima kallonta yayi yace"baki san komai bane Samira,amma yau zan gaya miki abinda baki sani ba saboda amanarki da gaskiya da yadda kika tsaya mana akan aikin nan cikin nuna hazaƙarki da ƙwarewarki ta aiki,bai saurara da maganar da yake ba har sai da ya tabbatar wa da Samira cewa bashine mahaifin Abdallah ba wan nan mutumin da aka sace shine mahaifin sa,
Wata irin zabura Samira tayi cikin matuƙar mamaki da tausayi har ta ma rasa abinda zata ce sai faman bin ƙofar da Abdallah yabi take bi da kallo baki sake da wasu tarin ƙwalla da suka cika idanunta,komawa tayi ta zauna cikin karaya da Al'amarin tace"innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un,astagfurullahi wa'atubu ilaihi, Allah alhakim Allah abin tsoro mugun mutum abin tsoro, tausayin Abdallah ne cike taf a ranta,sai ta kuma jin karsashin ci gaba da taimakawa rayuwar sa da dukkan ƙarfin ta da alajihunta da zuciyar ta.
Duk da cewa tana ɗokin dawowar sa dan sanar dashi babban al'amarin da ya ɓullo daga gurin Nafisa amma tafi ɗokanta da lokacin da take hasashe dan ida nufinta,tayi ƙoƙarin danne duk wani al'amari dake cikin zuciyar ta,tayi kuma ƙoƙarin sakewa Inno tunda har yanzu hasashe takeyi bata tabbatar da abinda idanun ta da zuciyar ta ke gani ba, Al'amarin Anty Nafisa ma ta ajiye shi gefe,sai dai lokaci lokaci tana jin faɗuwar gaba idan ta tuna da mugun nufin Nafisar akan mahaifinta,amma kuma tayi matuƙar dauriya ta miƙawa Allah assamadu dukan lamuran ta tasan cewa rayuwar mahaifinta ba a hannun Anty Nafisa yake ba,dan haka tayi yaƙini azuciyar ta cewa bata isa ta katse rayuwar Abba Umar ba sai dai idan Allah ya kawo lokacin sa,da wan nan ƙarfin gwiwar na tasirin imani ga Allah Bintu take tsaye cikin aminci tana gabatar da al'amuran ta na yau da kullum,