← Book details Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 120

Sashe 39

Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baza ka taɓa fahimtar halin da Oga Abdallah yake ciki ba saboda wannan dama ɗabi'ar sace, ita kuwa Bintu bata da maraba da hoto baƙaramin shock ta shiga ba saboda jin abinda Sayyid yake faɗa, wai anya kuwa ita Bintun yake nufi ko wata ce can daban mai sunanta? nutsuwa tayi ta zubawa bakin Alhaji Baba Ido dan jin abinda zai furta, Alhaji Baba ne yayi gyaran murya kana cikin zubawa Sayyid ɗin ido yace"ka tabbatar abin da kake faɗa har cikin zuciyar ka ne babu wata manufa ko yau dara? cikin sauri Sayyid ya kada kansa tare da cewa hakane har cikin zuciya ta da gaske nake ina sonta kuma zan riƙe ta amana!'wani ƙawa taccen murmushi Alhaji Baba yayi tare da cewa to Alhamdulillah Masha Allah hakan yayi kyau kayi tunani mai kyau Sayyid ka fanshi kanka daga irin mummunan hukuncin da na tanadar maka!' shiru yayi yana bin mutanen falon da kallo sannu A hankali har ya dire idanun sa kan Abdallah da kansa yake sunkuye balle na gwada ƙoƙarina ko zan gano muku halin da yake ciki,har yanzu dai babu wanda ya tanka ko Dady Mansur bai tanka ba tun lokacin da Hajjah ta ƙare mai tanadi,kowa so yake yaji abinda Alhaji Baba zai ce,kamar ya karanci zuciyoyinsu,cikin dattijan taka yace"naji daɗin maganarka Sayyid sai dai nariga nayiwa Bintu miji ɗan lokaci kaɗan nake jira na gabatar musu da juna,duk da ban nemi shawarar ta ba amma nasan faɗima bazata watsan ƙasa A ido ba,bazan baka faɗima ba Sayyid wannan yarinyar bata dace da mutum irin ka ba,sai da na daɗe ina tunanin mijin da ya dace da rayuwarta kafin hankali na ya kai kansa,zasu dace da junan su matuƙar da cewa,dan haka kaje kanemi matarka cikin gidan nan ko wacece zan aura maka ita amma banda faɗima matar tsadadden namiji!'

Wani irin ƙawa taccen murmushi ne ya shiga subcewa Hajiya Babba wanda ya fito tun daga ƙarƙashin zuciyarta, kuma ta kasa ɓoye shi kan kyakkyawar fuskarta,inno ma hakan yayi mata daɗi sosai dan ita kam tayi yaƙini cewa Sayyid ƙarya yake tunda tana sane da irin tsanar da sukayiwa Bintun,ta dai fi tunanin wani muguntar yake san shirya mata, Hajjah kuwa ita dariya tayi sosai tare da cewa haba Alhaji duk kasa fargaba ta rufeni dan kalaman ka sun fara nuni da kamar zaka amince da wannan maƙaryacin!'murmushi kawai yayi tare da cewa jafaru kayi shuru bazaka ce komai ba? ɗan muskutawa yayi kana yace"ai Alhaji Baba kaga ma faɗar komai muma abin ikonka ne barantana kuma yaran da muka haifa da kai da kaya duk mallakar wuya ne dan haka babu abinda zance sai fatan Alkhairi!'juyawa yayi ya kalli Dady Mansur da ya cika yayi fam tamkar zai fashe,yace mansur kana da magana ne? gyara zaman sa yayi dama abinda yake jira kenan samun damar magana, cikin gayyatowa kansa nutsuwa yace"nifa Baba Ina ganin gara abawa yaron nan dama tunda har yace"yayi nadama,duk wanda zaka bawa aurenta ai inaga bai kai matsayin Sayyid ba,kuma hakan babban rufin asirine A gareta tun da taimakon ta zaiyi!'Dady Habib yace"haba yaya me yasa baka tauna magana idan zaka faɗeta? ya mahaifin mu ya yanke hukunci amma ka nuna kamar baiyi dai dai ba!'a wannan karon Mansur bai tanka masa ba saboda yaga mugun kallon da Hajjah take aika masa, Alhaji Baba ba tare da yabi takan maganarsa ba yace" suje ya sallame su, Sayyid ta shi yayi yana kun bure kunbure tare da faɗar magana aciki babu wanda ya kula shi,Bintu kam ta riga kowa barin falon dan gani take kamar Alhaji Baba zai iya canja shawara yace ya bawa Sayyid aurenta,abinda bata fatan sa kenan ko da a mafarki ne,

Part ɗin sa ya wuce kai tsaye,yana shiga banɗaki ya faɗa ya sakarwa kansa shaya ya jima ruwan yana sauka A kansa kafin yayi wanka ya fito,shirya wa yayi cikin doguwar jallabiya fara ƙal wadda tayi matuƙar dacewa da tsayin sa na ingarma kuma zaki,kwanciya yayi saman gadonsa tare da lumshe idanun sa, shi kansa yanzu ba zaice ga abinda yake damunsa ba bai san halin da zuciyar sa ke ciki a kan wannan lamari ba,dan haka kawai sai ya jawo casbaha ta dannawa ya shiga ambatan Allah,

Bintu kam yanzu ta samu nutsuwar zuciyarta dan sam ita A ƙuruciyar ta bata saka maganar Alhaji Baba cikin ranta ba, ita atunanin ta ma yayi hakane dan ya kuɓutar da ita daga tarkon auren jikansa dan haka take jin mutumin har can ƙololuwar ranta,sai kuma mamakin Dady Mansur da ya kasa barinta,wato dai halinsa sak da ɗan sa babu abinda ya rabasu,a wannan lokaci fa tana buƙatar ganin Dije sosai kuma ya kamata tasan abin yi tunkan mutanen nan su cigaba da cutar da ita tare da mamaye ta ta ko ina.

A ɗakinsa ya sameta sai sintiri take, yana shigowa ta tare shi cikin sauri tare da cewa Allah yasa dai munyi nasara?kawar da kansa yayi daga kallon ta kana yace"shirin nan baiyi ba Taufiƙa Alhaji Baba ya rufe idonsa yace bazai auramin Bintu ba saboda yayi mata miji!'zaro ido tayi tare da cewa wa ya bata? yarfa hannu yayi alamun bai sani ba,kana ya ɗora da cewa Wallahi Ni dama ina son yarinyar nan ban san ina sonta ba sai da Alhaji Baba yayi wannan furucin na ya bawa wani ita yanzu me kike ganin zamuyi? Taufiƙa taja Ajiyar zuciya tace" ai Ni dama dan kar Ya Abdallah yace yana sonta ne amma tunda Alhaji Baba yayi mata miji bani da matsala yanzu sai yaƙin samo auren sa dan Ni ban damu da sai ya soni ba !'wani mugun kallo ya watsa mata tare da cewa Ni zakiwa butulci makira to yadda ban samu Bintu ba ke ma bazaki taɓa samun Abdallah ba insha Allah!'Sayyid yanzun nan mutuncin dake tsakanin mu zai watse dan aduniya bani da maƙiyi sama da wanda zai shiga tsakanin soyayya ta da Ya Abdallah dan haka kasawa bakinka linzami tun kafin na fito maka da baƙin halina!' tsaki yayi gami da shigewa banɗaki ya barta tsaye tana saƙe saƙen yadda zata ɓullo wa al'amarin.

Wayar da Anty Nafisa tayi mata ita ta tuno mata da tashin hankalin da take ciki,wayar na riƙe a hannun ta sai nombar Dije take gwadawa amma taƙi shiga to wai ta yaya zasu shawo kan matsalar nan ba yan basa haɗuwa da Dije? yanzu idan Dije yaudarar ta tayi ya zatayi kenan wa kuma zata tunkara dan ya taimaka mata?hannu tasa ta share hawayen da suke ta tsiyayowa daga idanunta, A fili take cewa fafi ina kake?ban san yaya zanyi ba al'amarin ya wuce duk yadda kake tunani,bazan iya ba,kai ne kace min zaizo ya taimakamin Amma har yanzu bai zo ba,a ina zan samo shi? Allah ka kawo min mafita cikin wannan cakuɗaɗɗen al'amari.

Ka in da na in suka shiga bincike A kan su Alhaji Nasir, yayin da Samira har ta samu sa ar kama Alhaji Sama'ila a hannun ta,cikin hikimar su ta ƙwararrun ma aikata masu himma da ƙwazo,acikin kwana biyu suka sami babban cigaba sun sami baya nai masu yawa,kuma suna da tabbacin zasuyi nasara, Abdallah ya gano a kwai wani abu guda da suke san mallakar sa acikin estate ɗin kuma wannan abun ga dukkanin alamu yana da matuƙar muhimmanci a cikin ahlin ALHAJI BALARABE,to abinda yake so ya sani shine meye wannan abun? kuma A gurin wa yake? san nan mallakin waye?yanzu abu mafi mahimmanci dayake son ganowa shine inda mahaifinsa yake da kuma sanin sirrin dakin nan da ainahin abinda ake rigimar akansa,lallai dole ne ya tashi tsaye tun da yanzu ne za a fara wasan,kowa na cikin ESTATE sai yayi bincike a kansa dan ta hanyar ne kawai zai gano annamimai kuma gurbatattun iyalan ALHAJI BALARABE.

Inno gaba É—aya ta kasa gane kan Bintu kwana biyun nan hakanan take kallon ta kamar wadda take cikin matsala,hakan ne yasa ta sameta har É—akinta ta ritsata da tambaya amma Bintu tayi fur tace" ita babu komai kawai dai yanayi ne, dole haka inno ta rabu da ita tare da binta da addu'a.

Acan kuma ɓangaren Abigirl har yanzu tana nan tana jiran dawowar fire,yayin da takasa yin wani kataɓus dan bata da wata hanya ta ganin bayan Abdallah sai haya killers,Bata da damar ko zuwa get ɗin estate din bare ta kaiga shiga ciki,kwata kwata hankalinta ba a kwance yake ba, kullum ta Allah gani take kamar asirinta zai tonu,mutumin nan babu Allah a ransa duk lokacin da ya gano ta ha'inceshi tabbas sai buzunta gara tun bai ankara da Abdallah a duniyar ba ta kashe shi hakan ne kawai zai samar mata da kwanciyar hankali,ko haɗuwa da mijinta ta rage yi saboda tasan zai iya gano sirrin da take ɓoye masa,wayar tace ta fara ƙara ɗagawa tayi da hanzari a tunanin ta ko fire ne ya dawo,sai dai kuma ba haka bane dan wannan lambar ma an ɓoyeta,duk da haka batayi ƙasa a guiwa ba tana sa ran shi ɗin ne,wata mahaukaciyar dariya taji ansakar mata tamkar dodon kunnen ta zai tsage har sai da tayi saurin kawar da wayar daga kunnen nata,a amsa kuwa ta sakata dan bazata iya jurar jin wannan mahaukayar dariyar A cikin kunnen ta ba,ta can ɓangaren akace mata sannu tsohuwar kafura.

A dai dai wannan lokacin kuma Daddy jafar yazo zai murɗa mariƙin ƙofar sai kuma ya dakata dan jin dariyar da ke fitowa daga cikin sifikar wayar,badan laɓe ya tsaya ba sai dan yana san gano wani abu game da matar tasa dan dama so yake ya gama kamata dumu dumu kafin ya sanar wa da Abdallah,dan yana matuƙar zarginta barin ma acikin kwana kin nan shi yasa yay matuƙar saka mata ido,
Chapter 39 · 0% Book details