Sashe 111
Kudurar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun abin na basu mamaki har ya koma basu kuka daga nan ya koma san yayayar musu da jiki da zuciya da ƙara san miƙa wuya ga ubangijin talikai,cikin wani irin yanayi na tsananin tausayin kai da tsinkewa da al'amuran duniya, Alhaji Baba yace"Habibu a ina kaji zancen diamon?tsit falon yayi masu kuka suka tsaida kukansu masu ƙus ƙus suka tsaya da gulmarsu,sai ido da yayiwa Dady Habib yawa,shi kuwa cikin yanayin alhakin da ya fara kamashi, yace"wata rana can shekarun baya nazo zan shiga ɗakin Hajjah sai naji tana surutai cikin ɓacin rai wanda da alama anyi mata wani abu da ya bata mata rai,to har zan shiga sai kuma na dakata sakamakon abinda naji tana cewa,yanzu Alhaji har san kan nasa ya kai ya ware Hajiya Babba ita kaɗai ya gaya mata wannan sirri mai matukar muhimmanci da hatsari ba tare da mu ya nemi ɗaya daga cikin mu ba,kuma har ita da ɗan ta,ƙwafa naji ta ɗan yi kana ta ci gaba da cewa yanzu yana nufin zaice ya barwa Abubakar diamon ɗin saboda tare suka tsinta,kuma ya bashi ya ɓoye baya gudun yayi masa halin ɗan yau,inajin wannan ban bari naji wani batun ba,nayi hanzarin barin falon nata,acikin zancen ta na fahimci cewa ABUBAKAR ya san inda diamon ɗin yake,shi yasa kai tsaye na saceshi saboda na kuma samun tabbaci!'Alhaji Baba ya maida duban sa kan Hajjah wadda kanta yake ƙasa daza a buɗe zuciyar ta kuwa da anyi mamakin irin bugun da takeyi,saukar Muryar sa a kunnen ta daidai yake da wata irin tsinkewa da zuciyarta ta kumayi wanda har saida ta dafe ƙijinta da yake barazanar fasowa ya waje, Alhaji Baba ba tare da ya kula da yanayin ta ko halinda take ciki na fargaba ba,yace"Ya gana ya akayi kika san da wannan maganar alhalin nasan Ni dai ban gaya miki ba?wata irin zufa ce take ta wanke mata jiki,a haƙiƙanin gaskiya Hajja tana cikin wani irin hali wanda bata taɓa tunanin zata shiga ba,da tasan wannan rana zata zo mata da bata aikata abinda ta aikata ba,da tasan asirinta zai tonu da batayi abinda tayi ba,da tasan a kwai ranar da zata mozanta a idanun ƴaƴan ta da mutanen da suke ganin kimarta da ba tayi abinda tayi ba,maganar da Alhaji Baba ya kumayi mata cikin ɗan fusata da tsawa shine ya dawo da ɗan guntun hayyacinta kansa,yace"ba magana nake miki ba Yagana?cikin karaya da saddaƙar da cewa yau ranar dubunta ce,yau ranar banƙada da tonon sililice,yau ce ranar ƙindillanci ranar jin kunyar duniya,tace"kayi haƙuri Alhaji!'Ya gana ba haƙuri zaki bani ba so nake ki gayan yadda akayi kiji wannan sirrin da har kika jawo na kusa rasa ahlina!'cikin rawar murya da tsoron Alhaji Baba da ya kuma kamata saboda ɓacin ransa da yafito sosai,tace"kamar yadda Habibu yaji ina sambatu na Ni kaɗai to nima haka nazo naji kuna maganar kaida Hajiya Babba.
Kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciyar wanda bai san abinda ta shuka ba,tana cewa dan Allah kugafarceni Alhaji kayi haƙuri nayi maka gagarumar laifin da banajin zaka iya yafe min amma dan Allah kayi haƙuri!'na kasance mayaudariyar mata a gareka mai fuska biyu,ban taɓa zama da matan ka da zuciya ɗaya ba,da da farko hankalina a kwance yake ganin inata haihuwa Ni kaɗai Safiya bata haihuba,amma daga baya da ta fara haihuwa kuma ta fara da namiji sai hankalina ya fara tashi,daga nan nasha alwashin Safiya bazata rayu da ɗan ta ba,dan tun yana ciki naso ɓarar da cikin Abubakar amma hakan bata samu ba,to kuma ashe nima ina da cikin Mansur alokacin ban sani ba sai daga baya na fahimta,hakan ne yasa na dakatar da kokarin zubar da cikin Safiya, na riga Safiya haihuwa dan ita sai da cikin ta ya haura wata goma, namijin da na haifane ya ɗan sanyayar min da zuciya har na ɗan fara haƙura da abuwan da nakeyiwa safiya ta bayan fage,sai dai kuma wata sabuwa,rana tsaka na kuma ganin Safiya da ciki wanda hakan ya matuƙar tada min da hankali,gashi Ni kuma bani da wani cikin kai ƙarshe ma tun a haihuwar Mansur likita ya tabbatar min da cewa mahaifata bazata ƙara iya ɗaukar ciki ba,saboda lokacin da na haihu ALHAJI ba ya nan,dan haka na ce da likita yayi shuru kar ya sake ya faɗa maka saboda hankalinka zai tashi,ya ɗauka da gaske nake hakan yasa shi yimin alkawarin ba zai taɓa sanar da kaiba,to shi yasa da safiya ta kuma samun cikin shima na shiga damuwa me tarin yawa wanda daga nan na fara saƙa mugun nufi akanta da yadda zanyi nima na samu ƴaƴa maza dan aganina soyayyar da kakewa Safiya har da dalilin yaran da ta fara haifa maka Abubakar ne,ban damu da zainab ba saboda itama kamar nice ƴaƴa mata take haihuwa naso mu haɗa kai da ita sai kuma naga kamar tafiyar ba zatayi daidai ba dan naga yadda takewa safiya biyayya abun har mamaki yake ban, duk yunƙurin da nake yi akanta da cikinta ban samu nasara ba,dan shima wannan cikin na Aliyu yaƙi barewa.
Wata rana ne na tashi da tsananin farin ciki saboda tunanin da nayi na samowa kaina mafita ta hanyar tara ƴaƴa maza ba tare da wata matsalaba a tunanina ke nan,shawarar da na bawa kaina tayi min ɗari bisa ɗari,tun daga lokacin sai nima na tsiri laulayin ciki,na fara amaye amaye da ɗan kwaɗayi irin na masu ciki,har dai Zainab ta fahimta take cemin Hajjan yara ko dai ankuma kamuwa ne na ga yanzu tsere kuke keda Hajiya Babba!'daga nan sai na samu hanya, kafin kice meye gida ya ɗauka nima ina da ciki,ban fara laulayi ba sai da na tabbatar na gama shirina kuma ya tafi yadda nake so,sai da muka zo daf da haihuwa nida Safiya ita cikin gaske Ni kuma na ƙarya,sai na ce da Alhaji dan Allah ya barni na tafi garin mu can maiduri na haihu saboda matsalar da na gaya masa na samu a mahaifa kuma a kwai buƙatar zuwa gidan a wannan lokacin,duk da Alhaji ba mai san irin wannan al ada bane,amma sai na samu nasara a wannan lokacin ya barni na hada kayana na tafi maiduguri,wanda dama duk acan na riga na kammala shirina,salamatu reza karuwar gida wadda take cin karenta a lokacin,ita najewa da buƙatata amatsayin ta na karuwa,ai kuwa tun alakocin ta sanar dani ai faduwa tazo dai dai da zama dan kuwa tayi sake a wannan karon ta ɗauki ciki,dan alokacin zubar dashi take ta faman yi yaƙi zubuwa,daga nan dai muka shirya me yuwuwa,muka tsara komai cikin dabara,dan haka lokacin da naje Maiduguri dan aihuwa,sai na sharawa mamana ƙaryar cewa a gidan mai magani zan haihu,na nuna mata ina da matsala kuma nice na samo mai maganin likitace ƙwararriya,ita zata karɓi haihuwa ta kuma ba aso haihuwar tazo babu ita akusa saboda matsalar da ka iya faruwa,ras ƙaryata ta yi tasiri azuciyar ka da na mamana,daga nan na shirya muka koma gidan da na karɓi hayar kwanaki, cikin ikon Allah kuwa sai salamatu reza ta haihu a cikin satin sai dai kuma tana haihuwa tace ga garin ku nan,duk da cewa naji mutuwar ta amma hakan bai hana Ni farin cikin cewa bani da wata sauran barazana arayuwata ba,babu wanda yasan me na shirya daga Ni sai ita sai Allah da yafimu sani,na dawo gida da yarona,daga nan kazo kayi masa huɗuba kace kuma mu zauna muyi arba'in saboda bai kamata nayi tafiya mai nisa ba,ka sakawa yaron suna Habibu!'
Innalillahi'wa'inna ialaihi raji un abinda yake fitowa daga bakuna mafi hankali kenan, daga ciki harda uban gayyar Alhaji Baba,wata irin zabura Dady Habib yayi kamar mahaukaci ya nufo Hajjah yana cewa ke muguwace Hajjah yanzu kina so kice Ni ba ɗan Alhaji Baba bane?Ni dan ban zamo ɗan ki ba ba abin damuwata bane,amma dan Allah kar kice Alhaji Baba ba mahaifina bane,duk irin mugun halina Ina fatan zama ɗan mutum na gari kamar Alhaji Baba!'sai ga Dady Habib yana zubda waye kamar ƙaramin yaro, Hajjah tace"Habibu sai dai kar a kuma domin kuwa ba kazamo ɗan Alhaji ba san nan kuma baka zamo ɗana ba,domin Allah bai bawa Alhaji gurɓataccen ɗa ba,kasancewar sa mutumin da yatsaya ga Allah,kuma ko ban fada ba dole anzo gaɓar da zaka sakawa mutane kokwanto azuciyar su,domin abinda kayi ya wuce hankali ya ɗauka cewa ɗan uwa zai iya yiwa ɗan uwan sa irin abin da kai kayi,Ni kaina habibu na ji daɗi da yakanance bani ce na haifeka ba domin mugun halinka ya zarta nawa nesa ba kusa ba!'wani irin kuka ne ya kufce mata tana mai cigaba da basu labarin abinda ta aikata ba ta ɓoye komai ba, ta ƙare da ɗurƙushewa gaban Hajiya Babba tana kukan neman gafarar ta, Alhaji Baba kuwa ya kasa cewa komai,sai kansa da yayi ƙasa dashi Allah kaɗai yasan halin da zuciyar sa take ciki,a hankali ya miƙe ya fara ratsa taron ƴaƴan sa da jikokin sa ya wuce can cikin ɗakinsa ya kulle,babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar dashi saboda sun san a wannan lokaci dole ayi masa uzuri dan ma ya kasance mutum mai tsananin tawakkali,da juriya akan ƙaddarar da tasameshi.